Showing 117001 words to 120000 words out of 185083 words

Chapter 40 - Kalbim Book 1 Complete Hausa Novel

Mamuhgee   

23 Sep 2025

5486

yarinyana dana gidanku ba daya bane,
Tana tashi sallah in time bata taba tsallakewa ba sai ayau karan farko data kwana a inda bai kamataba,
Ke baa koya miki sallah kan lokaci bane?
This is unbelievable" ya fada yana kashe wayarsa cikeda damuwan abinda yasaka Falaq zuwa zaadens da bai yadda da komai nasuba.

Shiru jannah tai da wayar a hannunta tana kalla idanuwanta suka ciko da hawaye masu dumi amma bata bari suka saukoba ta sunkuyar da kanta zuciyarta na daci sbd tinda take a duniya bata san komaiba bayan gata sai ciwon da Allah ya jarabceta dashi,

Bata taba sanin ya daci da ciwon fada,zagi ko baqar magana yakeba a rayuwanta,
Ta samu tarbiya duk gatanta iyayenta sun tsaya sun bata tarbiya daidai gwargwado hakama itama ta taso da sallah din akan lokaci bisa koyarwan iyayenta da yan uwanta musamman Ammar bai taba tashi sallah da asuba bai kirata ba ta tashi sunyi kusan lokaci daya.

Kalamansa ne suke mata radadi amma batasan ma metake ji ba akansu,
Ya kirata mara tarbiya ne ita kadai kokuwa harda Familynta??

Falaq ce ta fara motsawa alaman zata farka sbd indai lokacin sallan yayi sbd sabo to sai Allah ya bata ikon tashi.

Kallan falaq din tai kafin ta ajiye wayar hannunta ahankali jikinta a sanyaye hawayen idanuwanta n gangarowa ahankali ta zira kafafunta qasa ta sauko tana miqewa ta nufi toiletta shige.

Tana fitowa wayart na nuna haske alaman shigowan kira.

Falaq ce data tashi zaune idanuwanta suka fara sauka akan wayar taga qatuwar heart ce kawai da kiss take tasan Ammar ne ta sauko gadon tana tura baki tana magana qasa qasa harda buga qafa ta fada toilet.

Jannah kuwa mamaki ne ya kamata sosai na ganin kiran sbd ta dauka bazai dake kirantaba tadata sallah.

Jikinta dayake mace ta zaunar bakin gado tana daukar wayar ta dora a kunnenta cikin sanyi ta furta sunansa.

Ajiyan zuciya ya sauke da numfashin daya kusa barin kirjinsa sbd harga Allah bazai iya rayuwa babu jannah ba,
Bazai taba iya moruwa ba idan babu jannah a rayuwarsa,
Bazai iya barwa kowa jannah ba,
Yana mata wani irin mayen so da bazai taba jin zafi ko ganin laifintaba dan hakanne ma zuciyarsa ta kasa hanasa cigaba da sonta da nemanta tinda auren ance na wata uku ne ya yadda zai jira indai zata dawo garesa ya yadda ya zama wawa mahaukaci mara zuciya ya jirata.

Sake ambatar sunansa tai a natse tana danne damuwar datake ranta.

Cikin nutsuwa shima ya bude baki yace

"Time na sallah yayi"

"Na tashi already"

Shiru sukai kafin tace

"Thank you"

Kashe wayar tayi bayan ta fada hakan ta ajiye tana miqewa ta saka kayan sallah sukai sallan tareda Falaq daketa jin haushin kiran Ammar din.

Suna gamawa sun dan jima suna Adhzkhar kafin suka koma suka kwanta sbd dukkaninsu yayan hutu ne da basusan wahalarda kai da tashi da wuri ba.


Fiddausi kuwa a dakin data kwana gari na wayewa ta fito ta nufi kitchen ta gaisa da masu aikin gidan da chiefs dinsu suna yar fira tana aikin breakfast din falaq dana zuwa school dinta duk da tana SS1 sbd yanayin karatun can dana nan daba irin tsarin wanda tayoba bane sai aka sakata a ss1 sbd tagane na nan din yanda ya kamata amma tana zuwa da abinci sbd yanayin hygiene na abincin school da hankalinsa bai kwanta duka dashiba duk da tsadar school din da abincinsu da kamanma a makarantar qasashen wajen duk da haka na nata take zuwa.

Fiddausi na gama hada komai ta jera a tray ta nufi dakin Jannah.

