Showing 42001 words to 45000 words out of 152254 words
aibun Arfa ba, kuma a zuciyarsa ji yake kamar zai samu chance ɗin da zata zama mallakinsa, rashin gaya mata abun da yake ji game da ita kawai, ba ƙaramin azabtuwa yake yi ba.
Sanye take da face mask, tana rarraba idonta, ta ga ta ina zata ganshi.
Liti ya kalli Walid ya ce "Ka ganta ko?"
"Eh, amma bana ganinta sosai, ta rufe fuskarta da facemask".
Liti ya ce "Bari na yi wa gali magana"
Nabila na tsaye tana rarraba ido, wani matashi ya zo gabanta ya tsaya, ta ɗaga kai tana kallonsa.
"Ki sauke takunkumin fuskarki".
Cikin tsiwa ta ce "Ban gane ba, ina ruwanka da ni?"
Wayar hannunsa ya ɗaga mata, da take a kan kira, muryar liti ta ji.
"Ki sauke takunkumin fuskarki, ko kuma na fasa haɗaku"
Waiwayawa take yi, ta ga ta ina za ta ga liti, ta kalli matashin ta ce "Da kai zai haɗani?" Ya girgiza mata kai.
Ta din ga waige-waige ko zata ga daga ina liti yake ganinta, har ya san ta saka facemask. Kafin ta waiwayo, gali ya bar wurin.
Ta sauke facemask ɗin, tana rarraba ido.
Zabura Walid ya yi ya ce "Kai, a ina ka samo wannan yarinyar?"
"Jiya ta zo ta same ni, wai ita ƴar uwar viper ce, in taimaka in haɗa su, na shiga area jiya na ɗan yi wuru-wuru, an tabattar mini ita aka kwatantawa dabar madaki, ta je nemansa, suka sakar mata karnuka, ban san waye ya kwatanta mata ni ba".
Walid ya ce "Tabbas! Yakamata a haɗa su"
Liti ya ce "Idan kuma haɗin baki ne, ko wata maƙarƙashiya ce aka shirya masa fa?"
Walid ya ce "Zan kula da komai, amma yakamata su haɗu, ka ce ta dawo jibi da safe"
"Kana ganin babu matsala?"
"Babu matsala"
Nabila ta fara gajiya da tsayuwa, matashin ɗazu ya sake dawowa, ya miƙa mata wayar.
Ta karɓa ta yi sallama.
"Ki dawo jibi, ƙarfe sha ɗaya za'a haɗaki da shi".
Kamar Nabila ta yi zagi, dan haushi, amma ta danne ta ce "To shikenan, Allah ya kaimu" haka ta bar wurin jikinta a sanyaye, har ta fara tunanin ko dai raina mata hankali kawai zai yi.
Haka ta koma gida, ba tare da ta ji za ta sare ba.
Sumayya daga aiki gidansu Nabila ta je, dan su tattauna a kan umarnin da ta samu a wurin aiki.
A ɗaki ta tarar da Nabila, tana bacci, dan daga wurin su liti da ta dawo, kwanciya ta yi.
Tashinta tayi, Nabila ta tashi tana tsaki, saboda yadda ta tsani a tashe ta tana bacci.
"Ke baccin uban me ki ke yi, bayan azahar, har kin dawo daga aikin ne?"
Nabila ta yi miƙa ta ce "Ni ban je aikin ba ma"
"Allah ya shirya ki, tashi ki wanko fuskar ki, mu yi magana akwai case Arfa".
Nabila ta sake mayar da kanta kan fulo ta ce "Faɗi in ji"
"Dalla ki tashi ki saurare ni"
"Wai ba kunne ne yake ji ba?"
Sumayya ta ce "Kin gane mutumin da muka gani a reception, ki ka ce kin tsane shi? Ɗan majalisa ne"
"Yanzu takanas ki ka zo gaya mini ɗan majalissa ne? Ai na sanix
Sumayya ta ce "Dalla ki tsaya ki saurare ni, Honorable Ma'aruf indabo ne ai"
Nabila ta tashi zaune ta ce "And so?"
"Shi ne wai ni zan yi hira da shi, a madadin murtala, amma ya yi waya, wai sai dai na je gidansa na yi recoding ɗin program ɗin, shi ba zai samu zuwa ba"
Nabila ta waro ido ta ce "Saboda me?"
