Showing 114001 words to 117000 words out of 185083 words

Chapter 39 - Kalbim Book 1 Complete Hausa Novel

Mamuhgee   

23 Sep 2025

5483

zaunar dashi tana kulawa dashi tana rarrashinsa tareda masa adduoi.

Jannah ma sosai take basa kulawan duk da baicewa kowa komaiba kwata kwata yaqi bude baki yayi magana sbd har lokacin bai gama dawowa hayyacinsa ba kawai dai ragewa yanayin nasa tayi.

Su Dad ma duka sunzo sun dubasa da rarrashinsa har kusan 10 kowa na dakin kafin kowa ya fice Mimi saida taga ya samu bacci ta bar dakin ta koma dakinta tareda jannah wadda itama duk ta damu.

Haka suka kwana cikin yar damuwa sbd ga jannah dinma LIMBA yaqi cewa komai akanta amma tinda ba sauri sukeba suma sai basu masa magana ba dan su basuqi yabar musu ita din anan ba tai zamanta dan haka basuma yi tinanin masa maganaba.


Washe gari koda Ammar ya tashi ya dawo hayyacinsa Amma zuciyarsa ke tsananin ciwo da zafi dan haka ko fitowa baiyiba hakama rife kansa yayi a daki bayason kowa ya shigo bayan Mimi da jannah babu wanda yakeson gani.

Baa takurasa ba Mimin ce kadai sai jannah din ke shiga.


*****acan gidan kuwa Falaq ta damu da zuwan Jannah gidan mama ma da bata samu ganinsa ba tin jiyan sai yau kallansa tayi lokacinda ya fito daga hanyar bangarensa a shirye cikin brown Armanis da wayoyinsa a hannu da ipad sai qaramar jakar laptop dinsa
Sayd ya qarasa ya karba yana ficewa dasu zuwa mota tace

"AZIZ badai tafiya zakaiba??

Fararen idanuwansa ya saukar yana cewa

"Mama barka da safiya"

Amsawa tai tana sake jefe masa tambayarta cikeda mamaki
Yace

"Wani aiki ne me mahimmanci da dole saina isa gurin amma insha Allah kwana biyu ne ba jimawa zaayiba"

Sake shiga mamaki mama tai tana cewa

"To Jannah dinfa?
Tin jiya mukaita jiran maganar daukota da yan kawo amarya amma shiru harsu maryam suka gaji suka tafi
Yanzu kana maganar tafiya batareda ankawota ba idan ka tafi waye zai kawota to?

Falaq datake fitowa dakinta da sauri sanye da kayan bacci tayo gurinsa jin ana maganar tafiya tace

"Daddy tafiya zakai?
Nidai to a kawo jan kafin ka tafi"

Kallanta yayi itada maman kafin ya bude baki a natse dan bayason maimaita zance yace

"Idan na dawo zata taho amma yanzu zata zauna acan saina na dawo ayi maganar komai okay?

Bata fuska falaq tayi amma kuma ta gyada kai tana cewa

"Okay,Amma Besty karka dade kaji?

Shima gyada mata kai yayi yana shafa fuskanta yana cewa

"Banda yawo da gudu or tsalle tsalle"

Mama ma rasa abin fada tai sbd tasan tinda ya fada dole saiya dawon tinda baa shirya komaiba harna inda Jannah din zata zauna dan haka zata bari ya dawo amma idan ya wuce lokacinda ya kamata da kanta zata ta dauko jannah din sedai ya dawo ya taddata gidan nan.
#MAMUH
#BESTLOVE
#CRAZY LOVE
#FAMILY
#AZIZ AYOUB LIMBA
#JANNAH ZAD
#AMMAR ZAD


ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
61
Har mota Falaq ta rakasa tana jikinsa lafe idanuwanta na son narkewa sbd batason ya dade.
Sayd daya bawa latif luggage din AY din set biyu na akwatin LV babba da qarama kallan falaq din yayi yana cewa

"Keda kikeda wata bestyn meyene zakiyi kukan bakyason ya tafi"

Tura baki tai tana kallan Daddynta tace

"Daddy kaga Uncle ko?

Zagayota yayi da hannunsa a gefensa datake cikeda tsananin kulawa da kauna yace

"Kyalesa zai fuskanci aikin da babu hutu idan bai denaba,
Waya ce maka tanada bestyn daya wuce Daddynta?"

Dadi taji tana murmushi tace

"Karka basa aiki me yawa Daddy amma idan ya sake zance ka basa,
Kuma banda Besty bayan daddy
Jan da kake cewa ba my besty na bace she is my Jan,my Mummy"

Kallanta Sayd yayi yana dariya cikeda kauna da kulawa.