Tana isowa knocking tai so daya kafin ta bude dakin ta shiga ta maida ta rufe ta nufi table ta ajiye kayan hannunta tukunta ta zagaya bangaren Falaq ta durqusa bakin gadon tana kama hannun falaq din tareda ambatar sunanta a natse sbd baa tadata bacci cikin tashin hankali koyaushe kaman zaa sakata wani baccin ake tadata.

Sake ambatar sunanta Fiddausi tai tana gyara mata rufa.

Motsin gyaran rufar ya sakata motsawa Fiddausi ta sake kiran sunanta.

Bude idanuwanta tai ahankali tana kallan Fiddausi tace

"Banson school bazaki bari na hutaba kafin Mama da Daddy su dawo"

Murmushi Fiddausi tayi tana yaye mata abin rufa tana cewa

"Ki bari kije yau tukuna sai muyi wannan shawaran daga baya"

Bata fuska tai tana miqewa zaune tareda saukowa gadon tana cewa

"Fada kawai kikai bazaki yaddaba na sani"

Toilet ta nufa Fiddausi tabi bayanta da towel ta kai mata daman already tin jiya aka jere mata kayan wankanta da dauran amfaninta a cikin toilet din duk da koina tsadaddun kayan amfanin jannah dinne masu kyau da tsada amma dai haka itama aka jera nata.

Brush da wanka tai ta fito daure da towel lokacin jannah ta farka ta sallami Fiddausi dan haka itace ta tayata shiryawa tai breakfast suka fito.


Itace takaita school tareda Fiddausi da baa barin falaq zuwa ko gate ba tareda itaba.

Suna zuwa kafin ta shige saida tai waya da Daddynta kafin ta bawa Fiddausi wayanta ta shige suka juya.

Suna dawowa gida jannah bacci ta koma sbd duka mutan gidan babu wanda ya tashi.

Fiddausi ma komawa masaukinta tai sbd ta gama aikinta na dole waton kulawa da Falaq.


Sai guraren 10 suka fito daya bayan daya suna haduwa a dining.

Cikeda kulawa da kauna dad ya kalli jannah data zauna kusa dashi tana kama hannunsa tai masa ina kwana yace

"Ina Falaq Aziz?

"Tana school"

Maheer ne ya kalleta yace

"Waye yakaita?

"Nice na kaita"

Shiru sukai dukkaninsu cikeda tausayinta da kaunarta.

Breakfast suka fara ci Maheer na cewa

"Gobe xan sanar da driver na yaxo tinda safe ya kaita sbd sanyi zai shigeki idan kina wannan fitan na tinda safe"

Dagowa tai ta kallesa zatai magana sai kuma ta fasa.

Suna gamawa ta koma dakinta tana wayoyinta da chats har kusan 1 da wasu mintina ta tashi tai sallah.

Fiddausi dataga lokacin dauko Falaq din yayi ta samu jannah din ta sanar mata.

Fitowa tai zuwa daukota Maheer yace ta koma ya aika driver yaje daukota batareda anje da Fiddausi ba.

Ko kafin driver yaje school din saida Maheer ya aikesa office ya karbo masa wasu takardun ya dawo gida ya basa tukuna ya koma daukota.


Zuwa lokacinda ya isa an dade da tashi daga school din falaq da tinda take a rayuwarta bata taba fitowa daga class ba tareda driver da Fiddausi na gate suka jirantaba sai ayau kuwa,

Galabaita da tsoro ne sosai suka shigeta wanda ya saka idanuwanta fadawa sosai sbd sai 3 zuwa 4 aka daukota.

Koda aka iso gida da ita duk ta fita hayyacinta daman Fiddausi tinda lokacin daukota yayi taga baa kawotaba bata dake zamaba taketa yawon xuwa gate hankalinta a tashe zuciyarta na tsinkewa gashi tana tsoron kiran sayd ta fada batasan hukuncin da mai gidan zai dauka ba akan hakan.
#MAMUH


ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
63
*UMMU_MAHNOOR LUXURIES*
(Best luxuries shop)
08034469681
08135142610
Aslm Alaikm ina kuke masu neman luxuries na kayan alfarmar kece raini?
Ina masu son su saka sitirar alfarma ta zamani ta manyan mata masu aji da zaa kalleki kallo daya asan sitirar alfarma e kika saka?

