Showing 138001 words to 141000 words out of 185083 words
sbd muguwat ramar datai tayi pale sosai gabaki daya kammanninta sun sauya sbd ya dade bai gantaba....
Nauyi me tsanani ne ya danne zuciyarsa ya rintse idanuwansa yana sake budesu akanta cikin tsananin sanyi ya ce
"Meya sameta ta koma haka?
Ta dade ne batada lafiya?
Jannah ce ta koma hakan?
Meyake faruwa?
Maheer dauke idanuwansa daga kanta yana jin zuciyarsa na karyewa da tsananin tausayinta da jin ciwonta a cikin ransa..
Daddy mahmoud kuwa wayarsa ya fidda yana saka kiran Ammar daya kasa isowa haryanzu yazo ya duba musu ita kokuma su tafi da ita gida ayi mata komai acan sbd normally irin haka idan tai collapsing takan dauki kwanaki kafin ta farfado.
Ringing wayar Ammar keyi a gefensa yana kallo da jajayen idanuwansa dake cikeda radadi ya kasa dauka sbd zuciyarsa fashewa zatai idan ya bude baki yayi magana,
Barin gurin yakeson yi amma ya kasa koda motsa hannuwansa ne baya gani sosai sbd baqin ciki da ciwon daya danne masa kirji da zuciya.
Cigaba da sake kiransa Daddy mahmoud keyi amma wayar baa dagawa dan haka Maheer ya fidda tasa wayar shima yana saka kiransa amma abu daya ne baa daga wayar.
Saleem ne ya kalli Daddy mahmoud yace
"Daddy bara naje na dubosa tinda dai duka tare muka fito"
Juyawa yayi ya fice dakin yayi tsit babe me iya cewa komai Ammar suke jira kaman zuciyoyinsu zasu fada sbd qaguwan yaxo ya dubata dan ganin suke kaman bata numfashi kwata kwata gashi basada yadda ko imanin bawa wasu likitocin daman su dubata da asibiti kawai zasu wuce da ita batareda jiran komaiba.
Shi kansa AZIZ din ya kira nasa likitocin suna hanyar isowa shiru yayi yana jiran xuwan nasu yana kallan time akai akai cikin basarwa.
Sayd ne dayake bayansa ya dan dago kai ya kalla batareda yace komaiba.
Sayd din ficewa yayi yana fidda wayarsa ya sake saka kiran su dr Ashir a karo na ba adadin lattinsu.
Saleem a gate ya hangi motar Ammar dan haka ya qarasa da sauri yana kallan Motar da mamaki.
Bude masa kofa akai a mutunce da girmamawa ya fito yana kallan yanda securities din duka suke a shirye a position.
Motar ya nufa da sauri yana budewa yaga yanda jikin Ammar din ke rawa sosai idanuwansa sunyi jajir.
Saurin shiga motar yayi yana ambatar sunansa cikeda tashin hankali da fargaba.
Qara jijjiga jikin Ammar din yakeyi kirjinsa na kasa daukan ciwo da radadin da zuciyarsa ke masa take yanayinsa ya rikice a gurin kansa yafara juyawa yana wani irin rawa.
Saleem fitowa yayi da sauri ya zagayo ya tura Ammar din seat din gefe ya hau na driver bai tsaya komaiba yayi baya da motar yabar gurin dashi zuwa gida cikin tsananin damuwa da sabon tashin hankalin waye zai duba jannah datake tsananin buqatan taimako a yanzu.
Zaadens ya isa dashi wanda sai alokacin Mimi tasan abinda yake faruwa itada Anny dan haka dole Anny tafara basa taimakon gaggawa saleem na taimaka mata Mimi kuwa tashi hankalinta sosai sbd gabaki daya a yanzu cikakkiyar lafiya neman gagarar Ammar din takeyi wanda kuma hakan a cikin kwakwalwansa yakeyi dr ta fada a dena bari yana yawan shiga wannan halin akai akai sbd akwai matsala sosai da hakan.
Saleem ne ya buga waya ya sanar dasu Dad abinda ake take hankalinsu ya sake tashi da tsananin tinanin ina mafitar take sbd Ammar dinne kadai likitan da zai duba jannah gashi shikuma ciwonsa ya rasa lokacin tashi sai yanzu wanda suke mamakin menene ya samesa daya haddasa hakan.
A daidai wannan lokacin Su dr Ashir suka iso aka bude musu gate suka shigo tareda qarasowa ciki babu bata lokaci suka fara bata taimakon datake buqata shi da dr Sameera da nurse da suka taho da ita bayan kowa ya fice daga dakin.
