Showing 111001 words to 114000 words out of 185083 words

Chapter 38 - Kalbim Book 1 Complete Hausa Novel

Mamuhgee   

23 Sep 2025

5487

auren kaman yanda aka tsara ba dagawa,
Ayau yakeson mallakarta,.ayau yakeson maidata cikakkiyar macensa ta yanda babu iya rasashi da ita ko a magana bare a wani aikin.


Yanda ya tinkarota kai tsayen zai kamota Sayd yasha gabansa ahankali cikin nutsuwa tareda kallansa da idanuwansa da suke nuna zai iya rabasa da hannuwansa har lahira idan suka sauka akan jannah din.

Su baba Alhassan kallan kofar da Ammar din ya shigo sukai cikin mamaki

Dad Maheer ya kalla cikin mamaki da tashin hankali alamar yayi handling din Ammar din yayi masa batareda baqin sun gane ba.

Ammar cikin tsananin zafin gaske da yawon dayaji kaman tsintsaye nai masa cikin kai ya kalli Sayd zai ciresa daga gabansa ya wuce yace

"Kasan me kakeyi?

A lokacin Jannah ta juyo da sauri jin Ammar tana ganinsa cikeda mamaki take kallan yanayinsa ta daga kafa zata nufess Sayd ya juyo ya kalleta cikin nutsuwa da bata girmamawa da hannu ya nuna mata hanya yana matsawa gefe da nutsatsiyar sauti yace

"Pls Mrs LIMBA"

Hanya da inda yake nunawan cikeda girmamawa ta kalla da sauri hannuwanta na dan rawa cikeda mamaki da tsoro sai alokacin ta iya daga ido ta kallesa yana zaune dukansu basu ishesa kallo ba wayarsa ya dauka wadda Falaq ta kirasa cikeda kwanciyar hankali da nutsuwa ya dauka ya dora a kunnesa yana bude bakinsa yace

"Yes Falaq Aziz"

Abinda Falaq din ta fada kai tsaye a cikin wayar da wani irin farin ciki ya saka sai alokacin ya saukar da fararen idanuwansa akanta itama shi din take kalla tana neman zarewa ga Sayd bakin rai ya hanata wucewa zuwa ga Ammar wanda ya fara wani vibration yana.

Maheer ne yayi saurin isa ga Ammar din ya jasa da karfi cikin kyaftawar ido suka fice Ammar din na kwacewa yana son magana Ammar harshensa jin yake kaman ya karye sbd Bugawan da zuciyarsa ke kokarin yi.

Sayd cikin fuskewa ya rufe kofan palon yaja ya tsaya koda Ammar din zai dawo dan da alama yana kokarin zarewa ne dan haka yana taba abinda ba nasa ba zarar dashi zaiyi a cikin gidansu ya tafi yabar musu sabon nakasashen Ammar.

Tsit palon yayi kowa ya kasa cewa komai sbd yanayin da aka samu din saida Daddy Mahmoud ya fuske ya kalli jannah cikeda kulawa yace

"Jannah ki gaida iyayen LIMBA gasunan"

Bakinta rawa yakeyi sosai ta budesa batareda ta iya kallansu ta gaidasu tinaninta duk a rikice ta dena gane komai so kawai take ta fita taje gurin Ammar.

Amsawa su Baba Alhassan sukai cikeda kulawa suna mata Addua da saka albarka.

AZIZ takeson gaidawa shima amma ta kasa sake kallansa dan haka jiki a sanyaye ta juya tabar palon Dad dinta yabita da kallo cikeda tsananin kauna da kulawa.


Maheer kuwa koda ya fita da Ammar din daman Anny taga wucewansa da sauri tayo palon saiga Maheer ya taho dashi dan haka batai wata wata ba ta sake sakasa baccin da zai iya masa illa amma bata damuba.