"Wai ba shi da lokaci, Nabila tsoro nake ji, ko zaki raka ni? Jibi in Allah ya kaimu ne zan je,ba na son rasa aikina, kuma ina tsoron ya cutar da ni"
Nabila ta ce "Kash, gashi kuma nima zan je wani aikin ne, da na raka ki aminiya. amma menene a ciki, ke zuwa gidan ɗan majalisa ba cigabanki bane?"
A raunane Sumayya ta ce "Tsoro nake ji Arfa"
"Sumayya, wani abun fa dole sai mun cire tsoro, tsoronki yayi yawa, ki yi addu'a, duk abun da ya same ki, gidan radiyon will be responsible, babu wani abu in sha Allah, ai mun riƙe addu'a"
Yanayin fuskar sumayyan ya tabattar mata da gaske tsoron take ji.
Sai dai ita ba ta ga abun tsron kamar yadda sumayya ta ɗaga hankalinta ba.
Nan ta din ga jan ta da hira, har ta saki jikinta suka cigaba da hira, suka ci abinci tare.
Sai daf da magariba ta raka Sumayya ta tafi gida.
Duk da ƙirjin Arfa na tsananta bugawa, amma ba ta ji zata iya fasa abun da ta ƙudurta ba, domin kuwa sai ta ga ƙwal uwar daka, jibin nan za ta shirya ta sake komawa wurin liti.
Paid book ne ₦500 via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank
Sai shaidar biya ta 08081012143
Special 1k, wanda za su jira complete document shi ma 1k ne.
Ayshercool
08081012143
[7/26, 1:37 PM] null: *ƘARFE A WUTA*
Arewabooks : ayshercool7724
Watpad: ayshercool7724
What's app :08081012143
What's app channel
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
Paid book ne ₦500 via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda ba ss som group akwai special 1k.
12
Yau ma ba ta sake zani ba, a yanayin da Walid ya iske Viper, ya sha duk abun da yake tunanin zai sha, ya bugu yayi bacci, amma jikinsa ya mutu murus, ya kasa baccin.
Idanunsa sun yi jawur, tamkar ana iza wuta, jijiyoyin kansa sun kumbura, sai buɗe idonsa yake yi yana lumshewa.
Walid ya kalli ɗan mama ya ce "Ɗan mama kai ka ke kawo masa kayan nan ko?"
"Wallahi bani bane ba, da kansa ya fita ya samo abun sa, ban kawo masa komai ba".
Ya mayar da idonsa kan Viper ya ce "Ka na ji na?" Ya ɗaga kai ya kalli Walid alamar eh.
"Wai ba zaka daina fita ba, sai wani abu ya faru tukuna, ka sake sakamu a matsala?"
Viper ya kalli walid, amma yayi masa shiru.
Shikenan, ina son zamu fita da kai, zan nuna maka wani abu mai ban mamaki"
Viper ya ce "Walid" ya kira sunansa da dakakkiyar muryarsa.
Ya amsa da boss "Boss"
"Meyasa ba ka da zuciya ne?" Yayi maganar cikin maye.
"Na ce bana son sake ganinka"
Walid ya ce "Saboda duk sheɗancina, ɗan halak ne ni. Ya zaka bi ni mu je?"
"Ba zani ba"
"Yakamata ka fara sanin dalilin da ya sa yarinyar nan ta matsa a kan lallai sai ta haɗu da kai, ina.....
Cikin hargowa ya ce "Wai wace irin yarinya ce? Meye haɗina da ita? Wacece ita me take nema a wurina?" yadda ya firgice sai da Walid ya matsa baya da sauri.
Ya cigaba da cewa "Kowacece, a kawar da ita, bani da alaƙa ta kusa ko ta nesa da kowace mace, kar ka kuskura kar kuma ka fara, idan ba haka ba duk abun da ya biyo baya kai ne sila"
Walid ya ce "Na ji na fahimta, easy ka yi haƙuri".
Ya ja tsaki, ya yinƙura dan ya tashi da niyyar ya fita, amma jiri ya ɗebe shi yayi baya, cikin zafin nama walid ya riƙe shi, ɗan mama ya taimaka masa, suka kwantar da shi.
Ɗan mama ya ce "Da gaske ka ke wai sai ka haɗa shi da yarinyar? Kuma akwai alaƙar tsakaninsa da ita?".
Walida ya ce "Shi nake son tabattarwa".
"To ya ce baya so, amma kai ba ka tunanin ko ƙarya take yi?"
Walid ya ce "Ƙaryar ma take yi, amma yakamata su haɗu"
Ɗan mama ya sake cewa "Sai ka haɗa sun kenan, idan ya illata ta fa?"
