Showing 180001 words to 183000 words out of 185083 words

Chapter 61 - Kalbim Book 1 Complete Hausa Novel

Mamuhgee   

23 Sep 2025

5432

ba daidaiba ta zauna tareda dora kan jannah din a kafafunta tana rarrashinta a tinaninta bacci takeyi.

Har yamma suna gurin tukuna jannah ta farfado ko gani batayi sosai ta miqe daga jikin Umman tana jin zuciyarta na qafewa.

Dafawa tai ta tashi tareda miqawa Ummah hannu ta bude baki Ahankali tace

"Ummah muje"

Kama hannunta Umman tayi da sauri ta miqe suka farawa takawa suka bar gurin.
#MAMUH
#NEW LIFE
#BESTlove
#MothersLove
#JANNAH ZAD
#FATIMA UMMA ZAD
#The ZAADENS
#The LIMBAS
#BESTSTORY
#HOTLOVE
#HOTROMANCE
#CRAZY LOVE
#BESTLOVERS

ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
96
*SHOP WITH ME by RANO*
08030811300
Best children's clothing shop💯
https://chat.whatsapp.com/Gk4H76TlRgyAAWIWgx3Jo7

Kina neman in da zaki samun kayan yara classy kaya na yan gayu at a very affordable price? Ko kina son fara kasuwancin kayan yara amma baki da jarin da zaki saro kayan? Nesa ta zo kusa, kiyi joining community din nan muna saka kaya masu kyau available da inganci a farashi me sauki da zaki dauka ki tallata har ki samu naki kema.
Burinmu shine kowacce mace ta samu sanaar da zata dogara da kanta.



*********
Tafiya sukai me dan tsayi kafin jannah ta tsayar musu da mota suka hau batareda ta iya cewa komaiba sbd jikinta gabaki daya dayake a mace zuciyarta na bushewa da baqin ciki da damuwa.

Ummah data ga yanayin jannah din hannunta ta saka a cikin nata ta kama tana hadewa da nata cikeda kauna me tsafta da karfi tana jin kamar ta yaye duka kuka da damuwar dake damun jannah din ta dawo dashi kanta.

A hanya aka ajiyesu suka qaraso da kafa sbd kwata kwata baa barin motocin haya na shiga anguwar,
Suna isowa gida silalewa jannah tai ta zauna tareda rufe idanuwanta tana rafka wani irin tagumi da nisa a tinani.

Ummah zama tai gefenta tareda tagumin tana zubawa jannah idanuwanta shiru.

Lokaci mai tsayi suka dauka a hakan kafin jannah ta iya sauke ajiyar zuciya tareda miqewa tsaye ta nufi toilet tayo Alwala tazo suka tada sallah.

Suna zaune a gurin akai ishai suka miqe sukai,

Kwata kwata batajin yunwa damuwa da qunci sun cike mata cikin amma tasan umman na buqatan abinci dan haka miqewa tai jiki ba karfi suka fito tareda umman hannun Ummah na cikin nata suka fara tafiya tinaninta yayi nisa jefa kafarta kawai takeyi har suka isa gurin madam dinsu jannah ta karba abincin da suke karba suka zauna anan can bayan kitchen Umman taci ta koshi ta sakata cin dole itama suna gamawa suka fito suka koma gida.

Suna dawowa gida Umma ta kwantar da jannah kan kafafunta tana mata fita tana cewa tayi bacci.

Rufe idanuwanta tayi ahankali tana jin nutsuwa da sassaucin komai na ratsata,
Kasancewan Ummah a rayuwarta ta sani rahama ce me girman gaske wadda take sake jinta har cikin ranta,

A yanxu Ummah danginta,uwa kuma ubanta hakama abokiyar rayuwa.

Cikin Amincin Allah bacci me nutsuwa ya dauke a hakan wanda bata taba tinanin samun bacci ba a yau din.

Kwana Ummah tayi har asuba tana gadi da kulawa da jannah din wadda ta tashi cikeda wani irin tawakkali da karfin zuciyar rungumar kowace irin kaddara da Allah zai jarabceta dashi,

Allah ya bawa Ahalinta damar sake wata rayuwar idan sunyi juriya da hakurin shekara guda dan haka zata jure zata karba zata jira lokacin kuma tanawa Allah godiyar wannan damar daya basu.

Ajiyar zuciya ta sauke ahankali a lokacinda ta kalli time a jikin wayar taga karfe goma na safe kuma lokacinda kotu ta basu ta barin gidan karfe goma sha daya ne dan haka ta kalli yan kayan datake dasu har ita har Ummah iyakacinsu jaka daya.

