Showing 147001 words to 150000 words out of 185083 words
miki sauki har gida,
Karkice se masu kudi ke iya siya har kema me yar dama zaki samu naki da saukin kudi kuma best quality da kalar zamani data yan gayu,
Nidai Mamuh nace duk wadda ke son a buga gayun sallan bana da ita da 'yayanta to tazo gurin UMMU_MAHNOOR LUXURIES tai siyayyar sallanta harma zuwa gaba dan nasan zakuji dadi da fahimtar abinda nake fada akan kayanta💯💯
Abubuwan da zaki samu a gurinta with the best quality na wayayyun mata masu aji yan gayu sune;
Atampopi
Laces
Shadda
Materials
Shoes
Bags
Veils
Trolleys
Jewellerys
Oil perfumes
Numbers
08034469681
08135142610
Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries
*************
Mummy ganin yanda aka shige dashi itama taji kafafunta sun sare ta durqushe gurin tana fasa wani irin kuka mai tsananin gaske.
Itama Mimi kasa tsayuwar tayi tai baya Saleem da hannuwansa ke rawa ne ya tareta jikinsa yana rungumeta sosai jikinsa tana fasa kukan datake cikinsa duk tsawon lokacin nan da rayuwar Ammar take neman lalacewa.
Dzad ma Maheer ne ya riqesa da sauri a lokacin da Dr Abraham ya fito da sauri yana kallansu idanuwansa jajir sbd shima daddy mahmoud familynsa ne tinda ya dade da zama family ga zaadens,
Cikin tsananin ciwon abinda zai fada kansa qasa yace
"Sir Mzad ya riga ya tafi sai hakuri"
Wani Rikitaccen kuka me tsuma zuciya mummy ta sake hakama Anny datake jin zata zare cikeda tsoro da tashin hankali.
Mimi sake qanqame Saleem da hawaye ke gangaro masa itama tai.
Maheer ma rawa jikinsa yakeyi gabadaya idanuwansa sukai jajir suna masa wani irin radadi me ciwon gaske hawaye na cika cikinsu amma basu saukoba.
Dzad halinda daya shiga ya saka akai gaggawar yi kansa dan basa taimako kar ayi biyu sbd ba qaramar kauna me karfin gaske ce ba a tsakaninsa da dan uwansa da suka taso tare cikin gwagwarmaya ba uwa ba uba sai junansu da qanqarsu data fara tafiya tabarsu yanzu shima ya tafi ya barsa a lokacinda yake tsananin buqatansa sbd masifun da zuriarsu ke shiga batareda da sunsan ta inda abubuwan ke bullowaba.
Asibitin kuwa kusan tsit tayi sbd masu ita sunyi mummunan rashin daya girgiza ahalin gabaki dayansu,
Mummy kuwa Maheer ne ya dawo dashi da Mimi akanta suna kokarin ganin bata zare ba sbd yanda take kuka sosai kaman ranta zai fita.
Koda akai awa daya da rasuwar tini labarin ya fara gauraya koina anata sanarwa a kafafen yada labarai cikeda jimami da Alhini ga zadeens da akasan yanda suke tsananin kaunar junansu fiyeda sauran families.
A hanyar isowa gida Sayd ya kira AZIZ ya sanar da LIMBA Mahmoud Zad ya rasu.
Shiru sukai dukkaninsu batareda kowa yace komaiba sbd basu dauka Allurar anny zata kashesa ba a yanda tsarin yake idan taxo alluranta qarasa paralysing nasa zatai bazai iya magana ba tsawon lokaci to amma basusan wace alluran bace tai masa data kashesa duk da sunsan ba imani ne da Anny dinba amma bai taba dauka zata iya kashe wani daga familyn nasu ba.
Ahanya bude baki yace
"Allah ya masa rahama"
"Amin" Sayd ya furta yana qarasowa gidan.
Koda ya iso gida yayi parking ya fito a bakin Latif yaji labarin rasuwar ya kallesa da mamaki sai a lokacin ya fahimci labarin rasuwar ya yadu kenan.
Ciki ya iso ya wuce su mama a palo ya nufi palon AZIZ din yana isa ya sanar masa labarin rasuwar harya fita Jannah zata iya gani......
Sai a lokacin ya dago da idanuwansa ya kalli Sayd din.
Ajiye wayar hannunsa yayi tareda miqewa ya fice daga palon kai tsaye ya nufi bedroom din jannah wadda ya ajiye yabaro tana kukan batason nan gidansu takeso.
