Showing 171001 words to 174000 words out of 185083 words
iso wannan matakinba da ayau take jin inama tabar duniya.
Su kuwa suna isa gida kai tsaye bangarensa ya wuce batareda ya bari kowa yaga yanayin dayake ciki ba yana shiga tin a kofa ya zube qasa yana dafe kirjinsa dayake masa azabar dabazai iya daukaba,
Wasu irin hawaye ne suka gangaro daga idanuwansa masu tsananin zafi yana zubewa qasa kwance har lokacin hannuwansa na dafe da kirjinsa....
A daidai wannan lokacin Sayd ya shigo sbd tin a mota ya lura da yana cikin mummunan hali..
Sayd na shigo wani irin jini na fesowa ta bakinsa me karfin gaske idanuwansa na rufewa.....
Cikin matsanancin tashin hankalin daya saka kafafunta Sayd sarewa ya isa garesa da rarrafe hannuwansa na rawa ya ambaci sunansa da karfin daya saka duka jamaar gidan fitowa.
Mama na ganin AZIZ din da jini kasa qarasowa tayi itama jiri ya debeta ta zube a inda take.
Shi kansa Sayd bazai iya tuqi ba sbd mummunan halinda ya shiga dan haka ambulance aka kira babu dadewa sosai ta iso aka kwashesa zuwa asibitin harma da mama wadda itama manyanci da ciwon damuwa suka hade suna neman qarasata.
Fiddausi da Sayd ne a tsaye kawai kaf familyn sai baba alhassan wanda shima dole damuwa ta tada nasa jikin da ake lallabawa.
Se cikin dare aka samu Bugun zuciyarsa da numfashinsa suka dawo daidai sedai shima take ciwo ya qarasa maidasa abin tausayi sbd baisan waye ma yake kansa.
Sayd da damuwa take neman kashesa shi kadai tini ya qarasa hada kan komai nasu a cikin kwana biyu ya gama handling komai akai sabbin presidents da chairmans da directors a companies dinsu ya qarasa handing over na komai ga latif,
Securities ma da masu aiki na Mansion din dukkaninsu babu wanda baa bawa manyan kudaden da zai jima bai nemaba aka sallamesu duka kowa da kowa.
Washe gari zasu tafiyarsu subar qasar dan haka a daren Motar Sayd ta tsaya a kofar gate din Zaadens ya fito mota ya bude gate da kansa ya shigo sbd babu securities kamar zaadens din baya sai mai gadi daya wanda shima ya kasa tafiya ne yabar jannah kaman yanda me aiki daya ta tsaya shima tsayawa yayi.
Harabar gidan a kwai haske amma kamar baya ba,
Sanyi jikinsa yayi shima sosai farkon zuwansu Zaadens na dawo masa a lokacinda kowa na cikeda lafiya da kwanciyar hankali da burirrika amma ayau dagasu har su din kowa ya rasa abubuwa da dama da har abada bazasu taba dawowa ba.
A kofar palon ya tsaya ya miqa hannunsa ahankali yayi knocking idanuwansa jajir.
Shiru babu motsin kowa,
Sake bugawa yayi yana dan ja baya kadan...shiru baa budeba dan haka ya sake bugawa yana ci gaba da bugawa a natse cikin sanyi.
Shiru kusan tsawok lokaci me tsayi,
Ajiyar zuciya da numfashi me zafi ya sauke yana juyawa xai bar gidan aka bude kofar ahankali cikin nutsuwa da sanyi.
Me aikice ta bude kofar cikin fargaba a sanyaye.
Juyowa yayi ya kalleta itama shi take kalla cikeda damuwa.
Bude baki tayi tace
"Barka da zuwa"
Amsawa yayi yana sauke kallansa daga kanta yace
"Ms jannah nakeson gani"
Shiru tayi tsawon seconds kafin tace
"Batada lafiya amma bismillah bari na sanar mata"
Shigowa yayi ya zauna a natse a palon kansa qasa idanuwansa har lokacin jajir.
Wucewa tayi ciki ita kuma zuwa dakin jannah dake kwance shiru idanuwanta rufe.
Bude dakin tayi ahankali ta shigo da sallama me sanyi sbd tasan ko tayi knocking jannah bazata iya maganar cewa ta shigoba bare tasowa ta bude din.
Cikin nutsuwa da sanyi tace
"Sir Sayd daga Limba yazo yana son ganinki"
Bude idanuwanta tayi ahankali batareda ta motsaba.