Kallanta Maheer yayi zaiyi magana sbd bayason wani abin ya samu Ammar ta dakatar dashi da cewa

"Babu abinda zai samesa for his own good nake masa komai sbd kansa bazai iya daukan wannan tashin hankalin dayake saka kansa a ciki ba so yana buqatan hakan dan ya karba lamarin a hankali"

Ajiyan zuciya ya sake yana mata kallan kin tabbata
Gyada kai tayi tana kama hannunsa suka fice bayan ya gyarawa Ammar din kwanciya da rufa.

Suna fitowa dakin Jannah na isowa da sauri tana cewa

"Ina Ammar din,
Meya samesa?
Yaya na gansa haka?
Meyake faruwa ne??

Kokarin fadawa dakin take Anny ta riqota tana cewa

"Auren AZIZ LIMBA dayake kanki ne yake faruwa,
Ki kula sbd yanzu ke din matan wani ce wanin ma AZIZ LIMBA ake magana"

Dakatawa jannah tayi tareda juyowa gaba daya tana kallan bakin Anny kafin ta dawo da kallanta kan Maheer tace

"Meyake faruwa?
Ance an daura auren to waye aka daura dashi ni banganeba,
My Ammar kokuwa wani daban??

Riqota Maheer yayi tareda kokarin kwantar mata hankalin dayaga yana neman tashi sbd tsoro da firgici yace

"Kwantar da hankalinki my love kinji,
Da AZIZ LIMBA aka daura miki aure sbd samarwa da zuciyanki abinda takeso,
Bazamu taba iya hanaki abinda zuciyarki takeso ba koma meye"


Rawa hannuwanta suka fara a rikice tace

"No,no no
Ammar nakeson aura,
Ammar nakeson aura basai abinda zuciyana ke so ba,
LIMBA bai taba sona ba Ammar ne yake sona,
Meyasa zaku rabani da Ammar?
Ammar can't take ita zai zare,zai haukace zai iya zama komai akan hakan zai iya komai akan hakan..........

Anny ce ta katseta cikesa takaicin zantukan tace

"Kinsan shi LIMBAn waye akan haukar da zarewan?
Idan hauka Ammar zaiyi to ni banga alamar akwai rashin haukan a tattare da LIMBA dinnanba ki dena ganinsa kaman baya ji ko gani,
Kima aje LIMBAn kinga Sayd?
Kinsan komai zai iya akan LIMBA?
Kina ga bazai iya daukan ran Ammar dinba akan LIMBA"

Wani kallo Maheer yayiwa Anny din yana cewa

"Ke me kike fada?
Stop scaring her,
Kina daga mata hankali cant you see tana cikin damuwa da firgici"

Janyo jannah din yake kokarin yi tan kwacewa tana son shiga dakin Ammar wanda a daidai lokacin Mimi data taso ta iso gurin jikinta va wani karfi.

Da gudu Jannah tayi gurin Mimin ta rungumeta tana fasa wani kuka me sanyi tana cewa

"Mimi Ammar bazai iya daukan wannan hukuncin ba,
Inason a warware auren dan Allah a dauramun da Ammar"

Mimi wasu hawaye ne masu radadi suka gangaro mata dan daman koda ta fito ta fahimci tabbas andaura auren yau Amma bata dauka zasu iya daurawa wani auren jannah ba Ammar ba.


Rungume jannah din tayi batareda ta iya cewa komaiba sbd ciwon datake ji yana cike zuciyarta da bacin rai me tsananin gaske.

Dakin Ammar Mimin ta ja jannah zuka shige batareda tacewa Anny da maheer komaiba suka rufo kofa.

Kallo daya Mimi taiwa Ammar zuciyarta ta karye ta share hawayenta tana zaunawa gefensa.

Jannah ma gefensa ta zauna tana ambatar sunansa Mimi ta hanata tabasa da hannuwanta.

Kuka jannah din ta fasa wanda ta rasa na menene amma dai tasan tsananin tausayin Ammar bazai taba barintaba har abada da kuma kaunar da suka taso a cikinta ta kusanci da shaquwa.