Yana isa dakin kai tsaye ya bude dakin ya shiga daidai lokacinda ta miqe tsaye da waya a hannunta kafafuwanta na daukan rawa kafin ganinta ya dauke ta saki wayar...
Taku daya yayi ya dakatar da ita daga faduwan da zatai yana kamo fuskanta da hannunsa daya dayan kuma yana zagaye da ita a karan farko daya bude bakinsa ya ambaci sunanta a natse yana dan girgiza fuskanta.
Bude idanuwanta da sukai jajir tayi tana kallansa ta fashe da wani irin kuka mai tsananin ciwo tana fixge jikinta daga nasa har tana baya da qarfi zata fadi ya sake dawo da ita jikinsa yana rasa abin fada mata sbd kukane takeyi sosai me sauti.
Falaq ce da suka samu labarin itama ta nufo dakin da sauri ta taddata tana wani irin kuka me tsananin tsuma zuciya.
Rasa ya zaiyi mta yayi gashi bakinsa baida abin fada dan haka ya matseta jikinsa a hankali yana jin yanda take turesa da karfi tana dukansa amma bai saketaba har saida ta gaji ta qamqamesa tana sake fasa sabon kukan dayake jinsa har cikin kansa.
Falaq ma qarasowa tai ta rungumeta ta baya tana hawayen tausayinta da kuma tausayin Daddy mahmoud din daya rasu dukda bata san radadi da zafin rashi ba sbd koda ta taso batasan mamanta ba daddynta dasu mama ta sani kuma haryanxu bata rasa ko dayansu ba amma duk da hakan tana kwatanta zafin da akeji sbd idan ta kwatanta rasa dayansu jin takeyi kaman bazata iya daukaba.
Tsit gidan limbas din yayi sbd jimamin tausayin Jannah da kukanta ke tashi a gidan cikin tsananin ciwon rashin datai sbd itama batasan radadin zafin rashi ba sai akan Daddy mahmoud din,
Zuciyarta a cikin wani irin radadi da ciwo tareda qunci take daman shiyasa kukanta ya kasa daukewa.
Ganin ta gaji da tsayuwar duk da a jikinsa take saiya zauna da ita tana jikin nasa tana cigaba da kukan falaq na gefenta tana shafa bayanta cikin tsananin tausayi da kauna me tsafta datake mata.
Shiru sukai aka bata damar kukan har tayi ta gaji karfinta ya qare ya ciro wayarsa ya saka kiran Dr Sameera wadda tazo ta bata magani tai mata allura jikinta ya sake a cikin nasa alamar bacci ya dauketa.
Sai alokacin ya dago fuskanta ya xuba mata idanuwansa yana kwatanta radadin da zuciya ke shiga a lokacinda ta rasa makusanci da kake kauna...
Yasan tana cikin radadin rashinsa tinda ubane a gurinta wanda suka taso a cikin zunubi da haqqin rayukan da suke kansu sbd kaunarsu gareta amma ya tabbatarda radadin dasukeji qalilan ne akan wanda yake ciki har yau akan rashin rabin jikinsa da sune suka rabasa da ita,
Baiso zuciyarsa ta kasance me tausayawa Ko mutum daya daga cikin ahalin nasu ba sbd halin da suka sakasa tareda ciwon dayake tattare dashi wanda har abada bayajin zai warke sai lokacin da Allah ya kaddari zaibi Yar uwarsa da iyayensa,
Kuka sukeyi da jin azababben radadin rasa mutum daya da sukai a cikin su da sukeda yawa,
Shi kuwa Ita kadaice dashi a duniyarsa kaf baida kowa bayan ita amma suka rabasa da ita..
Zareta daga jikinsa yayi ya kwantar yabar falaq ta rufeta ya fice daga dakin sbd a duk lokacinda wani zaiyi kukan rashi nasa radadin rashin dayayi ne yake dawo masa sabo tin daga kan mahaifinsa da Mahaifiyarsa zuwa kan Ummitansa da rashinta yake jijjiga rayuwarsa haryanxu.
Su mama ma sanyi jikinsu yayi wanda ya saka kowa ma gidan jikinsa sanyi.
Bacci tayi sosai na nutsuwar gangar jiki amma bana zuciya ba dan haka karfe uku tana farkawa Babu kowa a dakin ta kasa tashi tana neman wanda zai taimaka mata saiga Fiddausi tazo dubata sbd falaq na toilet.
Itace ta qaraso da sauri ta kamata ta rakata har toilet ta fito tabarta.