Daddyn nata kuwa baice komaiba motan da aka bude masa ya shiga tareda kissing hannunta tukuna ya saki yana sake cewa ta kula.

Mota Sayd ya shiga Latif yaja suka bar gidan ta juya ta koma ciki tana tsallen zaadens zata daman jira kawai take ya tafi din taje taga Jan.

Tana shigowa gurin mama tai tana kwala mata kira tin a palo.

Mama dake daki tana waya tana jiyota taci gaba da wayarta sbd tasan shirme ne kawai ko karar Fiddausi zata kawo.

Tana shigowa dakin ta haye kafafun maman tama cewa

"Mama dan Allah zani gurin Jan"

Mama dake waya aje wayar tayi tana kallanta tace

"Ke haryanzu dai Allah bai kawo miki nutsuwa da sanin kin girma ba ko fatima?
Yanzu ki dubi girmanki kizo ki haye kafafuna ko tausayin tsufana bakyaji ko?

Sake gyara zamanta yayi akai duk tama kere maman daga zaunen tana sake bayyanarda shagwabanta tace

"Mama ai kece kika koyamun hawa kafafunki ko bayan na girma ai kina dorani idan zaki rarrasheni to yanzu ma ki rarrasheni Daddyna ya tafi ya barni"

Hannu mama ta daga zata zuba mata duka a baya tai saurin tashi tana cewa

"Me zakiyi mama?
Dukarwa the great AZIZ AY LIMBA 'ya?
Dan Allah mama wai yaushe zaki dena dukana ne,
Nafa fara zama yan mata"

Ajiye wayar hannunta mama tai gefenta tana cewa

"Sai ranar da kikai hankalin fara zama yan matan tukun zan dena"

Dawowa tai ta zauna gefen maman tana cewa

"mama pls zanje na dubo my Jan kinji"

Itama kanta maman ya kamata ta dubota tinda dai yayi tafiyarsa baice komaiba dan haka dole taje tayi gyaran zance dan idan aka biyesa haka zai bari auren ya gantale dan haka ta kalli falaq din tace

"Bari zuwa anjima zamu tafi tare nima zanje godiyar 'ya da suka bamu aure sbd jibi idan Alh Alhassan idan zaije gaisuwa wata rasuwa gida tare zamuje nima zan dubo dangi shekaru da yawa"

Cikin mamaki tace

"Mama nidai to bazanje ba gurin jan zan koma saikin dawo"

Ko kallanta mama bataiba tace

"Jan din daya kamata mu dauko bamu daukonba sai kuma kije ki zauna mata?"

"Eh nidai mama gurinta zan zauna gaskia kafin ki dawo,
Ga Fiddausi nan zata tayani zaman can din bazan dameta da komaiba tinda Daddy bayanan nidai ki bari dan Allah naje can din pls mama"

Magiya taci gaba dayi amma maman bata tankata ba saima anty maryam data daga wayarta ta kira akan atampopi masu kyau da tsada datake son a kawo mata taje dasu ganin gidan ta rabawa mutane.


Falaq kuwa barin palon tayi ta nufi dakinta ta dauki wayarta ta kira jannah wadda wayarta take kashe har lokacin.

Wurgi tai da wayarta tana jin ba dadin rashin samun jannah din.

Da yamma driver ya daukesu ya kaisu zaadens wanda suna isa cikeda girmamawa da kulawa aka tarbesu har ita Mimin bata nuna komaiba sbd bata iya wulaqanta mutane ba hakama ta riga ta samu kusanci da mama da bazata iya iya nuna mata tsanar dataiwa auren 'yarta da 'danta ba,
Dayan babban dalilin kuma shine duk tsanani Zaadens basa barin wani yasan matsalar data shafi iya sirrinsu na familyn dan haka bazata taba barin mama tasan ansamu cin amana a cikin ahalin nasuba na cutar Ammar da akai.

Da farin ciki ta tarbeta tana jan Falaq a jikinta datake cikeda murna tana cewa ina jan dinta.

Gaisawa kawai tai da Mimin tabar palon Fiddausi na biye da ita ta nufi dakin jan tana kwala sunanta da My Jan.

