Showing 63001 words to 66000 words out of 152254 words

Chapter 22 - ?arfe A Wuta Book 1 Hausa Novel Complete

15 Dec 2024

344

zaɓa ko ni ko ɗan ka, idan har zai cigaba da shigowa gidan nan, to wallahi ni zan bar shi, dan ba zai illatani da yarana a banza ba, ko ya lalata mini ƴaƴa ba.
Sanin kanka ɓaras ya karya mini ɗa, Allah ne yayi da sauran rabon Musa ya taka ƙafarsa a duniya, ga ni da yara mata, ya din ga shiga yana fita, ba ma wannan ba, yadda ya yi ƙaurin sunan nan a duniya, tsaf zai hana mini  ƴaƴa auruwa, to wa ma zai zo ƙofar gidan nan zance, yana tsoron a raba shi da rayuwarsa, ba zai yiwu ba gaskiya".

Ya numfasa ya ce "Rahila, da wani idon ki ke so duniya ta kalle ni? Idan na kore shi na hana shi zuwa gidan nan, yana da in da ya fi nan ne?"

"Idan ba shi da shi ka nema masa, ni fa ba zan cigaba da rayuwa da tantirin ɗan daba a cikin gida ba, ya sabauta mini rayuwata da ƴaƴana ba, Allah ya mayar da shi kurku ya dauwwama a can kowa ya huta, ina dalili za a hana ni rawar gaban hantsi, mutum ba tarbiyya duk na sangarta shi, an mutu an bar mutane da masifa da bala'i a bayan ƙasa, me ake da ɗa irin wanda zahra'au ta mutu ta bari, Aminu ai cikon asara ne a cikin al'umma, wallahi ta yi asarar haihuwa".

Yana tsaye a bakin ƙofar shiga falon, yadda ta ɗaga murya, ya sanya ya ji komai, zuciyarsa ta din ga wani irin hanƙoro, wani abu mai masifar ɗaci ya din ga taso masa.

Ya saka hannu ya danƙe handle ɗin ƙofar iya ƙarfin sa, saboda muddin ya shiga cikin falon, yadda yake jin sa a saman nan, ya cake da wiwi, babu abun da zai hana shi ɗaga matar nan, ya buga da ƙasa.

Ya kasa gaba ya kasa baya, shi bai shiga ba, kuma bai bar wurin ba, kunnuwansa suka cigbaa da karɓar miyagun maganganun da take faɗa a kansa.

Ƙarar da handle ɗin ya bayar ne, ya sanya su juyowa su kalli bakin ƙofar, ɓaras ya karya handle ɗin nan, duk ƙwarin sa, ya fara yi mata wani irin kallo, da ta kasa gane ma'anarsa.

Ayshercool
08081012143

🔞*PAID BOOK NE, ₦500 BOOK1-3 VIA 0009450228, AISHA ADAM JAIZ BANK, SAI SHAIDAR BIYA TA 08081012143*




Da sauri ta ɓuya a bayan maigidan, hantar cikinta na wani irin kaɗawa.

Ya nuna kansa da yatsansa ya ce "Haihuwata ce asara ko? Ni?"

Cikin tsawa ya ce "Kai aminu, ya isheka haka, kar ka kuskura ka aikata wani rashin mutunci, ko ka ce zaka yi mata wani abu, koma menene ba kai ka janyo ba, ka nustu ka zama mutumin kirki mana, kalli yadda ka yi shuhura a shashanci da harkar sara suka, ni kaina ban so fitowarka ba wallahi, yanzu zaka zo ka cigaba da ɗaga mini hankali, ka hana ni zaman lafiya da iyalina, dan haka ka bar mini gida, kar ka sake shigo mini gida, ba na buƙatar ka".

A hankali ya saki handle ɗin ƙofar da ya karya, ya kalli mahaifinsa ya ce "In daina zuwar maka gida, Abbu ina zani? Wurin wa zan je?"

"Ka je duk in da ya yi maka, ko wurin ƴan iskan da suka ka ke jin maganar su sama da tawa, amma kar na sake ganinka a gidana"

Yayi murmushi mai ciwo, ya ce "Shikenan, zan tafi zuwa lokacin da huce zan dawo"

"Ba na buƙatar dawowarka, tun da ban isa da kai ba, ka je ka ƙarata"

Tuni idanunsa suka rine, zuwa launin ja jawur "Ba a canza tuwo suna, ba ni da wanda ya kai ka ko ya fika, ba ni da gidan da yafi nan, dan haka ba zan daina zuwa gidan nan ba, amma idan ka matsa zan tafi, idan kuma na tafi na bar shi kenan har abada, wani aiki aka fito da ni na yi, da yiwuwar idan na gama aikin, na koma gidan yari, komawar da ba zan sake fitowa ba, sai ku huta da ganina" ya ƙarasa maganar kafofin gashinsa na mimmiƙewa saboda ɓacin rai.