Shin kunsan me ake nufi sa kayan asalin yan gayu da nuna gayu?
Sitirar Alfarma kikeson sakawa?
Sitirar da kike ganin manyan mata da ita?
Sitirarda zakiyi gayun sallah dake da yaranki a dauka waje kikaje da kanki kika siyota?
To kizo ga damarki ta sameki sbd UMMU_MAHNOOR LUXURIES ta kawo miki sauki har gida,
Karkice se masu kudi ke iya siya har kema me yar dama zaki samu naki da saukin kudi kuma best quality da kalar zamani data yan gayu,

Nidai Mamuh nace duk wadda ke son a buga gayun sallan bana da ita da 'yayanta to tazo gurin UMMU_MAHNOOR LUXURIES tai siyayyar sallanta harma zuwa gaba dan nasan zakuji dadi da fahimtar abinda nake fada akan kayanta💯💯
Abubuwan da zaki samu a gurinta with the best quality na wayayyun mata masu aji yan gayu sune;

Atampopi
Laces
Shadda
Materials
Shoes
Bags
Veils
Trolleys
Jewellerys
Oil perfumes

Numbers
08034469681
08135142610

Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries



*****************
Fiddausi na ganin shigowar motar harabar gidan ta fito da sauri tana nufar motar hannuwanta har rawa sukeyi ta bude motar.

Ko tsayuwa falaq din bata iya yi sosai sbd gabalaita ga ruwa tanason tasha dan haka da sauri Fiddausi hankali tashe tai ciki da ita a lokacin jannah itama ta fito cikin damuwa da key dinta a hannu zataje da kanta ta dubo sbd tin dazun takeson zuwa ana hanata.

Ganin Fiddausi da falaq din wadda idanuwanta sukai ciki sosai ya sakata qarasowa gurinsu da sauri tana kamo falaq din jikinta zatai magana falaq ta fasa kuka mara sauti tana cewa

"A kira mata daddynta"

Fiddausi na jin hakan ta sake shiga tashin hankali tanajin itama gidan takeson bari su koma gida.

Jannah da Anny kuwa cikin tsananin kulawa suka nufi dining da ita suka zaunar Fiddausi na zuba mata brown spaghetti da aka dafa dasu carrots da Naman kaza ba tareda qashi ba taje ta kawo mata ruwa masu dumi jannah ta karba tana bata da kanta tana shafa bayanta tana cewa

"Am so sorry Falaq ban dauka zaa kai wannan time din baa daukoki ba"

Ruwan falaq tasha kafin ta fara cin abincin da Fiddausi ke tsananin son ganin tashi.

Taci abincin sosai kafin ta miqe suka nufi daki ta cire uniform tai wanka tai sallolin dake kanta wanda koda ta gamasu sosai zazzabi ya rufeta.

Cikin tsananin damuwa jannah ta kira Anny ta dubata ta bata magani baccin wahala ya dauketa.

Fiddausi gaba daya jikinta sanyi yayi gashi mama tanata kira tanason magana da Falaq din amma sai karya take mata akan sun fita da Jannah.

Daddynta ma so uku yana kira Jannah bata iya daukaba sedai Fiddausi ce take dauka ta sanar dashi bacci takeyi.

Na biyu daya sake kira cewa tai tana toilet
Na ukun tana ganin kiran zuciyarta ta ringa tsalle da fargaba.

Har dare suna jinyarta da tarairayanta tayi sallah ta sake cin abinci a lokacin ta dauki wayarta ta kira Daddynta da kanta
Yana dauka hawaye ne na tsananin kewansa da mama suka gangaro mata da muryan da karamin kuka ke zuwar mata tace

"I am missing you Daddy pls ka dawo"

Shiru yayi yana karantar yanayin muryanta tsawon seconds kafin ya bude baki a natse yace

"Meya sameki?

Shiru tai tana share hawayenta kafin tace

"Ba komai i just miss you Besty"

Sayd dayake gabansa ya kalla take sayd ya fidda wayarsa ya saka kiran Fiddausi.

Fiddausi na dakinta kiran Sayd y shigo wayar.

Numfashi ta sauke ahankali tareda daukan wayar tana fara gaidasa cikeda girmamawa.

Amsawa yayi yana cewa

"Me yake damun Falaq Aziz?
Akwai abinda yake faruwa ne?

Sun mata riqon da baya iya musu karya hardai akan Falaq dan haka a natse ta sanar dashi abinda ya faru.

Dayake handsfree take komai akan kunnen AZIZ ya sauka kuma har lokacin bai aje wayan dayake da Falaq dinba dan haka numfashi ya sauke batareda yace komaiba.

Rarrashin falaq din yayi ya nuna mata zai dawo ta samu tai bacci ya wayar na aiki.

Wayar ya kashe Sayd na kallansa yai tinanin zaadens din zai kira sai yaga bai kirasu ba.

