Showing 165001 words to 168000 words out of 185083 words

Chapter 56 - Kalbim Book 1 Complete Hausa Novel

Mamuhgee   

23 Sep 2025

5492

wanda suka take suka saka mutane da yawa a ciki.


Tsit asibitin tai sbd kukan Jannah da Maheer dayake tashi a dakin yana fitowa waje ahankali...

Saleem suman zaune yayi har lokacin hannunsa na cikin na mahaifiyarsa yana jin zuciyarsa na mutuwa daga komai na duniyar gabaki daya.

A cikin daren suka dawo gida da gawar mimi wanda zaayiwa janazah da safe.

Kwanan zaune sukai dukkaninsu a palo
Sunyi kuka har hawayen kowannensu sun qafe babu komai sai jajayen idanuwa.

Washe gari karfe goma na safe akai janazah din Haj Mimi Zad wadda ta samu mutane ba laifi ciki hadda Baba alhassan da alh Saad sbd a limbas babu me kwanciyar hankali ko tinanin da zai iya zuwa.


A lokacinda aka dawo tinda ba zaman gaisuwa zaayiba tini kowa ya watse aka bar jannah kadai da masu aiki shiru gidan babu kowa ba komai sai tarin damuwa da qunci.
#MAMUH



ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
88
*UMMU_MAHNOOR LUXURIES*
(Best luxuries shop)
08034469681
08135142610
Aslm Alaikm ina kuke masu neman luxuries na kayan alfarmar kece raini?
Ina masu son su saka sitirar alfarma ta zamani ta manyan mata masu aji da zaa kalleki kallo daya asan sitirar alfarma e kika saka?

Shin kunsan me ake nufi sa kayan asalin yan gayu da nuna gayu?
Sitirar Alfarma kikeson sakawa?
Sitirar da kike ganin manyan mata da ita?
Sitirarda zakiyi gayun sallah dake da yaranki a dauka waje kikaje da kanki kika siyota?
To kizo ga damarki ta sameki sbd UMMU_MAHNOOR LUXURIES ta kawo miki sauki har gida,
Karkice se masu kudi ke iya siya har kema me yar dama zaki samu naki da saukin kudi kuma best quality da kalar zamani data yan gayu,

Nidai Mamuh nace duk wadda ke son a buga gayun sallan bana da ita da 'yayanta to tazo gurin UMMU_MAHNOOR LUXURIES tai siyayyar sallanta harma zuwa gaba dan nasan zakuji dadi da fahimtar abinda nake fada akan kayanta💯💯
Abubuwan da zaki samu a gurinta with the best quality na wayayyun mata masu aji yan gayu sune;

Atampopi
Laces
Shadda
Materials
Shoes
Bags
Veils
Trolleys
Jewellerys
Oil perfumes

Numbers
08034469681
08135142610

Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries



**************
Kwana biyu shiru rayuwa ta sauya a zadeens babu me fita babu me zuwa,
Walwala da farin ciki ya zama tarihi a rayuwarsu ko abinci ba koyaushe suke fitowa ci ba...

A wannan halin ne suka wayi gari Saleem yabar komai nasa ya bar gida baa gansaba.

Da farko sun jira ne har dare tukuna.

Har karfe 12 na dare Saleem bai dawoba hakama wayoyinsa ya barsu gida dan haka hankalinsu ya fara tashi.

Maheer ne ya fita a cikin daren yafara nemansa cikeda damuwa.

Suma su jannah da dad hankalinsu tashi yake sake yi dan haka suka ringa kiransa suna son jin ko ya gansa din.

Yawon garari Maheer ya ringa yi cikin daren har asuba baiga Saleem ba dan haka ya dawo gida.

Wuni daya ba saleem ba labarin,
Wuni biyu dan haka suka tabbatarda ya tafiyarsa ne sbd bazai iya rayuwa a cikinsu b Mimi ba Ammar ba.

