Showing 105001 words to 108000 words out of 185083 words

Chapter 36 - Kalbim Book 1 Complete Hausa Novel

Mamuhgee   

23 Sep 2025

5496

gidan AZIZ din da kansa yace mata ta shirya gobe zaa daura masa auren datake so.


A cikin palon Kuwa wani masifaffen tension ne me karfim gaske ya cike gurin sbd Ammar kasa motsawa yayi idanuwansa akan maheer dayake riqe da hannuwansa.

Mimi kuwa jin tayi numfashinta yana neman daukewa itama
Dad dinma jininsa sama ya ringa yi yana kasa kallan Ammar sbd bai san AZIZ zaiyi magana a gaban Ammar din ba.
#MAMUH*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
56
Falaq farin cikine ya ciketa gabaki daya na jin Daddynta zai aura Jannah dan haka a mota qanqame hannunsa tayi tana bayyanar da farin cikinta ta kalli fuskansa da babu alamar farin ciki ko kadan a kanta tace

"I love you Daddy"

Juyowa yayi a hankali cikin nutsuwa ya saukar da idanuwansa akanta yana karantar asalin farin cikin me tsanani dayake bayyane akan fuskanta tana murmushi tana jin kaman tin yau ta tafi da jannah din gidansu.

Sayd dayake gaba shiru yayi yana sauraransu ta wani bangaren kuma shima hakan shine abinda yake tsananin so wato rabo zuciyar Ummitah daga zaadens sbd kada ta gurbata kaman yanda duka zuciyar familyn take a gurbace,
Babban fatarsa kafin su illata familyn ya zama zuciyar Ummitah tana tareda su dan haka shi wannan hukuncin shine daidai garesa kuma abinda yake jira dan haka daga lokacinda akai auren ta gama shigowa hannunsu komai ya nutsu to lokacin tarwatsa familyn zai fara duk da suna nan suna tsananin neman Dr ken wanda shi sukeson ya shiga hannunsa kafin komai sbd shine ya basu Ummitah,
Sunason Farawa Dasu dr Abraham amma kuma dole saisun fara kama dr ken sbd shine komai ya fito ta hannunsa dan haka nemansa suke sosai saidashi komai zai tafi yanda akeso.

Mama kuwa jin tayi zuciyarta kaman ta zuba ruwa a qasa tasha dan haka koda suka isa gida kasa shirin bacci tayi ta zauna tahau wayoyi.

Anty maryam ta fara kira akan lefen datakeson a hada mata na gani na fada a qanqanin lokaci.

Anty maryam na jin maganar auren farin ciki me tsanani da mamaki me girma suka rufeta lokaci daya da kuma Acikin yayanta dataita kwadayin ya auri daya amma duk da hakan farin ciki sosai tayi ta matsu goben tayi su isa LIMBAs din.

Baba alhassan ma daman yana nan har lokacin dan hana mama na sanar masa Sayd ya kira yaji komai daga bakinsa sbd AZIZ din ya shige ya hana kowa sake ganinsa sbd tsananin zafin kansa dayakeji yana jin kaman hakan bai kamata ba ga UMMITANSA to amma yana tsananin buqatan zuciyar Ummitah a kusa dashi.

Ruwa ne ya sakarwa kansa batareda ya cire kayan jikinsa idanuwansa a rufe ya qanqame jikinsa yanajin kaman kansa zai juye sbd tsananin zafin dayake tashi a cikinsa,

Yana tsananin qin Zaadens da jannah din kanta tsana me tsananin gaske da zai iya komai dan faduwarsu koda hakan na nufin su fadi tare,
Ta bagare daya yana tsananin Kaunar duk abinda ya shafi Ummitah koda qazantace indai ta Ummitah ce sonta yake da gaske,
Baitaba qi ko gudun abinda ya shafi Ummitah ba,
Ta bar duniya bazata taba dawowa har abada amma zuciyarta na duniya taba bugawa tayaya zai tsani kirjin da zuciyar Ummitah take bugawa a cikinta????

Zuciyarsa ta kasa hakan,
Ya tsani jannah tsana mafi muni a lokaci day kuma yana tsananin kaunar zuciyar datake bugawa a kirjinta....

Rawa jikinsa yakeyi sosai yana wani irin jijjiga yana sake qanqame jikinsa da karfi sbd trauma dinsa da shima babu lokacinda bata tashi idan ya samu kansa a cikin wannan tsananin ciwo da radadin tinanin kauna da tsana dake cinsa lokaci daya wanda babu wanda ya taba sanin da hakan.

