Showing 144001 words to 147000 words out of 185083 words

Chapter 49 - Kalbim Book 1 Complete Hausa Novel

Mamuhgee   

23 Sep 2025

5493

sbd ganin kaman ransa a tsananin bacen da basu taba gani ba.

Ciki nufa kai tsaye zuwa bangarensa,

Koda ya shigo main Living room na gidan su Mama na zaune suna fira amma babu wanda ya iya ko kalla ya wuce ciki.

Yana isa palonsa tin a kofa yafara zare rigarsa ya nufi bedroom ya fada toilet ya sakarwa kansa ruwa da sauran kayan jikinsa.

Sayd ne ya samesa har bathroom din dauke da Maganinsa da ruwa ya basa ya karba ya shanye yana rufe idanuwansa ahankali.

Ficewa Sayd yayi yabarsa tsawon mintina ya samu dawowa daidai ya fito sanye da bathrobe fara kal ya zauna kan kujeran gaban dresser yana zubawa fuskansa idanuwa,

Gangaro da idanuwansa yayi akan lips dinsa da suka sauya kala,

Kasa motsawa yayi tsawon lokaci kafin ya rintse idanuwansa ya bude yana jin tsanar kansa kawai,

Tsanar zuciyarsa yaji yanayi sosai da sosai sbd ta cutatar da kaunar dayakewa Ummitansa,
Zuciyarsa ta zama tamkar maqiyiyarsa a yanzu data bawa kanta damar karban feelings din dabai kamata ba,
Tayaya zai iya bari zuciyarsa tayi wannan gagarumin lefin na budewa batareda sani ko ankararsaba,
Tayaya wani yanayin daba na fishi da zafi da tsana da qiyayya ba zai samu qanqanuwar dama?

Rintse idanuwansa yayi da suka sauya take yana jin tsanar kansa da gasken gaske,

Zaiyi yaqi da zuciyarsa da gasken gaske bazai taba barin kowane irin yanayi ya shigesa ba koda hakan na nufin illata kansa ne,
Bazai taba bawa Zaadens damaba,
Bazai taba barin kowane irin yanayi ya shiga tsakaninsa da tsananin tsanarsu da qinsu da suka riga suka zaune a ransa ba dan haka zai tabbatarda yayi abinda yake gabansa ya raba kansa da duk wani abu dazai sake tina masa su har abada.



*******A zadeens kuwa wata irin jijjiga Ammar keyi kaman wanda ya samu ciwon jijjiga,

Zuciyarsa ce ke neman kasawa dan haka cikin gaggawa Maheer ne ya daukesa suka fito dashi zuwa Dakinsa Anny na kokarin hada masa taimakon gaggawa duk da wannan karan gabaki daya basu taba ganinsa a mummunan hali irin wannan ba,

Dad dayake jin jininsa ya gama hayewa sama da kansa ya ciro wayarsa ya kira Abraham yace cikin gaggawa su qaraso Zaadens kawai.

Suna jin hakan driver ya juyo zuwa zaadens dasu batareda sun isa masaukinsu ba.

Jannah gabaki daya jin tayi ta qarasa rasa kuzarinta jikinta yayi sanyi sbd zuciyarta tagama mutuwa akan inda bai kamataba,
Zuciyarta ce ke juyata batada tinanin kanta ko hankalin kanta sai abinda zuciyarta take sakata,

Son AZIZ LIMBA kaddara ce da jarabawa me girman gaske da Allah ya kaddaro mata wadda batasan tayaya zata iya yakice ta daga ranta ba,

Ayau idan ba karya idanuwa da zuciyarta suka gano mata ba tsananin kishint ne ta hango a idanuwansa wutarsu na ci,

Kishi ne mai zafi da karfin gaske da bata taba ganin irinsa a idanuwan Ammar ba,
A irin wannan yanayin ne kuma ta hango trauma me kargin gaske a tattare dashi da zata iya cewa zai iya komai a lokacin sbd fita hayyaci,

Hope taji tasamu akan soyayyarta da batada tabbas,
Jin tayi a daidai wannan lokacin zata iya cigaba da jure komai akansa,
Jin tayi zata iya kasancewa dashi har karshen rayuwarta sbd basa kulawa da kariya a duk lokacinda yanayinsa zai iya motsawa wanda ta tabbatarda duniya batasan dashiba kaman yanda na Ammar dinsu yake kusan a bayyane.