Juyawa tayi ahankali ta kalli jakarta dake rataye jikin bango wadda ta dauki lokaci bata ko kalla inda take ba sbd abinda yake cikinta abu ne da har abada bazata iya budewa ta kalla ba.

Hannu ta miqa ahankali ta ciro jakar tareda saka hannunta ciki ta ciro takardar da Saleem yabar mata sbd tinanin zata iya buqatan hakan.

Akan envelope din dayake ciki hannunta ya fara sauka wanda ya sakata rintse idanuwanta ahankali tana jin kamar wuta ce hannunta ya sauka akai.

Janye hannunta tayi ahankali tareda lalubo takardar Saleem wadda take dauke da Sunan garin da batama san yaya zatai pronouncing nasa ba amma kuma rayuwa ayanxu can zata kaita a cikin mutanen da batasan yaya zasu karbeta,
Bata sansuba basu santa ba rana tsaka zataje garesu tace itace jikar yar uwarsu data shafe shekaru da rasuwa kuma yayanta vasu nema danginta ba sai yanxu.

Numfashi ta sauke idanuwanta na jajir amma koma me zata tarar a kauyen ta shirya zata dauka zata daure zata zauna ta jira fitowan iyayenta su taru su koma kauyen sbd acan Allah kuma yanzu ya zabar musu rayuwa.

Tattara musu kayansu tayi a jaka ta rufe ta sake duba dukkanin tamardun ahalinta na karatu da id cards nasu da sauran duka takardunsu masu mahimmanci suna hannunta dan haka ta sake sakasu qasan jakarta kafin ta miqe tsaye tareda miqawa Ummah hannu wadda ta kama da sauri tana miqewa.

Numfashi me dumi jannah ta sake saukewa tana jin kirjinta na mata wani irin nauyi rauninta na neman bayyana sbd rayuwa taza mata matakin karshe na fadawa wata rayuwar wadda batasan wane qalubale kuma zata tarar ba.

Bude kofar dakin tai ahankali tareda juyowa ta kalli Ummah da idanuwanta da sukai jajir wani irin radadi mara faduwa ne yake cinta da zuciyarta ta bude baki Ahankali cikin tsananin sanyi tace

"Ummah zaki bini??

Da sauri Ummah ta gyada kai tana sake qanqame hannunta cikeda kauna datake ji har ranta tace

"Duk inda zaki tafi bazan taba barinki ba har abada,
Bazan qara rabuwa dake ba,
Muna tare ba rabuwa UMMIJAN"

Wani numfashin ta sake saukewa tareda ficewa daga dakin Ummah na sake murmushi a fuskanta na kasancewanta da Umminta.

Suna fitowa daidai gate din gidan motocin kotu da lawyers suna isowa tareda yan media anan aka karbi dukkanin takardun komai dayake rubuce aka tabbatarda duk abinda yake rubuce na kadararsu ansamu takardar mallakarsa a cikin takardun data bayar akai komai ta saka hannu da hannunta dake rawa a qasan signature dinsu Dad dayake jere a takardun wanda saida aka kai musu gidan yari suka saka hannun sun bada komai tas tukuna.

Juyawa tayi tabar gurin batareda ta iya juyowaba tanaji anata daukan hoton da yar hayaniya amma bata dakata ba bare juyowa sukai tafiyarsu itada Ummah.

Tafiya sukai kafin suka isa gurin madam wadda tasan da komai kuma ta amince ta sakasu a cikin ma'aikatanta masu kwana kafin su samu abin tafiya dashi.

Daki ne me dan girma wanda yake store ne na ajiyar abinci anan masu aikinta biyu rak data yadda dasu suke kwana sai kuma su jannah din yanxu.

Bata bari ciwon dayake ranta ya takureta ba aikinta data saba ta kama jiki a mace tana kokarin hana kanta mara godiar Allah daga sassaucin da suka samu na hakan.

Wuni tayi aiki har saida aka rufe restaurant din da dare tukuna ta samu ta watsa ruwa taxo tayi sallan ishai ta kwanta a gurin wahalallen bacci mai hade da zazzabi yana dauketa.

Ummah ce ta dawo kusa da ita ta rufe mata jikinta ahankali tana daukan abin fifita tana kore mata sauro da kuma dan zafin dake akwai cikeda kulawa tana dan danna mata kafafunta da hannuwanta data san sun gaji matiqa.