Damuwar Dad ninkuwa tayi dan haka Maheer ya sake tada musu shirinsu na barin qasar su koma inda zasu bude sabuwar rayuwa.

Jannah da passport dinta baya tareda ita dole shiryawa tayi ta tafi Limbas dauko Kayanta masu mahimmanci su passport da id cards dinta.

Se dare ta isa gidan sbd batason Falaq ta ganta ko ita taga falaq kunyarta da ciwon ganinta takeyi,
Kunyar kallanta da zuciyar Ummitah a kirjinta takeyi,
Kunyar kallan mama da zuciyar 'yarta a kirjinta takeyi dan hakanne take sake jin nutsuwa da rabuwa dasu rabuwa ta har abada.

Karfe 10 na dare ta isa da motarta tai parking motar a can waje bata shigo da ita ba sbd batasan ma asan tazo har ta tafi.

Securities gate suka bude mata ta shigo kai tsaye ta nufi ciki.

Main Living room ko data shigo babu kowa tsit gidan hakama duhu ankashe wutar koina.

Kai tsaye dakinta ta nufa kafafunta a sanyaye ta bude ta shiga ahankali ta isa bakin gadonta ta zauna a darare idanuwanta na zafin quncin dayake kirjinta.

Hoton falaq dayake aje gefen hotinan familynta dake gefen beside ta zubawa ido tana kalla tanajin tsananin kauna me karfin gaske datakewa falaq tana taso mata tana danne kirjinta,

Hawaye ne masu tsananin zafi sika silalo mata ahankali tana daukan hoton ta rungume hawayenta na qara gudu sbd tinawa da ranar da Falaq din tafarajin Zuciyar mahaifiyar data haifeta aka cire aka saka mata irin shock din data shiga wanda batasan yaya ta iya handling da karban komai ba haryaxu'
A wane hali zuciyarta take akan zancen yanzu?
Ta tabbatarda Falaq ta tsaneta ne shiyasa bata taba nemanta ba ko a lokacinda ta rasa mahaifiyarta tana tsananin neman wani a tareda ita.

Miqewa tayi da Hoton a jikinta ta nufi inda passport dinta da id cards dinta suke su kadai ta dauka ta nufo kofa hawayen fuskanta na tsananta gudun radadin datake ji a zuciyarta na rabuwa da falaq da wanda zuciyarta ke tsananin yiwa son dayake kaddara da dana sani garesa.

Fitowa tayi daga dakin kukanta na tsananta,

Taku biyu tayi tayi karo da mutum a gabanta tsaye cak.

Babu haske sosai sai kadan wanda na dakinta da bata rufe bane yake haskosu.

Kayan hannunta ne suka zube qasa sbd yanda ta bugu dashi batasan dashiba,

Qin dagowa tayi sbd qamshinsa daya tabbatar mata da wanda ta sani dinne....

Shima qin kallanta yayi ya xubawa passport dinta daya fadi qasa da id cards dinta idaniwansa da sukai tsananin nauyi da ja sbd mummunan halin dayake ciki na yarsa dayake ji yana gani yana neman rasawa.

Shiru sukai babu wanda ya motsa bare kallan dan uwansa sai idaniwansa dake kan passport dinta har lokacin zuciyarsa na sosuwa me tsananin ciwo da zafi tarewa yankewa.....

Durqusawa tayi ahankali ta miqa hannunta zata dauka ta wuce sbd zuciyarta dake neman dena bugawa a gabansa din.

"Kin zabi guduwa dasune sbd tseratar dasu bayan girman cutatarwa da quncin da suka saka mutane da dama hadda falaq da batasan komai da kowaba??
Zuciyar Ummitah bazata taba zabar wainda suka cutatar da AZIZ da falaq ba,
Ashe a jininku yake kenan ba a zuciya bane......

