Showing 162001 words to 165000 words out of 185083 words
shima,
Mama Latif ta cewa maza ya fidda mota ta fito itama da komai nata ke rawa sbd tashin hankali...
A jere cikin tsananin tashin hankalin da basu taba shiga ba tin rasa Ummitah suka bar gidan zuwa asibiti babu wanda bai kusan zarewa a cikinsu musamman Ubanta dayake rungume da ita har lokacin yana jin zuciyarsa na mummunan tsagawa.
Silalewa ahankali jannah da kafafuwanta suka mutu murus tayi ta zube a tsakiyar palon da aka barta tata zuciyar itama tana kasa daukan dukkanin wannan masifar datake gabanta,
Hannuwanta dake rawa ta miqa ahankali ta fara bin takardun dake qasa zube tana karanta sunayen jamaar da suka rasu sbd neman zuciyarta,
Wani irin azababben ciwo da radadin gaske kirjinta yakeyi idanuwanta na neman makancewa sbd tsananin radadin hawayen da suke neman sauko musu,
Akan takardar datai gefe daban ta fadi ta dora hannunta dayake rawa ta juyota hoton Ummitah da sunanta UMMITAH ABDULAZIZ LIMBA ya bayyana wanda ya sakata fasa wani irin azababben kuka me tsananin ciwo da qunci tana dafe kirjinta setin zuciyarsa tana rintse idanuwanta kukan na tsaga zuciyarta.
Masu aiki dake jinta tsit suka sake yi jikinsu na sake tsananin sanyi sbd tausayi.
Kuka takeyi sosai kaman zuciyarta zata fashe sbd zallar qunci da rashin madafa,
Ciwon rayuwarta takeji,
Inama ta jima da barin duniyar,
Inama Allah ya bawa familynta a baya sun hakura sun barta tabar duniyar da duka basu samu kansu a wannan kaddarar me nauyi ba,
Inama bata rayuwa ba anbar Falaq da mahaifiyarta,
Inama ba zuciyar Ummitah ce a kirjinta ba,
Inama zaa iya dawo da baya data miqawa Limbas zuciyarsu kowa yayi rayuwarsa yanda ya saba........
Inama zata iya goge wannan mummunan kaddarar akan ahalinta..
Zubewa tayi kwance tana dafe kirjinta cikin tsananin azaba da kukan dayake fitowa daga zuciyarta.
Fiddausi ce ta iso ahankali cikin palon ta iso kafafunta a sanyaye kan jannah din tana bin komai dayake gurin da kallo har idanuwanta suka sauka akan fuskan Ummitah itama.
Wasu zafafan hawaye ne suka gangaro mata ta juya zata fice sai kuma ta kasa sbd wani irin kuka dayake ratsa zuciyarta da Jannah ke yi a kwance kaman zuciyarta zata mutu.
Dawowa tai ahankali tareda durqusawa ahankali ta dafa bayan jannah din tana kasa cewa komai.
Jannah bata iya cewa komaiba sai tsananta da kukanta keyi jikinta na rawa ahakali.
Ahankali Fiddausi ta bude baki tana kallan fuskan Ummitah dake jikin hoton tace
"Ummitah itace duniyar ABDULAZIZ LIMBA gabaki daya,
Rashinta shine ya maidasa AZIZ LIMBA wanda babu komai acikinsa sai emptiness,
Ya rasa Ummitah falaq ta maye gurbin dayake riqe dashi,
Rashin Ummitah ya taba kwakwalwa da hankalinsa da a yanxu rasa Falaq Allah ne kadai yasan kaddarar daya tanadar masa a gaba wadda bama fata sbd AZIZ LIMBA issa pure soul,
Naji nasan Kashe Ummitah akai ta hanyar rabata da zuciyarta,
Kinsan waye Ummitah a rayuwarsa??