Dayake wannan karan shine zuwansu na farko limbas dan haka palonsa na baqi aka isa dasu suka zauna Maheer na rasa zabin daya wuce yayi contacting Su Abraham sbd akwai yiyuwar dole sai sun taho din tinda Ammar da aka saka ran zaiyi handling situation din basai sun dawoba ya rikice shima dan haka bazai iyaba dole su qaraso su karba idan ba hakan ba babu bata lokaci wasu doctors din zasu san anmata dashen zuciya wanda zaa iya buqatan history na ciwonta abinda bazasu taba bari ko a tsautsayiba wani ya taba gani ba kenan.
Sai dare sosai aka samu bugun zuciyarta ya dawo daidai tareda numfashinta amma bata farfadoba har lokacin.
Nurse aka bar mata su dr Ashir din suka wuce suma su Dad sai alokacin suka tafi bayan Daddy mahmoud ya nuna sunason tafiya da jannah din acan Zaadens kafin ta warware sai a dawo da ita.
Dago idanuwa AZIZ yayi ya xuba masa yana kallansa cikeda rashin ganin girmansa a idanuwansa kafin ya dan dauke idanuwan nasa akansa yana gyara zamansa a natse kafin ya bude baki yace
"No zata warware anan din doctors dina zasuji da komai she'll be fine and good"
Dad kallansa yayi yana son sake magana ko yayane ya basu ita sedai kuma yasan bata bakinsa da energy dinsa kawai zaiyi amma AZIZ din bazai basu itaba ba kuma dan komaiba sbd ya nuna musu karfinsa akanta yanzu ne.
Zuciya ba dadi suka baro limbas din cikin tsakar daren badan rayukansu sun so hakan ba.
Suna barin limbas Securities suka rufe gate din gidan gabaki daya babu me sake shiga ko fita sai kuma safe insha Allah.
#MAMUH
ZAFAFA BIYAR
KALBIM 500
mamuhgee
A DUNIYATA 500
Huguma
AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul
KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo
Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi
Shedan biya
09033181070
Or mtn vtu at
09032345899*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
74
*UMMU_MAHNOOR LUXURIES*
(Best luxuries shop)
08034469681
08135142610
Aslm Alaikm ina kuke masu neman luxuries na kayan alfarmar kece raini?
Ina masu son su saka sitirar alfarma ta zamani ta manyan mata masu aji da zaa kalleki kallo daya asan sitirar alfarma e kika saka?
Shin kunsan me ake nufi sa kayan asalin yan gayu da nuna gayu?
Sitirar Alfarma kikeson sakawa?
Sitirar da kike ganin manyan mata da ita?
Sitirarda zakiyi gayun sallah dake da yaranki a dauka waje kikaje da kanki kika siyota?
To kizo ga damarki ta sameki sbd UMMU_MAHNOOR LUXURIES ta kawo miki sauki har gida,
Karkice se masu kudi ke iya siya har kema me yar dama zaki samu naki da saukin kudi kuma best quality da kalar zamani data yan gayu,
Nidai Mamuh nace duk wadda ke son a buga gayun sallan bana da ita da 'yayanta to tazo gurin UMMU_MAHNOOR LUXURIES tai siyayyar sallanta harma zuwa gaba dan nasan zakuji dadi da fahimtar abinda nake fada akan kayanta💯💯
Abubuwan da zaki samu a gurinta with the best quality na wayayyun mata masu aji yan gayu sune;
Atampopi
Laces
Shadda
Materials
Shoes
Bags
Veils
Trolleys
Jewellerys
Oil perfumes
Numbers
08034469681
08135142610
Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries
**************
Koda suka isa Zaadens babu wanda zuciyarsa bata cikin damuwa da bacin rai musamman a halinda suka tararda Ammar,Dad jin yayi kaman zai hadiye zuciyarsa sbd tsananin 'daci.
Maheer kuwa gabaki daya hankalinsa na kan magana dasu Abraham da daren zaa fara musu shirin tahowa dan rashin zuwansu kaman akwai barazana ga sanin zuciyar wata ce a kirjin jannah dan haka sam shi baya wasa da koman qanqantar hanyar da zata iya kawo musu matsalar sirrin dayake rufe dan haka hankalinsa yake kai yake kuma kan Jannah din da Ammar da dukkaninsu suke mamakin abinda ya samesa.