Ruwan zafi sosai ta gasa jikinta dashi wanda ya saka ta samu kuzari tai alwala ta fito ta shirya cikin doguwar Turkish Abaya tai sallah tana idarwa yana shigowa a shirye zai tafi janazah din da zaayi karfe hudu.
Kallo daya tayi masa ta dauke kanta wanda ya sanasa fasa fadar abinda zai fada ya juyawansa ya fice.
Yana ficewa ta miqe ahankali ta nufo kofa bayan ta zari key din motarta.
Ko data iso palo ashe bai riga ya fice ba dan haka bata tsaya kallansa ba ta nufi kofa kokarin ficewa ya bude baki a natse yace
"Ba inda zaki bakida lafiya so ki koma dakinki"
Taso wucewa ta kasa tankasa sai kuma ta tina da idan taje gate ko zata mutu idan bai bada umarniba bazasu bari ta fita ba dan haka ta juyo ta kallesa idanuwanta na cikowa da hawaye ta maida idanuwanta kan mama sbd bama zata iya masa magana ba ta bude baki muryanta na rawa tace,
"Mama inason na tafi gidan dan Allah"
Mama da duk tausayinta yake sake rufeta kama hannunta tayi tana karban key din hannunta da kulawa tace
"Maganar danake masa kenan yabarki kije,dan haka bakida lafiya bazakiyi driving da kanki ba can zamu dukanmu saimu tafi tare"
Shiru tai sbd so tayi ta tafiyarta ga familynta ita kadai sbd suna tsananin buqatan juna a yanzu.
Baice komaiba sbd umarnin mama koyaushe shine abinda baya musawa dan haka wucewa yayi gaba.
Mama tura jannah din tai gurinsa suka tafi a motarsa ita kuma ta tafi a mota daban itada Baba alhassan,
Falaq Daddynta yace babu inda zata daman itama tsoron zuwan takeyi hankalinta dik ya tashi.
A mota babu me magana shiru har suka isa Zaadens a lokacin ake kokarin fara janazah din dan haka jannah ce kadai ta wuce cikin gida shikuma anan suka tsaya wajen ayi dasu.
Tana shiga kai tsaye bangarensu Mummy ta nufa sbd kowa na can.
Kallo daya taiwa Mummy da Mimi wasu sabbin hawaye suka zubo mata da gudu ta qarasa ta rungume Mummy wanda har karfinta tas ya qare gurin kuka.
Anyi janazah din Mahmoud Zad a cikin radadi na rashinsa da akai an dawo,
Bazasuyi zaman gaisuwa ba dan haka ana dawowa kowa ya watse sedai masu zuwa suna tafiya,
Securities ne sosai acike da layin sbd manyan mutanen dake zuwa suna tafiya,
Acan cikin gida ma babu mutane tsit ne duk wanda yazo yai gaisuwansa tafiya yakeyi sbd basason zaman da hayaniya kadaici sukeso.
Su mama anan suka bar jannah wadda dataga da gaske zai iya cewa ta koma din kuma saita koma din dole ta roki mama ta sakasa barinta gidan ta kwana biyu.
Dan haka acan aka barota daman shi tin daga gurin janazah bai dawoba ya wucewansa.
Familyn Mummy dake Germany sun iso gaisuwa da tsayawa Mummy din wadda gaba daya ta shiga wani hali na rashin Mijin datake tsananin so yana tsananin sonta sbd itace bata haihuwa amma bai taba damuwa ko raayin aureba sbd samun haihuwa sbd kawai girman son da sukewa juna ya yadda ya zauna ba haihuwa yayan dan uwansa da yar uwansa sun ishesa.
#MAMUH
ZAFAFA BIYAR
KALBIM 500
mamuhgee
A DUNIYATA 500
Huguma
AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul
KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo
Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi
Shedan biya
09033181070
Or mtn vtu at
09032345899*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
79
*UMMU_MAHNOOR LUXURIES*
(Best luxuries shop)
08034469681
08135142610
Aslm Alaikm ina kuke masu neman luxuries na kayan alfarmar kece raini?
Ina masu son su saka sitirar alfarma ta zamani ta manyan mata masu aji da zaa kalleki kallo daya asan sitirar alfarma e kika saka?
Shin kunsan me ake nufi sa kayan asalin yan gayu da nuna gayu?
Sitirar Alfarma kikeson sakawa?
Sitirar da kike ganin manyan mata da ita?
Sitirarda zakiyi gayun sallah dake da yaranki a dauka waje kikaje da kanki kika siyota?