Ahankali idaniwanta na yin ja tafara bayyana mata waye Ummitah da AZIZ LIMBA,
Su waye asalin iyayensu hakama waye mama a gurinsu,
Waye Sayd a gurin Ummitah da kuma waye asalin mahaifin Falaq tareda yanda rasuwar Ummitan ta sauya rayuwar kowanne a cikinsu musamman AZIZ da irin jinyar dayasha da mutuwar daya kusan yi wanda anan ne ma ya samu duk matsalar da ake tinanin yanada ita..
Dena sauti kukan Jannah yayi sai ahankali kukan ke fita sbd karfinta daya kare tareda zuciyarta da azabar ciwo da radadi,
Qunci ne kawai take ji tako ina yana tsagata yana kashe duk wani halittar da Allah yayi a jikinta kalaman Fiddausi na yaga azabtaccen radadi akowane saqo na jikinta da zuciyarta dake karban kowane zancen da ciwonsa dayake yankanta direct.
Miqewa Fiddausi tayi ta fita dan kawo mata ruwa ko zata iya dawowa daidai sbd gabaki daya ta koma kalar qunci da tsananin tausayi,
Idanuwanta sunyi munin da ko gani sosai bata yi dasu.
Awanni ta share a zube tsakiyar palon tana kukan da har zuciyarta ta kasa dauka kafin ahankali ta tashi hannuwanta babu karfi ta tattara takardun palon ta fice dasu.
Fitowa tayi babu karfi ko kadan a jikinta bare zuciyarta ta fice daga gidan.
Yau securities basu hanatava sbd ganin yanayinta kamar ta zare dan ko gani sosai batayi gashi kuma dai suna cikin tsananin jimamin abinda yake faruwa dan haka babu me energy na hayaniya.
Tafiya takeyi da kafa tana dafe zuciyarta dakejin kaman zata buga,
Ciwon gaske take mata ba iya na qunci ba ciwon azaba take mata.
Tafiya tayi sosai kafin ta samu motar data tsayar ta shiga tana rintse idanuwanta da babu kyan gani ko kadan tanajin tsananin tausayin AZIZ LIMBA da ahalinta da rayuwar kowannensu ta lalace a daidai gabar da ake yanzu dukkaninsu sbd ita,
Kaddara ta riga ta hada rayuka biyi a guri daya,
Gangar jikin Zaadens da Zuciyar Limbas wanda kowannesu a yanzu neman mafitar fita daga wannan mummunan kaddadar suke.
Asibiti ta iso Allah yasa Saleem yana dawowa kenan shima dan haka shine ya biya mai motan yana kallanta cikin mummunan tsoron wata masifar ce ta kunno kenan.
Ciki sukayo tana handa hanya bata gani sosai hakama jikinta yayi weak sosai....
Suna isa dakin da Dad yake zaune Maheer yana basa tea ahankali yana sha Mimi ma na zaune gefe tayi shiru tareda nisa a tinani sosai batama san tinanin datake ba sbd depression da yayi mata mummunan kamu itama.
Shigowan Jannah din da yanayinta ya sakasu duka juyowa kanta suna kallanta da mamakin ganin yanda ta koma kamar mahauciyar da batada gata ko kadan.
Takardun hannuwanta ta dago hawaye masu tsananin ciwo suna gangarowa daga cikin idaniwanta ta miqawa Maheer tana bude bakinta dayayi tsananin nauyi muryanta bata fita sosai tace
"Shin dukkanin abinda yake cikin nan da gaske ne?
Shin ni har nakai matsayin macen da zaa hallaka rayuka da dama sbd na rayu?
Shin mummunan kaddarata takai na saka imanin ahalins ko nace iyayena fita su iya kisan mutane da dama harda me tsohon cikin datake rokon a saukaka mata?????
Zubewa tai qasa tana fasa sabon kukan dayake fitowa rin daga zuciyarta tana rintse idanuwanta hawaye na fita sosai.
Dad kasa dago idaniwansa da sukai jajir yayi yana jin ciwo da radadin da Jannah din ke ji na samunsu da wannan mummunan aikin da shine yake lalata rayuwar kowa a yanzu harda tata din da sukai komai dan ta inganta.