Anny da maheer ma basu samu cewa komaiba sbd ganin Mimi ta daure fuska sosai suka juya suka bar gurin zuciyar Anny fes.

Acan palo kuwa Sun fito sun fice sunbar zaadens din zuwa gida wanda Falaq ta matsu daddynta ya dawo sbd yau itace ta tayasa shirin daurin aurensa ta rakasa har mota tana jin kaman ta hanasa zuwa gurin daurin auren ya wuce ya dauko mata Jannah din kawai ya fara kawowa nan.

Suna isowa Falaq ta fito da gudu Fiddausi tayi saurin riqeta tana hanata gudun sbd kada matsala ta biyo bayan gudun.

Yana fitowa motan da sauri ta qarasa gurinsa ta fada jikinsa tana cewa

"BestDaddy ya zama nawa nida Jan"

Dariyar zancenta Baba alhassan yayi yana cewa

"Wannan baturiya bata da hausa ko kadan sai iyayi da surutu"

Sayd ma dariyar zancen nata yake yana cewa

"Aa daya a cikinku dai zai daukesa"

Sake qanwamesa tayi tana cewa

"No,Tin farko har karshe nawa ne ni kadai yanzu ne dai na yadda ya zama namu mu biyu da My jan sai kuma babies biyu da kawai nakeso ta haifo mana sun isa banason na bawa Daddyna da yawa"

Kallanta AZIZ din yayi da idanuwansa yana mamakin yanda haryanzu ta kasa wayo duk da girmanta.

Sayd tsokanarta zai sake yi AZIZ ya kallesa saiya fasa fadan abinda zai fada yana dariya yace

"6 mukeso"

Da wani irin tsalle ta kallesa tana dawowa da kallanta kan Daddyn zatai magana ya girgiza mata kai ahankali alaman Ba haka bane kafin ya kalli Sayd din yana cewa

"Zaka rikitamun ita ko?"

Dariya sosai Sayd ya sake yana shigewa palo yana cewa

"Ba ruwana a bakin mama naji,
Kuma ashe da gaskiyan mama wata a gidan nan batada wayo sam"

Jin sunan Mama ce ta fada hakan kallansa tayi da sauri sbd tasan baya wuce umarnin mama daidai suna shiga palon tace

"Daddy d gaske kanne har 6 zaka mun??

Mama dake fitowa dakinta cikin mamaki tace

"Ke bakinki komai fada yake ko??
Uban naki kikewa wannan tambayar?

Tura baki tayi tana son amsarsa sbd jin tayi kaman ma batason ko guda daya zatai magana magana

Mama tayo kanta da gudu tayi bayansa tana cewa

"Ni banason ko daya ma na fasa abarni daga ni sai Jan mun isa"

Mama sake kallanta tayi zatai magana ya bude baki yana janyota gabansa yace

"Babu wanda zai zo ya dameki da daddynki,
Amma karki sake maganar nan kwata kwata ok??

Gyada masa kai tai tana dawowa mood dinta na baya tace

"Daddy yaushe Jan zata taho?
Yau?
Anjima?
Wat time?
#MAMUH

ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
60
*TALK WITH SIDDEEQAH*
Operation Ciniki Dole
08149588205
Ni Olayyah na shiga uku na kwashe kudi na saro kaya domin in fara kasuwanci online, na gaji da zaman sai Yallaɓai ya bani kudin kashewa, kullum ni ce koma baya cikin danginsu, dukda yana kokarin sa, amma dai gwara in nemi na kaina kodan yan uwa da iyaye.

Amma bari in kira Besty nah Huriyyah nasan zata samu maganin wannan damuwar tawa.
Tunda na kira Huriyya na faɗa mata abunda ke hanani Bacci ta faɗa mun wani sirri da ya girgizani.