Sake maimaitawa me aikin tayi kafin ta juya ta fice daga dakin.
Shiru shiru bata fito ba tsawon lokaci kafin ta bude dakin ta fito sanye da doguwar hijab har qasa fuskanta ta rame sosai tayi haske sosai.
A hankali ta tako ta iso palon ta zauna a natse batada karfi ko kadan sbd ciwon dayake tattareda ita tsawon kwanakin.
Nunfashi ya sauke ahankali sbd shiru sukai dukkaninsu babu wanda yace komai.
Dagowa yayi Ahankali ya kalleta zuciyarsa na cika da damuwa me tsanani gaske ya zura hannunsa cikin aljihun qatuwar jacket din dake jikinsa ya ciro daguwar envelope din datake sealed ya miqe ahankali ya isa gabanta ya ajiye mata muryansa na wata irin sanyi me tsananin gaske sbd damuwar datake rinjiyarsa yace
"Daga AZIZ LIMBA.......""
Rintse idanuwanta tayi ahankali wani mashi me tsananin zafi na sukar tsakiyar kirjinta ta dora hannunta akan kirjin ahankali tana karban azabar datajin da dukkanin imaninta kafin ta miqa hannunta dayake rawa ta dora akan tanardar ta dauka tareda dago idanuwanta da sukai jajir ta kalli Sayd din ta bude baki Ahankali tace
"Thank you for everything"
Rintse idanuwansa yayi yana juyawa ya fice yana fatar Allah ya kawo musu sassauci su duka.
Yana ficewa damqe takardar tayi a cikin hannunta tana son fashewa da kuka amma sam babusa hawayen sun qafe sai jajayen ido.
Miqewa tayi daqyar tana hada hanya bata gani ta isa dakinta ta daga takardar tana son budewa ta karanta yanda aurenta ya mutu amma idanuwanta ma ganinsu daukewa yayi jin take tana neman mutuwa,
Da rarrafe ta isa gurinda jakarta take ta bude ta saka takardar a ciki tana zamewa qasa....
Idan lissafinta yaje daidai a date din dayake jikin ticket dayazo dashi a ranar gobe ne tafiyarsu tafiya ta har abada ba dawowa kila.
Silalewa qasa tayi yana kwantawa tareda rufe idanuwanta ahankali tana hadiye duk wani qunci da ciwo.
Karfe goma sha biyu saura Ta isa asibiti a lokacin data san babu kowa a asibitin tareda Falaq sai Fiddausi.
Ko data isa itama a cikin ciwo da rashin karfi take amma zuciyarta na tsananin son yiwa falaq ganin karshe..
Tana shiga dakin Fiddausi dake zaune ta gama sallah tana addua tana ganinta ta miqe da sauri suka rungume juna tana fashewa da kuka itama jannah din fashewa da kuka tai tana kallan fuskan Falaq data koma kaman babu nama a cikinta anma rufeta sosai baa wani budewa.
Sosai suka jima a hakan kafin jannah ta isa ga Falaq ta rungumeta ahankali tana shafa fuskanta tana kuka sosai hawayenta na lalata fuskanta gabaki daya.
Bakinta takai tayi kissing gefen fuskan falaq din kafin tayi kissing goshinta shima tai kissing hannunta da kafunta tana jin kamar ta bude kirjinta ta ciro zuciyar dake ciki ta bawa falaq din..
Kamar a mafarki falaq ta bude idanuwanta da basa gani sosai ta kalli fuskan jannah din idanuwan suka koma suka rufe.
Fiddausi ce ta sake sanar da ita zasu tafi ne ba lallai Falaq ta samu donor ba dan haka sun hakura sun barwa Allah komai.
Kasa cewa komai tayi bayan kukan datakeyi tana sake kissing falaq tako ina tana mata addua tamkar uwar data haifeta tareda mata fatan nasara da saukin da duk Allah yasan shine rahama gareta.
Ko data fice daga dakin bata sake waiwayowa ba har tabar asibitin ta nufi gida tana sakawa kanta dangana.
Ko bayan isarta gida bata rintsa ba yanda taga rana haka taga daren har gari ya waye tayi sallah ta koma ta zauna ta zubawa agogo idanuwanta da sukai jajir tana bin kowane second da agogon ke bugawa har lokacinda karfe 11 na rana tayi wanda shine lokacinda jirgin ahalin Limbas gabaki daya zai tashi daga qasar Nigeria sunyi tafiyarsu bayan sun bar komai zasuje su fuskanci sabuwar rayuwa a duk yanda zatazo.
