Showing 183001 words to 185083 words out of 185083 words
karfin tsayawa boye komai sbd so take su karbeta a yanda Allah ya maidasu tace
"Daddy Mahmoud ya rasu,Mimi ta rasu,
Dad da sauran yan uwana biyu suna gidan yari sai bayan shekara guda zasu fito"
Da sauri dukkaninsu suka kalleta kawu isiya na cewa
"Mahmoud ya rasu??
Kasa cewa komai tayi.
Jin hakan ya saka Modibbo cewa a kaisu jannah din dakin Yakumbo su huta a basu abinci da nono me dumi su sha su huta da kyau tukuna ayi magana daga baya idan ta nutsu yanda ya kamata.
Dakin yakumbo aka kaisu matan gidan da yara na musu sannu da zuwa cikeda mutuntawa da farin cikin ganin jikar zeenah ce yau a gidan.
Kasa cin komai jannah tayi wanka tayi da ruwan sanyi a bandakin da baida rufi take sanyi da zazzabi suka rufeta.
Daqyar yakumbo ta sakata shan sabuwar madara me dumi wadda ta dan taimaka mata amma sallah kawai tayi ta dunqule guri daya tana rawar sanyi idanuwanta na tsiyayo da hawaye masu dumi.
Ummah ma taci abinci tayi wankan amma itama zazzabin ne ya kwantar da ita.
Washe gari duk yanda ake tinanin ciwon yabar jannah kasa barinta yayi dan haka tsoro ya kama su Modibbo kawu isiya yace karta mutu su tattarata su sallemeta yakumba tace aa.
Ummah ta warware ita dan haka tafara kulawa da jannah din wadda ta rafke lokaci daya ta sake komawa kalar tausayi.
Satinta daya ana jinyarta anata maganin hausa kafin tafara warwarewa ta dawo daidai.
Sai a lokacin hankalinsu kawu ya fara kwantawa harma suka zauna da ita ta fada musu komai sedai ta boye cewan da sanin iyayenta akai komai tadai sanar dasu zuciyar da aka kawo musu ashe ta kisa ce bata hanyar gaskia bane batareda saninsu ba wanda hakan ne ya saka rufesu shekara daya.
Su kawu Modibbo dasu kawu isiya da kukansu da komai na tausayin yan uwansu wanda kukansu kadai ita jannah tsoro ma ya ringa bata sbd tamkar kukan yayan aljanun dare haka suka ringa matso hawayen suna darzar idanuwa kaman masu gasar kuka sbd ta gani idan su Dad din suka fito ta fada musu da waye da waye sukai kuka sbd su samu rabo me tsoka sbd basu yadda da kakaf komai aka kwace musu ba dan kamar bame yiyuwa bane dan haka zasu kula da ita kamar kwai har su Dad din su fito su samu suma su lasa arziki.
Bangaren Asalin kakansu na gidan daya dade da mutuwa Modibbo yace samarin gidan su saka karfi suyi aikin qasa su gyara daki biyu ne da bandaki sai madafa a gyarawa su Dad din kafin su fito.
Su Garba da fodio da Idris sune matasa samarin gidan masu ji da lokaci tini suka fara aikin kowa da abokinsa ake aikin sbd kowa da kudirinsa na shirin dawowan su Dad din rayuwa a cikinsu da santaleliyar buturiyar 'yarsu data zama tamkar bayyanar Zinariya a kauyen.
A cikin gida kuwa kamar jannah bazata iya rayuwar kauyenba sai kuma tafara sabawa sbd kauna da kulawa datake samu tako ina a gidan harma da wajen gidan wanda ya saka mata farin jini.
A cikin gidan akwai budurwa tsararta 'yar kawu isiya wadda mijinta ya rasu ta dawo gida da yarinyarta 'daya itace tafara zama abokiyar hirarta.
