Showing 177001 words to 180000 words out of 185083 words

Chapter 60 - Kalbim Book 1 Complete Hausa Novel

Mamuhgee   

23 Sep 2025

5494

shikenan zaa sallameta,

A wani kauye tayi rayuwa me tsayi sosai inda maigarin kauyen ya aureta duk da batada hankalin shi dai tai masa ta kwanta masa yana kaunarta,

Bai taba komai da ita sbd magani da aketa nemar mata tsawon shekaru har Allah ya dauki ransa yabar duniya bata warke ba dan haka yayansa da matansa suka koreta ta sake shiga duniya wanda duk tsawon wannan lokacin bata taba dena ambatar sunan 'yayantaba.


Jannah sake qanqameta tayi tana jin nutsuwa itama ayau ta samu wanda ta runguma tana sauke hawayen samun sassaucin abinda yake cin rayuwarta na tsananin kadaici da qunci.

Ahankali Umman tafara rage kukanta yanayin qasa tana ambatar sunan Ummi wanda ya saka jannah amsawa dole sbd bata damar dawowa hayyacinta har ta dena kukan tayi shiru a jikin Jannah wanda itama tayi shiru babu me motsi a cikinsu har akai ishai suna hakan.

Ahankali jannah ta janye jikinta ta miqe ta kamata suka koma suka sake alwala suka dawo sukai sallah
Suna idarwa abincin ta sake janyowa ta kama hannunta ta saka mata a cikin abincin suka fara ci Ahankali kowannensu jikinsa a sanyaye har suka gama.

Tattara gurin jannah tai ta shiga toilet tayi wanka ko data fito Umman tai bacci daga inda take zaune cikin tsananin gajia da zazzabi.

Cikin tausayi jannah ta gyara mata kwanciyarta kafin itama ta saka doguwarta har qasa ta bacci taxo ta kwanta gefenta suka rufe da abin rufa guda duk da ya musu kadan.

Kaman yanda akace mutum rahama ne hakan ne ya faru ga jannah sbd ayau datake tareda da wani ba ita kadaiba kaman yanda ta saba bacci ta samu yau din ya dauketa har safe wanda rabonta da hakan ta manta.

Da asuba sallah sukai suka sake kwantawa Umma ta ringa baccinta hankali kwance Jannah ta zuba mata idanuwanta ahankali tana kallan fuskanta kafin ta gangaro da idanuwanta akan hancinta da gurbin idonta datake samun Kammanin wanda yake maqale a zuciyarta a lungu ta boyesa boyo na har abada da bazata fidda ba kuma bazata farfado ba.


Numfashi ta sauke ahankali wasu hawaye masu dumi na gangaro mata na Saleem da har abada bazata yafewa limbas ba idan suka raya tasu yar ta hanyar rabasa da tasa rayuwar.

Meyasa saleem zai mata hakan?
Meyasa ya zabi barinta a lokacinda tafi komai da kowa buqatarsa,
Rashinsa ya sakata jin rashin tsoro da shakkar janyo matarda bata saniba a jikinta tana samun nutsuwa da ita,
Rashinsa ne ya sakata takejin matar da batasaniba a cikin ranta harma da tinanin inama uwartace.

Sauti kukanta yafara ta saka hannuwanta biyu tana rufe bakinta tana juya baya kirjinta na nauyi.

Kukan kewan iyayenta tayi sosai tareda tsananin kewar uwa datake tsananin buqata har jikinta na rawa kirjinta ciwo yake mata sosai tana sake rufe bakinta da hannuwanta....

Ba tsammani taji saukan hannun Umma a bayanta tana shafa bayanta ahankali jikinta a sanyaye tana jin kukan jannar har cikin ranta ta bude baki a hankali tace

"Ummah batason kina kuka,
Ki dena kuka kinji Umminah"


Bude idanuwa jannah tayi tana kasa kallanta sedai tana jin yanda take rarrashinta cikeda kulawa har cikin ranta dan haka ta dakata da kukan tana rufe idanuwanta daga kwancen suka sake shiru tsawon lokaci har suka dawo daidai kowannensu kafin jannah ta miqe ta duba abincin datake dashi bread da lipton da ruwan zafin heater ta toilet sukasha sukai wanka ita kadai ta sauya kaya a cikin kayanta da suka fara ganin rayuwa suma,
Umma kuma sbd ba kaya hakanan ta maida mata dana jikinta ta kama hannunta suka fita.