A yanxu kuma da idanuwanta suka sauka akan mummunan yanayin da Ammar yake ciki jin tayi ta tsani kanta gabaki daya sbd bataiwa soyayyar da suka taso a cikinta adalciba,
Ammar shine yaya mafi soyuwa aranta da ko babu aure zai iya komai akanta kaman yanda yakamata ta kula dashi fiyeda kowa a familynta...

Isowan Dr Abraham ya saka aka fara basa taimakon gaggawa wanda ya saka hankalinsu sake mugun tashi sbd jikinsa baya karban kowane taimakon da ake kokarin bawa zuciyarsa dake neman dena bugawa.

Cikin damuwa Dr Abraham yace dole ayi gaggawar zuwa asibiti dashi.

Basuda zabi dole aka daukesa suka kwasa cikon matsanancin tashin hankali aka nufi asibiti dashi.

Ana isa dashi kai tsaye bangaren masu asibitin aka nufa dashi take likitoci dasu dr Abraham din aka rufa akansa.

Mimi tayi kuka har idanuwanta sun gaji dan haka suka zubawa sarautar Allah ido suna jiran tsammani,

Gabaki dayansu suke asibitin banda jannah da bazata iya fita koinaba sbd ita kanta a yanzu tsanar kanta takeyi sbd tana tsakiyar da batasan me takeso ba.

Daddy mahmoud gida aka koma dashi sbd zuciyarsa dake masa ciwo shima sbd sai yanzu yake jin kansa cikin tsananin nadama da baqin cikin abinda akaiwa 'dan zayneb,

Sbd girma da tsananin kaunar da sukewa zayneb ne jannah ta samu kaunar me girman da suke mata a yanxu wanda Ammar ne ya bata wannan kaunar wadda shi ya kamata suwa,

Shine wanda sukewa kaunar zayneb bayan barinta duniya sedai kuma irin tsananin kauna da kwallafa rai da yayi akan jannah tinda ta fado duniya ya saka suke mata kaunar datake a cikinta ayanzu amma a lokaci daya son zuciya da makancewa ya sakasu sakasa a wannan mummunan halin dayake a ciki yanzu a lokacin daya kamata su tsaya su hana ko waye tabasa.

Dad ma tsananin damuwa da baqin cikin hukuncinsu ne y saka nasa hawan jinin tashi anan asibitin shima aka shiga basa taimakon sbd sosai jininsa ya hau din.

Har dare kwata kwata baa samu sauki a lamarin Ammar ba wanda duk rashin imaninka kallo daya zakai masa ya baka tsananin tausayi sbd ciwo dai ya sauyasa a lokaci daya.

Kaf ahalin zaadens babu wanda baya cikin damuwa me tsananin gaske da tausayin Ammar din,

Jannah kanta datake gida tayi kuka mai tsananin gaske tana jin inama rayuwarsu ta baya familyn ta dawo a lokacin da suke tsananin kaunar juna basa cikin matsala ko damuwar komai ta duniya.

A asibiti gabaki dayansu familyn suka kwana banda daddy mahmoud da jannah dake fama da kansu a gida.
#MAMUH

ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
77
*UMMU_MAHNOOR LUXURIES*
(Best luxuries shop)
08034469681
08135142610
Aslm Alaikm ina kuke masu neman luxuries na kayan alfarmar kece raini?
Ina masu son su saka sitirar alfarma ta zamani ta manyan mata masu aji da zaa kalleki kallo daya asan sitirar alfarma e kika saka?

