Showing 51001 words to 54000 words out of 152254 words
bai dame ni ba, koma wacece, Ma'aruf , madaki, da kuma wannan yarinyar da ka kawo, sai na tabattar da na kashe su gaba ɗaya, ko ta halin ƙaƙa".
"A'a master, mace ce, wataƙila sakata aka yi, dan Allah ka yi haƙuri, zan yi maka bincike a kanta "
"Idan ka kuma gaya mini wannan sunan, zan hankaɗaka daga kan dutsen nan"
Walid ya yi murmushi ya ce "Baka girmama sunan ne viper, idan har ka damu har haka, yakamata ka bawa kanka da lafiyarka kulawa, ta haka ne zaka yi abun da ka ke so, yanzu ka taimaka ka sakar mini kafaɗata, wallahi kamar na karye"
Ƙurawa walid ido yayi, Walid ya sunkuyar da kansa, ya san ya tunzuro zuciyar Viper, sakar masa kafaɗarsa ya wuce shi, ya fara sauka daga kan dutsen.
Har bayan azahar Nabila ba ta farka ba, su kansu ma'aikatan asibitin, sun yi mamakin irin baccin da Nabila take yi.
Hankalin sumayya kuwa yayi mummunan tashi, ganin Nabila ba ta farka ba.
Bayan la'asar sai ga Abba, tare da Salim, wanda ƙani ne ga Nasir.
A ɗakin da Nabila take suka tarar da Sumayya.
Sumayya ta gaishe su, Abba ya amsa ya ce "Sumayya ke ce a wurinta?"
Ta jinjina kai ta ce "Eh Abba"
"Ai ni ce mini tayi, ba wani abun damuwa bane, ana gama yi mata abun da za ayi mata, za ta koma gida, sai da na koma na tarar ba ta dawo ba"
Sumayya ta ce "Eh, ai ta samu bacci ma".
Idonsa ya sauka a kan gefen rigarta, da take a huje ga jini, cikin mamaki ya ce "Ya nake ganin jini a jikinta?"
Da sauri Sumayya ta ce "amm, dama wai faɗuwa suka a adaidaita sahu, shi ne ta ji rauni"
"Amma ni bata gaya mini haka ba ai" yayi maganar cikin matsananciyar damuwa.
Wata irin miƙa Nabila ta yi, tare da yin salati, duk suka yi kanta suna yi mata sannu.
Suka din ga jera mata sannu, suna yi mata ya jiki.
Sumayya ta kirawo likkta, ya zo ya ƙara duba Nabila, yayi rubuce-rubuce a file ɗin ta, ya sallame ta.
Abba ya din ga yi mata faɗan meyasa ba ta gaya masa ta faɗi a adaidaita sahu ba, ta nunawa likitoci ciwon da ta ji.
Sumayya ta kalleta, suka haɗa ido, sai ta fahimta, dan haka ta ce "Ai ba wani ciwo bane Abba, mu tafi gida na gaji".
"Kin tabattar babu wani abu da yake yi miki ciwo?"
Ta jinjina kai alamar eh, suka fito zuwa motar Abba, suka tafi tare da sumayya, su ajiyeta a gida.
Sumayya ta kalli Nabila ta ce "Wai ya aka yi ɗazu daga fita ta, ki ka fara bacci, kusan awa huɗu ki na bacci?"
Nabila ta ɗan yi shiru tana tunani, ta ce "Wani likita ne ya shigo yayi mini allura"
"Ba Nurse ba, likita da kansa?"
Nabila ta jinjina kai alamar eh, Sumayya ta yi shiru ba ta ce komai ba, a zuciyarta, take jinjina tsagwaron rashin imanin honorable Indabo, kenan idan ba ta yi abun da suke so ba, za su kashe Nabila kenan.
Gabanta ya faɗi, ta kalli Nabila da ta kashingiɗa, tana ta lumshe ido, alamar baccin bai isheta ba.
Tunani take da wa zata tattauna wannan maganar ne? ko wurin hukuma ta kai, ba ta da shaida ta zahiri, kuma ta san babu wani mataki da za a iya ɗauka a kai.
***
Yana kwance a kan gadonsa yana kaɗa ƙafa, hannunsa ɗaya yana riƙe da waya, ɗaya kuma kan shisha, yana ta fesar da hayaƙi.
"Hello" sautin muryar mace ya fito daga cikin wayar.