Rintse idanuwanta tai maganganunsa na sukar kirjinta hawaye masu zafi suka gangaro mata ta bude baki tareda dagowa ta kallesa ta bude baki cikin jin ciwon kalamanta ita kanta tace

"Zuciyar Ummitah ce a kirjinta amma jinin mahaifina ne yake yawo a jikina yana harbawa har cikin zuciyar Ummitan datake kirjina,
Zuciyar Ummitah sonka takeyi tana kaunar Falaq amma kuma jinin Zaadens ne yake yawo a jikina bamu taba juyawa namu baya ba komai tsanani,

girman son da zuciyar Ummitah takewa AZIZ LIMBA bazai taba wanke kaunar mahaifin datake jinin gangar jikin da zuciyar ummitan takeba,

AZIZ LIMBA Zuciyata na maka tsananin son da bazan iya cirewava har abada sbd zuciyar datake kirjina wannan shine kaddarata danake son gogewa kaina"

Cikin idaniwansa dayake kallanta da wani irin radadi tayi tana tsiyayo hawayen dake bayyanar da tsananin sonsa dayake kasheta kowace daqiqa.

Kuka ta fashe dashi mara sauti tana rintse idaniwanta ta zube qasa tana dukan kirjinta da karfi tana kukan dayake qarasa yamutsar da kansa yana neman qarasa zarewa shima.....

Juyawa yayi zai bai gurin ta bude baki cikin wani irin qunci da kuka tace

"Dan Allah ka rabani da Zuciyar nan daga kirjina,
Dan Allah ku rabani da ita nima na gaji,
Na gaji banaso,
Inaso na kwanta na huta kamar Ummitah,
Bazan iyaba,ciwo nake ji,
Zuciyata bazata iya daukaba,
Bazan iyaba inason hutawa nima,
Inason hutawa kaman Ummitah da Mimi........

Wani irin kukan daya saka qafafunsa sarewa ya zube qasa shima takeyi tana maganar wadda takeyi cikin tsananin qunci da ciwo da radadin dayake cikeda rayuwarta da babu abinda ya rage sai baqin ciki da damuwa.

Shi kansa hutawan yakeson yi kaman Ummitah da mahaifinsa da mahaifiyarsa,
Baida abinda ya rage masa a duniya sai Falaq wadda itama zata tafi tabarsa,
A yanxu tabbas so yake ya bar komai ya tafi ga iyayensa da Ummitah sbd bazai iya daukaba...

Miqewa tayi kukanta na qaruwa ahankali mara sauti tana neman barin gurin jikinta na rawa ta taka kafarsa ta sake zubewa qasa akansa.

Tafin hannuwanta biyu ne suka sauka akan fuskansa da hawaye ke gangarowa ahankali.

Jin hawayensa a tafin hannunta ya sakasa zubowa da wasu hawayen.....

Hannuwana biyu ya saka akan nata ya rufe fuskansa dasu yana girgiza mata kai wani irin kuka mara sauti yana fito masa....

Itama kukan takeyi tana girgiza masa kai alaman rabuwansu shine mafi alkhairi.....

Yanda yake kukan ne ya saka kukanta qaruwa sosai ta qanqame fuskansa tana kukan datake neman wanda zataiwa tsawon lokaci dan haka dukkanin quncin dayake dunqule a kirjinta kukansa takeyi tana zubewa a jikinsa ya qanqameta tareda hade goshinsu guri daya hancinsu na gogar na juna.

Ahankali muryansa na rawa ba sauti a galabaice yace

"Pls dont"

Girgiza kai tayi kukanta na qaruwa ta bude baki tace

"I cant"

Sake bude baki tayi zata sake cewa i cant ya hade bakinsa da nata yana hanata fada kukansu na qaruwa duka su biyun sbd abinda bata saniba a gobe ne da safe zaa kama iyayenta sbd anriga an gama binciken komai a goben kamasu zaayi a hanya mafi muni.