Walid ya ɗora yatsansa a kan leɓensa alamar yayi shiru, dan ya san Viper idonsa biyu kuma yana jin sa.
***
A office ɗin su Nasir kuwa, hira ta yi hira, ake gaya wa Nasir, wani ɗan majalisa ne, yayi belin yaran madaki da aka kama, ya saka aka sake su.
Cikin takaici ya ce "Allah wadaran naka ya lalace, muna tufka suna warwarewa, mun zama tamkar bayinsu, kullum cikin ganin gazawarmu ake, alhalin muna iya ƙoƙarinmu"
Suka cigaba da tattaunawa, a kan yadda manyansu kan yi musu karan tsaye, a kan harkar aiki, da hana ruwa gudu.
Ramma ce take ta murƙususun ciwon ciki, hankalin mahaifiyar ta a tashe, take ta ba ta jiƙe-jiƙen magunguna, da ta zuƙa kaɗan sai amai, ba ta iya cin abinci ga wani irin zazzafan zazzaɓi da yake damunta.
Kullum ta na ɗaki, ko tsakar gida idan ba dole ba, bata fita, saboda yadda labarin cikin nan ya watsu ya cika garin su, dama ta san isa sai ya bayar da labari, tun da ɗan cikin garinsu ne, ku ma shi ne ya tabattar da akwai cikin.
Cikin matsananciyar damuwa ta dubi ramma ta ce "Sannu ramma, na baiwa sani kuɗi ya sayo miki maganin zazzaɓi, kin ga haryanzu babu shi shiru bai dawo ba".
Cikin kuka ta ce "Mama mutuwa zan yi".
"Ki yi haƙuri ramma, ba zaki mutu ba, kina karya mini gwiwa, ki daure. Amma anya ba zamu yadda a cire cikin nan ba? saboda rufin asirinmu, kuma kema ki huta"
Cikin sauri ta girgiza kai ta ce "Mama tsoro nake ji"
Rasa abun yi ya sanya maman ramma, sakata a gaba suka cigaba da kuka tare, a zuciyarta ta din ga ja wa Abdul duk wani nau'i na masifa da jafa'i.
Yau sumayya za ta je program gidan honorable Indabo, maimakon ta kasance cikin farin ciki, a dalilin zata shiga gidan babban mutum kamar sa, amma ta gaza nutsuwa da yin farinciki a kan hakan, sai wata irin fargaba da faɗuwar gaba da take fama da ita.
Sai da ta fara shiga wurin aiki, ta gabatar da ayyukanta na ranar, sannan ta fara harhaɗa kayan aikin da za ta yi amfani da su.
Gaba ɗaya jikinta babu ƙwari, sai tsananin tsoro da fargaba.
Murtala ne yake ta kwantar mata da hankali, tare da nuna mata, hakan ma wani cigaba ne, ta sani ko daga program ɗin su daidaita da honorable ɗin.
Jin sa kawai take yi, tare da murmushin yaƙe.
Har bakin motar gidan radiyon da za a kai ta a ciki, yana ƙarfafa mata gwiwa, "Sumayya, abun da zan gaya miki shi ne, ki san iyakar ki a kan program ɗin nan, iya tambayoyin da aka rubuta miki, ki yi masa su zaki yi masa, kar ki ƙetare su ki jawo wa kanki matsala, ƴan siyasar nan ba kowa ne mai imani a cikin su ba"
"In sha Allah uncle murtala zan kiyaye, na gode sosai"
Ta shiga motar ta zauna, direban ya ja suka tafi.
Nabila kuwa tana office tare da barrister Habib, dan yanzu ya saukko ya fara yaba mata, tana ƙoƙari, ya fuskanci kawai shiririta ce take damunta a kan aikin, da rashin mayar da hankali.
Tana yi tana kallon agogo, kar ta saɓa lokacin da a ka bata.
"Barrister" ta kira shi, ya ɗago yana sauraren ta.
"Ban sani ba ko kana jin radiyo"
Ya ce "Ina ji mana, meyafaru?"
"Cases da dama, idan suka faru mussaman na masu ƙaramin ƙarfi, sai in ga barrister bunkure ta tsayawa mutane, wai ita ba dan kuɗi take aikin ba, dan barrister ce da ba kowa yake iya ɗauka ba, amma tana tsayawa marasa ƙarfi, ko kuɗi ne suka yi mata yawa?"