To kizo ga damarki ta sameki sbd UMMU_MAHNOOR LUXURIES ta kawo miki sauki har gida,
Karkice se masu kudi ke iya siya har kema me yar dama zaki samu naki da saukin kudi kuma best quality da kalar zamani data yan gayu,
Nidai Mamuh nace duk wadda ke son a buga gayun sallan bana da ita da 'yayanta to tazo gurin UMMU_MAHNOOR LUXURIES tai siyayyar sallanta harma zuwa gaba dan nasan zakuji dadi da fahimtar abinda nake fada akan kayanta💯💯
Abubuwan da zaki samu a gurinta with the best quality na wayayyun mata masu aji yan gayu sune;
Atampopi
Laces
Shadda
Materials
Shoes
Bags
Veils
Trolleys
Jewellerys
Oil perfumes
Numbers
08034469681
08135142610
Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries
*********
Ranar da akai kwana uku da rasuwar sawun ya zuwa gaisuwa ya dauke suka koma iya su familyn,
Dad jikin nasa sai ahankali shima sbd damuwa me girman gaske ce ta cike zuciyarsa ya kasa cirewa dan haka gabaki daya walwalar familyn ta dauke basa cikin farin ciki ko kadan,
Ammar ma andawo dashi gida sbd gabaki daya dai kansa ya juye suke gani haryanxu sunan AZIZ LIMBA ne a bakinsa.
Mummy a ranar da akai ukun da yamma bayan angama addua ta buga waya cikin rashin bata lokaci saiga motocin Dss kusan guda biyar sun iso Zaadens sun zagaye gate din da gefen gidan.
Anny suka taho kamawa a bisa tabbacin itace ta kashe Mahmoud Zad.
Mummunan tashi hankalin Su Dad da maheer yai harma da Mimi da dukkaninsu.
Sai a lokacin Mummy ta fito ta nuna babu wani sulhu ko tsayawa sauraron bayani komai Anny ce ta kashe Mahmoud kuma dole zata karbi hukuncin hakan sbd a gaban saleem ne shima gani,
Jannah ma da mijinta sun gani hakama yan aiki duka shaida ne,
Zata tabbatarda Anny ta karbi hukuncin kisa akan abinda tai idan kuma akwai wanda ya isa ya tsaya mata zasusha mamakinta sbd gabaki daya dukiyarta da itace share dinsu datake riqe dasu ayanxu zata janye ta kuma yi sharia dasu da dalili a lokacinda basuda karfin ko power din iya fada da ita sbd sunsan ita din ko wace.
Wannan itace sabuwar masifar data diro musu wadda ta saka yan jarida fara yada labarai akan zaadens din.
A lokacin da zaa tafi da Anny din kasa yadda tayi da hakan tai gaggawar boyewa bayan bayan Maheer tana riqesa hannuwanta na zuba wata irin rawa cikin matsanancin tsoro da tashin hankali me girma tace
"Maheer wlh banyiba,dan Allah karka bari su tafi dani,
Bazan iya zuwa prison ba dan Allah karka bari su tafi dani"
Komawa tayi kan Mimi tafara rokonta idanuwanta kaman zasu fito sbd tashin hankali da firgicewa.
Kan dad ta koma ta zube qasa tana kama kafafunsa cikin tsananin kukan tashin hankali tana cewa
"Dad wlh bansan zai rasa ransa ba,banyiba dan Allah karka bari su tafi dani"
Mummy da idanuwanta suka gama rufewa da tsananin fushi da bacin rai me tsananin gaske takowa tayi ta dago Anny din ta saukar mata da lafiyayyan marin daya sakata zubewa qasa hancinta na zubo da jini.
Da sauri Maheer yayi kanta ya dagota jikinsa yana rungumeta ya dago ya kalli Mummy din idanuwansa jajir yace
"Mummy baa zartar da hukunci a cikin fushi batareda bincike me kyau ba,
Tayaya zamu bari muna matsayin family irin wannan matsalar me girma ta fita zaa iya bincike a gane a magance cikin gida......."
Cikin mamaki sa sabon bacin rai Mummy ta kallesa kafin ta maida kallanta kan Dad daya kasa cewa komaiba sbd yafara jin inama shine yabar duniyar ya huta da wannan baqin cikin dayake zuwa wani bayan wani
Tace
"Dzad kanajin abinda Maheer yake fada akan mutuwar dan uwanka wanda kake ikirarin rabin jikinka bakada kamarsa?