Jin muryan Falaq a gidan ya saka jannah dake kwance tashi tana daidaita yanayinta cikin nutsuwa ta sauko gadonta tana nufar kofa daidai suna shigowa Falaq ta fada jikinta tana cewa

"My Jan wayanki a kashe duk na damu sbd tin jiya naketa jiran zuwanki shiru"

Cikin kulawa da kauka fuskanta a sake sosai tace

"Duk ki aje wannan nima nai missing Baby falaq Aziz"

Dariya falaq din tai suna qarasowa ciki suka zauna Fiddausi na gaidata cikin girmamawa da sakewa itama tace

"Tin kiya kam munata jiranki
Mutuniyar ma daqyar tai bacci"

Dariya falaq tai tana cewa

"Na dena damuwa sbd Daddy yana dawowa zata koma can shikenan"

Labarin yanda sukai bikinsu acan LIMBAs tafara bata tana nuna mata hotina harda na daurin aure data saka fahad ya tura mata duka.

Akan fuskan AZIZ dayake zaune sanye da manyan kaya a lokacinda ake daura auren masu hoto suka ringa daukansa ta xubawa idanuwanta tana kalla.

Ganin yanda take kallan hoton jikinta na mutuwa tausayin kanta na rufeta na gangancin dataiwa kanta na barin son datake wa wannna bawan Allahn ya fito fili gashinan ta qare da aurensa bayan bata ga alamar zata taba daraja a hannunsa ba,
Falaq ta sauya hoton da nemo wani hoton dayafi fitowa sosai yayi wani irin kyau a cikin kayan daurin auren nasa duk da black ne ya saka amma hakan yayi masa kyanda zaka dauka auren farin ciki ne.

Numfashi me sanyi a boye jannah ta sauke tana dauke idanuwanta akai tana jan hannun falaq din da akaiwa lalle simpe me kyau da Anty maryam ta kawo me lalle tai mata tace

"Falaq da henna"

Kallan hannun tai tana cewa

"My first time and i like it"

Saleem ne ya shigo dakin falaq ta gaidasa a sake sbd shima yana tsananin kaunarta dan haka mutuminta ne a familyn shi da Anny amma sam bata yin Ammar ko kadan.

Fira sukeyi sosai har seda Dad ya dawo gida suka fito suka gaidasa Yana nunawa falaq din kulawa da kauna sosai
Mama ma sun gaisa tai godia tareda sakawa auren albarka ta kuka basu hakurin tafiyar gaggawa ce ta kamasa yana dawowa zaa aiko daukan Jannah insha Allah.

Shiru dukkaninsu sukai sbd jin lamarin wani iri shi kuwa dad din cewa kawai yayi Allah yakaimu sbd daman baba alhassan ya kirasa ya sanar dashi hakan tareda basu hakuri shida Daddy mahmoud.

Lamarin ya mugun sosa ransu sbd kamarsu ace an aure Macen datafi kowace mace daraja da matsayi a familyn kaf ace anbarsu da ita gabansu tsabar wulaqantawa ko kiransu bai samu yi ba bare ita jannah din wadda sai yanxu suke ganin ma kamar baigama noticing nataba.

Mimi nauyi kirjinta ya qara akan abinda akaiwa Ammar amma daurewa tai ta nuna itama ai ba komai tinda duk harkan gida ce.

Anan suka qara kaiwa dare kafin suka koma gida bayan jannah ta daure cikin jin nauyin maman tace dan Allah abar mata falaq kafin maman ta dawo,

Maman tana kaunar jannah amma batai saurin yadda ba saida Mimi ta saka baki dan haka ta amince sbd daman batason zuwa da falaq din kauye dan bazata iya ko kwana daya acan ba kila hakama tana zuwa ita falaq zata san ba AZIZ ne mahaifinta ba Sayd ne dan haka tafi samun nutsuwar barinta anan tinda dai yanxu Jannah kaman Mum dintace.


Farin ciki agun falaq baa magana dan haka washe gari koda su mama ke shirin tafiya tini itama Fiddausi ta shirya mata nata kayan a tsadaddiyar luggage dan haka ko daddynta bata fadawa ba da sukai waya.

Washe gari tin karfe goma na safe driver ya iso daga zaadens daukanta ta fito itada Fiddausi suka wuce bayan sunwa su mama fatan sauka lafiya.

Suna wucewa da mintina suma su maman suka fito da sabuwar me aikinsu da baba alhassan Latif ya kama hanya dasu a cikin wata lafiyayyar tsadaddiyar beymach.


Su falaq koda suka isa zaadens a lokacin Ammar da Mimi suka fito a shirye zasu nufi airport suma tafiyar sati biyu zasuyi daga shi sai Mimi sbd ya warware ya dawo mata Ammar dinta su dawo dan tai masa alkawarin dawo masa da jannah hannunsa dan hakan ne ma ya samu ya nutsu zasuyi tafiyar sbd ya dawa a Ammar dinsa ya dawo da jannah hannunsa kota halin yaya koda hakan na nufin kowama ya mutu.