Fatma itace tafara fita da ita garin da gurare daban daban tin tana tsoron mutane harta saba tana shiga cikinsu sosai,
A gidan kowa ta kansa yakeyi dan haka tana ganin lokaci yafara ja ta fara koyan sanaar saqa da siyarwan da Fatma keyi itama tafara ita kuma Ummah tana taya matan su Kawu harkan nono da manshanun da sukeyi dan haka itada Ummah sai ya zamana suna dan samun abinda suke kulawa da kansu basu bari sun zamarwa kowa lalura me gajiya ba.
Kaunar datake tsakaninta da Ummanta ya wuce dukkanin tinanin da mutanen gidan dana waje keyi akansu sbd Ummah babu abinda takeyi a rayuwarta yanzu bayan duk abinda zata kula ta tattala rayuwar Ummijan dinta,
Duk aikin wahalar datakeyi a gidan sbd jannah ne hakama duk daren Allah kwana takeyi kulawa da jannah dinta harta saba bata iya bacci sauro bin jannah,bata iya bacci idan jannah na cikin damuwa bata iya komai saida jannah dinta.
#MAMUH*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
98
*SHOP WITH ME by RANO*
08030811300
Best children's clothing shop💯
https://chat.whatsapp.com/Gk4H76TlRgyAAWIWgx3Jo7
Kina neman in da zaki samun kayan yara classy kaya na yan gayu at a very affordable price? Ko kina son fara kasuwancin kayan yara amma baki da jarin da zaki saro kayan? Nesa ta zo kusa, kiyi joining community din nan muna saka kaya masu kyau available da inganci a farashi me sauki da zaki dauka ki tallata har ki samu naki kema.
Burinmu shine kowacce mace ta samu sanaar da zata dogara da kanta.
**********
A bangaren jannah a yanzu data samu kwanciyar hankali da nutsuwar datake jin babuta sai a kauye da babu tashin hankali sai rayuwar rufin asiri,
Ummah ce hasken idaniyarta da zuciyarta,ummah ce karfinta,Ummah kuzarinta,duk abinda takeyi tana yinsa ne sbd Ummah dan haka a ranta takejin Ummah uwartace da bazata iya rabuwa da itaba har abada dan haka ma ta yanke shawaran hada ahali da Ummah daga ranar da Dad dinta ya fito.
Angama gyara dakunan da zasu zauna dan haka itada Ummah suka fara komawa da Fatma wadda take takure a rabe dakin yadikkonta.
******lokaci yafara tafiya sosai sbd shekara ta kusa cikewa dan haka lissafin su kawu sai ninkuwa yakeyi shi kawu isiya har batan lissafin abubuwan da zaiyi yakeyi,
Shikuwa Modibbo bature yakeda niyar binsu ya zama duk inda zasu kafarsu kafarsa shima.
Su garba kuwa shirin sosai sukeyi na yanda zasu tarbi ahalinda zasu iya zama sirikansu dan kuwa dadi da wuya zasu tsaya bazaa bar kauyen da jannah ba sai waninsu ya aureta ko zaa tafi kasar wajen dasu suma.
Rayuwa tayiwa jannah da Ummah daidai babu me damuwar komai a cikinsu saita kewan nasu idan ta taso musu,
Ciwon Ummah yana dadewa bai tashiba idanma ya tashi jannah rungumeta takeyi duk dukan dazai mata bata iya saketa haka zata ringa hadiyewa cikim azaba harda rauni da komai bata iya rabuwa da ita har saita dena ta fara kuka shine zata rungumeta susha kukansu tare su gama batareda wani yasan halinda suke ciki ba.
Jannah Zad kaman yanda rayuwarta ta sauya ita kanta ta sauya tako ina,
Rama da quncin data fito a cikinsa ya tafi,
Jikinta ya dawo daidai bame qiba ba ba kuma ramammiya ba,
Halaye da dabiunta da yawa rayuwa ta sauya mata su,
Kaman yanda komai nata ya sauya hatta sunanta ya sauya sbd a yanzu kaf garin ba jannah suka santa ba da sunan da Ummanta ke kiranta aka santa dashi wato UmmiJan,
Rayuwa ta koyar da ita darasi,
Rayuwa a cikin mutane daban daban ya koyar da ita abubuwa da dama na rayuwa tareda sanin meye rayuwar a yanzu.