Ruwan sosai sike sauka jikinsa jikin nasa na sake daukan jijjiga idanuwansa sunyi wani irin jan da idan da wani zaigansa a lokacin tsoro zaiji.


Azaba ce sosai yake ji a cikin kansa yafara buga kan a jikin bango da karfi kafin qafafunsa suka kasa riqesa ya silale a gurin qasa yana qanqame jikinsa har lokacin ruwa na sauka akansa.

Tsawon lokaci yana matse da jikinsa qasa kwance jikinsa na rawa sosai ruwa na sauka akansa ahankali ahankali harya nutsu yayi shiru idanuwansa a rufe wasu hawaye masu tsananin zafi suna gangarowa daga idanuwansa ya budesu ahankali yana ganin kamar Ummitansa na gabansa ya qurawa gabansa ido kaman itada mahaifiyarsa suna tareda shi.

Ya jima a hakan zuciyarsa na karairayewa kafin ya lumshe idanuwansa yana fatan duk suna cikin rahamar ubangiji.

Daqyar ya iya kai hannunsa ya sauya zuwa ruwan zafi ya miqe ya zare kayansa yayi wanka da tsadaddun shower liquids dinsa kafin ya zari daya daga cikin towels din dasuke jere a toilet din masu yawa sa laushi ya daura a jikinsa ya fito fararen idanuwansa da suka sauya sunyi wani iri kaman sexy dan da akwai macen da zata gansa a lokacin tabbasa zata iya kasa riqe kanta dan kallo daya zai maka dasu ka nema zarewa da neman nutsuwarka ka rasa.


Tin daga lokacinda ya Ummitah tabar duniya tabarda da wannann trauma din babu daren da baya samun kansa a wannan yanayin batareda da kowa ya taba saniba,
Shi kadai yakeshan azabarsa ya gama ya fito batareda kowa y saniba sai dr Nico wanda shine likitansa,

Azaba sosai yakesha sbd zuciyarsa haryanzu ta kasa fita daga radadi da ciwon rashin yar Uwarsa wadda sai ranar daya bar Duniya zai huta daga wannan ciwon.

Ko Sayd baitaba saniba sai daga baya bayan shekaru ya sani a wani tafiya da sukai ya samesa dakinsa da daddare akan wani issue ya tararda yana bathroom wani irin kuka da nishin dayake jine ya sakasa nufar bathroom din wanda ya tarar dashi a wannan halin,

Tim daga wannan lokacin ya san ashe AZIZ din bai warke daga trauma dinsaba sai tsananin data qara amma tsawon shekaru basu taba saniba sbd ya zabi ya boye ya ringa jin radadinsa shi kadai.

Tin daga wannan lokacin Sayd ya tsananta kaunarsa da kulawansa akan AZIZ din,
A lokuta da dama shine yakan rungumesa idan yanayin yazo masa dan sassauta masa ciwon yana hawayen radadin ganinsa a cikin wannan yanayin.

Dr Nico na iya kokarinsa akan hakan sbd shine therapist dinsa dan haka sauki yake samu sosai ana samun cigaba sosai sai gashi kwatsam Maganar kashe Ummitan akai ta bayyana wanda ya dawo da komai baya dan kwata kwata yanzu ya dena karban kokarin da akeyi akan yanayin nasa.

Tsananta yanayinsa yayi sbd yanda aka kashe Ummitah shine kisa mafi tsananin ciwo da rashin tausayi,
Abinda yake Tsananta yanayinsa a koyaushe shine yasan Ummitah zataso inama ace Allah zai bata ikon ganinsa yazo gareta,
Inama zasu tausaya mata su barta ta koma ga dan uwanta da mijinta da abinda ta haifa da mamanta,
Ya sani a wannan lokacin da suke kokarin rabata da duniya tayi hawayen azaba,tayi na rashin sanin ayau zata bar duniya,tayi na tausayinsa sbd tasan zai shiga tashin hankalin da babu ranar fita...

Tina irin wannan ne yake sakasa hawayen tausayin kansa dana yar uwarsa a kowane lokacin da yanayinsa ya taso.