Girgiza kai tayi hawayenta na sake gudu sosai bakinsa na cikin nata cikin kukan suke kissing juna ahankali yana sake qanqameta itama rungume kansa tayi tana jin inama bata wannan kaddarar suka hadu ba,
Inama haduwa sukai suka kamu da son juna kaman hakan suyi aure kaman kowa familynsu na son juna da girmama juna,
Inama itace uwa shikuma uban falaq suke suka haifeta ta hanyar soyayya me dadi da kwanciyar hankali dika babu wannan.

Kissing juna sukeyi ahankali yana jin zuciyarsa zata buga da abinda yake ji a cikinta gameda ita din....

Ita kanta tasani soyayyarsa masifar da zata iya hallaka ce dan haka ta bude idanuwanta da sukai jajir da kuka suka kumbura sosai ta sauke a fuskansa hawayenta na tsananta gudu shima ita din yake kallo duniyarsa na juyawa yana jin kirjinsa na sake nauyi me karfin gaske akanta.

Ahankali ya fara zare mata rigar jikinta yana dora bakinsa kan nata yana kissing dinta cikin tsananin sanyi da son maidata macen Limba daga yau.....

Ita kanta zuciyarta ta riga ta amintar mata da zama daya dashi a daren da zasu rabu kuma bazata taba regretting ba dan haka ahankali ta rufe idanuwanta tanaji yana kokarin rabata da Rigar jikinta.....

wayarsa data fado ce daga jikinsa tayi haske sunan Sayd tsaf ya bayyana akan kiran daya shigo wayar.....

Cak ya dakata daga abinda yakeyi yana kallan fuskanta datake hawaye har lokacin sbd zuciyarsu su dukan ta dade da mutuwa akan juna.....

Wayar ya miqa hannu a sanyaye ya dauka tareda saka handsfree sbd bazai iya dagawaba dan zuwa lokacin ciwon kirjinsa ya gama gauraye jikinsa.


"Falaq ta farfado sedai aman jinin ya dawo,
Hamma muna rasa Falaq......" cikin wani irin kukan daya saka zuciyar AZIZ dena bugawa Sayd ya fada maganar...

Ita kanta jannah mummunan bugawa zuciyarta tayi ta kallesa sedai kokarin kamuwa da attact yakeyi wanda ya sakata ambatar sunansa da karfi wanda hakan ya fiddo da mama daga daki da sauri wadda batada lafiya sosai ma daurewa kawai takeyi.

Su Fiddausi ma duka fitowa sukai ana kunna wutar palon haske ya bayyana...

Yanayin da suka ga AZIZ ne ya hana mamakin ganin jannah kwata kwata sbd attack din gaske ya samu a take.

Securities aka kira cikin matsanancin tashin hankali aka fiddo dashi zuwa asibiti cikin sabon tashin hankalin daya samesu.

Koda suka isa asibiti cikin gaggawa aka karbesa sai alokacin jannah ta isa dakin falaq zuciyarta na wata irin mummunan bugawa.

Tana tura dakin tin a kofa ta zube qasa zaune tana rintse idanuwanta cikin hawaye kukan na kasa zuwama sbd gabaki daya karfinta da rayuwarta da suka qare yanzu agun kuka.

Sayd ne a dakin dukkanin Alamun tafiya da nisan ciwo ya gama bayyana a tattareda Falaq din dan haka ayau yayi kukan da ko lokacin mutuwar Ummitah baiyiba sbd a yanzu duk mai imani ya kalli Falaq a yanda ta koma imaninsa zai qaru.

Kukan da jannah keyi tin tanada karfi har karfinta ya qare a dakin ta kwana zaune.

Karfe goma na safe Falaq ta sake bude idaniwanta ahankali akan fuskan jannah dake jeme gabanta gabaki daya ta koma kamar ba jannah zad ba ta jeme ta bushe sbd masifar dasuke ciki.