Jannah tashiga damuwar tafiyar tasu mimi amma zuwan falaq ya sakata jin ta dawo daidai dan haka suka koma ciki cikeda farin ciki.

Da daddare ta gaji sosai da surutu da yawo cikin gidan Fiddausi ce ta kawo musu abincinsu a daki sukaci sukai wanka kowannensu ya shirya cikin kayan bacci.

A gefen jannah dake kan sofa zaune tana video call da Mimi falaq ta zauna tana kwantar da kanta kan cinyarta tana kallan Mimi datake nunawa jannah kauna.

A karo na farko dataji wani iri akan rashin uwa,
Kwata kwata batajin damuwa ko kewa ta uwa sbd mahaifinta ya cike mata wannan gurbin bai taba barinta shiga damuwa ta rashin uwaba,
Dashi da uncle da mama da Fiddausi sun tabbatarda bata samu damuwar rashin uwa ba ko kadan.

Kewan Daddynta taji ya ciketa dan haka ipad dinta ta tashi ta dauko ta dawo ta sake kwantawa jikin jannah din wadda ta gama wayarta ta ajiye gefe tana kama gashinta na qananun kitson dayake kanta na kusan 3 cuku tanason daurewa dan suna damunta sosai sbd tsayin gashin.

Muryansa kwatsam taji a kunnenta cikin wani irin lafiyayyan sauti na mai aji da burgewa yace

"Hey Besty"

Kallan inda muryan ta fito ta kalla tana sake kitsanta data kama suna dawowa zube.

A cikin idon juna idanuwansu suka sauka batareda sanin tana tareda jannah ba hakama itama bata dauka da gasken muryansa tajiba.

janye nasa idon yayi batareda ya nuna alamar yama ga mutum a tareda falaq din ba yace

"Kina ina??

Daga ipad din tayi kai tsaye batareda tsammaninsu duka ba ta karawa Jannah wadda rigar baccinta mara hannu tana cewa

"Ina gurin My Jan,ni banbi inna inda zata tafiba gurin jan nakeso shine na taho tareda Fiddausi"

Janyewa jannah tayi daga jikin Falaq din tana barin gurin gabaki daya zuciyarta na dan rawa,

Shikuwa kashe kiran yayi gabaki daya yana jefar da ipad dinsa gefen gadonsa dayake sanye da fararen kayan bacci masu santsi da tsadan gaske yana jin bacin ran zuwan falaq zaadens zama harda kwana.
#MAMUH#
KUYI HKR DA POSTING DA NAKE LATTI UXURI NE AMMA INSHA ALLAH DAGA YAU NA GAMA ZAMU KOMA KAMAN YANDA MUKE DA WURI#*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
62
*UMMU_MAHNOOR LUXURIES*
(Best luxuries shop)
08034469681
08135142610
Aslm Alaikm ina kuke masu neman luxuries na kayan alfarmar kece raini?
Ina masu son su saka sitirar alfarma ta zamani ta manyan mata masu aji da zaa kalleki kallo daya asan sitirar alfarma e kika saka?

Shin kunsan me ake nufi sa kayan asalin yan gayu da nuna gayu?
Sitirar Alfarma kikeson sakawa?
Sitirar da kike ganin manyan mata da ita?
Sitirarda zakiyi gayun sallah dake da yaranki a dauka waje kikaje da kanki kika siyota?
To kizo ga damarki ta sameki sbd UMMU_MAHNOOR LUXURIES ta kawo miki sauki har gida,
Karkice se masu kudi ke iya siya har kema me yar dama zaki samu naki da saukin kudi kuma best quality da kalar zamani data yan gayu,

Nidai Mamuh nace duk wadda ke son a buga gayun sallan bana da ita da 'yayanta to tazo gurin UMMU_MAHNOOR LUXURIES tai siyayyar sallanta harma zuwa gaba dan nasan zakuji dadi da fahimtar abinda nake fada akan kayanta💯💯
Abubuwan da zaki samu a gurinta with the best quality na wayayyun mata masu aji yan gayu sune;

Atampopi
Laces
Shadda
Materials
Shoes
Bags
Veils
Trolleys
Jewellerys
Oil perfumes

Numbers
08034469681
08135142610

Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries


*****************
Kallan ipad din hannunta falaq tai tana cewa

"Daddy hang up"

Tayi mamaki sbd bai taba hakanba yawanci ma shine yake cewa sai tayi bacci ya kashe.