Kana jin yana cewa a rufe maganar wadda ta kashe Mahmoud sbd tana matarsa,
Wannan shine adalci ko sakamakon da Mahmoud zai samu daga gareku?bayan duk sadaukarwa da zunuban daya dauka sbd kai da yayanka Dzad?
Wasu hawayen baqin ciki ne suka zubo mata a cikin tsananin fushi ta fixgo Anny ta jefawa Dss da take suka kameta aka saka mata cuffs tana wani irin kuka da ihun tashin hankali me tsananin gaske sbd tsoron a kasheta itama.
Dad dagowa yayi ya kalli Mummy ya bude baki yace
"Nafeesat nasan Zuciyarki tana cikin zafi da radadin rashin Mahmoud kaman yanda nake ciki amma hakan bashine mafita ba,
Qarawa kanmu matsaloli zamuyi bayan bamu magance na gabanmu ba,
Zamu bari duniya tai mana dariya ne maqiyanmu zasu samu damar sake cutatar damu dan haka ki janye ya saki Anny zamu ji da matsalar a nan cikin gida"
Kallan dayake kama dana tsana Mummy kewa Dzad din tana jin baqin cikin sadaukarwa da zunuban da Mahmoud ya ringa dauka akan dan uwansa harya bar duniya gashi yanxu dan uwan nasa ne ke bude baki yana cewa ayi shiru akan wadda ta kashesa.
Bata iya cewa komaiba juyawa tai tabar gurin ta nufi bangarenta bayan anwuce da Anny wadda ta zare take.
Mimi da idanuwanta suka bushe har hawaye sun qafe mata juyawa tayi ta koma ciki jikinta a tsananin mace kirjinta na mata ciwo itama.
Jannah ma bayan Mimin tabi itama kirjinta na matsa tsananin ciwo me dacin datake jinsa har bakinta.
Maheer kadai aka bari harabar gidan bai iya motsawaba yana jin duniyar na juyawa dashi sbd tsananin quncin daya rufe zuciya da idanuwansa gabaki daya.
Mummy Former spokesperson a Germany hakama ta zauna matsayi me girma a italy dan hakama familynta duka yan boko ne sosai dasukeda manyan matsayi da arziki sosai itama dan haka koda ta dena aiki tana da arziki sosai wadda ta zuba rabinsa a business din zaadens dan haka kusan arzikin zaadens din tanada share me girma a cikinsa,
Yanzu daga baya da suka samu matsalar da aka samu sauran shares dinta dake wasu manyan companies ne ta karba ta bayar aka hada maja da LIMBAs dan haka a wani bangaren dai kusan dukiyarta ce yanzu a zaadens din take riqe dasu hakama tanada sauran kadarori da wasu shares din masu girma a wasu guraren dan haka kai tsaye a yanzu a halinda suke ciki sunsan ja da ita zai musi wuya shiyasa dole lallabata zaayi ta janye dan basuda power din fada da ita da familynta.
Kwanan damuwa me tsanani akai a zaadens wanda ya saka jannah tashi da rashin lafiya.
A waya falaq taji yanayin Jannah dan haka ta shiga damuwa itama.
Karfe goma da mintina Su Dr Abraham sika iso Zaadens sbd yanayin jannah wadda haryanxu ma basu samu dubata dinba.
A daki na musamman da aka ware sbd jinyar family members na zaadens tamkar a asibitin lafiyayye acan aka kai jannah wadda ta laushi sosai sbd damuwar datai mata yawa.
A daidai wannan lokacin ne motar AZIZ LIMBA ta iso gidan aka bude masa gate ana masa barka da zuwa.
Parking Sayd yayi ya bude masa ya fito suka nufi ciki Saleem daya fito tarbansa ya gaidasa cikeda girmamawa suka nufi dakin da aka kai jannah din.
Abraham ne yake dubata dan haka hankalinsa gabaki daya yana kan Jannah din...
Ken dayake tsaye yana duba monitoring heart dinta a injin kaman a mafarki idanuwansa suka dago cikin slow suka fara sauka akan fuskar AZIZ AY LIMBA wanda ko zaa zare ransa a dawo masa dashi bazai mantasa ba,
Kasa motsawa yayi kansa da jinin dayake yawo a jikinsa suna tsayawa daga kowane motsi ahankali idanuwansa akansa kaman yanda yake kallansa shima idanuwansa a cikin nasa suke yana masa kallan dayake dauke masa ji da ganin komai daidai.
Bayyanar Sayd a bayan AZIZ din ya saka hannuwansa sakewa
Sai ganin akai jini na gangarowa daga hancinsa ahankali me kauri.
Cikin Mamaki