Wato ashe itama da ta fara business online kuma bata ciniki amms tunda aka bata number din Coach Saddiqah komai ya fara tafiya daidai a kasuwancin ta ( Talk with Saddeeqah).

Tunda ta shiga OPERATION CINIKI DOLE ONLINE BOOTHCAMP komai ya warware mata ciniki babu kama hannun yaro. https://wa.link/8al2f0
Ai ba shiri na nemi Coach Saddiqatu nima domin in shiga tsarinta na Saddeeqah Biz Growth Academy.
Kuma Alhamdullilah ina shiga nafara ganin canji a business dina, har ma sabon online business na buɗe daga cikin abunda na koya a Operation Ciniki Dole Online Boothcamp.
https://wa.link/8al2f0
Gaskiya wanda ya koya a wurin ƙwararriya ya huta domin ko dubu 100,000 akace in biya in shiga OPERATION CINIKI DOLE ONLINE zan biya domin amfanin da na samu cikin Boothcamp bazan iya faɗaba, gashi yanzu na samu na sayi machine din delivery na maida daki guda shago cikin gida na.
Hurayyah ta taimaka da ta haɗa ni da Coach Saddiqah. OPERATION CINIKI DOLE ONLINE ya bani damar yin ciniki yadda ya kamata ba tare da wana damuwa ba.

Indai kina business ko kina son ki fara Operation Ciniki Dole Online Boothcamp shine ajin farko da Coach Saddiqah zata rike hannun ki ta nuna miki duk wani sirri da dabaru na kasuwancin online.

Daga rashin ciniki zaki koma sold out domin kuwa zaki dinga yin 6 figures monthly, in kin shiga OPERATION CINIKI DOLE ONLINE BOOTHCAMP baki ga sauyi mai kyau a business dinki ba za'a maida miki kudinki bayan 90days.
Da Naira Dubu Goma kacal Pre-lunching Price zaki samu damar shiga OCD.( Kina biya zaki fara kwasar ilimi)
Zakuma ki iya jira sai 20th January ki biya Naira Dubu Ashirin.


*************
Kallan fuskanta yayi yana sake ganin doki da murnan dabai saba ganinta dashi ba idan baa kansaba,

"Meyasa take tsananin kaunar wadda bai kamata ta kaunata din ba" shine tambayar da zuciyarsa take masa yana kallan Falaq din.

Sake riqe hannunsa tai tana cewa

"Daddy pls yaushe ne zata taho?"
Kaine zakaje ka daukota?
Ka aikani na dauko ta yanzu pls BestDaddy"

Numfashi ya sauke yana shafa fuskanta yanajin kaunarta na sake ratsasa,
Ayau zuciyarsa cikin tsananin qunci da daci take sbd kaddarar auren daya shiga tsakaninsa da familyn da bai hada tsanarsu da komaiba amma ganin farin cikin dayake fuskan Falaq wanda daga zuciyarta yake fitowa saiyaji ya dan samu sassaucin tsananin dacin dayake ransa.

Bude baki yayi cikin kulawa da nutsuwa yace

"Karkiyita murna da yawa tareda tsalle tsallen nan banason wasa da lafiyanki kin sani so ki kula sosai okay?

Gyada kai tayi tana cewa

"Zanyi amma daddy pls when zata taho?

Bai amsa tambayarba ya wuce palonsa yana jin mama na kiranta.

Yana shigewa cire babban rigan jikinsa yayi tareda zame kayan duka sbd ya samu sakewa.

Wani wankan ya sake yi ya sauya kaya zuwa qananun kayan D&G bai fitoba ya kashe wayoyinsa dan hutawa.

Su mama kuwa bikinsu sukeyi cikeda farin ciki da kwnaciyar hankali sbd su anty maryam duka da iyalan Alh Saad din dana Alh Ahmed duka suka gidan anata taya mama murna.

Sayd ma shigewa yayi dan hutawar sbd Uban gidansa na hutawa ba wani aiki.