Ya ce "Hello, how far?"
Ta amsa da "Ya aka yi?"
"Mun yi magana da tsoho, ashe kin gano in da yarinyar nan take?"
"Eh, na gano, sai dai sun ce ba za su karɓi kuɗi ba, hakkinsu suke nema, dan haka sai ka san yadda zaka yi"
Yayi murmushi ya ce "Ki san yadda za ki yi dai, ai kin san dolenki ki ɓoye laifin nan ma, kamar yadda ki ka saba".
Cikin takaici ta ce "Ka ce dole?"
"Ƙwarai dole, idan asirinmu ya tonu ai kema naki ya tonu, yanzu wane matakin ki ka ɗauka?".
Tayi ajiyar zuciya ta ce "Yadda na lura, takamaimai, ba su san waye kai ba, daga ita bar babarta, dan haka zan je gidan ita Antyn taka, a bamu adress ɗin maigadin da suka kaita Asibiti lokacin da abun ya faru, duk da Yallaɓai ya gaya mini, an sallame shi daga aiki, amma dole za mu yi framing ɗin sa da laifin, in case wani zai tayar da maganar, sai mu ce mai laifin ya shiga hannu, abun da nake ƙoƙarin yi kenan"
Ya kwashe da wata irin dariya ya ce "Daɗi na da ke akwai brain, anyway ina ne gidan su yarinyar, she needs to learn a lesson, da ita da babarta da ɗan jaridar da ya saka zancen".
Da sauri ta ce "Kar ka kuskura, ba zaka ɓata mini aiki ba, na gaya maka ba su san kai waye ba, idan kuma ka yi wani yinƙuri, da ya samar da wata ɓaraka babu ruwana a ciki na gaya maka"
Abdul ya ce "Na ji, ina son ganin yarinyar ne kawai"
"Abdul, ina da abubuwan yi da yawa a gabana"
"Naja'atu, kar ki katse mini waya, ki bani adress ɗin yarinyar".
Kashe wayar ta yi, tare da jan tsaki, ta cigaba da rubuce-rubucenta.
Nabila sai wajen sha ɗaya saura na dare, sannan ta ɗan dawo dai-dai, sai a lokacin ta samu ta yi wanka, a cikin ɗakinta ta tsaya tana kallon cikinta, da ciwonta, da haryanzu yake yi mata zafi.
A haka ta lallaɓa, tayi shafe-shafen skin routine ɗin ta, ta fita kitchen ta haɗo tea, ta dafa indomie, ta koma ɗakinta, ta saka wayar Viper a caji.
Ta ɗauki wayarta ta tarar da tarin missed calls ɗin Nasir, ta kira shi ta saka wayar a hansfree, tare da kashingiɗa.
Ya ɗaga tare da yin sallama, ta amsa masa a hankali.
"Arfa ko ki neme ni, ki ji ya na sauka ko?"
A shagwaɓe ta ce "Am sorry, i got a little accident ne, a asibiti na wuni"
A ɗan rikice ya ce "Subhanallah, garin yaya meyafaru?"
"Don't mind, akwai labari ne"
"Wane irin labari? Amma dai kina lafiya ko?"
Tayi murmushi ta ce "Gashi muna magana da kai, lafiya ƙalau nake, ka ce Viper daga prison aka sake shi ko? Laifin me yayi aka kama shi?"
Nasir ya ce "Ohhh my God, meyasa ki ka damu da lamarin nan ne har haka Arfa?"
"Ni ka amsa mini Please"
Ya ce "Yeah, amma ya shiga prsion, ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba, shigarsa na ƙarshe ne, ya ɗan daɗe, kuma da alama laifin da ya yi babba ne, sai dai ba wannan ne a gabana ba, kama shi nake son yi.
Akwai jami'anmu suna yawo a farin kaya, suna neman bayanai a kansa"
"Ka daina wahalar da kanka, na samo maka abubuwan da za su sauƙaƙa maka komai"
Ƙasa-ƙasa yayi da murya ya ce "What do you mean? Ba na son wasa fa".
Ɗan shiru ta yi, ta tabattar idan ta gaya masa gaskiya a yanzu, ba gwaninta za ta yi masa ba, dan muddin ta gaya masa ta san in da yake, zai ce ta je wurin ƴan daba, zaneta zai yi, kuma sai ya gaya wa Abba ta shiga uku.