Gurin dubo su Dad sukaje sukai wunin banza baa bari suka gansu ba haka suka dawo.

Koda suka dawo bread da lemu suka sake ci Umma ta bige da baccin wahala.

Shiru jannah tai tana jin inama itace take samun irin wannan baccin.

Da dare gurin me abincin data bada kudin masu yawa tintini karbowa kawai takeyi taje ta karbo musu abinci mama na biye da ita kafa da kafa kamar qaramar yarinya.

Suna dawowa sukaci abincin suka koshi suna gamawa suka kwanta jannah ta jima zaune bacci bai dauketa ba sai daga baya.


Washe gari haka suka sake fita yawon garari taje da Umman inda suka hadu dan neman wanda ya santa amma sam babu kowa sai cewa yakeyi batada hankali motar zuwa wani garin neman yayanta take nema.

Haka suka dawo a gajiye suka kwanta,

Hakan ta kuma faruwa washe gari yawon neman wanda ya san Umma ta ringa yi kwana biyu cikin wahala da azabar yunwa da rana amma sam babu wani haske zancen daya ne mahaukaciyace ake ce mata.

Jin tayi a zuciyarsa Umman na samu wani matsayi da gurbin uwar datake tsananin nemarwa kanta,
Idan mutane na kallan Umman mahaukaciya mara kowa da baa san inda ta fitoba ita a ido da zuciyarta kallo da matsayin uwar datake nema ne Allah ya jeho mata,

Idan Umma batada kowa itama batada kowa zata riqeta a matsayin Uwa,abokiyar rayuwa kuma sabon ahalin da zata ginawa Zaadens,

Shigowan Umma rayuwarta tamkar wata rahama ce Allah ya kawo mata sbd tsananin son da umman ke mata duk da bata yadda ba umminta bace hakama itama kallan Miminta take mata dan haka tai Alqawarin riqeta su bawa juna sabuwar rayuwa tamkar jini daya,
Zata zamo Zaadens zata rayu a cikinsu su bata sunansu,zasu bata gurbin Miminsu da suka rasa da yardar Allah.

Da wannan ta budewa Umma zuciyarta gabaki dayanta ta karbeta kaman yanda Umman tin ranar farko bata dena mata kallan kauna me karfi ba hakama kaman yanda take a baya komai Hamma ne ke musu suna biye dashi kaman yayansa a yanzu ma biye take da jannah sawu da sawu koina tana gudun ta sake bace mata wanda hakan ke sake kashe zuciyar jannah akan Umman.


Kowace safiya idan suka samu abinda suka ci wanka sukeyi su fita hannun Umman na cikin na jannah riqe su bazama yawon zuwa gurin su Dad wanda aka fara sharia me karfi akansu.

Duk zuwan da sukeyi Hannunta na riqe dana Umma wadda tausayinta da kaunarta ya cikasu sbd ta zamo mutum daya kacal da Jannah take samun sassaucin qunci sbd ita duk da Batada hankali basu damu da hakan ba suma kamar jannah kallan cikakkiyar mutum suke mata sbd kaunar datakewa jannah a bayyane take daga nata bangaren.


Ammar ne kadai ya kasa dawowa daidai sbd rasuwar Mimi data kasa sakinsa dan itace tamkar uwar data haifesa a rayuwarsa.

Yawan zuwan dasuke ahankali ahankali Ummah ta fahimci Masoyan Jannah ne suke xuwa gurinsu dan haka itama tafara sabo da zuwa garesu din.
#MAMUH


ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
95
*SHOP WITH ME by RANO*
08030811300
Best children's clothing shop💯
https://chat.whatsapp.com/Gk4H76TlRgyAAWIWgx3Jo7

Kina neman in da zaki samun kayan yara classy kaya na yan gayu at a very affordable price? Ko kina son fara kasuwancin kayan yara amma baki da jarin da zaki saro kayan? Nesa ta zo kusa, kiyi joining community din nan muna saka kaya masu kyau available da inganci a farashi me sauki da zaki dauka ki tallata har ki samu naki kema.
Burinmu shine kowacce mace ta samu sanaar da zata dogara da kanta.