A zuciyarsa yaso kiran Dzad ya sanar dashi kaf zadeens babu me amfani amma kuma saiya fasa sbd 'yarsa suka taba,sanyin idaniyarsa da zuciyarsa dan haka zasuji yanda yaji.

Karfe 4 da mintina kiransa ya shigo wayar Falaq wadda take bacci sosai sbd rashin karfin jikin data kwana dashi.

Jannah ce kiran ya tada wadda ta dade batai bacci ba tana kulawa da falaq din.

Kaman bazata dauka ba saita tina maganar daya caba mata jiyan akan rejecting kiran dan haka ta tashi zaune ahankali ta miqa hannu ta dauki kiran tareda dora akan kunnenta da sanyin murya tace

"Asslm Alaikm"

A zuciyarsa ya karba sallaman yana bude nasa bakin yana hadiyewa bacin ran daya kwana a cikinsa yace

"Akwai mutum daya a Zadeens dayakeda tinanin daya kamata?
Wane irin tinani ne kuke dashi daya banbanta dana sauran mutane?
Kunsan bazaku iya kulawa da falaq ba kika saka mama ta bar miki ita?
Are you guys for real?
Kunsan waye falaq Aziz kuwa?
Tafi duka Zaadens da abinda suka mallaka idan kanku bai baku ku kula da ita sbd mahaifinta ba ai zaku kula da ita sbd nacin kaunarta akanki,

Kasheta kukai niyan yi kome?
Bakwajin komai a gurin kisan mutum ne or wat?

Hawayen dake ta tsiyayowa jannah suka ta fara fidda sautin sheshekan kuka ahankali can qasa wanda ya sakasa sakin qaramin tsoki yana kashe wayar yana jin sabon takaici da bacin rai na rufesa.

Ita kuwa gudu hawayenta suka qara sosai tana jin kirjinta na nauyi da maganganunsa da suke kai tsaye zagi da qarshen wulaqantawa gashi ko magana bata samun yi yake kashe wayarsa koyaushe.

Ajiye wayar tayi tana rufe fuskanta da tafukan hannunta biyu tana girgiza kai alaman bazata iyaba,
Bazata iya da aurensa ba,
Bazata iya daukan wannan baqin cikin da qarshen wulaqancinba har karshen rayuwarta,
Tana tsananin sonsa da kaunar 'yarsa amma bazata iya rayuwa dasu ba ta hakura dan Allah a raba auren nan.

Sallah ta sauko gadon taje tayo alwala tayi ta jima tana rokon Allah zabin Alkhairi a cikinsu,
Idan Ammar ne Alkhairi a gareta Allah yayi gaggawar kawo mata mutuwar wannan auren da batama san ya sunansa ba.

Tana gama adduarta gurin falaq ta nufa ta tadata cikin kulawa tai sallah ta koma ta kwanta bayan ta bata warm milk tasha sbd ba maganar zuwa school yau.

Bayan falaq ta tashi guraren 10 tai wanka a daki aka kawo mata breakfast dinta taci wanda jannah din ce take aikin.

Wuni tai tana kulawa da ita duk da falaq din ta warwarewanta daman yar wahala ce da bata saba da itaba ta tabata dan haka ta sakewanta sosai.

Washe gari tinda safe Jannah ta tashi ta nufi kitchen da ita Fiddausi ta hada mata breakfast da komai na zuwa school sbd ko ayau da asuban saida ya fada mata maganganun da suka sakata tashi cikin damuwa akan yarsa dan hakanne ta tashi aikin da bata taba sabawa dashiba.

Saida falaq ta gama komai itace ta kaita school din ta dawo.

A gajiye take jinta dan haka ta kwanta ko baccin isashe bata wani samu ba lokacin tashi saura mintina 40 ta nufi school din itada Fiddausi suka jira aka tashi ta dawo dasu gida.

Sallah da abinci kadai sukaci ta sake ficewa kaita islamiyya sbd malaminta bayanan yayi tafiya dan haka makarantar ake kaita kafin ya dawo.

Ganin bazata iya dawowa gida ta komaba zaunawa tai a makarantar har aka tadasu sika dawo gida.

Wannan karan itace mugun zazzabin wahalar da bata sababa ya kama
Idanuwanta sunyi wani irin laushi gwananin tausayi amma ta daure ta hana su Dad ganewa bare suyi magana.

Washe gari ma haka ta qare a cikin wahalar dare nayi zazzabi yansake rufeta daqyar ta iya tashi sallan asuba.



A cikin kwanaki kadan ta koma abar tausayi ko Fiddausi tsananin tausayinta takeji gashi umarni ne daga AZIZ din itace zata kula da falaq tinda itace ta saka aka kawota.