Shin kunsan me ake nufi sa kayan asalin yan gayu da nuna gayu?
Sitirar Alfarma kikeson sakawa?
Sitirar da kike ganin manyan mata da ita?
Sitirarda zakiyi gayun sallah dake da yaranki a dauka waje kikaje da kanki kika siyota?
To kizo ga damarki ta sameki sbd UMMU_MAHNOOR LUXURIES ta kawo miki sauki har gida,
Karkice se masu kudi ke iya siya har kema me yar dama zaki samu naki da saukin kudi kuma best quality da kalar zamani data yan gayu,

Nidai Mamuh nace duk wadda ke son a buga gayun sallan bana da ita da 'yayanta to tazo gurin UMMU_MAHNOOR LUXURIES tai siyayyar sallanta harma zuwa gaba dan nasan zakuji dadi da fahimtar abinda nake fada akan kayanta💯💯
Abubuwan da zaki samu a gurinta with the best quality na wayayyun mata masu aji yan gayu sune;

Atampopi
Laces
Shadda
Materials
Shoes
Bags
Veils
Trolleys
Jewellerys
Oil perfumes

Numbers
08034469681
08135142610

Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries


************
Wash gari dole Dad gado aka basa a asibitin sbd Bp dinsa kwata kwata yaqi dawowa daidai.

Mimi ma taqi yadda ko kadan ta baro asibitin itada Saleem wanda Ammar yake cikin ransa sosai dan haka dole Maheer shima ya kasa baro asibitin.

Karfe 11 na rana Sayd y iso asibitin sanye d face mask da fcap daukan Jannah wadda tinda sassafe ta iso asibitin ko tsayuwa bata iya yi da kujera aka kawota.

Sayd na shigowa dakin Ammar na farfadowa dan jannah ta kalli Sayd din tace yabarta zata dawo daga baya.

Baice komaib wayarsa ya fidda ya saka kiran LIMBA yana dauka ya bata wayar yana juyawa ya fice daga dakin yabarta tayi magana dashi idan ya Yadda.

Harta yanke bai dagaba dan haka ta ajiye wayar akan kafafunta tana kallan Ammar wanda idanuwansa dake a jeme suka sauka akan hoton dayake kan wayar sayd baro baro na Ummitah da AZIZ wanda asalin kamanninsu suka bayyana kaman an tsaga kara tana dariya a jikinsa.

Duk da baya gani sosai rawa hannuwansa suka fara yi yana son nuna hoton Ummitah dayake cikin wayar wadda sukeda hotonta haryanzu a cikin file na jannah.

Rikicewa gabaki daya yayi yana wani irin yunkurin magana hannuwansa da bakinsa na rawa.

Sayd ne ya shigo dakin ya karbi wayarsa yana barin asibitin da jannah ya maidata gida sbd itama neman rikicewa jikinta keyi sbd tashin hankalin ganin yanayin Ammar.

Da gudu likitoci sukayo dakin tareda su Mimi dasu Maheer dasuka je dakin dad dubosa.

Suna shigowa Ammar ya damqe maheer da karfin gaske yana kallansa yana kallan Abraham muryansa n sarkew yace

"AZIZ limba da donor dinmu,
Zuciyar dayake bugawa a zuciyar Jannah AZIZ LIMBA,AZIZ LIMBA ya.....

Ganin yana neman fallasa komai a gaban mutane da sauran likitocin batareda yasan me yake fada ba ya saka hankalinsu gabaki daya tashi cikim mugun faduwar gaba da shiga Rikitaccen yanayi dr Abraham ya masa allurar data sakasa zubewa a gurin yana tinanin kwakwalwan Ammar tabbas ta tabu.