*************
Ahankali rayuwa tafara tafiya wata irin shaquwa me karfi da kauna me tsafta da tsananin karfi ta shiga tsakanin Ummah da jannah wadda ta koma kaman Uwar data haifeta take jin Umman,

Komai na rayuwar Umman itace takeyi mata shi a yanzu cikeda kulawa da tattali,
Itace tsaftace mata gashinta da tsaftar jikinta tareda farcenta da komai nata,

Batada karfin siya mata sitira da wasu abubuwan dan hakan a cikin gidan ta shiga ta samowa Umman Kayan Mimi kusan guda biyar wainda da sune rayuwar take tafiyar musu yanzu,

Shigowan Umma rayuwar jannah ta samu sassaucin qunci da damuwar datake ciki sbd tanada me debe mata kewa,

Umma duk da batada cikakkiyar hankali amma ba hauka takeyiba idan dai ba yanayinta yaso tashi bane idan taso ganin hammanta wanda babu sbd tini Jannah ta riga ta cika gurbin Ummi amma kwata kwata bata son ganin hawaye na fitowa daga idanuwan jannah ko kadan koda kuwa itace ta sakata hawayen sbd idan ciwonta ya tashi taso ganin hamma babu tasha yiwa jannah rauni wanda daga baya zata dawo tana kukan raunin jannah din,

Wata sabuwar babin azabar ce ta bude a rayuwar jannah ta bangaren ciwon Umman sbd sosai take fita hayyacinta tayiwa jannah abinda da yawa jini ke fita a jikinta amma a hakan jannah taji ta gani ta zabi cigaba da kaunarta har ranta bazata taba iya rabuwa da itaba sbd hakan sbd idan Miminta ce ahakan bazata taba guduntaba hakama ta tabbatarda idan ma ummi ce ko hamman bazasu gujeta ba dan haka ta rungumeta a hakan bata taba gajiyawa ba.

Ta bangaren shariarsu Dad sosai komai ya dauki zafi duk ranar shiga kotu suna zuwa itada Ummah,

Ita kanta Ummah ta samu kanta a kaddarar da batada dadi ta qunci da tarin baqin cikin rayuwar da Zaadens suke ciki sbd ahankali ahankali quncin dasuke ciki ya shigeta itama kwata kwata ba walwala ba farin ciki sai kuka yunwa azaba da baqin cikin da babu ranar fitarsa amma duk da hakan bata taba jin zata iya barin jannah ba wadda a take kira da Ummijan sbd Jannah ta kasa yadda da Ummin ita kuma Umman ta kasa yadda da jannah kadai saita hada da ummin.


Lokaci yafara tafiya sosai ahankali yanayin shariar ya fara sauya salo wanda yake farin ciki da baqin ciki tareda tashin hankali sbd samun nasarar su Dad na nufin Saleem Zad ya sadaukar da rayuwarsa ga limbas.

Wannan tinanin ya saka jannah shiga firgici da sabuwar damuwa me tsananin gaske gashi sunfara kaiwa maqura a rashin komai,

Abincinta da zai dade bata nemaba sbd yawan kudinta a gurin me abinci ya rage yawa ne sosai sbd yanzu ba ita kadai bace dan haka tafara zuwa aiki gurin me abincin data nuna mata zata dauketa aiki.

Itada Ummah suke zuwa aikin wanke wanken kayan abincin da aikin su fere dankali da doya haka da wanke kayan miya dasu cabbage.

Ajiye Ummah takeyi gefe ta hanata komai itace me aikin wanda idan suka wuni suka dawo da dare bata iya bacci sbd azabar ciwon jiki sai ahankali Ummah ta gane abinda yake hanata bacci dan haka kullum suka dawo zata kwantar da ita ta ringa mata tausa cikeda kulawa da kauna ahakan Jannah ke samun dan bacci ya dauketa Ummah xata zauna ta ringa kulawa da ita tana fita har safe tukuna ita kuma idan sukaje gurin aikin ta kwanta tai nata baccin da bata samu da dare ba Jannah na aiki.


*******Ayau da zaa shiga tinda safe taje tai aikin da zatai sauran ta sanarwa Madam dinsu zuwanta kotu dan haka ba musu ta bata damar zuwa.

Suna gamawa sharp sharp ta fito itada Ummah suka kama hanyar kotu tana jin kirjinta na wani irin nauyi hakama hannuwanta har wani rawa sukeyi.

Ummah ce ta kalleta a natse taga yanda duk take fita hayyacinta sbd fargaba kaman koyaushe idan zasu shiga kotun haka take sbd tsananin tsoron koyaushe zaa iya cewa yau an yankewa ahalinta hukuncin kisa.

Wannan tinanin kadai rabata da nutsuwarta yake yana sakata shiga mummunan yanayin datake neman zarewa.