Lumshe idanuwanta tayi lokacinda sha daya din ta buga a kan idaniwanta tanajin wani nauyi ya tsaya cak a tsakiyar kirjinta wanda ya tsaya kenan bazai saukar mata ba har abada ta sani.
#MAMUH
ZAFAFA BIYAR
KALBIM 500
mamuhgee
A DUNIYATA 500
Huguma
AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul
KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo
Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi
Shedan biya
09033181070
Or mtn vtu at
09032345899*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
92
*SHOP WITH ME by RANO*
08030811300
Best children's clothing shop💯
https://chat.whatsapp.com/Gk4H76TlRgyAAWIWgx3Jo7
Kina neman in da zaki samun kayan yara classy kaya na yan gayu at a very affordable price? Ko kina son fara kasuwancin kayan yara amma baki da jarin da zaki saro kayan? Nesa ta zo kusa, kiyi joining community din nan muna saka kaya masu kyau available da inganci a farashi me sauki da zaki dauka ki tallata har ki samu naki kema.
Burinmu shine kowacce mace ta samu sanaar da zata dogara da kanta.
**************
Zamewa tayi ta kwanta ahankali tana rufe idanuwanta tana karban sabuwar kaddadarta daga yanxu da Limbas suka barsu kwata kwata har abada.
"AZIZ LIMBA haduwa da kai da shigarka xuciyata shine abu mafi dadi da samun gamsuwan zuciyar dazan samu har abada dan haka ina maka fatan alkhairi tareda samun dukkanin farin cikin rayuwa da abinda kakeso"
Wannan kalaman sune abinda zuciyarta take fada
Wunin ranar ko bakin kofar dakinta bata fitoba tana daki a kwance sallah kawai ke tadata a sanyaye sbd ko karfin jiki batada.
Abinci daya aka kawo mata ta tashi xaune duk da bata iya ci amma hakanan ta cusawa cikinta ci idanuwanta jajir ta gama ta koma ta kwanta.
Har dare haka take har safe bata rintsa sai guraren yamma washe gari ta fito ta cusawa cikinta abinci da ruwa ta samu karfi ta fice yawon neman su Dad.
Sai dare sosai ta dawo tai sallah ta nemi guri ta kwanta.
Washe gari batada mai batada kudin da zata sakawa motar mai dan haka ta nufi dakin dad tayita neman key din tasa motar ta samu ta dauko da ita ta fita tayita yawo sai dare ta dawo ko ranar.
Sake dawo da yawon nemanta ta cigaba dayi ba dare ba rana wanda ya saka duka mayukan dake cikin motocin gidan suka qare ta koma neman yanda zata cire kudi a acct din dad da Maheer ko mimi ko Ammar amma dukkaninsu babu Atm card sbd sam basa amfani dashi banki ake zuwa a ciro musu kudi a manyan jaka a kawo musu haka suke,
A lokacin da suna Germany ne suke amfani da cards da sauransu amma anan basu damu da wannan ba kudi ake ajewa sababbi marasa nauyi dauka kawai kakeyi ka zuba aljihu ka fita ko jaka.
Rasa yanda zatai dan haka kai tsaye ta siyar da motarta cikeda quncin rashin masifar da zata taimaka musu ga abinci suna nema.
Bata iya siyayyar abinci ba dan haka mai aikin ta bawa duka kudin bayan ta cika motocin gidan da mai tace tayo siyayyar komai na abinci da suke buqata.
Bayan fitarta mai aikin kallan tarin kudin da suke hannunta tayi masu yawan da bata taba riqewaba rayuwarta sbd abinci ne me yawa jannah tace ta siya wanda zasu dade sosai da sosai basu nema ba...
Shedan ne ya fara gurbata mata tinaninta akan lokacin tafiyarta itama yayi dan haka dakin mimi ta nufa ta tattara dukkanin yan sarkokinta da abubuwa masu tsadar gaske ta fito ta tattara kayanta da wanda ba nata ba ta fito ta fice ta samu mota tai tasha kai tsaye sbd barin garin.
Sai dare jannah ta dawo gidan bataji motsinta ba ta dauka tayi bacci ne dan haka itama shigewa tai kawai.
Da safe tana fitowa kitchen ta fara nufa taga alamar babu wani abu da akai a kitchen din tin jiya sbd komai a bushe ba alamar ma an shigo tin jiyan.