Maheer kuwa damqe file din yayi shima ciwo da radadin abin na saka idaniwansa jajir hannuwansa na rawa sautin kukanta na ratsa kowa dakin.
Mimi ce ta kalli Dad gabanta na faduwa kafin ahankali ta dawo da kallanta kan Maheer da hawaye masu tsananin ciwo suka gangaro masa...
Jin tayi gabanta ya sake mummunan faduwa ta kalli saleem da shima mafi girman tashin hankalin ya shiga yana kallansu kafin ya miqa hannunsa yana rawa ya ciro file din daga hannun Maheer ya fara budewa yana karanta abubuwan dake a ciki a fili muryansa na wani rawar tashin hankali da firgici....
Yana isowa na Ummitah ya ambaci sunanta wanda yake hade dana AZIZ LIMBA take Mimi tayi baya tana jan numfashi ta fada jikin bango shima Saleem dagowa yayi hawyae na bin fuskansa ya kalli jannah wadda ta bude baki tace
"Zuciyar Ummitah Limba ce a kirjina,
Zuciyar mahaifiyar Falaq ce take bugawa a kirjina,
Zuciyar macen da aka kashe ce da tsohon ciki ce a kirjina,
Zuciyar macen da a nata ahalin itace haske kuma idaniya a kirjina.........
Maheer ne yayi saurin miqewa yana isa ga jannah din cikin dana sani da ciwo
Yace
"Duka sbd ki rayu ne Jannah"
Wani mummunan jan numfashi Mimi tayi tana zubewa qasa sbd tsananin shock da tashin hankalin jin abinda bata taba jiba....
Saleem da ganinsa da jinsa ya dauke take shima zubewar yayi qasa zaune yana qurawa Maheer da Dad idaniwansa...
Ahankali Maheer ya bude baki yafara fadar duk abubuwan da suka aikata din wanda take zuciyar Mimi da Saleem harma da jannah suka kasa dauka
Mimi tafara jan Numfashinta dake neman katsewa tamkar me asthma,
Ganin tana neman rasa numfashinta Saleem da baya gani sosai yayi kanta sa rarrafe yana kokarin ambatar sunanta amma bakinsa ya kasa buduwa hakama hannuwansa shima sun mutu sai yaji kawai komai baya motsawa a jikinsa hawaye suka fara gangaro masa kafin yayi yunquri yana ji yana gani Mimin ta juye a gurin numfashinta ma dakatawa cak.
Ita kanta jannah a jikin Maheer ta zube dan haka dole Maheer din hankali tashe ya nemo likitoci aka kwashesu su ukun zuwa emergency.
Dad da maheer kuwa jigum sukai babu me iya cewa komai suka zubawa sarautar Allah ido suna fatan ba wannan shine karshensu ba na shedar da mutuwar rayuka mafi soyuwa a rayuwarsa akan laifin da sune suka aikataba.
Har dare babu labarin komai da kowa a tsakanin su ukun dan haka Dad da Maheer din suka sake shiga mummunan yanayi na dana sani da damuwa me tsanani.
#MAMUH
#BEST LOVE
#AZIZ AY LIMBA
#JANNAH ZAD
#LIFE CHANGING
#NEW LIFE
#NEW BEGINNING
#AYSH
ZAFAFA BIYAR
KALBIM 500
mamuhgee
A DUNIYATA 500
Huguma
AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul
KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo
Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi
Shedan biya
09033181070
Or mtn vtu at
09032345899*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
87
*UMMU_MAHNOOR LUXURIES*
(Best luxuries shop)
08034469681
08135142610
Aslm Alaikm ina kuke masu neman luxuries na kayan alfarmar kece raini?
Ina masu son su saka sitirar alfarma ta zamani ta manyan mata masu aji da zaa kalleki kallo daya asan sitirar alfarma e kika saka?
Shin kunsan me ake nufi sa kayan asalin yan gayu da nuna gayu?
Sitirar Alfarma kikeson sakawa?