Kallan Jannah data isa gado ta haye ta kwanta tana rufe jikinta yayi tayi tana cewa

"Jan baki gaisa da daddy ba harya kashe wayan meyasa kika tashi?

Kallanta jannah tayi da idanuwanta tana kasa cewa komai kafin ta dan bude bakin tace

"Zo ki kwanta sbd kinsan gobe Monday akwai school"

Tahowa tayi tana hawowa gadon ta shige abin rufar itama tana cewa

"Jan banason school sam"

Murmushi me sauti Jannah tai tana cewa

"Did your Daddy know that??

"No" tace tana karanta adduarta ta bacci tana rufe idanuwanta.

Babu bata lokaci bacci ya dauke falaq din hankali kwance.

Ajiyar zuciya Jannah ta sauke ahankali tareda tashi zaune tana zubawa fuskan falaq idanuwanta dake cikeda azabtacciyar soyayyar da batada amfani gareta,
Tamkar copy dinsa ne akan fuskan falaq har mamakin kamanninsu takeyi,
A duk lokacinda take kallan fuskan Falaq shi zuciyarta take gani,

Sake sauke numfashi tai tareda miqa hannuwanta ta gyarawa falaq din rufa tana gyara mata hulan baccin daya zame daga kanta ta sake mata addua tana jin kaman zuciyarta zata bude sbd tsananin kaunar datakewa Falaq din da mahaifinta,

Ayau da zata fara kwana guri daya da falaq jin tai kaman baccin ya qaurace daga idanuwanta so take kawai taita kallanta har ta cika zuciyarta.

Zamewa tai ta kwanta ahankali tana facing Fuskan falaq din wadda take bacci hankali kwance,

Kallanta take a natse tana jin nutsuwarta na dawowa da jin farin ciki na mamaye zuciyarta ahankali
Ahaka bacci me dadi da nutsuwa ya dauketa.


Da Asuba wayar falaq dinne ta tadasu bacci.

Cikin bacci jannah taji ringing din wayar a cikin kunnenta sbd tana ta gefenta akan bedside dan haka hannu kawai ta miqa tana jin bacci na sake cike idanuwanta.

Dauko wayar tayi batareda ta duba sunan me kiranba tai rejecting ta ajiye tana dake qaramar tsoki sbd tama manta kwata kwata da ba ita kadaice ba ayau din so ta dauka tata wayarce.

Sake kira akai kai tsaye sbd a nasa bangaren tinda yarinyarsa ta fara wayo yake koya mata sallah akan lokaci shiyasa ya sabar mata duk asubar duniya yana nan ko baya nan saiya tadata sallah akan lokaci, tin bata saba ba harta saba yana kira take tashi tayi sallanta a lokaci ta koma ta kwanta,

Ayau karo na farko na rayuwarsa da akai rejecting call nasa kuma daga wayar 'yarsa shiyasa kai tsaye ya sake saka kiran.

Wannan karan kiran na sake shigowa Jannah ta sake motsawa tana miqa hannu a fusace ta dauka ta batareda ta duba sunanba dan ko gani batayi sosai sbd baccin dayake idonta ta saka handsfree kafin tai magana muryansa ce mai kauri da sautinta yake bada wani irin sexy vibe din da zai iya juyar da kan da yawa wasu idan suka ji sbd a lokutan da ake tashi bacci a lokacin muryan mutane da dama sautinta komawa yake na tada hankalin wasu,

So tasa muryan a koda yaushe hakan take idan har ya tashi bacci yayi magana to zai iya daga hankalin me sauraronsa dan haka ahankali muryansa ta bayyana a cikin wayar a natse yana cewa

"Why did you reject the call???

Bude idanuwanta dake rufe jannah tai tana kallan sunan dayake kan wayar jikinta na wani irin mutuwa ta tashi zaune tana kokarin hana sautin numfashinta shiga wayar amma saida ya shiga cikin wayar ahankali ya sauka a cikin kunnensa.

Cire wayar yayi daga kunnensa yana saka handsfree ya ajiye gefensa yana sake jefa tambayarsa

"Why did you reject the call?

Yasan ba yarsa bace sbd har abada Falaq bazata taba rejecting kiran Daddyntaba.

"Numfashi me dumi ta sake sauke ahankali bugun zuciyarta na dan qaruwa ta bude baki Ahankali da muryanta dake cikin sauran yanayin bacci tace

"Sorry na manta na dauka wayana ne"

Takaici da mamaki ne ya kamasa lokaci daya kamar bazai tankata ba sai kuma yace

"Tarbiyan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login