Ita kanta falaq tsananin tausayin Jannah din wadda ta fara rama a kwanakin take sbd tsananin wahalar da bata sababa ta fara yimata yawa gashi taqi denawa.

Duk inda damuwa da qunci suke sun cike Familyn zaadens sbd sunaji suna gani Jannah din take wannan wahalar sunyi sunyi ta dena ta kasa denawa,

Har sabuwar mota takanas dad ya siyawa falaq tareda drivers dan a ringa kaita Jannah ta huta amma sam AZIZ LIMBA yace baya wasa security din 'yarsa sbd baisan drivers dinba adai bari Jannah din taci gaba kafin ya dawo.

Maganar dawowansa ma jin Dad yayi hankalinsa ya tashi ya shiga damuwa sosai akan tarewanta sbd tsoron irin wannan wahalar zataje kawai tasha dan haka sukaji auren yafara fita ransu tin baa tareba.

Mimi ma datake yawan video call da ita ganin yanda taga Jannah din ta koma sai taji kuma ta shiga damuwa sosai da tausayinta.

Duk familyn zaadens babu wanda yake jin dadin ganin halinda jannah take ciki gashi sam taqi nuna damuwa ko gajiyawa duk da yanayinta ya nuna hakan sbd duk dare da zazzabin wahala take kwana.

Ammar ma tinda yaga jannah so daya yaji hankalinsa ya tashi da son dawowa dan haka suka tattaro suka dawo batareda sun sanar ba.


Da yamma su Mimin suka dawo lokacin jannah na kitchen tana tareda Fiddausi suna aikin cake da falaq tace zataje school dashi.

Yau tasha wuya sosai sbd tinda ta tashi da asuba bata komaba tana kan yawo da aiki.

Ko abincin kirki bata ciba gashi Class party ne zaayi a school din.

Jin ana murnan dawowansu Mimi ta goge hannunta da qaramin towel ta fito tana nufo babban palonsu.

Ammar dayake sako kai a palon akanta idanuwansa suka fara sauka zuciyarsa tai wani irin daukewa wani irin nauyi me sanyi yana danne kirjinsa batareda ya dauke idanuwansa akantaba yana kallo.

Itama shi din idanuwanta suka fara sauka akansa ta zuba masa ido
Yayi kyan gani ya samu nutsuwa ba kamar yanda yabar gida ba.

Numfashi me sanyi ta sauke tana dauke idanuwanta akansa tana maidawa kan Mimi tareda sake murmushin farin cikin ganinsu ta nufi Mimin da gudu ta rungumeta tanajin zuciyarta tana karyewa tace

"Mimi nayi kewanku dan Allah kada ku sake tafiya ku barni"

Mimi da bataji dadin ganinta a yanda ta ganta ba murmushin karfin hali ta sake tana rungumeta tace

"Ina zamu dake kina matar wani"

Basar da zancen jannah tai tana dawo da kallanta kan Ammar da har lokacin ita yake kalla tace

"Barka da dawowa Ammar Zad"

Murmushi me kyau ya sake mata yana cewa

"Thank you Jannah Zad"

Maheer ne ya qaraso ya rungume Ammar din yana cewa

"Welcome back Bro"

Amsawa yayi yana rungumesa batareda komai a ransa ba yace

"Yaya muka sameku?

Anny ma Mimi ta rungume tana musu barka da dawowa kafin suka qarasa ciki gabaki dayansu.

Falaq ma fitowa tai da murnanta taiwa Mimi oyoyo tana rungumeta.

Cikeda kauna Mimin ta rungumeta tana cewa

"Falaq yaya kike?
Yaya baqunta?

Murmushi tai tana amsawa tana sake musu sannu da zuwa.

Fiddausi da sauran yan aikin gidan fitowa sukai suna musu barka da dawowa.

Da daddare bayan kowa ya nutsu ya huta suna kan dining suna cin abinci Jannah data iso tareda falaq din kallansu kowa yayi cikeda tausayin Jannah,

Zama sukai suka fara cin abincin Ammar ya kasa samun nutsuwan ganin abincin da Jannah zataci dan haka da kansa ya miqe ya sake serving nata wani abincin sbd gaba daya ta zabge kamar bata cin abinci.

Cikeda kulawa yace

"Kici wannan you don't look good"

Thank you" tace tana murmushi.

Falaq data kasa cin abincinta tana kallansa jin tai gabaki daya cikinta ya cika dan haka fasa cin abincin tai ta miqe tabar dining din.

Babu wanda yace komai hakama dukkaninsu jannah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login