Ahankali ta motsa hannunta daqyar cikin sanyi ta dora akan na jannah dake gefen nata hawaye masu radadi suna gangaro mata na tsananin kaunar jannah din da tausayin Daddynta dazai shiga wani halin rashinta kaman yanda ya rasa mahaifiyarta.

Ahankali jannah ta dago ta zubawa falaq ido idanuwanta na bushewa da radadi jajir ba hawaye.

Kasa magana dukkaninsu sukai har aka bude kofar dakin AZIZ daya koma kalar tausayi shima aka turo a kujera idaniwansa akan falaq wadda ta maida idaniwanta akansa hawaye naci gaba da gangarowa daga idaniwanta.
#MAMUH

ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
89
*UMMU_MAHNOOR LUXURIES*
(Best luxuries shop)
08034469681
08135142610
Aslm Alaikm ina kuke masu neman luxuries na kayan alfarmar kece raini?
Ina masu son su saka sitirar alfarma ta zamani ta manyan mata masu aji da zaa kalleki kallo daya asan sitirar alfarma e kika saka?

Shin kunsan me ake nufi sa kayan asalin yan gayu da nuna gayu?
Sitirar Alfarma kikeson sakawa?
Sitirar da kike ganin manyan mata da ita?
Sitirarda zakiyi gayun sallah dake da yaranki a dauka waje kikaje da kanki kika siyota?
To kizo ga damarki ta sameki sbd UMMU_MAHNOOR LUXURIES ta kawo miki sauki har gida,
Karkice se masu kudi ke iya siya har kema me yar dama zaki samu naki da saukin kudi kuma best quality da kalar zamani data yan gayu,

Nidai Mamuh nace duk wadda ke son a buga gayun sallan bana da ita da 'yayanta to tazo gurin UMMU_MAHNOOR LUXURIES tai siyayyar sallanta harma zuwa gaba dan nasan zakuji dadi da fahimtar abinda nake fada akan kayanta💯💯
Abubuwan da zaki samu a gurinta with the best quality na wayayyun mata masu aji yan gayu sune;

Atampopi
Laces
Shadda
Materials
Shoes
Bags
Veils
Trolleys
Jewellerys
Oil perfumes

Numbers
08034469681
08135142610

Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries




Miqewa jannah tayi ta fice daga dakin tabar asibitin ma gabaki daya tana zuwa gida.

Tin daga nesa taga gurin a tsananin cike sosai da sauri ta qaraso tana ratsa mutane harta isa gate din gidan wanda yan media da jamian tsaro sukaiwa mummunan kawanya aka fito da Dad dinta daure da cuffs wani irin mugun daurin daya sakata tahowa da gudu kansa Maheer na bayansa shima a daure idaniwansu jajir.

Da gudu tayi kansu tana fasa wani irin kukan dayake neman fasa zuciyarta tana kiran sunasu.

Kallanta Dad yayi idaniwansa cikeda wani irin ciwo me radadi yace

"Jannah kiyi hakuri na kasa zamowa gatanki a lokacin da bakida kowa kike buqatanmu"

Girgiza kai takeyi tana kuka me tsanani tana jin kamar ranta zai bar jikinta.

A mota aka sakasu aka tafi dasu anata musu hoto mutane wasu harda jifansu.

Ana barin gurin dasu zubewa tayi a gurin qasa tana wani irin kuka me tsanani da tsima rai.

Miqewa tayi kamar zararra tayi cikin gidan taje dauko file dinta ta fito ko gani batayi ta hau mota tayi asibiti tana isa gaban AZIZ ta tsaya tana masa wani irin kallon dayake cikeda wata irin tsanar gaske.