Dan haka ta ce "Da gaske nake, na je wurin wata client ɗin mu, a unguwar da yake, na samo labari, yana da yaransa da suke ƙananan dilallan tabar wiwi, amma ba su san in da yake ba, wai akwai wani guda ɗaya a tal'udu, yana sayar da katin waya bayan magariba, amma ƙwayoyi yake sayarwa, ya san in da yake".
Ya ce "Look arfa, ba na son wasa, daga zuwa unguwar wurin client, har ki ka samu wannan rahotannin?"
"Haba DSP, kar ka manta ni ma fa ma'aikaciya ce, wallahi ba ƙarya nake yi ba, daga majiya mai ƙarfi na ji labarin, na je wurin kuma na ga mutumin yana zaman sayar da katin wayar, idan baka yarda ba, idan ka dawo da kanka ka bincika"
Yayi ajiyar zuciya ya ce "No, ba sai na dawo ba, zan aika a bincika mini, ina fatan baki gaya wa kowa ba?"
"No, babu wanda na gayawa"
Nasir ya ce "Good, amma kar ki kuskura ki yi wani abu, da zaki saka kanki a cikin hatsari kin ji ko?"
Nabila ta ce "To, idan ka dawo zan baka wani abu mai muhimmancin da zai taimaka maka, amma sai idan zaka yi mini alƙawarin ba zaka dake ni ba, ko ka yi mini faɗa" tayi maganar tana kallon wayar Viper.
"Menene abun?"
"Sai ka dawo tukuna zan gaya maka, take care"
"Shikenan, Allah ya kaimu na dawo ɗin, ki kwanta ki huta"
"Ok bye-bye" ta kashe wayar ta ajiye, ta ɗauki ta Viper, da ta yi caji, ta kunna ta.
Ta kai wayar hancinta ta sinsuna, ga warin sigari tana yi, ga ƙamshin turare.
Ta fara shige-shige a wayar.
Cikin call log ɗin sa ta duba, ga lambobi nan, sai dai duk kiransa ake yi ba ya kira, sai jerin private number da ake kiransa da ita.
Ta duba cikin messages ɗin sa, babu komai a ciki, sai dai a cikin drafts ɗin sa, yayi saving ɗin wasu kwanakin wata.
Tayi shiru tana tunanin yadda ta ɗaukko wayar ta sa, lokacin da take tattare kayan jakarta, da ta buɗe idonta ta gansu a tarwatse, ta ga wayar a gefe, ta haɗa da ita tana sane.
Tayi ajiyar zuciya ta ce "Wani laifi ka yi aka kama ka, sannan aka sake ka, ba bisa ƙa'ida ba? Shi yafi cancanta ma in mayar da hankali in binciko, yadda ana kama ka, zan yi raising case ɗin nima, a hukunta waɗanda suka sake ka" tayi maganar tana sake mayar da wayar ta sa caji.
"Ko ban ce na san in da ka ke ba, wayarka zata bawa jami'an tsaron damar nuna in da ka ke".
Ta mayar da kwanukan kitchen, ta dawo ɗakin ta rufe ƙofarta ta kashe fitila za ta kwanta, sai dai tana kashe fitilar, sai ta ga kamar Viper ne a tsaye a gabanta, saura ƙiris ta kurma ihu, ta kunna fitilar tana zazzare ido, tana cigaba da ƙarewa ɗakin kallo, zuciyarta na saƙa mata ko ya biyo ta.
Da ƙyar ta nufi gadonta ta kwanta, gabanta na faɗuwa, ba tare da ta kashe fitilar ba.
Zumbur ta kuma tashi zaune, ta ɗauki wayar ta sa, ta sakata a cikin wardrobe ɗin ta, ta rufe ta ta dawo ta kwanta tana rarraba ido.
Sai dai fa fafur ta kasa bacci, tsoro ya baibayeta, mussaman idan ta tuna ya ce idan suka sake haɗuwa sai ya kashe ta, sai yanzu ma ta fara tunanin da yaya zata miƙa wayar nan ga DSP Nasir, dan dolen dole sai ya tuhume ta, to idan ya tuhume ta wace amsar za ta bashi? Yaya aka yi wayar ɗan daba ta zo wurinta?.
Sai kuma ta koma tunanin, yaya iyayensa suke ji, sun haifi ɗa ya zame wa mutane masifa a gari?.