Mimi kwana tai akan Ammar tana hawaye sbd halinda daya kwana a cikinsa wanda takejin kaman sun kasa riqe marayan Allah da baida uwa baida uba tinda uban baitaba nemansa ba a matsayin dansa.
Har cikin ranta take tsananin kaunar Ammar fiyeda sauran yayanta sbd irin kauna da tsananin son dayakewa Jannah tin tana ciki hakama dole ta kaunaci jinin Zayneb.
Su kansu dad a damuwar suka kwana ta Ammar din da jannah,
Kawai abinda ya saka suke jin ta jannah sosai shine hadda sbd sirrin dayake tattare da nata ciwon.
Washe gari da sassafe Falaq ta fito ta nufi bedroom din jannah wanda tana isa ta bude kofar kai tsaye ta shiga.
Ga mamakinta Daddynta ta tarar zaune a sofa sanye da kayan geamin dinsa da alama daga can din yayo nan din.
Fararen idanuwansa ne akan jannah din wadda kallo daya zakai mata zuciyarka ta karye sbd ta qarasa komawa abin tausayi gabaki daya ciwon boye dana bayyana ya bugar da ita a lokaci kankani.
Kallanta yake a natse kowace halittar dake fuskanta tana tsayawa a cikin idanuwansa tana shiga kansa...
Falaq qarasowa tai zuciyarta na farin cikin ganinsa a dakin gurin jannah wadda ta gama yadda a yanxu bayan Daddynta da Uncle dinta babu wanda take jin tana tsananin kauna kaman Jannah din dan haka bazata qara bari ko daddynta ne ya sake saka jannah din damuwa ba indai tana kusa.
Zaunawa tayi ahankali gefensa tareda kama hannunsa tana kallansa ganin yanda yayi relaxing yana kallan Jannah din a natse hotonta abinda ya faru jiya yana tsaye cak cikin kansa na kiran wayar Ammar da daukanta.
Idanuwansa falaq din taiwa kallo daya taga yanayin da bata taba ganin Daddyn nata a ciki ba sbd baya taba bari a gane yanayinsa koda ta cikin idanuwansa ne ya qware a boye komai na cikinsa amma a yanxu ba ja sosai idanuwan sukai ba wani tsoro taji data kalla cikinsu ta kwantar da kanta jikinsa da sauri batason kallan cikin nutsuwa tace
"Goodmorning Daddy"
Rufe idanuwansa yayi Ahankali tareda sauke boyayyar numfashi kafin ya juyo ya kalleta a natse yana kama hannunta dayake cikin nasa ya bude baki cikin kulawa da kaunarta datafi masa komai yace
"Morning Falaq Aziz,
Yaya?karki saka damuwa a ranki sosai akan nata ciwon,she'll be fine"
Kallansa falaq tai ahankali tana jinjina kai kafin ta bude baki tace
"Daddy banason komai ya samu My Jan,
Batada lafiya,tanada heart problem Daddy"
Kallan falaq din yayi da sauri yana mamakin yanda akai ta sani
Gyada masa kai tayi tana cigaba da cewa
"Yes Daddy,ta fada mun sbd naga yanka a gurin heart dinta inata tambayanta meya jin mata ciwo a gurin so ta fadamun,
Daddy tayi fama da ciwon zuciya na shekaru masu yawa tin yarinta,
Ta rasa shekarunta na yarinta,
Ta rasa childhood nata,
Ta taso a boye sbd ciwonta,
Ta cire rai daga rayuwa kwata kwata sbd ta kasa samun donor sai a lokacin da time ya qare mata aka samu donor daga wani namiji wanda aka bata zuciyarsa shine Allah ya bata sabuwar rayuwa sbd kwananta be qareba,
Daddy jannah nada zuciya me kyau wanda ban saniba ko zuciyar datake kirjin nata ne amma tin daga lokacin data warke haryanxu bata denawa wanda ya bata zuciya addua ba..."
Yanda hannuwansa suke rawa sosai yana kokarin hana falaq din ganewa sbd yanayinsa dayake sauyawa matsalansa na neman dawowa ya sakasa miqewa yana kasa iya cigaba da saurara ya bar dakin baya ko gani sosai ya nufi palonsa ya shige ya rufe ya nufi bedroom dinsa wanda yana isa kasa iya cire kayan jikinsa yayi sedai ya yagasu da karfin gaske yana jefarwa ya fada toilet ya sakarwa kansa ruwan dumin da hayaqinsu ke dan fita ahankali suna gauraye toilet din shikuma sosai jikinta ke rawa ya daki bangon toilet din da karfin gaske har saida hannunsa ya fashe amma sam bayajin komai sai masifar dayake ji a cikin kansa da kirjinsa mai tsananin gaske.