A yanzu dayakeson yi musu tsanar datafi komai karfi da muni a yanxu dinne kuma zuciyarsa ke jin tsananin kaunar Zuciyar tata datake bugawa da tsananin sonsa da kaunarsa amma a wani kirjin da bana Ummitanba,
Ta tafi tabar masa bugun zuciyarta dayake tsananin son jinsa a hannunsa,
Ya tsane Jannah amma yana kaunar bugun zuciyarta tayaya zai iya barin kansa ya hada wainnan feelings din guda biyu?
Tsananin tsana da kuma tsananin kauna...
Wannan tinanin ke sakasa tsanar kansa tsana me tsananin gaske,

Amma duk da hakan bazai taba samun nutsuwa ba saiya tabbatarda Jannah bata sake dandanar farin cikin duniya ba,

Zaadens suna kallo zai mayarda rayuwar da sukafi so fiyeda komai ba komaiba,
Suna kallo zai maidata abar tausayi da baqin cikin kallo bazasu iya komaiba sbd sun riga sun daura aurenda bazasu iya rabawaba sai lokacinda ya gama da ita zai jefa musu ita a lokacinda batada amfanin komai a duniyar dan haka Auren a goben ba fashi ya karba sadakarta hakama ya bawa falaq abinda takeso itama mama ya cika mata umarninta na son yayi auren.


Su Mama kuwa hankali kwance sukam sunga hidimar farin ciki gabansu,
Baba alhassan Alh saad ya kira ya sanar masa maganar auren da babu shiri dan haka ya sanar masa goben dai sune wakilan ango.

Bayan ya kira Alh saad Alh Ahmed ya kira abokin aikin Baban AZIZ din wanda shine ya kawosa gurin su Alh saad tin lokacinda mahaifinsu ya rasu.

Shima sosai yayi farin ciki dan haka da shirinsa ya kwana yace shine zai biya sadaki Baba alhassan yace aa shine zai biya,shima Alh saad cewa yayi shine zai biya baba alhassan yace sam shine zai biya sadakin.

Qin yadda sukai sukace aa yabari su biya,
Ganin kowannensu nason ya kasance shine ya biya sadakin auren wanda sukejinsa har cikin ransu tamkar sune suka haifesa dan haka suka yadda akan kowa ya bada 500k su biya sadakin 1.5.

Baba alhassan ne yace aa sbd albarkar aure baa son sadaki me yawaba 100k kowa zai bada ayi sadakin 300k ma ya isa.

Amincewa sukai sa hakan dan haka kowannensu a cikin daren yafara kokarin buga wayoyin gayyatar jamaarsa da manyan mutane.

A cikin daren Sayd yasa aka buga wata lafiyayyar invitation ta waya a cikin daren aka fara yadawa manyan mutanensa dake kusa harma da wanda basa kusa bazasu samu damar zuwaba sbd kurewan time amma a cikin daren kafin safe maganar Auren AZIZ AY LIMBA da JANNAH ZAD ta fita anata mamakin lamarin amma dayake already Zaadens sunyi gayyata tin kafin yanzu sai ya zama mutane da yawa da manyan kasashe da dama da zasu halarta already suna abuja sun iso a ranar sbd goben sai gashi a daren suke samun kuma AZIZ LIMBA ne wanda zaa daura dashi goben.



**********
A ZADEENs kuwa AZIZ da familynsa na barin mansion din shiru sukai kowa ya kasa motsi sbd ya bude aikin da basu shirya tarbansa yanxuba.

Ammar wani irin ja idanuwansa sukai yana jin kansa da tinaninsa na toshewa kasa cewa komai yayi bayani yake jira daga duk wanda Allah ya bawa ikon fara samun dawowa hayyacinsa a cikinsu sbd yasan suma shock din suke ciki na jin zancen haukan da LIMBA yayi.
#MAMUH

ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
57
Mimi ce ta iya bude baki dakyar zatai magana hannuwanta na rawa Anny tai saurin riqe hannuwanta da sauri cikin kulawa dan hanata maganar da zata fada tace

"Mimi karkice komai,ki kwantar da hankalinki Abinda kikaji ba hakan bane muje ki samu nutsuwa sai amiki bayanin komai daga baya.

Zare hannunta mimi tai daga na Anny tana kallan Maheer kafin ta maida kallanta kan Dad tace

"Auren Ammar da jannah buri na ne tin daga ranar dana haifeta ta diro duniya,
Bazan taba karban Kowane miji ga jannah ba bayan Ammar,
Idan akwai abinda yake faruwa ku sani ban yadda dashiba Koda wasa aka fasa auran Ammar da jannah kunci Amanata da Ammar harma da jannah din"

Maheer baice komaiba ya kalli Anny batareda yace komaiba ta fahimci abinda yake nufi na taja Mimin zuwa daki.