Washe gari da karfin jikinta ta tashi tana rage damuwa a ranta ta zauna tana taya Ummah gyara farcenta kafin ta gama ta kalli Umman tace

"Ummah kiyi baccinki idan zanje nayi aikina idan na gama saina hada miki ruwan wanka kada ki fito kiyi zamanki tinda kinga madam tace batason wanda ba ma'aikacinta ba na fitowa gurin ayyukan,
Kinji Ummah?

Gyada kai Umman tayi tana cewa

"Idan kin gaji ki aje ki dawo ki hutawanki kinji"

Wani murmushi da iyakacinsa bakinta ne ya kubce mata daya saka ramammiyar fuskanta kyau tace

"Ummah zan huta amma ba yanzu ba insha Allah"

Itama umman murmushi tai mata tana kallanta harta fice.

Madam din data iso tafara zuwa ta gaida cikeda girmamawa kafin ta wuce gurin aikinta wanda tafara da wani uban tarin yankan cabbages da vegetables tukuna ta koma fere Dankali wanda kusan buhu guda ne aka zazzage.

Saida tai kusan rabi tukuna aka basu abincin breakfast ta karba ta koma dakin da suke takaiwa Ummah suka zauna sukaci suna gamawa Ummah taqi xama ta biyota ta zauna gefenta tana kallan yanda take fama da aikin fere dankalin dan haka itama ta karba ta fara tayata daman ta iya tinda tayi aiki a gidajen abinci itama.

Kaman wasa sai gashi Ummah ta ringa tayata aikin da har yanzu bata wani qwareba sbd bata saba ba.

Sai yamma sosai suka samu saukin aikin suka koma aikin wanke wanke.

Ana magrib suka samu kammala komai suka tafi wanka tafara kaiwa umman ruwa toilet tayi kafin itama tayi,

Sallah sukai suna gamawa dukkaninsu a gurin bacci ya daukesu kamar matacci na wahala.

Sai dare sosai Ummah ta farka ta rufe jannah din tana mata aikin korar sauro da fita tanaji tana gyangyadi ahaka dai suka ga asuba.

Washe gari ma haka suka wuni a aikin wahalar baji ba gani ba hutu sai dare suka samu hutu,

A hankali suka fara shude kwanaki a cikin gurin wanda babu komai sai aikin bauta da wahala,
Tinda suka shiga basu taba fitowa ba sbd babu inda zasu idanma sun fito din,

Ahankali Ummah ta shiga cikin aikin sosai sbd bata iya kallan jannah cikin wahalar datai mata yawa ita kadai,

Da farko Jannah bata bari sai daga baya ganin Umman bata iya bari hakama ta fita iya komai sai ya zamana tare suke komai,

Ita kanta madam din dataga Ummah na aiki sosai saita dan qara musu kadan akan abinda take bawa jannah duk da ba yawa.

Duk yanda Jannah zatai ta hane a gane Ummah ba lafiyayya bace tana yi sbd batason kowa yayi mata kallan mara hankali ko makamancin hakan,

Tana kulawa da Ummah sosai tana kiyaye dik abinda zai tayar da ciwonta,
Bata wasa da lulurar umman ko kadan,

Itama Umman ta nata bangaren duk dare bata iya bacci kwana takeyi kulawa da Jannah bata barin sauro ya cijeta shiyasa take kwana tana kulawa da tattalinta kamar qaramar yarinya.

Sauran abokan aikinsu basu san Ummah ba asalin mahaifiyarta bace sbd kaunar da tattalin datake mata shiyasa suke dan respecting Umman kadan.

Tin jikinsu bai saba da wahala da yanayin gurinba har suka saba jikinsu ya sabu da wahalar sbd suna cikin wata na biyu a gurin.


Lokacin da suka shiga wata na uku a lokacin ne albashin da suka samu yakai abinda suke nema na tafiya gida dan haka Jannah taje ta sanar da madam tafiya zasuyi.

Da farko kamar bazata barsu tafiya ba amma ganin yanda jannah din tai wata irin rama da duhu sosai ya saka tausayinta cikata sbd yarinyar tabbas tana buqatar hutu da kwanciyar hankali koda a kauye ne indai zata samu nutsuwa.

Sallamarsu tayi ta tattara dan abinda zata basu ta basu sukai godia cikeda girmamawa suka hada kayansu akan washe gari zasu tafi.