Anny jin tayi zufa ya rufeta hankalinta na neman tashi da abinda yake shirin faruwa idan baa nema maganin ciwon Ammar da gaggawaba zai iya tona asiri su shiga masifar da babu fita.

AZIZ LIMBA karfe 7 na dare motarsa ta isa Zaadens tareda Sayd wanda suke shirye tsaf dan gama komai su tattara su koma inda suka fito.

Babu kowa kaf a mansion din sai masu aiki da securities sai Daddy mahmoud daya fito jin isowansu sbd matarsa mummy tayi asibiti da daren dubo Ammar da kaiwa su Mimi abinci masu tarin yawa kala kala.

Kasancewan Daddy mahmoud din shima yanada weak heart ya saka abu kadan yake sakasa samun attack ko bugawan zuciya shiyasa ko farkon samun matsalar financial crisis dinsu ya kamu da paralys dakyar ya dawo daidai dan hakanne tin jiya yake fama da ciwon kirji.

A yanayinda ya fito yana kallansu ya saka AZIZ masa kallo daya ya hango zuciyarsa gap take da bugawa dan haka fasa zama yayi ya kalli Say wanda yayi amfani da sabuwar waya ya tura sako zuwa wayar Anny.

Kallan Daddy mahmoud din AZIZ yai a qasqance kafin ya bude baki yace

"Ka dena daga hankalinka akan Ammar Zaaden sbd ya riga ya rasu.........

Wani mummunan bugawa zuciyar daddyn tayi ya dago da sauri yana kallan AZIZ hannuwansa na rawa da kafafunsa ya bude baki zaiyi magana AZIZ din ya katsesa da cewa

"Tinda wuri zaka buga zuciyarka bayan baka gama jin abinda zan fada maka ba"

Girgiza kai daddy mahmoud yayi yana dafe kirjinsa muryansa na rawa yace

"Ammar ya rasu??

"Ba shi kadai ya rasu ba hadda Dan uwanka shima lokacinsa yayi na......

Faduwa Daddy mahmoud yayi yana dafe kirjinsa da karfi zuciyarsa na kokarin bugawa ganinsa na daukewa yana son yayi magana amma ya kasa azababbiyar azaba kirjinsa ke masa....

Durqusawa gabansa AZIZ yayi shima hannuwansa na dan rawa idanuwansa n sauyawa zuwa jajir yace

"Kirjinka baya iya dauka ko?
Fiyeda hakan na samu kaina a lokacinda na samu labarin mutuwar yar uwata,rabin jikina,rayuwata,uwar Falaq Aziz wadda ayau zuciyarta take bugawa a kirjin 'yarku da kukaso ta rayu kuka kashe tawa rayuwar........

A cikin tsananin azabar datafi karfin kirjinsa Daddy mahmoud y dago idanuwansa da sukai jajir din azaba ya kalli AZIZ cikin tsananin mamaki da shock idanuwansa n fitowa sosai sbd azaba sa shock yana kallan fuskan AZIZ wanda sai a lokacin yake ganin kammaninsa da Yarinya me cikin da suka samarwa Jannah sbd akwai hotonta a cikin file din jannah har yau.....

Magana yakeson yayi amma ina maganganun AZIZ ragargaza zuciyarsa sukeyi zuciyarsa na qara samun bugawa.

Shi kansa AZIZ din cikin wani matsanancin halin yake magana yana fada masa yanda ya shiga cikinsu da yanda zai qarar dasu daya bayan daya ya tabbatarda ko sunansu aka fada sai an la'ance su an tsinewa zuriarsu.


Kofa Sayd ya kalla sbd jin shigowan mota gidan ya tabbatarda Anny ce wadda ta iso gidan a gigice.

Ko gani batayi sosai ta iso gidan sbd sakon daya shigo wayarta na cewa

AZIZ LIMBA na hanyar isa Zaadens Daddy mahmoud ya nemesa zai basa takardun ciwon jannah daya buqata kuma tafi kowa sanin Sun goge sunan Ammar a cikin likitocin ciki daga nata saina sauran likitocin.