Rahila ta ce "Allah ya raka taki gona"

Juyawa ya yi ya fice, har da sassarfa, dan yanzu abun da zuciyar sa ke raya masa, ba iya ya bugata da ƙasa bane, ya raba maƙogwaronta da wuƙar ƙugunsa haka yake ji.

Tafiya kawai yake yi, yana tunani barkatai a cikin zuciyarsa, har ya ƙarasa in da yake son zuwa.

Suna ganinsa suka mimmiƙe tsaye, sun risunar da kawunansu, tamkar dai yadda ake yi wa shugabbani, a wurin shugabancinsu, ba tare da ya ce komai ba ya zauna, yayi shiru.

Liti ne yayi gyaran murya ya ce "Allah ya taimaki mai dogon zamani, menene damuwarka ne?"

Al'amin yayi shiru, dan shi bai san me zai ce ba ma.

Ba yadda ba su yi da shi ba, amma yaƙi magana.

Liti ya miƙo masa wani satchet ɗin magani, ya ce "Ga wannan ka sha rabi, yanzu za ka ji ka ɓata, ka manta komai, wasu ƴaƴan matsalarka duk za su sauka, daga hau ka saukko za ka ji komai ya goge"

Ya saka hannu ya karɓa, yana jujjuya satchet ɗin.

"Ka saka ɗaya a ƙasan harshenka, shikenan".

Ya ɓalli ɗayan ya saka a ƙasan harshen sa, ya jingina da bango, zuciyarsa na cigaba da tafasa.

Sai dai bai fi mintuna sha biyar ba, idanunsa suka fara lumshewa.

Yayi gyaran murya ya ce "Liti"

Liti ya ce "Boss".

"Chairman ya fito da ni saboda na yi masa aiki, ya ce na je yana son ganina, zai gaya mini aikin da zan yi masa, sai dai kafin na yi masa aikin zan yi nawa, ko da kuwa zan koma gidan yari ban yi nasa ba"

"Allah ya taimaki maza, wane aikin ne, a shirye muke mu yi maka ko menene"

Ya jinjina kai ya ce "Madaki zan kashe! Sai na kashe madaki!!"

Liti yayi turus ya ce "Maza, duk lokacin da muka yi yinƙurin ɗaukar fansar nan, wahala muke sha madaki fa har tsafi yake yi wallahi, ya gagaremu"

Ya ɗora yatsansa a kan laɓɓansa ya ce "Shhhh, ni bai gagare ni ba, zan kashe shi na koma gidan yari"

Liti ya ƙura masa ido sannan ya ce "Maza ko ƙwayar ta fara yi maka aiki ne?"

Ya buɗe idanunsa da suka yi ja, ya kalli liti, sannan ya mayar ya lumshe su a hankali, bacci yayi awon gaba da shi.

***

Rana ta take sosai, ƴan makaranta na ta ɓullowa da ga lungunaa da titunan unguwannin.
Sosai jauhar take sauri, ta je gidan da take yi musu shirin dutse, ta kai wanda ta yi, ta karɓo wani su bata ƴan kuɗaɗenta.
Babban layi ne sosai, ababen hawa na kaiwa suna komowa, ta tabattar babu abun hawa, wata danƙareriyar mota, ta shawo kwana a guje, ba tare da ko yin horn ba.
Gaba ɗaya ta ruɗe, ta kasa gaba ta kasa baya, kawai ta tsaya ta ɗora hannunta a kan ta, tana maimaita lahaula wala ƙuwwata illa billah.

Da ƙyar ya iya cin burki, ya fito a fusace mutumin, babban mutum ne sosai, ya kusa sa'an Baba ma, ya hau ta da faɗa "Ba kya gani ne, wannan wani irin rashin hankali ne?"

Ta kalleshi da fararen idanunta ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri, wallahi na duba ban ga mota ba, ka yi haƙuri dan Allah"

Mutanen wurin da suka saddaƙar sai ya buge Jauhar, suka taso suna salallami, sai dai aka rasa me nuna masa shi ne yayi kuskure, saboda uwar shaddar da ta bi lafiyar jikinsa ta kwanta.