Dayake Fahad ma a mansion din ya sauka shi kam yana cikinsu mama da mutuniyarsa falaq kafin daga baya ya fita zuwa wani guri.


***Karfe 4 da mintina Ammar ya farka yana fara motsawa Mimi da jannah dake dakin har lokacin sukai saurin yi kansa mama na ambatar sunansa tareda kamasa ya tashi zaune ta rungumesa da sauri hawaye na gangaro mata na tsananin kaunarsa me karfi da tausayinsa.

Jannah ma hawayen ne suke gangaro mata tana kasa dagowa ta kallesa tana jin tsananin tsanar zuciyarta data kasa riqe amanar shekara da shekaru,
Ammar bai cancanci hakan daga gareta ba,
Taci Amanarsa taci amanar kanta sbd ta sani har abada wanda aka aura mata din bazai taba sonta kamar Ammar ba wanda zai iya vada rayuwarsa akanta.

Kansa da yayi masa tsananin nauyi da zafi ya dan dafe kafin ahankali ya bude idanuwansa da sukai jajir alamar baccin dolen da aka sakasa zuciyarsa bata hutaba ko kadan.

Akan jannah ya saukar da idanuwansa ya kafesu akanta yana mata wani irin kallo zuciyarsa na karban wani azababben yanayi me tsananin ciwo da radadi,
Tinda Allah ya saka masa tsananin son jannah tin tana cikin mahaifiyarta har isowanta duniya da gwagwarmayar neman lafiyarta zuwa yanzu bai taba kawowa ko a mafarki ko tinanin Jannah zata iya zamowa matar wani ba duk duniya bayansa,

Da ransa da lafiyarsa da hankalinsa da tinaninsa aka daura auren jannah da wani yana kwance yana baccin Asara da baqin cikin da aka sakasa sbd cimma buri batareda an dubi nasa halinda zai shiga ba a rashinta....

Rintse idanuwansa yayi sbd wani irin radadin daya yanki zuciyarsa da kirjinsa yana kasa riqe radadin ya rintse idanuwan.

Mimi jin saukan hawayensa masu wani irin tsananin zafi taji a bayanta wanda tajisu tamkar sun sauka a zuciyarta ne dan haka bata san lokacinda ta fasa qaramin kuka me sautiba dan tasan babu a duniya abinda zaa fadawa Ammar din akan wannan lamarin ya sassauta radadinsa,

Anyi masa illar da har abada bazai warke ba sedai samun sasssauci,

Jannah ganin hawayensa zubewa tayi qasa tana fasa kuka itama tana son ambatar sunansa amma baqin cikin kanta datakeji ya hanata fada.

Gangarowa hawayensa keyi ahankali akan bayan Mimi datake rungume dashi kafin jikinsa ya fara rawa ahankali yana kakkarwa ta sake qanqamesa da karfi tana girgiza masa kai tana cewa

"Ammar no pls,
No pls, karka bari ka shiga wani hali zuciyana bazata iya daukaba"

Dad ne ya bude kofar dakin ya shigo Maheer na bayansa suna ganin ya farka suka qaraso kowannensu idanuwansu na kansa.

Yanayinsa ya saka Maheer saurin isa garesa ya janyosa jikinsa ya qanqame yana kokarin hana jikinsa jijjigan dayake yana jin zuciyarsa na karyewa.

Dad ma qarasowa yayi daidai lokacinda Ammar din ya rikice gabaki dayansa komai na jikinsa rawa yake idanuwansa a rintse yana sake qanqame Mimi maheer kuma na sake qanqamesa.

Cikin sauri Dad ya kalli saleem daya shigo dakin yace ya kira dr.

Da sauri saleem ya ciro wayarsa yana kokarin saka kiran.

Daddy mahmoud ma qarasowa yayi dakin cikin damuwa da kulawa yana kallan Ammar din yace Maheer ya cire masa Cardigan din dake jikinsa.