A yanda tasan Familyn tsaf zasu cire sunan Ammar abar nasu hakama akan neman lafiyan jannah zasu iya fidda file dinta a bawa AZIZ LIMBA wanda hakan na faruwa sun gama Rayuwa a doran qasa sbd bazai rufa musu asiriba,

Hakama matakin da Ammar yake kai yanzu na rashin lafiya harda kusan wadda ta shafi kwakwalwa take familyn zaa rifesa a matsayin baida lafiyar kwakwalwa ya sha ita kuwa fa??

Inaaa,bazata yadda ba wlh ko kadan....

Kwata kwata fita tayi hayyacinta taji bata gane komai bayan ta riga isa gidan kafin isar LIMBA.

Gabaki daya ta fice hayyacinta sbd maganar Ammar datake yawo a cikin kanta wanda sai yanxu take kokarin tina kammannin donor din jan wadda take son hadawa da kammanin AZIZ din tanajin kanta na neman kuncewa.

Kafafunta har rawa sukeyi ta iso palon daidai lokacinda Su AZIZ sun riga sun bar palon Daddy mahmoud ya daga hannu ya bude baki zai ambaci AZIZ din cikin tsananin azaba Anny bata tsaya lura da yanayinsa ba kawai ta dauka AZIZ din zai kira dan masa magana dan haka ta fidda allurar data taho da ita ta soka masa a wuya tana juye masa ruwan ciki daidai lokacin Saleem da mommy na shigowa palon shikuma AZIZ da sallama me nutsuwa ya qarasa cikin palon jannah wadda ke zaune shiru idanuwanta sunyi jajir ta qara fadawa sosai a kwana da wunin.

Dago idanuwanta tayi ta kalli kofar jin muryansa da qamshinsa a lokaci daya.

Ajiye kafafunta qasa tayi ahankali qasa tana kallansa a sanyaye sbd rabonta da ganinsa ko jinsa tin shekaran jiyan daya bar nan din.

Takowa yayi ahankali cikin nutsuwa shima yana kokarin daidaita kansa daga halinda yake ciki na tafarfasan zuciya da tsananin ciwon zantukan daya maimaitawa zuciyarsa na yanda suka rabasa da Ummitah.

Kallon dayake mata ne ya sakata miqewa ahankali tana jin zuciyarta na narkewa akansa taku daya tayi ta kasa ta tsaya tana kokarin faduwa qasa zaune ya tarota jikinsa yana kallan tsakiyar idanuwanta da suka kasa daukan kallansa ta lumshe su tana sauke ajiyan zuciya jiki a mace.

Shiru yayi baice mata komai fuskanta kawai yake kalla yana jin yanda zuciyarta ke bugawa Kirjinsa....

Komai nata yana nuna yanda take tsananin sonsa ne wanda hakan yake masa illa mai girma a nasa bangaren sbd yasan soyayya zata iya zama rauninsa kaman yanda take rauninta...

Ihun Mummy me karfin gaske ne ya sakashi lumshe idanuwansa ahankali ya budesa akanta ita kuma a lokacin ne ta bude nata idanuwan ahankali tana kallan kofa.

Jame jikinta tai ahankali tana son zuwa palon amma batada karfin hakan a jikinta ko kadan dan haka ta kasa dagowa ta kallesa.

Lura da hakan ya saka hannunsa ya zagoyo qugunta ta mannu da jikinsa ahankali ya dauketa gabaki dayanta a jikinsa ya nufo kofar da ita zuwa babban sitting room na gidan da hayaniyar ke fitowa ta can.