Tsananin zurfin da tayi a cikin tunani, ya sanya, wani ɓarawon bacci, ya yi awon gaba da ita, sai dai baccin bai je ko ina ba, ta din ga jin numfashi a fuskarta.
A hankali ta buɗe idanunta, jin saukar numfashi a fuskarta, sai dai me, tayi tozali da fuskar Viper, ya kafeta da manyan idanunsa da suka yi jawur, dogon karan hancinsa yana taɓa nata, ko ƙiftawa ba ya yi.
A firgice ta yi ihu, ta faɗo daga kan gadon, jikinta na wata irin kyarma, tana jejjera numfashi, sai dai ta buge wurin ciwonta, dan har ya fara zubar da jini.
Sai da ta ɗago ta sake kallon gadon, sannan ta ga ashe filo ne yake taɓa mata hanci, sai ta ga kamar Viper.
Ta rintse idanunta tana addu'a, tare da dafe gefen cikinta da yake ta yi mata zafi.
Ɓangaren sumayya ma hakan take, dan kasa bacci tayi, dan ita kwanciyar ma gagararta ta yi, tayi dana sanin sha'awar fara aikin jarida, wace irin masifa ce haka tana zaman zamanta, ana neman mayar da ita ƴar ta'adda, saboda an fi ƙarfin ta.
Alwala ta yi, ta tayar da salla, ta din ga addu'a, tana fatan Ubangiji Allah ya tsare su daga sharrin honorable Indabo, mussaman Nabila da ba ta san wainar da ake toyawa ba, gashi a yau kawai an yi wasa da rayuwarta, ba tare da ta san hakan ba, nan gaba ba ta san me za su yi mata ba, kuma ta san muddin ta gaya wa Nabila, akwai ƙura dan za ta iya aikata abun da zai sanadin su rasa rayuwarsu gaba ɗaya.
Sai dai tana ta tunanin wace hanya Nabila ta bi ta ga Viper, tun da ta ce sun haɗu to lallai sun haɗu ɗin, hatsabibancin Nabila da taurin kanta, har tsoro yake ba ta. Tun da ta ƙududi aniyar yin sunan nan, idan ba wuƙa ta gani a maƙogwaronta ba, babu lallai ta haƙura.
Honorable Ma'aruf ne a tsaye yana ta zazzagawa Abdul masifa kamar zai ari baki, shi kuma sai cika yake yana batsewa yana harare-harare.
"Na fara gajiya da rashin mutuncinka Abdul, na gaji, gashi a banza ka nemo magana a wurin ƴar matsiyata, sun ƙi yadda a haɗa kai da su, a binne taiyar da ka shuka, dole sai na ɗau mataki a kai. In the next couple of years, kai zaka tsaya takarar deputy governor a garin nan, kamar yadda muka yi yarjejeniya da party, kafin na shiga, amma sai shashanci ka ke yi, so ka ke yi sai lokacin ya yi ƴan adawa, su ɓata mana shiri, na gaji da zubar da jini, saboda rashin hankalinka da wautarka, na ce ka yi aure ka ƙi, daga shaye-shaye sai neman mata, idan ma zaka yi yakamata ka san abun da ka ke ciki"
Abdul ya numfasa ya ce "Ka yi haƙuri, ni yakamata na goge wannan ɓarnar da kaina, ka karɓar mini address ɗin yarinyar, zan san abun yi"
"A baka ka je ka kuma yi wa mutane wani shirmen ko?"
Ya girgiza kai ya ce "No, na yi maka alƙawarin ba wani shirmen zan yi ba, zan goge komai ne kawai"
"Ɓace ka bani wuri" yayi maganar yana hakin baloƙoƙon da ya yi.
Nabila fa abu ya zame mata ga ƙoshi, ga kuma kwanan yunwa, wayar Viper ta zame mata larura, ta rasa yadda za ta yi.
Da safe Abba ya ce ta zauna a gida ta huta, saboda jikinta, amma ta ce masa ita ta ji sauƙi, fita za ta yi, da kansa ya ɗauke ta a mota, ya tafi kaita wurin aikin, suna tafe yana yi mata nasihohin da ya saba yi mata, amma da za a yankata, ba zata iya faɗar me yake cewa ba.
A gate suka haɗu da Director, yana ganin major kamar zai dungura, saboda risunawa cikin girmamawa, ya gaida major.
Ya amsa masa cikin girmamawa yana tambayarsa aiki.