Sitirar da kike ganin manyan mata da ita?
Sitirarda zakiyi gayun sallah dake da yaranki a dauka waje kikaje da kanki kika siyota?
To kizo ga damarki ta sameki sbd UMMU_MAHNOOR LUXURIES ta kawo miki sauki har gida,
Karkice se masu kudi ke iya siya har kema me yar dama zaki samu naki da saukin kudi kuma best quality da kalar zamani data yan gayu,
Nidai Mamuh nace duk wadda ke son a buga gayun sallan bana da ita da 'yayanta to tazo gurin UMMU_MAHNOOR LUXURIES tai siyayyar sallanta harma zuwa gaba dan nasan zakuji dadi da fahimtar abinda nake fada akan kayanta💯💯
Abubuwan da zaki samu a gurinta with the best quality na wayayyun mata masu aji yan gayu sune;
Atampopi
Laces
Shadda
Materials
Shoes
Bags
Veils
Trolleys
Jewellerys
Oil perfumes
Numbers
08034469681
08135142610
Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries
***************
Cikin dare sosai Likitoci suka samu fitowa daga dakin Falaq zuciyoyinsu da fuskokinsu babu farin ciki ko kadan saima tausayinta dana familyn nata da suke asibitin a cikin mummunan yanayi na sanyi.
Dr Ashir ne ya tsaya gabansu tareda sauke ajiyar zuciya me sanyi yana kallan AZIZ LIMBA wanda idanuwansa sukai ciki gabaki daya sbd tsananin tsoro da damuwar data gama cinye dukkanin kuzari da jarumta tareda karfin halinsa.
Irin kallan da dr Ashir yake masa ya saka dukkaninsu juyawa suna kallan AZIZ din wanda ya koma ahankali ya zauna yana dauke idanuwansa daga kan ashir din Mama tai saurin dafasa tana riqe hannunsa cikin kokarin basa kariya da kwarin gwiwan da itama bata dashi.
"Ta riga takai stage din datake buqatan heart transplant batareda bata lokaci ba ko daukan lokaci ba...."
Ahankali ya zame daga kujeran dayake zuwa qasa yana qanqame hannun mama datake riqe dashi ya cusa fuskansa a tafin hannuwanta wasu hawaye masu tsananin zafi da tashin hankali suna gangaro masa jikinsa na daukan rawa gabaki daya wanda ya saka kowa dayake gurin tsit kafin kukan daya kasa riqewa ya kubce masa sbd kaman ana fada masa ne Falaq tafiya zatai ta barsa kenan..
Sautin kukansa ne ya tayarda tsikar jikin dukkanin wanda yake gurin yana ratsa zuciyoyinsu,
Jijjiga jikinsa keyi sosai fuskansa na tafin hannuwan mama datake hawayen tausayinsa har cikin ranta,
Sayd ma silalewa yayi ya zauna a qasa hawaye masu tsananin zafi da radadi na tsinke masa sbd kai tsaye kaman dama ce aka sanar dasu ta kwanakin dasuka ragewa Falaq a duniya.
Mama ma ganin kukan Sayd sai ta kasa riqe sautin kukanta ta rintse idanuwanta tana sake jin saukan hawayen AZIZ masu zafi a tafin hannunta.
Dr Ashir da suke saka hawaye taruwa a idanuwansa barin gurin yayi yana jin tausayin familyn gabaki daya sbd shi kansa yasan samun donor abu ne me wuyar gaske da ahaka suna ji suna gani lokacinta zaiyi tabar duniya.
Daqyar mama ta iya kama hannunsa ta dagar dashi ta kama hannun Sayd shima dayake kuka rasa 'yarsa da har yau batasan matsayinsa na mahaifintaba,
'Yar dayake kallo a lokutan quncinsa ya samu sassauci da sanyi,
'Yar dayake wa kallan mahaifiyarta daya rasa,
'Yar da har yau bata taba kallansa a uba ba bare ambatarsa da sunan uba ko so daya ba...