Sayd shima a lokacin ya shigo palon kaman yanzu yake shigowa shima,

Anny da hannuwanta ke rawa kallan Daddy mahmoud din dayake wani irin numfashi yana kokarin rasa ransa sbd Alluran datai masa kwata kwata baa yiwa wanda yake cikin heart attack hakan na matiqar hadarin gaske,

Ganin su Mummy da Saleem akanta ya sakata fara rawar jiki tana kokarin daidaita kanta ta kalli Mummy tana cewa

"Mummy koda nazo inaga ya samu attack ne ina kokarin basa taimako ne zamu iya gaggawan kaisa asibitin"

Mummy bata iya amsata ba da gudun tayo kansa itada saleem tana ganin yanda yake wani irin jan numfashin wahala idanuwansa na rufewa shine ta fasa ihun me karfi tana kiran sunansa.

A lokacin ne AZIZ da jannah din suka fito idanuwan Daddyn akan AZIZ yana kallansa wasu hawayen azaba da dana sani dana son ya fada musu waye AZIZ limba suka gangaro masa idanuwansa suka rufe ahankali cikeda azaba.

Saleem ne da Sayd suka daukesa da gaggawa zuwa mota hakama jannah rawa jikinta yafara tana kallansu cikin tashin hankali da fargaban sabuwar masifar data tinkaro su.

Fitowa sukai dukkaninsu harabar gidan yacewa Sayd yaje tareda Saleem ya taimaka masa shikuma ya karbi key din motarsa ya saka jannah a ciki motar saleem na fita tasa tabar mansion din shima ya nufi gida da ita.

Mummy da duk ta fita hayyacinta take sbd tsananin tashin hankali daqyar Anny ta iya sakata mota itama a rude hannuwanta na rawa suka bi bayansu saleem din sai a lokacin take jin tsoron rashin tinanin datai na bin sakon da kyau taga inda ya fito ta jefa kanta cikin kaddara,
Hakama waye wannan dayasan sirrin su bayansu dazai mata text din wanda takeda tabbacin yayi magana ne sbd yasan sirrin dasuke boyewa.

Tin a mota saleem cikin damuwa da tashin hankali ya sanarwa Maheer suna hanyar asibitin da Daddy mahmoud.

Miqewa Maheer yayi cikin tashin hankali yana kallan Dad daya ji abinda aka fada dukkaninsu hankalinsu na tashi da sabon tsoro.

Koda aka iso asibitin da Daddy mahmoud gabaki dayansu Dad harda Mimi sun fito tareda tarin likitocin da zasu karbesa da nurses a shirye sbd gaggawar basa taimako sbd sanin shi din yanada matsalar samun attack.

Dad da maheer idanuwansu sunyi jajir dad wani irin tsalle zuciyarsa keyi kansa na tsananin sarawa hakama maheer mimi kuwa duk ta rikice damuwa na qarar mata.

Motarsu n shigowa asibitin da gudun gaske saleem ya iso emergency din da ita da gudu aka rufu kansu ana fiddosa hadda Sayd wanda fuskansa ke rufe sa facemask sbd Abraham da Ken na gurin.

Yanda aka daukosa akai ciki dashi ne ya saka zaadens din gabaki dayansu shiga matsananciyar damuwar datafi ta farko sbd koda aka iso asibitin Rai ya riga yayi halinsa sedai hakuri.
#MAMUH



ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
78
*UMMU_MAHNOOR LUXURIES*
(Best luxuries shop)
08034469681
08135142610
Aslm Alaikm ina kuke masu neman luxuries na kayan alfarmar kece raini?
Ina masu son su saka sitirar alfarma ta zamani ta manyan mata masu aji da zaa kalleki kallo daya asan sitirar alfarma e kika saka?

Shin kunsan me ake nufi sa kayan asalin yan gayu da nuna gayu?
Sitirar Alfarma kikeson sakawa?
Sitirar da kike ganin manyan mata da ita?
Sitirarda zakiyi gayun sallah dake da yaranki a dauka waje kikaje da kanki kika siyota?
To kizo ga damarki ta sameki sbd UMMU_MAHNOOR LUXURIES ta kawo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login