Mimi da maheer dinne suka cire masa a lokacinne jikinsa ya sake gaba daya.

Maheer cak ya daukesa tareda nufar toilet da sauri Dad ne ya kunna masa ruwan dumi aka zaunar da Ammar din har lokacin maheer na riqe dashi dan haka ruwan su biyu yake jiqawa shima dad din kusan ya jiqe amma dai basason Ammar yana passing out sbd likitarsa data bada umarnin hakan a dena barin yana suma.

Cikin ruwan Daddy mahmoud ne da jannah suka shiga ruwan lokaci daya suna girgizasa tareda kiran sunansa cikin tsananin kulawa da son ganin idanuwansa sun bude.

Qara gudun ruwan Dad yayi sosai Maheer na sake riqesa da kyau.

A cikin qanqanin lokaci gabaki dayansu suke neman zarewa da tashin hankali da firgici sbd Idan aka cire son ran da sukai masa wannan karan to kaf familyn bayan jannah babu wanda ake tsananin so irin Ammar din sbd jinin Zeynab ne da basu hadata a duniyarsu da komaiba,

Su kansu a yanzu sun rasa gane wace kaddarar ce takaisu ga wannan lamarin wanda basusan Abinda Allah ya boyeba a cikinsa sai kuma Allah ya kaddara jannah din saita fara auren wani wanda ba Ammar ba.

Koda Dr ya iso Ammar din bude idanuwansa daqyar jajir wainda bama ya ganin komai dishi dishi yake gani hakama sama sama kunnuwansa kejin sautin sunansa dasuke ta ihun kira.

Akan jannah ya tsayar idanuwansa baya ganinta sosai amma yanajin sautin kukanta da yanda take kiran sunansa.

Sake rufewa idanuwansa sukai aka cirosa Maheer ne ya sauya masa kaya bayan kowa ya fice ya kwantar dashi a gadonsa da Jannah ta gyara da sauri hannuwanta na rawa tukuna dr yafara dubasa.

Palonsa suka koma suna jiran fitowan likita da Maheer dayake ciki shika suna jin kaman su tattaro likitocin abujan kaf suzo su dubasa.

Dr ya dade sosai a ciki kafin komai ya daidaita ya fito yana musu bayanin yanda zaa kula da kiyaye Ammar din kafin ya wuce.

Dukkaninsu kaman masu zaman makoki haka suka koma tareda manta hidimar bikin da ake gashi dare ma yayi baqi duka sun watse batareda anma tina da maganar kai amarya ba hakama ta bangaren AZIZ din babu wanda yai maganar zuwa daukan Amaryan.

Sallan magrib suka fice yi aka bar Ammar din ya huta sbd yanzu baccin nutsuwa ya samu.

Mimi ma sai lokacin ta koma dakinta tayi wanka da ruwan zafi sosai jikinta ya sake tai sallah tukuna aka kawo mata abinci da tea me zafi wanda tea din kawai tasha.

Jannah ma bedroom dinta ta koma ta kwabe kayan jikinta tai wanka ta sauya kayan zuwa riga da wando masu fadi sosai da kauri tai sallah ta zauna tana adduar Allah ya kawo musu sassaucin wannan kadaddarorin dasuke afko musu daya bayan daya ya maidasu rayuwarsu ta baya.

Kowama bayan dawowa sallah wanka sukai suka sauya kaya zuwa na shan iska basu fitoba sai lokacin ishai suna dawowa sallan angyara dining amma basu wani ci abinci ba kowa yawanci tea da snacks yaci sai Saleem ne ma sai Anny sukaci abinci me nauyi.

A lokacin ne Ammar ya tashi
Mimi da jannah ne sukai feeding dinsa abincin da bai wani ciba amma dai yasha tea sosai shima.

Sallah Mimi ta taimaka masa yayi kafin ta basa magani yasha ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login