Store ta nufa taga babu komai wayam alamar baayi siyayyar ba,
Fitowa tayi a sanyaye ta nufi dakin me aikin ta bude taga babu komai nata ta kwashe sai tarkace kawai.
Fitowa tayi ta nufi dakin Mimi ta duba taga duk an yamutsashi an kwace sarkoki da wasu abubuwan harma da sitirarta aka kwasa.
Numfashi me dumi ta sauke ahankali tanajin jikinta na sanyi sbd ta fahimci abinda ya faru matar ta gudu kenan sbd kudin.
Palo ta dawo kafafunta na sagewa ta zauna tana tallafe fuskanta da tafin hannuwanta.
Batasan matar na son kudi ba da zata siyar da abubuwa da dama ta bata kudin sbd ta zauna da ita ta sabu da ita a yanzu kuma ta sake komawa ita kadai a rayuwarta me aikin ma datake tayata quntacciyar rayuwarta ta gudu ta barta.
Ta dade a gurin zaune kafin ta miqe ta nufi daki ta sako hijab ta fito ta fita gidan a hanya taje ta siya abinci ta xauna cikin mota tana ci tana jin kaman zai shaqeta ta mutu sbd kwata kwata ba abinci ne a rayuwartaba kawai cikinta takeson abincin ya shiga sbd kada ta rasa karfin tsayuwa da kafafunta ta taimaki iyayenta.
Wani abincin ta sake siyowa ta dawo dashi gida ta bawa me gadi kudi shima tace ya ringa cin abinci.
********Sati Biyu da tafiyar me aikinta tana kokarin fita da safe motocin jamian tsaro suka iso gidan tareda zungureriyar takardar karbe komai na Zaadens komai da komai hatta siritar sakawansu sbd zaa fara shariarsu dan haka ana buqatar dakatar da komai nasu har sai yanda shiriar ta kaya dan anason kaf rayukan da suka dauka sai anbiya diyyarsu me girma.
Zamewa tayi jikin bango tana rintse idanuwanta da kuka ya qafe musu tana sauke numfashi tareda ambatar sunayen Allah a cikin rant.
Da kansu suka shiga suka rufe koina ita kadai aka bari ta dauki kayan sakawarta a cikin yar qaramar jaka ta fito suka karbe keys na duka motocin gidan ana rubuce rubuce da daukan hotinan komai.
Dakin me gadi da aka sallama take aka bata damar zaunawa har a gama komai ita duk bata damu da wannan ba nutsuwa taji tana samu na fito da iyayenta da zaayi a fara shariar sbd tasan a wannan lokacin Allah ne kadai yasan irin azabar da suke cikinta.
Washe gari tinda safe ta shirya da dan sauran canjin dayake hannunta ta fito dakin me gadin tareda rufe kofar dakin ta fice gate ta rufesa shima tafara tafiya me dan tsayi sosai kafin ta samu abin hawan dazai kaita inda daga karshe aka sanar da ita suna can bama a cikin garin abuja bane fita akai dasu.
Headquarters din da zaa taho dasu ta nufa tana isa sauka tayi ta nemi guri ta rakube ta zauna tana jiran a iso dasu.
Tinda ta iso ake kyararta ana mata wasu tambayoyi masu ciwo da wulaqantawa bata cewa komai sbd jikinta rawa ma yakeyi na tsoro amma kuma zuciyarta ta riga ta bushe ta kafe akan ahalinta dan haka ta kasa bari tsoronta ya rinjayeta ta gudu daga gurin.
Zaman awa daya tayi idanuwanta duk sun qanjame bakinta ya bushe zuciyarta harbawa takeyi sosai tana zubawa hanya ido.,
Kunnuwanta ne suka fara jiyo mata jiniya wadda ta saka yan media dake boye fitowa da yawansu suna cike kofar shiga gurin da yan kallo sosai harma da yawa daga cikin familyn wainda aka kashe nasu na nan Nigeria sbd an bayyanarda da sunayen wasu daga cikinsu sosai a yanda labarin ke yawo..
Miqewa tayi tsaye tana fitowa inda ta rakube kanta bugun zuciyarta na tsananta tana kafe motocin da idanuwanta har suka tsaya aka bude bayan motar prison din,
Dr Ken ne wanda ya rasa kafarsa daya aka fara fitowa dashi gabaki daya kammaninsa sun sauya ya koma kamar mahaukaci idonsa daya ya tsiyaye.