Jinin dayake zuba a hannunsa ne yake gauraya da ruwan dayake sauka a qasa daga jikinsa suna sauya kala suna gangarawa.
A duk lokacinda maganar yanda aka raba Ummitah da ranta ta taso yanayinsa tashi yake wanda duk yanda yake ganin likitocinsa many akan hakan yanayin ya kasa rabuwa dashi lokaci daya duk da ya rage sosai amma yanayi me matiqar hadari yake shiga batareda sanin kowa duk duniya ba bayan Sayd.
Trauma din Ammar Zad a bayyane take wanda shi kuma tasa dataci uban ta Ammar din yake a boye sbd yafisa sanin gwagwarmaya da iya taku tareda kwarewa a iya controlling kansa sabanin shi nasa dayake bayyane ga duniya ma kila.
Ya dade a ciki kafin ya samu iya controlling kansa yanayinsa ya fara dawowa daidai ya zari towel ya dauro a qugunsa ya fito bayan ya nade hannunsa dayake dan zubar da jini har lokacin ya shirya a natse yana kallan fuskansa cikin mirror zantukan falaq na yawo a cikin kunnuwa da zuciyarsa har lokacin,
Menene Jannah din take nufi da zuciyar namiji ne a kirjinta?
Boye gaskiar ne takeyi kokuwa iyayen nata da lover boy din nata basu fada mata gaskia ba?
Shin kafin komai ma da saninta kuwa suka raba wata da ranta dan bata zuciya?
Ta Aminta da a raba mace me tsohon ciki da ranta dan ita ta samu sabuwar rayuwa?
Dakatawa yayi daga saka agogon diamond din dayake hannunsa ya zubawa mirror idanuwansa da har lokacin basu qarasa komawa daidaiba abubuwa da yawa ne suke cikinsu suna qonasu.
Karfe goma ya fito dauke da wayarsa yana duba tarin misscalls daga Zaadens wanda babu wanda ya gani bare dauka.
Su mama dake palo dukkaninsu Qamshinsa ya gauraye palon cikin sanyi ya sakasu kallan hanyar fitowansa
Sai gashi ya fito kwarjinsa da kamewansa ta saka su fadilah sauke idanuwansu mama kadai ce bata dauke idanuwanta akansa ba cikin kulawa ta amsa gaisuwansa tana sake tambayar jikin jannah duk da taje ta dubota har so biyu da safen.
Fadilah dagowa tayi cikin girmmawa da wayewa ta gaidasa ya amsa batareda ya kalleta ba ya nufi dining.
Dukkaninsu yau sukai breakfast kaman yanda suka saba hadda falaq sbd jannah nata farfado ba.
Suna gamawa su dr Sameera suka iso shikuma ya fice daga gidan.
Yana ficewa Anny da Mimi tareda saleem da maheer da mommy suka iso gidan sukuma.
Dukkaninsu babu wanda zuciyarsa bata tabu da yanda suka gantaba da yanda ta koma.
Abinda ya dan ragewa Mimi tsananin nauyin da kirjinta yayi shine ganin yanda falaq take kulawa da jannah din sbd koda suka iso ta rage mata kayan jikinta tana goge mata jikinta da lallausan qaramin towel da ruwan dumi sosai ita da Fiddausi.
Hadiye hawayenta Mimi tayi sbd duk gwagwarmayansu akan jannah ta qare a inda masu aiki ne da qaramar yarinta ke kulawa da ita tana yashe a daki batareda anbata taimakon datake buqata ba.
Ga wanda bai taba mahimmancinta da komai na rayuwarsa ba an cutatar dashi ta hanyar hana masa abinda zuciyarsa ke so ita kadai idan Ammar ya samu ya yadda ya fuskanci kowane irin talauci da ukubar rayuwa idan har jannah na tare dashi.
Anny ma sanyi jikinta yayi sbd bata taba dauka jannah zad zata taba dawowa haka ba,
Idan har zaa iya daukan rayukan mutane akan jannah to bata taba tinanin zata taba ganin jannah a irin wannan halinba na daukanta batada mahimmanci ko kadan.
Suna gidan likitocin da suke dubata suka buqaci zaa koma asibiti da ita sbd acan xaa bincika ciwonta dakyau yanda ya kamata.
Kai tsaye Maheer ya nuna rashin Amincewansa da hakan karshe ma ya mama yayi magana da ita da kansa akan suna son tafiya da jannah din sbd tanada likitocinta na musamman da zasu taho dan ita kadai daga wata qasar.