Director ya amsa da "Aiki Alhamdilillah, yau kuma da kanka ka kawo ta?"
Major ya ce "To ya na iya, ƴar gudaliyata babu lafiya, kuma ta dage sai ta fito aiki. Ina fatan dai yanzu tana mayar da ka?"
Director yayi murmushi ya ce "Alhamdilillah, ta rage shiririta, tana aiki sosai ranar Alhamis ma za ta fita trial ita ce incharge of case ɗin"
Major ya ce "Masha Allah, idan ki ka yi wining, akwai special gift" Tayi murmushi kawai ta sauka daga motar, dan ba wani ganewa take yi ba.
A wurin aikin ma, jin ta ta din ga yi tamkar wadda ta shekara tana amai da gudawa, gaba ɗaya gaɓoɓinta a sage suke, da ta motsa, sai ta ga kamar za ta ga Viper a gabanta.
Layin Nasir ta kira, tayi sa'a ya ɗaga ya ce "Ya aka yi kuma?"
"Ka aika a bincika maka maganar mutumin nan ne?"
"Ki kwantar da hankalinki mana, ina sane zan aika".
"Ai kar ka zo ka ce ƙarya nake yi ne"
"Haba dai ni na isa ma"
"Yaya"
Ya amsa da "Na'am barrister Nabila maitama".
"Wane laifi Viper yayi na ƙarshe ne, aka rufe shi?"
"Ban gani ba a cikin record ɗin sa, waɗanda na gani dai, kawai rigima ce da mutane, da ta'amalli da miyagun ƙwayoyi da kuma dillancin su".
"Wace kotu da wace kotu aka taɓa kai shi?".
"Arfa ban sani ba wallahi, wai menene akwai matsala ne?"
Ta kashingiɗa ta ce "No, babu wani abu sai anjima"
Ta kashe wayar ta ajiye, ta tashi ta tafi office ɗin Barrister Habib.
Bayan ta yi sallama, ya amsa mata, yana ƙura mata ido, har ta ƙarasa ta zauna.
Kai tsaye ya ce "Menene matsalar?"
Ta ce "Na yi kama da mai matsala ne?"
"Eh mana, yau ba kwalliya, ba ƙwalisa ba biscuit, ba sweet a hannu, duk yau dai sai a hankali"
Tayi murmushi ta ce "Barrister ka bani dariya, saka mini ido ka ke yi kenan, ka san jiya a asibiti na wuni, shiyasa ban zo ba jiya"
"Eyya, ai na zata mulkin ne ya motsa, ki ka ƙi zuwa, tun da ke ba tuhumarki ake yi ba, ba kya laifi"
Sake sunkuyar da kai ta yi tana murmushi.
Shi ma murmushin ya yi ya ce "Ina jin ki, meyafaru, dan ba kya zuwa office ɗin nan sai da dalili"
Ta gyara zamanta ta ce "Barrister, na san ka san wani ɗan daba da ake nema ko? Aminu Viper"
Yayi mata ƙuri da ido yana kallonta.
"Dama wani labari na ji, wai wani laifi ya yi aka kai shi prison, kuma kawai sai aka sake shi ba bisa ƙa'ida ba, gashi sai ɓarna yake yi a gari" sai kuma ta yi shiru.
Yayi ajiyar zuciya ya ce "Ina jin ki"
"To shi ne, sonake na san wani laifin ya yi, ban sani ba dan Allah ko zaka bincika mini, a wace kotun aka yi masa shari'a"
"Meyasa ki ke son sani?"
"Eh, sonake idan an kama shi, na bibiyi shari'ar da za ayi masa, kuma na binciki meyasa aka sake shi da"
Wata ƴar dariya ya yi ya ce "Nabila kwanan nan na ga you are so much serious, amma kin san hakan kamar tarar aradu da ka ne ko? Amma let's see how far you can go, zan bincika miki in sha Allah, nan da 3days zan neme ki"
"Na gode sosai babban yaya, Allah ya ƙare ka, na gode sosai da sosai"
Yayi murmushi tare da jinjina mata da hannunsa ya ce "Ki huta little barrister "
***
Can gidan su rahama kuwa, ta samu bacci, mamanta na tsakar gida tana ta shara, kasancewar ta mace mai son tsafta, jin motsi a bayanta, ya sanya ta waiwaya domin ta ga abun da yake faruwa.
Matasa ne su uku, zabga-zabga cikin shigar banza