Ahalin Modibbo sun kaunace ta a lokacinda batada kowa batada komai,
Sun karbeta hannu bibbbiyu batareda gudunta ba sbd iyayenta sun gujesu dan haka har cikin ranta a yanzu take kaunarsu sbd a yanzu ne ta gane me dangi da yawa suke nufi,
A kauye suke suke rayuwa a cikin dajin da babu wuta babu ruwa amma a hakan tasamu nutsuwar da bata samu ba a can inda daular take dan haka take rokon Allah ya bawa ahalinta ikon iya rayuwar da zasu taho su tarar anan din.
Babbar muguwar halin da gidan suke dashi shine tsananin son abin duniya wanda a tsakanin kawunnin nata bata san wanne yafi wanne kwadayi da son abin duniya ba.
********BAYAN SHEKARA GUDA
Ayau itace ranar datafi kowace rana a rayuwar UMMIJAN sbd itace ranar da zata isa abuja dan haduwa da mutanen da sune rayuwarta sune rabin jikinta data rasa.
Itada kawu Isiya da Modibbo ne suka shirya tin asuba suka shirya da Ummah da kudin da suke tarawa itada Ummanta na tarban su Dad da lalurar motarsu da komai dana abincin da zasu ringa ci har dan tsawon lokaci kafin su samu aikin yi a kauyen da zasu tallafi kansu.
A mota kasa rintsawa tai duk tsananin baccin dayake son daukanta kasawa tayi haka ta zubawa hanya ido zuciyarta na wani irin harbawa hannuwanta rawa sukeyi saida Ummah ta damqe mata su tana kallanta itama kallanta takeyi tana jin kaunar Ummah na sake rufeta sbd Ayau Allah ya kawo karshen damuwarsu.
Su kawu kuwa sai zare idanuwa sukeyi a mota da manyan rigunansu da sukai uban squeezing.
Tafiya me tsayi da azaba sukai har zuwa porthcrt wanda daga can a ranar suka kamo hanyar abuja wadda suka kwana suna dukan hanya kowa zuciyarsa baa kwance ba.
Koda suka iso abuja anfito asuba har gari yayi haske dan haka a tasha sukai sallah su kawu suka siya bread manya manya da lemu suka zauna suka sha suka koshi dayake suna fitowa binni dan haka basuda wani kauyenci sosai.
Ummah ma tayi tayi jannah taci wani abin amma sam ta kasa sakawa cikinta komai harbawa zuciyarta keyi sosai tsoro takeji sosai da fargaba.
Ummah ganin jannah ta kasa cin komai itama kasa cin komai tayi suka samu mota suka hau suka kama hanyar prison.
Karfe goma motarsu ta tsaya a bakin gate din da ake tsayawa jira.
Fitowa tayi kafafunta na kasa daukanta tayi baya zata zube Ummah tayi saurin tareta tana kallan idanuwanta da sukai jajir kamar zasu kone sbd harbawan da zuciyarta keyi numfashinta fara sarkewa yayi ta zubawa kofar fitowan idanuwanta kowace daqiqa numfashinta sake sarkewa yakeyi tana kallan time na agogon dayake gaban qatuwar kofar shiga akan idonta karfe goma sha daya ta buga wadda tai daidai da bude karamar kofar da akai Ammar ne yafara fitowa wanda taja wani irin numfashi tana yin baya ahankali kafin Maheer ya sako kai waje shima a natse fuskarsa cikeda qasumbar fuskar data sauya kammaninsa ya koma kamar uztaz......
Sake numfashim me karfi ta sake ja idanuwanta na cikowa da hawaye masu tsananin zafinda kafin su gangaro Dad dinta ya sako kai ya fito take ta fasa wani kukan daya sakasu dagowa suna kallanta ta tafi wani irin gudun gaske ta nufesa tin bata qarasoba ya bude hannayensu yana jin ayau dukkanin baqin cikinsa da quncinsa ya qare.
Fadawa tayi kansa suka rungume juna da karfin gaske yana sama da ita a jikinsa yana ambatar sunayen Allah cikeda gode masa.