A daren jannah bata iya bacci ba sbd bawa kanta karfin zuciyar iyawa,
Basuda komai,
Basuda abinda zasu zaunar da kansu a birni sbd a zero suke yanzu abincin da zasuci ma basuda hanyarsa matiqar bata tafi kauyenba ta nema danginsu dad din ba ta samar masu mafakar da suna fitowa zasu je su fake su dora sabuwar rayuwa daga can ba to tabbas suna fitowa garari da wulaqanta zasuyi dan haka ta zabi komawa kauyen ta karbe dukkanin zafi da tsangwamar da zaayiwa su Dad din kafin fitowarsu ta yanda koda zasu zo ta gama gyara alaqarta da dangin bazasu tozartasu ba idan sukaxo.
#MAMUH

ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
97
*SHOP WITH ME by RANO*
08030811300
Best children's clothing shop💯
https://chat.whatsapp.com/Gk4H76TlRgyAAWIWgx3Jo7

Kina neman in da zaki samun kayan yara classy kaya na yan gayu at a very affordable price? Ko kina son fara kasuwancin kayan yara amma baki da jarin da zaki saro kayan? Nesa ta zo kusa, kiyi joining community din nan muna saka kaya masu kyau available da inganci a farashi me sauki da zaki dauka ki tallata har ki samu naki kema.
Burinmu shine kowacce mace ta samu sanaar da zata dogara da kanta.

*************
Da wannan ta tashi da sassafe suka shirya tin asuba sukai wanka sukaci abincin data samar musu tin dare koda karfe 7 na safe tayi sun fito bayan sunyi sallama da abokan Aikinsu.

Mota suka tara suka shiga zuwa tasha,
Takardar hannunta ta sake budewa tana  karanta sunan porthcrt da sunan wani kauyen dayake da nisa sosai a cikinsa wanda batama san ya zatai pronouncing nasa tareda sunan familyn Mahaifiyarsu Dad duka a jiki harma da sunanta ita kanta mahaifiyarsu dad din da hotonta danasu dad din.

Ajiyar zuciya ta sake saukewa ahankali tana lumshe idanuwanta tareda maida takardar jakarta ta rufe.

Suna isa tasha babu bata lokaci akai directing nasu ga motar da zasu shiga tareda biyan kudin komai suka shiga suka zauna daga ita har Umman jikinsu a mace.

Basuyi zaman mintina Arbain ba motar ta cika aka rufe koina motar ta tashi ahankali ana musu Allah ya kiyaye suka fita ta lumshe idanuwanta ahankali tana kwantawa jikin Ummah wadda ta fara shafa bayanta ahankali itama tanajin kamar tinaninta zai dawo sbd damuwa da nauyin kirjine ya rufeta sedai bata iya cewa komaiba.

Tafiya sukai sosai kafin suka fice daga abuja suka kama hanya dakyau.

Tinda suka hau hanya bata bude idanuwanta ba har sukai tafiyarda ta dauki awanni tukuna ta bude idanuwanta da sukai jajir tana dagowa daga jikin Ummah datai shiru ta zubawa fuskan jannah din idanuwanta cikeda kulawa da tinanin da batama san tanayi ba.

Kasa kallan Umman jannah tai sai kawai ta maida kanta ta sake kwantarwa jikinta tana godewa Allah daya kawo Ummah rayuwarta dan a yanzu batama fatan yan uwan umman su bullo takoina tana fatan Ummah ta zama tata har mutuwa.

Tafiya me tsayin gaske sukai wadda takaisu ga isa dare sosai dan haka ko bayan isarsu a tasha suka kwana cikin baqin dake kwana tasha tinda asuba aka sakasu motar kauyen da zasu tafi me tsananin nisan gaske.

Ummah kadai ta siyawa Abinci wanda itama umman bata wani iya cinsa ba sbd sun galabaita,
Jannah jin hankalinta na tashi tsoro da fargaban abinda zata iya tararwa na ciketa dan haka tayi shiru a sanyaye tana kallan hanya.

Sai yamma lis suka isa kauyen wanda aka ajiyesu a farkonsa,

Drivern da kansa ya hadasu da yan gari tareda fada musu gidan da zaa kaisu.

Kallansu mutane dake gurin keyi suna mamakinsu sbd ganin yanda dukkaninsu sukai laushi sosai sukai zuru zuru musamman Jannah da bata taba tafiyar mota me tsayi ba hakama a rayuwarta bata taba xuwa kauye ba batama san rayuwa a daji shine kauyenba sai yanxu data samu kanta a dajin Allah me nisan gaske.

Tsoro da fargaba me tsananin gaske ke shigarta tanajin kaman bazata iyaba amma kuma sbd samarwa ahalinta mafakar rufin asiri dole ta iya.

Tafiyar qasa suka fara a wahale cikin kishirwa da gajia amma hakanan suka daure suka ringa bin wanda aka hadasu dashi yana tafiyarsa ba gajiya ko kadan sbd sabo.