Barrister Habib ya girgiza kai ya ce "Ke dai kawai ayi sha'ani"
"Ka san wani abu kuwa? Akwai wani case da wata mata, ta je gidan radiyon su sumayya, ta kai koken an yi wa ƴar ta fyaɗe, an dawo mata da ita daga gidan aiki, ta je gidan da yarinyar take aiki, an hana su shiga, ta kai wurin ƴan sanda, amma ana ta yi mata yawo da hankali, wai yaron ɗan manya ne. To na ji an ce ta shiga case ɗin, amma haryanzu babu wani update, ka san da na so na jarraba sa'a ta, nima na shiga case ɗin ayi da ni, na tausayawa matar da yarinyar, amma na san ana babbakar giwa, wa zai ji ƙaurin zomo, na san ba za ta saurare ni ba ma".
Barrister Habib ya tattara hankalinsa a kan Nabila ya ce "Nabila"
"Na'am"
"Just be yourself, ke dai ki kalli mutum a riga kawai, Naja'atu kura ce da fatar akuya, ba wata abar burgewa ba ce, da zaka yi koyi da ita ba. Yarinyar ƴan siyasa ce, babu wani taimakawa masu ƙaramin ƙarfi, ta fake da wannan ne, dan sunanta ya ƙara fitowa, kuma ya rinjayi ɓarnar da take aikatawa, ai mun yi karatu da ita tare, ƙwalluwar shegiya ce, ke abun bai baki mamaki ba, ace kowace shari'a idan ta tsaya maka, zaka yi nasara, ace komai kai ka ke nasara akwai ayar tambaya ai, dan haka ki yi ta kanki kawai.
Duk da mu ma ɗin wasu lokutan, muna take gaskiya, amma yanayin aiki ne ya zo da haka, kuma nata ya ƙazanta".
Nabila ta yi ajiyar zuciya ta ce "Biri yayi kama da mutum"
Nabila a zuciyarta ta ce "Idan haka ne, ba gaba da gaba yakamata na yi da ke ba, tona miki asiri zan yi"
Habib ya ce "Ya dai?"
"Nothing sir, jikina ne yayi sanyi kawai na gode sosai da bayaninka"
Ba tare da neman iznin kowa ba, ta ɗauki jakarta ta fita.
A in da ta tsaya shekaranjiya, nan ta je ta sake tsayawa, tana fatan Allah ya sa ba jirgata za su yi ba.
Ta shafe a ƙalla awa guda a wurin, har ta sare zata tafi, matashin da ya kai mata waya, liti yayi mata magana da ita, ta gani a gabanta.
Bai ce mata uffan ba, ya miƙa mata wata takarda.
Sunan wata unguwa ne a jiki,da dai-dai wurin da zata je ta tsaya, saboda tsabar wauta da rashin hankali, ta yi masa godiya ta tari abun hawa ta nuna masa takardar.
Mai baburin ya gaya mata kuɗinsa, babu neman ragi, ta afka ciki ta ce su tafi.
Lissafin da take ma a zuciyarta, na mamakin yadda Naja'atu tayi mata kallon ƙasƙanci ne, ta wulaƙanta ta alhalin ma ba wata mutuniyar arziki ba ce.
Babban abun da ta fuskanta, ƙasar nan ba zaka taɓa samun wasu damarmaki ba, har sai ka taka wani babban matsayi na musamman, ka shahara sai dai hanyoyin bi a shahara ɗin ne, ko da kasada ko ka kauce hanya.
Ta yi wa kanta alƙawarin, dole za ta bibiyi case ɗin yarinyar nan, ba naja'atu ba, ko a hannun ƙaramar hukumar bunkuren case ɗin yake, sai ta bibiya, ai da ƙananan kasada ake babba, ga kuma babban target ɗin ta, Viper, ta san idan aka kama shi, dole a sara mata, ta shiga cikin mata da suka kafa tarihi.
Da wannan gurguntaccen tunani na Nabila, mai cike da wauta da rashin lissafi, suka cigaba da tafiya can ta ce "Malam, wai haryanzu ba a zo ba?"
"Ba ki taɓa zuwa unguwar ba ne?"
Ta ce "Eh, sai yau zan fara"
Ya ce "saura kaɗan in sha Allah"
Sai dai gabanta ya fara faɗuwa, tun bayan da ta ga sun bar cikin mutane, sun fita wajen gari. Dai-dai wani gidan gona ya ajiyeta, wurin duk shuke-shuke, da alama akwai mutane a daf da wurin, amma sai an yi tafiya kan a tarar da in da suke. Shi kansa titin wurin, babu ababen hawa da suke kaiwa suna komowa a wurin.