Ahankali Ummah ta kwantar mata da kanta a jikinta tana shafa bayanta ahankali tana cewa

"Zamu dawo dasu gida,
Zasu biyomu gida"

Koyaushe Ummah ta fada mata hakan jin takeyi tana samun yar nutsuwa da qwarin gwiwa duk da abu ne me wuyar gaske amma bata dena fadawa Allah ba itada Ummah koyaushe Adduarsu kenan.

Koda suka isa kotun guri sika nema kaman koyaushe suka zauna jiran isowan su Dad daga gidan yari kafin judges.

Zaman kusan awa daya sukai kafin aka iso dasu Dad din kowannensu ba kyan gani musamman Ammar da gabaki daya ya fita hayyacinsa,
Ya koma kamar me ciwon sida ya bushe ya qanjame ya koma kamar wanda aka ciro daga rami,

Maheer komawa yayi kamar mahaukacin dayake cikin tsananin qazanta,
Dad kuwa ganinsa kwata kwata sai ahankali har wannan lokacin gashi su Maheer sun fisa jikin kuruciyar jure azaba da wahala.

Dr ken kuwa yana gap da rasa ransa gava daya sbd kafarsa dai ta rube taimakon gaggawa yake buqata idan ba hakan ba zai iya rasa ransa.

Anny ma kwata kwata batada kyan gani gashi mahaifinta shima case din ya biyo ta kansa tinda duka akwaisa a ciki wanted ake nemansa ido rufe amma ya boye baasan wace qasar yake ba.

Miqewa Jannah tayi tsaye itada Ummah suna kallansu Dad din cikeda kauna da kewansu dake kasheta kowace daqiqa.

Zuba musu idanuwanta dake cikowa da hawaye tayi tana musu kallan dayake kasheta sbd yanayinsu abune dayake yankar zuciyarta.

Matsowa tayi tanason ta kama hannun mahaifinta ko zai samu sassaucin abinda yakeji itama ta samu sassaucin quncin dayake cin ranta amma aka dakatar da ita ahankali ta ambaci sunansa sautin ya shiga kunnensa ya dago yana kallan inda take baya iya ganinta sosai amma dai ya zuba mata idanuwansa yanajin sanyi yana dan ratsa ransa da ruhinsa.

Ammar ma kallanta yayi yana jin baqin cikin da radadin halin da suka sanyata,

Maheer ne kadai ya iya bude bakinsa ya sakar mata wani murmushin wahala daya sakata sunkuyar da kanta tana tsiyayo hawaye masu zafi.

Ciki suka isa suka zauna Ummah na gefenta riqe da hannunta cikin nata tana share mata hawaye kaman zata ciro ciwon da Jannah din ke ji ta dawo dashi kirjinta.

Shariar yau itace wadda ake saka ran zaa yanke hukunci dan haka dukkaninsu kowa jikinsa yake a mace babu iya dago kai ya kalli dan uwansa jimami da ciwo me radadi ne yake cike kirjin kowannesu,

Kowannensu halinda Jannah zata shiga a rashinsu ne yake cin ransu da kuma rashin sanin me zasuje su tarar a gaban ubangijinsu akan abinda suka aikata sbd sun riga sun saddakar ga hukuncin kisan da zai iya hawa kansu.

Bayan gama gabatar da sauran jawabai da manyan lawyers sukai da duka abinda aka hada dana fili da wanda akai bayan fage kotun tayi tsit a lokacinda babban alkali yake gabatar da hukuncin karshe na case din.

"Bisa bayanai da dukkanin shedu na fili dana rubuce tareda kundun bincike da tabbaci da komai akan case din kotu ta yankewa dukkanin likitoci da Nurse da sukai aikin hukuncin kisa ta hanyar rataya banda Dr Ammar Zad wanda dukkanin bayanai da likitocin da aka saka suka dubasa sun tabbatarda baida cikakkiyar lafiyar kwakwalwa maana baida hankali dan haka Dzad,Maheer zad da Ammar Zad Zasuyi zaman shekara Daya gidan yari tareda aikin wahala me tsanani na horo a gidan yarin hakama kotu ta karbe dukkanin abinda suka mallaka na koina dan biyan diya ga rayukan da aka salwantar da hanyarsu hakama har abada kotu ta soke lasisin karatun Ammar zad na likitanci harma da sauran...."