Kasa sakin juna sukai tana wani irin kukan farin cikin dayake neman fasa kirjinta.
Shima qanqameta yake sake yi yana ambatar sunanta hannuwansa har rawar farin ciki sukeyi kamar zuciyarsa zata bude sbd farin ciki.
Sakinsa tayi ahankali ta fada kan Maheer wanda yake jin tsananin kaunarta me karfin yana shafa kanta yana cewa
"Alhamdullilah ya Allah"
Sakinsa tayi ta juya kan Ammar dake kallanta yana tsiyayo hawayen kewarta ta fada jikinsa shima tana rungumesa cikeda tsananin sabuwar kaunarsa da kewansu duka.
Rungume junasu sukai su dukansu suna kuka kafin suka saki juna suna juyawa gurinsu kawu da Ummah dake tsaye suna kallansu.
Zubawa juna idanuwansu sukai tsakanin Dad dasu kawu sbd sun gane junansu tsaf dan haka kunyarsu ce ya rufe Dad din.
Barka da fitowa su kawu sukai musu cikeda kulawa kafin Ummah itama tai musu sannu da zuwa suka fada mota gabaki dayansu suka bar gurin hannun jannah na cikin na mahaifinta dayan hannun kuma yana cikin na Ummah da suka saba zama a hakan.
Tasha aka mayar dasu sbd basuda gurin zuwa.
Sallah sukai gabaki dayansu kawu ya siyo musu bread da panke da lemu sukaci suka koshi kowannensu farin ciki kamar zai fasa zuciyoyinsu musamman Ammar daya kasa dauke idanuwansa daga kan jannah dayake kamar ya hadiyeta ya bata rayuwar da babu wanda zai tana ganinta babu farin cikinsa kamar yanxu da babu auren kowa akanta AZIZ LIMBA yabar rayuwarsu har abada ba dawowa.
A tashar suka kwana a zaune suna manne da juna tana tsakanin Ahalinta da Ummanta.
Ana sallame sallar asuba motar da zasubi ta fara shirin dagawa
Karfe 7 motar ta fice daga tashar ta kama hanyar zuwansu kauyen da basusan rayuwar da zasu tarar acanba wadda basu tana sanin yaya akeyinta.
#MAMUH
#BESTStory
#BEST LOVE
#NEW LIFE
#KALBIM
#BEST ROMANCE
#AZIZ AY LIMBA
#JANNAH ZAD
#AYSH NICKY
#AMMAR ZAD
#FATIMA UMMAH ZAD
#DZAD
#END OF PART 1
ALHAMDULILLAH INA GODIA GA ALLAH DAYA NUNA MANA KARSHEN PART 1 WANDA ZAMU FARA PART 2 INSHA ALLAH BAYAN RAMADAN IDAN ALLAH YA NUNA MANA WANDA KUMA GABAKI DAYA LABARIN INSHA ALLAH YANA CIKIN PART 2 WANNAN DUKA SHIMFIDA NE,
INA ROKONKU AKAN KADA KUCE KOMAI GAMEDA TAFIYATA HUTU TIN YANXU SBD WLH TALLAHI BANDA LAFIYA SOSAI DAUREWA KAWAI NAKEYI SO BANASON NA LALATA MANA LABARIN SBD HALINDA NAKE CIKI SHIYASA,
KUYI MUN UXURI KUNSAN DUK ME RAI YANA TAREDA ZUWAN LALURAR CIWO,
KODA BAN TAFI HUTUN BA YANXU DOLE ZANJE HUTUN AZUMI DAN HAKA KUYI HAKURI MU JIRA DAWOWAN HUTU INSHA ALLAH ZAMU TSIMA MU NISHADANTU MU ILAMANTU KUMA MU SAMU DUK ABINDA MUKESO A LABARIN WANDA YAKE TAFE DA ABUBUWA DA YAWA.
NGD ALLAH YA NUNA MANA MUN DAWO HUTU LAFIYA AMIN.
ALLAH YA SAKAWA KOWA DA ALKHAIRINSA NA BIBIYATA DA KUKAI.