Dakin falaq din mama ta shiga dasu ta isa dasu har bakin gadonta ta saki hannuwansu suna kallan yanda Allah ya Maidata a lokaci daya ba kyan gani,
Oxygen ne da wasu abubuwan a fuskanta da bakinta harma da kirjinta,
Tayi haske a lokaci daya tai wani irin jemewa idanuwanta a rufe,
Kallo daya zakai mata kasan ciwo me girma ne a tattare da ita wanda Allah ne kadai yasan ko zata tashi kokuwa tafiyarta zatai itama ta huta da wannan duniyar me wahalar zama.
Silalewa AZIZ yayi ya zauna a gefe yana kallanta sbd yanayinta dake nuni da azababben ciwone take cikinsa duk da bata hayyacinta..
Sayd ma sunkuyar da kansa yayi yana zuba mata dukkanin idanuwansa jikinsa a mace.
Shiru dakin yayi babu me motsi,
Ayau falaq datake da gatan da dayawa basada gata a kwance numfashin datake shaqa ma na Oxygen ne zuciyar da zata rayu take buqata,
Kudi da gatanta ba zasu iya bata hakan ba,
Soyayyar mahaifinta bazata iya bata hakan ba sai abinda Allah yaga damar yi da ita.
Tsawon Lokaci ahakan har aka fara kiran asuba suka fito
AZIZ na gaba Sayd na gefensa kowannensu idanuwansu sunyi nauyi sosai.
Masallaci suka nufa sukai sallah suka zauna suna adhkar har gari yai haske kafin AZIZ ya dago idanuwansa ya kalli Sayd tsawon seconds kafin ya bude baki Ahankali ya furta
"Ka sanar da Dr Nico komai da ake ciki a sakamu na list din gaggawar neman donor"
Gyada kai Sayd yayi yana sauke numfashi.
A kusan qasashe 6 Sayd ya buga da neman zuciyar cikin lokacin daya ragewa Falaq din wadda take qara wani irin sauyawa daga kwancen tana rasa duka albarkar jikinta.
Duk yanda suke tinanin zasu iya riqe abin sun kasa su kansu a cikin budadden qunci suke daya nauyaya zuciyoyinsu.
Gida suka dawo aka baro Fiddausi dataje can,
Tsit gidan yayi ga dining an jere abinci amma babu wanda ya iya fitowa a cikinsu kowa na daki.
Wanka yayi ya sauya kaya ya zauna yana buga wayoyi a wayarsa kansa na zarewa ahankali ahankali gurin neman ta inda zai samu zuciyar dasawa 'yarsa.
Acan asibitin Zaadens kuwa Saleem ne ya fara dawowa daidai kafin jannah wadda ta zubawa mahaifinta dake zaune gabanta idanuwanta da sukai tsananin laushi.
Mahaifinta kaunarsa a jininta take da duk laifin da zai aikata a duniyarnan bazata taba dena so da kaunarsa ba,
Bazata taba gudunsa ko qyamarsa ba,bazata taba jin tsanarsaba,
Kaunarsa ce take sake rufesa da tausayinsa sbd duka wannan mummunan lamarin daya faru ya farune sbd kaunarta da shedan daya shiga zuciyarsu ya gurbata tawakkalinsu.
Ahankali wasu hawayen baqin ciki da dana sani tareda kunyar yarsa suka gangarowa Dad ya dago ya kalleta itama shi din take kalla idanuwanta na tsiyayar hawaye.
Saukar hawayensa Kan tafin hannunsa dayake bude ne ya sakata rintse idanuwanta da karfi tana jin zuciyarta na tsananta ciwon ganinsa ahakan...
Bude bakinsa yayi Ahankali cikin sanyi yace
"Akwai son zuciya da rinjayar shedan a lamarin da muka aikata,
Nayi dana sanin nema miki zuciyar datake jirjinki bata hanya halastacciyaba sbd kema kin shiga matsalar da mune muka janyota,
Jannah ni mahaifi ne da idanuwana sika rufe akan kaunar danakewa 'yata a baya,
Kuma a yanzu ma na shirya zama uba da idanuwansa zasu rufe akan kaunar dayakewa 'yarsa na aminta na shirya karban da fuskantar sharia sbd hana rayuwarki shiga quncin da babu fita,
Bakida masaniya dan haka zan miqa kaina da kaina sbd na kasa baki farin ciki daga karshe sai kuka da qunci......