Sake kama hannun Mimin tayi tana cewa

"Mimi muje ki huta babu abinda zai faru insha Allah ki kwantar da hankalinki wlh bazaa aurawa jannah kowaba sai wanda takeso dan haka muje ki huta gobe ranar farin ciki ce"

Dad da baice komaiba kallan Anny yayi wanda itama shi ta kalla take ta fahimci nasa Kallan itama dan haka jan Mimi tayi cikin kulawa zuwa bedroom dinta sbd sosai ta shiga tashin hankali da shock dan haka jininta ya hau sosai.

Suna isa daki taimaka mata tai ta kwanta taje qaramin dakin maganin da ake dashi a mansion din sbd ciwon jannah kawai da duk sauran ciwon yan gidan duka tinda sunada nurse sunda likita shiyasa komai akwai gidan.

Magani ta dauko me karfin gaske tasa a juice ta bawa Mimin cikeda kulawa tana cewa Mimi sha zaki samu dan sauki saikiyi baccin ko minti 30 kanki ya sake.

Sha Mimin tayi sosai sbd maqoshinta daya bushe sbd tashin hankalin.

Tana miqawa Anny cup din taji idanuwanta na juyawa kanta ma na juyawa kafin tayi wani motsin ta zube a gadon.

Gyara mata kwanciya Anny tayi tana sauke ajiyar zuciya tareda rufeta tana cewa

"Sorry Mimi koda zaki tashi Jannah ta jima da zama JANNAH LIMBA,
Mrs AY LIMBA
Daga baya kinyi bayanin Alkawarin aurenta da Ammar saiki hada da hakuri"

Juyawa tayi ta fice dakin tana rufowa ta koma palon Dad dan tayasu handling Ammar sbd ba wata dubara ce dasu ba zasu iya lalata komai.

Tana shigowa palon Ammar na miqewa tsaye zaiyi magana jikinsa na wata irin jijjiga sosai da sauri ta isa gurinsa tana cewa

"Ba maganar komai zaayiba a fara neman lafiyan jan tukuna."

Kaman dukkaninsu jira suke suka sake yi kan Jan har Ammar din wanda yake ransa kansa akan duk abinda ya shafi jannah.

Jannah din ta dawo daidai numfashinta ya daidaita sedai idanuwanta a rufe suke bata iya komai.

Dad ne ya kalli Maheer yace ya dauketa yakaita dakinta.

Cak Maheer din ya dauketa ya fice da ita sai alokacin Ammar ya dago jajayen idanuwansa ya kalli dadi hannuwansa na tsananta rawa ya bude baki muryansa na hadewa da rawa yace

"Dad what's going on?
Is there something daya kamata na sani?
Abin nufi Dad akwai abinda yakamata na sani??
Dad bakaji me bastard dincan ya fada bane kafin ya fita?
Yana magana akan auren My jannah,
My jannah,my jannah fa dad.,

Anny ce tayi saurin cewa

"Ammar you have to calm down kafin ka fahimci abinda ake nufi,
AZIZ zai auri jannah ne sbd yana son bawa yarsa uwa,
Mu kuma muna tsananin buqatan dukiyarsa gabaki dayanta...


Wani mahaukacin kallo yayi mata da idanuwansa dake wani irin sauyawa kaman zasubkama da wuta yace

"Are kidding me?
Meya hada aurena dana jannah da duk abinda kike magana?
To hell with his daughter,
Idanma mutuwa zatai i dont care
I don't give a damn
Ta mutu kawai shima ya mutu amma bazan taba bari wani yama sake furta maganar auren Jan dita ba batateda na dauki matakin illatasaba"

Dad Zaunawa yayi Ahankali har lokacin baice komaiba sbd harga Allah baisan tayaya zai bullowa lamarinba sbd AZIZ ya janyo musu matsalarda bata hakan yaso bullowa Ammar dinba.

Anny ce ta sake bude baki ganin koina jikin Ammar din rawa yake yana neman loosing control ya fara musu fashe fashen kaya karshe ma zai iya raunana kansa ya raunana wani tace

"Ammar pls calm down"

Batada zabin daya wuce shirya masa karyan da zata fiddasu dan haka kallan dad tayi kafin ta kalli Maheer dayake nufar Ammar din da tausarsa tayi saurin tare Maheer din kada yaje Ammar ya rasa control nasa ya illatasa dan haka tace

"Ammar abinda yake faruwa shine
Falaq Aziz nada ciwon da mutuwa zatai she only hv 3 month to live,
Tana tsananin son Jan as her mum
Kuma ka sani akwai kauna tsakaninsu sosai,
Daddynta na son bata farin ciki a kwanakin da suka rage mata so ya roka abasa auren jannah for only 3 month shikuma zai bamu dukkanin abinda ya mallaka in return......