Sai kuma jikinsa yayi sanyi, ganin yadda take ta bashi haƙuri, duk da shi ne mara gaskiya, pressure da yake ciki da tension ne ya sanya shi hucewa a kanta.

Sai kuma ya kwantar da murya ya ce "Ki yi haƙuri, ai ba ki ji ciwo ba ko?"

Ta ce "Babu abun da ya same ni" daga haka ta tsallaka ta shiga layin da take son shiga.

Kusan dozen biyar tayi na shirin, aka bata naira ɗari da hamsin, ta kuma karɓo wani tana lissafin saura ɗari biyu da hamsin, ta samu kuɗin pad, wanda magana ake ta saura ƴan kwanaki jinin ya zo.

***
Al'amin ne zaune a kan kujera, yana wasa da zoben azurfar hannunsa, Indabo yana ta bayani, amma sam hankalinsa ba a kansa yake ba, dan bai san me ma yake faɗa ba.

"Aminu magana nake fa"

Ya ɗaga idonsa ya kalle shi ya ce "Ina jinka"

"Yaƙin neman zaɓe da zan je, ina son a zubar da jini ne, a tayar da tarzoma ayi hatsaniya sosai da sosai, sai kuma ranar zaɓe"

Ba tare da ya kalle shi ba ya ce "Shiyasa ka fito da ni, saboda zan yi maka aiki shi ne ka fito da ni ko?"

"Eh saboda haka ne, kai ne ba ka ji, ka fiye rigima, na yi na yi ka fita sabgar madakin nan, ka haƙura, amma kamar annabi da kafiri, kullum cikin harin juna ku ke, kai ne faɗa a nan kai ne a can, wai fa har sayen rigima ka ke yi"

Ya katse shi da cewa "Nawa zaka biyani?"

"Zan baka dubu hamsin kai da yaranka".

"Ɗaurin shekara biyar a gidan yari, shi zan yi a dubu hamsin ni da yarana, ka duba babbar kasada ce"

Indabo ya yi murmushi ya ce "Baka da matsala in dai kuɗi ne"

Ya tashi tsaye ya ce "Kamar yadda ka yi a wannan karon, ka neme ni kai tsaye, haka nake son ya cigaba da kasancewa, ba na buƙatar sanya wani P.A ɗinka ya neme ni, ya sanar mini da saƙonka"

"Na fahimta, ka san mu ƴan siyasa dole sai muna yi, muna ɓad da sahu, baka da matsala".

Al'amin ya jinjina kai, ya sa kai ya bar falon, cikin takun ƙasaita.

*****
Saifu ne ya shigo gida, wajen ƙarfe uku da rabi, ya tarar da Jauhar tana wanki a tsakar gida, gidan babu kowa, yaran duk sun tafi makaranta.

Ta ɗago ta ce "Yaya sannu da zuwa"

Ya amsa da Yauwwa "Ina makarantar islamiyyar?"

Shiru ta yi ta sunkuyar da kai, ba ta amsa masa ba.

"Da ne nake fa"

"Amm..dama ban biya kuɗin makaranta bane, sun ce kar na sake zuwa sai na biya"

"Kuna kin gaya wa Baba?"

Ta girgiza kai alamar a'a.

Cikin takaici ya ce "To saboda me?" Ta yi shiru ba ta ce komai ba.

Saifu ya ce "Ke dai sokuwa ce wasu lokutan, dubu uku ne ko? Tashi ki saka uniform ki tafi" yayi maganar yana ciro kuɗi daga aljihunsa, ya miƙa mata dubu uku.

Fuskarta ta faɗaɗa da murmushi, ta saka gwiwoyinta a ƙasa, ta saka hannu biyu ta karɓa ta ce "Na gode sosai da sosai yaya, Allah ya ƙara arziki".

Ya ce "Amin, bar wankin, tashi maza"

Ta ce "To kar maman su Hafsa ta dawo ban gama ba, labulayenta ne"

"Ajiye, su hafsa idan sun dawo su wanke mata, maza ki tafi".

Cikin murna ta tashi, ta tattare kayan wankin, ta shirya cikin uniform ɗin ta, ta tafi islamiyya.

Duk da yau ma sai da aka zane ta, sannan ta shiga ta kai kuɗin makarantar tana ta kuka, dan ba ta ƙaunar duka sam.