Jannah da zuciyarta ta dena bugawa a farkon maganarsa ta yanke hukuncin kisa ga likitocin jin banda Ammar zubewa qasa tai tana fasa wani irin kuka mai tsananin gaske ma samun dawowan rayuwarta daidai sbd saura kadan ta rasa ranta daga wannan hukuncin wanda ya sumar da dukkaninsu su Dad din suma sbd jin hukuncin da suka dauka hadda Ammar wanda bazasu iyaba zasu gwammaci a rataye su su dukan.

Jin badashi ba Maheer ya fasa wani irin kuka mai tsuma zuciya daya saka Dad rungume Ammar jikinsa na tsananin rawa take ma yaji zuciyarsa ta kasa daukan mummunan shock din da suka shiga na dan lokaci ya dafe kirjinsa jikinsa na neman sakewa daga na Ammar din wanda ya kwata kwata baima cikin hankalinsa shi.

Rungume jannah Ummah tayi da sauri tana fasa kuka itama ganin yanda jannah ke kukan tsananin ciwon daya danne kirjinta wanda ta tabbatarda Saleem Zad yabarsu tinda aka yankewa Ahalinsu wannan hukuncin me sassaucin da sun tabbatarda akwai abinda akai.

Kukan farin ciki da tsananin ciwon zuci ne takeyi lokaci daya tareda tinanin tayaya zata iya fadawa su Dad Sun rasa saleem shima wanda har abada bazai dawoba sun rasasa kaman Mimi.

Anny kuwa yanke jiki tai ta fadi a gurin hakama dr ken wanda take yafara shure shure zuciyarsa na neman bugawa,

Hakama dr Abraham a rana daya zaa ratayesu dashi da 'dansa acan tasu qasar suma wanda ahalinsu ke cikin tsananin tashin hankali mai girma.

Ammar zuri yayi baima da abin fada ko yi sbd ba komai yake ganewa ba ko fahimta wasu lokutan.

Tattarosu akai zaa fita kotun dasu jannah ta miqe da sauri har tana faduwa ta nufesu da gudu ta kamo hannun Dad dinta da ake riqe dashi baya iya tsayuwa sbd hawan jininsa da yayi mummunan tashi.

Da hannuwanta biyu dake tsananin rawa ta sake qanqame hannuwansa da ake banbareta cikin wani irin kukan quncin daya gama rufeta da dabaibaye rayuwarta muryanta na rawa cikeda wani irin kukan daya saka Dad din fashewa da kuka shima tace

"Dad Zan jira ranar fitowanku,
Zan jira Dad,
Dad duk tsanani duk wuya ku tina ina nan ina jiran fitowanku,
Dad dan Allah ka daure duk wuya ka fito inanan ina jiranku"

Kuka Dad din kawai yakeyi yana jin kaman kirjinsa bazai iya daukan kukanta da maganganunta ba dan shikam kila bazai fito ba sbd bayajin yanada wata shekara guda din a gaba sedai ko Su Maheer.

Cireta akeyi anason rabasu tana tsananta kukanta tanajin kaman zuciyarta ce ake kokarin rabata da ita sbd a hukuncinsu babu ziyara daga nan har ranar fitowansu.

Su kansu dukkaninsu kuka sukeyi sosai banda Ammar da kansa ya juye baya iya komai yana tsaye yana kallan Jannah dake shidewa tana jin kaman ranta ne zai bar jikinta.

Ummah ma riqe jannah tayi sosai tana kuka tana janta jikinta tana dukan wainda suke kokarin banbare jannah din daga Dad dinta.

Dukkanin masu tausayi da raunin zuciyar dake kotun sauda suka tausayawa jannah cikeda tsananin sanyin jiki wasu hadda kwalla.

Saida aka gada da karfi da duka aka iya rabasu da ita ta zube qasa a gurin tana fasa kuka me tsananin radadi da ciwo tanajin zuciyarta na mutuwa.

Ummah dake kukan itama rungume jannar da bata hayyacinta kwata kwTa tai tana share mata hawaye tana kiran sunanta.

Tana kallo aka sakasu mota aka rufe aka tafi dasu tafiyar da sai bayan shekara guda zata sake ganinsu,
Tafiyar da batasan ko zata sake haduwa dasuba sbd azaba me tsananin da zasu tarar a zaman gidan yari,
Tafiyar da basusan cewa Saleem suka rasaba suka sameta.

Motar na ficewa daga harabar kotun idanuwanta suka rufe ahankali ta some a jikin Ummah dukkaninsu jikinta na sakewa.

Taimakawa Ummah akai aka fitar dasu kotun zuwa waje acan Ummah sbd kan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login