File din hannunta ta daga ta kunnawa wuta ta jefar a gabansa ta dago ta kallesa hawayen idaniwanta na gangarowa tace

"Ayau inason Ka cire zuciyar kirjina ka bawa falaq zuciyar mahaifiyarta sbd ayau ni Jannah Zad banason bana kaunar duk wani abu dayake na Limbas,
Ayau ni jannah zad na zabi barin duniya na baka abinda shine ya hadani dakai,
Idan zuciyar Ummitah zata cire maka fushi da fansar datake cikeda ranka ayau na baka damar ka cire banaso na gaji,
Na gaji,
Na gaji,
Inason hutawa....

Zubewa qasa tai tana kukan daya saka dukkanin su mama dake gurin yin tsit banda Falaq datake kukan itama tanajin indai sai raba jannah da zuciyar dake kirjinta ita kam ta hakura da rayuwa..

AZIZ file din data kona a gabansa wanda shine zai bawa tasa yar samun sabuwar rayuwa a duniya sbd a cikine manyan bayanan da zasu saka a iya bawa falaq zuciyar daya daga cikinsu suke,

A ciki manyan original bayanan da zasu saka a wa Zaadens hukunci daidai abinda sukai amma a gaban idonsa ta tarwatsa wannan damar sbd samarwa yan uwanta sassaucin da baya musu fata ko kadan.

Tafasa da wani irin zafi kirjinsa ya dauka ya dago ya kalleta kallon dayake jin tana ficewa ransa shima kaman yanda take jin tsanarsa.

Miqewa tsaye yayi yana kallanta da jajayen idanuwansa yace

"Tinda da bakinki kin fada bakya buqata babu amfanin barin Zuciyar a kirjin naki tabbas zaa cire a sakawa wadda ta cancanta,
Daman kashe wata akai dan rayaki kema ba illa bane dan kin tafi wani ya rayu"

Qarasa kalaman yayi suna yankar zuciyarsa yanka me tsananin ciwon gasken daya sakasa dauke idanuwansa daga kallanta tsananin fushinsa da bacin ransa na bayyana.

Zuba masa idanuwanta tai hawaye ba tsiyaya tana jin kalamansa har cikin zuciyarta sbd ayau ya gama bayyyanar mata da girman qin dayake mata da jininta,

Numfashi ta sauke ahankali tana share hawayenta ta bude baki tace

"Wallahi tallahi ni Jannah na Amince da yaddata ba tirsasawa ka cire Zuciyar dake kirjina ku dauki abarku"

Mama data kasa cigaba da sauraron wannan kalaman na zallar baqin ciki da qunci ficewa tayi daga dakin tanajin duniyar na futa kanta itama gabaki daya hakama zuciyarsa na jin zafi da rashin kaunar ganin jannah wadda taketa kokarin hana zuciyarta qinta sbd ba laifinta bane amma zuciya batada kashi hakan na neman gagararta.

Fitowa Jannah tayi idanuwanta jajir suna sake bushewa tabar asibitin tabi hanya tana tasa gurin zuwa ta nema bakin hanya ta zauna tana saka kanta a cikin qafafunta ta fasa kukan da batasan rayuwar da zataiba gwara ta zuciyar Ummitah ta huta itama da wannan masifun.

Har dare tana gurin zaune bakinta da idanuwanta sun bushe qayau ta miqe ta nufi gidansu wanda yayi tsit ma kowa duka familynta dake rayuwar jin dadi da wadata a cikinsa yau an wayi gari babu kowannensu.

A palo ta zube qasa kwance tana rintse idanuwanta sanyin tiles na ratsata,

Bazata iya barin mahaifinta da dan uwanta da Ammar dasuka rage mata ba a duniya su shiga mummunan halin da zasu rasa rayuwarsu ba suma.

Zata tsaya da duk abinda ya rage musu suke dashi ta yaqi AZIZ LIMBA akansu,
Zata tsaya sai ta fidda yan uwanta a wannan masifar sbd bazata taba barin ya samu abinda yakesoba akansu,

Ya samu iya fansarda dan haka ta isa haka sun biyasa harda qari

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login