"What¿" Ammar ya fada cikin tsananin mamaki da sabon tashin hankali sbd zancen kadai neman sake juyar masa da kai yakeyi.


Dad kuwa da sauri ya kalli Anny kansa na sarawa da tsananin ciwo shima jin abinda take fada...

Magana zaiyi Maheer ya bude baki a hankali yace

"Dad a tafi a hakan atlast idan ya aminta zamu samu ayi auren daga baya asan yanda zaayi"

Maheer dinne ya karbi zancen d cewa

"Ka sani muna cikin financial crisis hakama shine biggest catch namu da muka sani zai iya tadomu,
And atlast tinda anzama kamar family bazamu iya taimaka masaba akan yarsa?
Auren wata 3 fa?
Idan harmu dukanmu zamu iya yadda da hakan meyasa kai bazaka iyaba,
Babu wani soyayyar dayake tsakaninsu,
Kana tinanin akwai abinda zai girgiza soyayyar da jannah take maka?
Ita kanta zatai ne sbd falaq,
Gabaki daya assets dinsa zai bayar a matsayin auren kankanin lokaci,
Bazaka iya sacrificing wata uku naka ga familynka ba?
Karka manta mun taso da taru a tinani daya da tabbatarda ci gabanmu,
Meya canza Ammar?
Kana tinanin har abada zamu taba son wani ya auri jannah akanka?
Wlh muna kaunarka fiyeda yanda kake tinani ta yanda ka dauka hakan da zamuyi babu zabi ne kuka bamu yadda da hakan bane saida muka tabbatarda lokaci muka bawa auren zamu dawo da ita gareka."

Ganin zancen yafara shigar Ammar ya saka Dad dago idanuwansa da suka sauya ya kalli Ammar yace

"Ammar indai nine na haifi Jannah insha Allah nai maka alkawarin aure maka ita indai har zaka iya hakura a yanzu dan samarwa kanmu mafitar abinda mukeso,
Ban basa aurenta dan ta zauna dashi har abada ba na basa ne sbd ita kanta Jannah din ta samu abinda takeso a can amma insha Allah zata dawo a lokacin ne zan daura muku aure da hannuna,
Ka sani Ammar ina sonka sbd kai jinin Zayneb ne da har abada jinin Zeynab yafi komai dana mallaka daraja amma ayau ina rokon ka bamu lokaci kankanin a cikin soyayyar da kakewa Jannah"

Wasu irin hawayen masu tsananin radadi da baisan suna fito masa bane suka fara gangarowa Ammar din kafafunsa na wata irin rawa zuciyarsa na neman bugawa ya zube gurin jikinsa na rawa ya fara girgiza kai yana cewa

"No,no i can't"
Har abada bazan iya kallan jannah a hannun wani ba koda na minti dayane bare wata uku,
Bazan iyaba dad
Mutuwa zanyi,
Zuciyata bugawa zatai,
Dad bazan iya ba,
Mutuwa zanyi"


Kirjinsa ya dafe yana masa wani irin tsananin radadi da azaba kansa na neman juye masa yana jijjiga yafara daga murya sosai yana cewa bazai iyaba mutuwa zaiyi,
Indai aka aurawa jannah wani zai iya kashesa ya rabasa da duniya koma waye.

Anny na ganin hakan ta kalli su Dad tace

"He's looking it,inaga ai masa Allura ya samu bacci idan ya tashi kansa ya sake zaifi fahimtar abinda ake nufi amma a yanzu yana rikicewa komai zai dagule"

Kallanta dad yayi yace tai masa alluran kawai sbd yana rikicewan nan raunana kansa zaiyi wanda ya tsani ganinsa a cikin yanayin da zai raunana kansa dan harga Allah tin daga zuciyarsa kaunar Ammar take amma kuka bazai iyawa jannah auren da bataso ba wanda hakan zai iya kawo matsala a cikinsu dan daman tin farko sbd basason matsala ta shigo tsakaninsu sbd tsananin kaunar da sukewa juna basa wani son auren zumucin amma kuma sbd dagewan Mimi da ganin yanda Jannah din take tsananin son Ammar da yanda yake mutuwar sonta suka kaunace auren harya sabu da jin bazai iya kaita aure wani gurin ba bayan na nan cikin gida.

Kafin suyi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login