Dauke idaniwanta tayi akansa sbd bashi take buqatan gani ba,
Ammar ne na biyu wanda yanda ya koma ya sakata yin baya tana neman faduwa zuciyarta na kasa dauka sedai kafin ta ja wani numfashin aka fito da Dad dinta wanda ta ambaci sunansa da karfin gaske tana yi kansa da tsananin gudu wanda ya saka duka jamian tsaro da yan media dawa da kallansu akanta hakama kafin jamian tsaro suyi yunqurin tareta da sauri tini ta isa kan mahaifinta ta fada jikinsa da karfin gaske sukai baya zasu zube sbd baida karfi ko kadan Ammar dayake tsayuwa da qyar da sauri ya tsaya bayan Dad din yana taresu ta qamqame dad da wani irin karfin gaske wanda shima duk da baya gani sosai sbd azabar dasuke cikinta wata irin runguma yayi mata me karfin gaske yana cewa
"Jannah kece?????
Qanqamesa ta sake yi da karfin gaske tana ambatar sunansa kawai zuciyarta kaman zata tarwatse a gurin ta fasa wani irin kuka me tsanani karfin gaske tana kiran sunansa kawai bata iya cewa komai tana jin kaman Allah ya dauki ranta a gurin a jikin mahaifinta.
Shi kansa da baya ganinta sosai qanqameta yakeyi yana ambatar sunanta hannuwansa na tsananin rawa bakinsa ma na rawa..
Ammar ma juyawa yayi yana kasa kallanta kuka me karfin gaske yana zuwar masa kaman yanda Maheer ma kasa kallanta yayi kansa n qasa idanuwansa sunyi jajir.
Securities mata aka kira da sauri suka fito aka fara banbareta daga jikin dad dinta ta sake qanqamesa tana qin sakinsa tana tsananta kukanta tana kiran sunansa.
Kasa cireta daga jikinsa akai zuwa lokacin shima kukan yakeyi sosai sbd gabaki daya zuciyarsa matacciya ce akan 'yarsa..
Dukanta Securities din suka farayi tana qin sakinsa dan haka suka fara tsanantawa Ammar ya juyo da saurin yana rufeta jikinsa hakama Maheer dad ya rufe wanda shima ake dukansa sbd rufesu da duka akai ana kokarin rabasu jannah na sake riqe dad din wanda yake banbareta da jikinsa shima sbd a dena dukanta.
Ba tausayi aka rufesu da duka gabaki dayansu dan haka Dad ya saka karfinsa ya cinketa daga jikinsa akai saurin riqeta tana zubewa qasa cikin tsananin kukan dayake neman qare mata tana rintse idanuwanta bakinta na fidda jini.
Jansu akai zuwa ciki da karfi kowannensu bakinsa da hancinsu na fidda jinin dayake kona zuciyarta yana kasheta ahankali.
Sai alokacin aka fito da Anny da dr Abraham wanda zaa miqa kasarsu acan xai karba nasa hukuncin sbd acanma sun kashe rayuka akai ciki dasu Anny bata iya ko tsayuwa sbd daurin dayake hannuwa da kafafunta.
Ana shigewa dasu aka saketa tareda barinta zaune a gurin tana kukan da babu sauti sai numfashi kawai.
Duk yanda taso sake ganinsu baa bata damaba dan haka a gurin ta wuni sai dare ta koma gida zazzabi me karfi na cinta.
Kwantawa tai kawai bata iya komai sai jikinta dake rawar zazzabi har wani azababben bacci ya dauketa a gurin.
Tsakiyar dare cikin bacci taji motsi a kofa ta bude idanuwanta ahankali daqyar sbd nauyinsu ta motsa tareda dafawa ta tashi zaune ta miqe tsaye tareda nufar window datake jin motsi kullum tinda ta dawo kwana dakin kullum tana jin motsi kaman akwai wanda yake kwana kofar dakin dan haka yau bude window tayi kai tsaye.
"SALEEM" ta furta cikin tsananin sanyi da mutuwar jiki tareda kasa yadda da abinda idanuwanta suke nuna mata.
#MAMUH
ZAFAFA BIYAR
KALBIM 500
mamuhgee
A DUNIYATA 500
Huguma
AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul
KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo
Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi
Shedan biya
09033181070
Or mtn vtu at
09032345899*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
93
*SHOP WITH ME by RANO*
08030811300
Best children's clothing shop💯
https://chat.whatsapp.com/Gk4H76TlRgyAAWIWgx3Jo7
Kina neman in da zaki samun kayan yara classy kaya na yan gayu at a very