Wani irin kuka me tsima zuciya ta fasa tana fadawa jikinsa ta rungumesa da karfi tana girgiza kai quncinta da radadin zuciyanta na tsananta.
Rungumeta yayi shima yanajin kasawarsa da lalata rayuwar duka 'yayansa a matsayinsa na uba.
Maheer dake gefensu kuka yakeyi sosai shima har yana jijjiga zuciyarsa na radadi shima yana jin zai iya bin mahaifinsa a duk matakin da zai dauka a wannan rayuwar me kyau da mara kyau dan haka idan mahaifinsa ya aminta dasu miqa kansu su karbi hukuncin daya kamata ya aminta da hakan ya shirya binsa har lokacinda da zaa kashesu kaman yanda suka kashe.
Kuka sukeyi gabaki dayansu a dakin cikeda tsananin so da kaunar junansu da haryanzu babu abinda ya sauya daga cikinta,
Saleem ma mahaifiyarsa da likita ya sanar dashi ta samu paralys ya rungume yana wani irin kuka mai tsima zuciya.
Jannah dagowa tayi ta kalli mahaifinta kafin ta maida kallanta kan Maheer dayake gefenta riqe da hannunta daya ta bude baki cikin sanyi tace
"Neman tuba da yafiya a gurin Allah shine farko kafin komai,
Insha Allah zamu cinye wannan jarabar Dad"
Dakin Mimi suka nufa dukkaninsu idanuwa a jeme a can suka tararda mugun labarin daya qarasa collapsing duniyarsu gabaki dayanta.
Sabon zama suka dora na jimami har dare.
Tsakar dare Mimi ta farka ta bude idanuwanta ahankali daqyar cikin wani irin sanyi tanajin dukkanin quncin zuciyarta ya yaye ganin ahalin dai daga karshe kansu ya sake hadewa basu rabu ba duk da munin aikin dasu Dad suka aikata.
Akan Saleem ta tsayar da idanuwansa tai masa kallan mintina ya saka hannunsa cikin nata yana hango kewan Ammar a cikeda idaniwanta wanda babu bakin furtawa,
Maida idanuwanta akan Maheer tayi tana jin tsananin tausayin kaddarar data hau kansu wadda batasan hukuncin da zasu fuskanta ba amma koma menene tana masa fatar samun sassauci da rayuwa me kyau a gaba idan yanada rabon tsallakewa.
Maida idaniwanta tai kan jannah da itama ita take kallo idaniwanta sun bushe sunyi jajir babu abinda yake cikinsu sai qunci da damuwa.
Hawayene suka gangaro daga gefen idanuwan Mimin tana jin tausayin rayuwar jannah da batasan yaya zata kasance ba idan ta wayi gari batareda gata da dukkanin ahalinta...
Maida kallanta kan Dad tai wanda kallo daya tai masa idanuwanta suka rufe ahankali.
Maheer ne yafara kiran sunanta ahankali yana miqewe tsaya zuwa ga fuskanta yana tabawa hannuwansa na rawa.
Saleem ne ya fahimci Mimi ta riga tabar duniyar ta barsu rai yayi halinsa.
Maheer kasa yadda yayi da hakan ya fara jijjigata yana kiran sunanta.
Jannah ma fadawa tai kan Mimin tana kiran sunanta cikin wani matsanancin halin daya cinye karfi da zuciyarta.
Dad sunkuyar da kai yayi hawaye na tsiyayo masa daga karshe dai duka sunata girban abinda suka aikata ta hanya me ciwon dayafi wanda suka saka mutane,
Ahankali Allah ke dandana musu zafi,ciwo da radadin rashi