Mimi ma baki ta saka suka buqaci Amincewan maman sbd ita kadaice zata amince su tafi da jannah din AZIZ ya dawo baice komaiba.
Mama ita kanta batason a tafi da jannah din amma yanda mimi tai mata bayanin yanda yanayin ciwon jannah din yake sai tace saita kira AZIZ ta sanar masa.
Kiransa tai yana dauka kai tsaye ta sanar masa tanason ya bari iyayen jannah suje da ita gida likitocin da suka saba dubata su dubata tinda haryanzu bata farfado ba.
Shiru yayi batareda yace komaiba tsawom mintina kafin ta sake maimaitawa ya bude baki a taqaice yace
"Ba damuwa duk yanda kikace mama amma su tafi zan kaita na kaina amma sai likitocin nata sun sauka qasar ina buqatan ganinsu da kaina"
Yana gama fadan hakan ya kashe wayar sbd yasan suna sauraronsa.
Mama kallansu tai sbd sunji da kunnensu idan sun aminta da hakan shikenan idan basu aminta ba itama tafiya da jannah bai kwanta mata bare falaq datake jin kaman zatai kuka zuciyarta da jikinta na sanyi.
Basada zabin daya wuce amincewa da hakan dan haka suka tattara suka koma da jiran saukar su Abraham da Ken Nigeria sbd tin barin Ken Nigeria ya koma yaron Abraham ya zama baturen kansa shima sbd ya tabbatarda idan ba cigaba yayi da binsu ba zai samu kansa a matakin da dr ismail ya taka sbd duk wanda yake cikin wannan sirrin an dade da rife babinsa iya su yanzu suka rage.
Wanna sharadin na AY LIMBA ya saka dole zuwansu Abraham ya dawo a kwana daya dan haka a washe gari ake jiran saukarsu Nigeria.
Ammar ya dawo daidai sedai ciwone yanzu me tsananin radadi yake cin zuciyarsa,
Kewan mahaifiyarsa yake sosai radadin rashinta na dawo masa,
Ya rasa walwalwansa da farin cikinsa gabaki daya bayajin dadin komai na duniyar jin yake inama yabi Amminsa ya huta da abinda yakeji a zuciyarsa da gangar jikinsa.
Hoton jannah dayake dakinsa ya qurawa idanuwansa dasuke masa yaji da radadi sunyi jajir ya bude baki zaiyi magana amma baya iya cewa komai sbd tsananin damuwar datake neman taba kansa.
Mimi da Saleem suke tsananin jin ciwonsa a cikin ransu suna jin tasu zuciyar na cikewa da nauyi da dacin ganinsa a halin dayake ciki sbd ya dena fitowa kwata kwata,
Dad da daddy mahmoud duk yanda suke zaryan zuwa dakinsa sam baya budewa sbd bayason ganin kowannensu sbd idan yana ganinsu Amminsa yake gani a tare dasu dan haka baya son ya tsanesu sbd tsananin kaunar dayake wa Amminsa.
#MAMUH
ZAFAFA BIYAR
KALBIM 500
mamuhgee
A DUNIYATA 500
Huguma
AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul
KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo
Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi
Shedan biya
09033181070
Or mtn vtu at
09032345899*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
75
*UMMU_MAHNOOR LUXURIES*
(Best luxuries shop)
08034469681
08135142610
Aslm Alaikm ina kuke masu neman luxuries na kayan alfarmar kece raini?
Ina masu son su saka sitirar alfarma ta zamani ta manyan mata masu aji da zaa kalleki kallo daya asan sitirar alfarma e kika saka?
Shin kunsan me ake nufi sa kayan asalin yan gayu da nuna gayu?
Sitirar Alfarma kikeson sakawa?
Sitirar da kike ganin manyan mata da ita?
Sitirarda zakiyi gayun sallah dake da yaranki a dauka waje kikaje da kanki kika siyota?
To kizo ga damarki ta sameki sbd UMMU_MAHNOOR LUXURIES ta kawo miki sauki har gida,
Karkice se masu kudi ke iya siya har kema me yar dama zaki samu naki da saukin kudi kuma best quality da kalar zamani data yan gayu,
Nidai Mamuh nace duk wadda ke son a buga gayun sallan bana da ita da 'yayanta to tazo gurin UMMU_MAHNOOR LUXURIES tai siyayyar sallanta harma zuwa gaba dan nasan zakuji dadi da fahimtar abinda nake fada