Sai rukunin manya manyan kamfanunnuka a wurin, na shinkafa da na taki, wurin shiru sai ƙarar injinan da masana'antun ke amfani da su.
Sai da ta sallami mai a daidaita sahun, sannan ta fara tunanin, to ina ma za ta nufa?
Tsayawa ta yi, tana waige-waige, kawai ta hango wani mutum ya tunkarota, nan ta fara ja da baya, tana tunanin ko zurawa za ta yi da gudu.
"Mu je" ya ce mata a kausashe.
Ta turje ta ce "Ina?"
"Ba ke ce baƙuwar Viper ba, mu je"
A raunane cike da tsoro ta ce "A'a, ka kirawo shi mu yi magana a nan, ni dama kaya nake son saya a wurinsa"
Cikin mamaki ya kalleta ya ce "Wani irin kaya?"
"Wanda yake sayarwa" tayi maganar a tsorace tana kallon Walid.
Ya gyaɗa kai ya ce "Baki san waye shi ba amma? Kin yi kasada nafi muni, wuce muje kafin na saraki biyu a wurin nan"
Cikin rawar jiki ta ce "Dan Allah ka yi mini rai, ni ka kirawo shi nan kawai".
"Wallahi zan saɓa ki a ka, wuce mu je"
Salati Nabila ta din ga yi, dan tun da ta yo dakon kasadar nan, sai yanzu ta ga zunzurutun wautar da ta aikata.
Ya sakata a gaba, suka nausa bayan kamfanunukan.
A can gidan honorable kuwa, yana da office a cikin gidan sa, in da yake ganawa da mutane na mussaman.
Hankalin sumayya ya ɗan kwanta, bayan da ta ga mutane na shiga suna fita a gidan, da alama ba shikaɗai ne a gidan ba, kuma gidansa ne da yake zaune da iyalinsa.
A harabar gidan aka dakatar da wanda suka rako sumayya, aka ce itakaɗai za ta shiga.
Wani security yayi mata jagora, zuwa wani sashe na gidan, ya kaita wani falo, ya ce ta jira a nan, ta samu wuri ta zauna, a kan kujera, tana zaune a falon office ɗin, tana ɗan kalle-kalle, tana jira kamar yadda aka umarceta.
Cikin office ɗin kuma, Barrister Naja'atu ce suke magana da honorable.
"Ni fa na yi iya ƙoƙarina, amma da alama mutanen nan, su na da taurin kai, juyin duniya sun ƙi saduda, sai iƙrarin a karɓar musu hakkinsu suke yi, ina ga kawai a ɗauki matakin da ya dace a kan ta".
Indabo ya ce "Lallai dama haryanzu akwai masu ƙi faɗi a talakawa?"
"Akwai su fa, ku kuna gefe, mune muke shiga cikinsu da rufe bakunanansu a kan ɓarnar da ku ke aikatawa, sai dai kan mage ya fara wayewa, babban abun damuwar sun gaya mini an tabattar musu tana da ciki"
Yayi saurin ɗaga kai ya kalleta "Ciki kuma? Sau nawa yayi mata fyaɗen ne?"
Ta ɗage kafaɗa ta ce "Wannan kuma shi za ka tambaya, ba zan iya cigaba da ɓata lokacina a kan wannan kucakan mutanen ba, ina da abubuwa masu muhimmanci kawai ayi abun da ya dace".
Yayi ajiyar zuciya ya ce "Abdul, ban san lokacin da zai yi hankali ba, ina tsoron lokacin zaɓe, a samu wani ya fito da miyagun halayensa, in the next couple of years, sonake ya samu ref, ko deputy governor a tsayar da shi takara, saboda yarjejeniyar da muka yi, da jam'iyya kenan kafin na yarda na zauna a cikinta, amma al'amarin sa kullum ƙara lalacewa yake yi"
Barrister Naja'atu ta ce "To, gara dai ka san abun yi"
"Anyway, shikenan, ki tura mini address ɗin su ita yarinyar, za ayi abun da aka saba" ta miƙe tsaye ta ce "No problem"
Ta buɗe ƙofar office ɗin ta fito, kallo ɗaya sumayya ta yi mata, ta gane ta, saboda yadda Nabila take ɗora hotonta a status ɗin ta a baya.
Cikin son tabattar da abun