Gap da magrib suka isa cikin garin qauyen wanda sai a lokacin suka ga mutane sosai da gidaje sosai kowa na harkan gabansa,
Fulanin daji ne kaf kauyen wanda kana kallansu ba tambaya zakasan kusan kowa a garin bafulatani ne baqaqe da farare gasunan kowa harkan gabansa yake.

Kallansu akeyi cikeda mamakinsu sbd ana ganinsu anga baqin da suka taho daga nesa.

Wani gida me girma da sashe sashe suka nufa har kofar gidan matashin ya kallesu yace

"Ga gidan nan ku shiga sai kuyi bayani"

Dagowa jannah tayi ta kallesa da idanuwanta da bakinta daya bushe qayau ta budesa tace

"Mun gode sosai Allah ya saka da alkhairi"

Kallanta yayi ya washe bakinsa yana cewa
"ba damuwa ai da ganinku na gida ne"

Sallama ya kwada a cikin gidan yana ambatar sunan abokinsa Garba dayake gidan.

Garban ne ya fito daman yana kusa zai fito kenan.

Washe da baki ya fito yana kallan bellon kafin ya maida kallansa kansu jannah dake tsaye a rakube.

Zuba mata idanuwansa yayi sosai yana kallanta cikeda mamaki kafin ya maida kallansa kan Ummah ya juyo gurin Bello cikin fulatanci yace

"Daga ina?
Su waye?
Waye suke nema?

Kallansu bellon yayi shima cikin fulatanci yace

"Daga binni suke nan gidan suka taho ka shiga dasu ka kaisu gurin kawu Modibbo mana.

Garba dayaji daga binni suke da sauri yana washe baki ya kallesu yana cewa

"Barkanku da zuwa,
Bismillanku"

Juyawa yayi ciki dasu yana cewa bello ya jirasa.

Suna shiga gidan jannah ta sake riqe hannun Umma suka nufi ciki har babbar tsakar gidan wanda kowa ya fito aka fara kallansu cikeda mamaki.

Modibbo ne babba a gidan kuma me fada a ji kuma mafadaci dan haka kowa hanyar dakin Modibbon ya kalla Garba na wucewa dasu can yana sake musu sannu bakinsa a washe.

Modibbo ne ya fito sanye da Babbar rigarsa datake zuba qamshin ajiya maana qamshim rima da wularsa da shape dinta yafi kama da kofin silver fari tas dashi.

Yana ganinsu sake gyara zaman hularsa yayi yana kallan Ummah ita datake babbah sai yaga ta sauke kallanta qasa.

Jannah ya maida kallansa kanta yana cewa

"Garba su waye?
Daga ina kuma?

Sake washe baki garba yayi daidai nan kawu Isiya da kawu jibo suka iso suna kallansu jannah din dukansu baki a sake.

Garba yace

"Modibbo baqi ne daga birni nan gidan suka taho"

Maida kallansa kansu yayi yace

"To baqi barkanku da zuwa,
Daga ina?

Numfashi jannah ta sauke ahankali ta bude bakinta jikinta na mutuwa gabaki daya tace

"Sunana Jannah Zadeen jikar Hajiya Zeenah Zadeen.....

Tsit sukai gurin gabaki dayansu tareda kallan junansu cikeda mamaki a bayyane kafin Modibbo ya hade fuska yana cewa

"Kikace jikar haj zeenah??
Yar Mahmoud ko Ahmed?

Sake sunkuyar da kanta tayi ahankali ta bude baki tace

" 'yar Ahmed"

"Da wane shedan zan iya gane hakan??

Hannunta ta zira a jakarta ta ciro hoton kakarta dasu Dad ta miqa masa.

Karba yayi su kawu isiya na sake matsawa da sauri duba hoton suma cikeda mamakin abinda ya kawota gurinsu.

Zubawa hoton idanuwansu sukai suka kafawa yar uwarsu idanuwansu sbd da mahaifin daya haifesu su ukun da haj zeenah din uwa daya uba daya suke.

Shiru sukai kafin Modibbo ya dago ya zuba mata idanuwansa yana karantar kamannin Mahmoud da Ahmed daya sani tin suna yara suka taso tare amma tinda mahaifinsu yayi kudi ya bar qasar dasu basu sake nemansu ba haryanxu.

Cikin nutsuwa da sanyi yace

"Ina su Mahmoud da Ahmed din suke??

Dago jajayen idanuwanta tayi ahankali kai tsaye ba kwana kwana sbd batada

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login