Sai dai duk da kukan da tayi, hakan bai hanata farincikin ganin ta koma makaranta ba.

Sai dai bayan ta koma gida, Anty ta rufeta da bala'in ta tafi ta bar mata bedsheets ɗin da ta saka ta wanke mata.

Jakarta kawai ta ajiye, ta hau wankin da aka sakata, bayan ta sha uban zagin tsamar nama, ita duk hakan bai dameta ba, ta kammala wankin sauran bedsheet ɗin, ta wanke kwanuka ta mayar da abincin dare.

Duk ƴan matan gidan suna zaune, itakaɗai take aikinta a tsakar gidan, idan baƙo ya zo sai ya yi zaton mai aiki ce.

***

Yau tun a makarantar boko, Jauhar ta ji period ya zo mata, gashi kuɗin pad ɗin nata saura ɗari da hamsin ba su gama cika ba, sai kame jikinta take yi, saboda tsoron kar jini ya ɓata ta.

Da ƙyar ta isa gida, tana ta lissafin yadda za ta yi, gashi idan ta yi amfani da tsumma, lalata mata fata yake yi, ƙuraje duk su feso mata, ta rasa in da zata saka ranta.

Haka ta wuni tana fama, ga uban ciwon mara, kamar tayi hauka, dan ma ta samu paracetamol a wurin Yaya saifu ta sha, ga uban aiki dan babu mai ɗaga mata ƙafa, haka nan ta saka tsumman, take amfani da shi, idan ba haka ba ta san haka za ta yi ta staining.

Da magariba, tana zaune a tsakar gida, ta cinye ɗan abun da ta samu ta ci, wanda sam ba ta ƙoshi ba, duk da ita ta girka, sai lashe hannu take yi, Baba yayi sallama.

Aka din ga jera masa sannu da zuwa, yana amsawa.

Ya kalli Jauhar ya ce "Waliyiyya ya na ga kina suɗe hannu, ba ki ƙoshi bane?" Tayi murmushi ta girgiza masa kai ta ce "Alhamdilillah, na ƙoshi baba".

Ya ce "To madalla, Allah shi ne abun godiya, akwai wani mutum da ya zo wurina yayi mini maganarki, ban sani ba, ko ke ki ka turo shi" Gaban juahar ya faɗi, ta kalli in da mama ke zaune a kan tabarma, ita ma tana cin nata abincin. Sau ɗaya saurayi ya taɓa biyota gida, mama ta ce idan wani ya kuma zuwa wurinta, ko ta bawa wani damar ya zo wurinta, sai ta kusa halakata, yayyenta ba su auru ba, ba za ta fara kawo musu maza ba, duk da dama shekarun nata ba yawa ne da su ba, haryanzu a SS2 take shekara goma sha shida, sai dai hasken fatarta ke ɗaukar idon samari ƴan bana bakwai, su biyota wai suna so, saboda kashedin mama ta koma saka niƙab.

But Anty, babar su hafsa ta fito daga ɗakin ta, tana jiran ta ji ƙarashen maganar.

Mama ta ce "Ba magana ake yi miki ba?"

Jauhar ta girgiza kai ta ce "A'a Abba, wallahi ban san kowa ba, ban turo kowa wurinka ba"

"Ƙarya ki ke yi, zaki aikata, ba abun mamaki bane ba kina halin kule-kule a waje, dan a zahiri kina da fuskar tsoron Allah, amma a baɗini ba kya ji" Anty ta ara ta yafa ta ƙarar da zancen.

Baba ya ce "No, shi ma ya gaya mini, bai yi mata magana ba, ya zo ya fara samuna ne, na dai tambayeta ne kawai dan na tabattar, zan bashi dama ya fara zuwa wurinta, dan naga da gaske yake yi."

Dumm ƙirjin Jauhar ya buga, ta fara zance yanzu, makarantar kuma fa, ga burinta na son yin karatu, duk da aure ba ya hana karatu, to amma idan wanda zata aura ɗin ba zai bari ba fa?.

Da sauri mama ta tashi ta bishi ɗaki, tana yi masa magana "Yanzu aurar da jauhar ɗin zaka yi, ga yayenta duk a jibge, su kusan biyar babu wadda ka aurar?"

Ya tsaya ya kalleta ya ce "To laɗifa, tara su zamu yi tayi ba zamu aurar ba? Tun da ita Allah ya fara kawowa sai mu fara da ita, ita ma ta huta"

A take ta haɗe rai ta ce "Ban gane ita ma ta huta ba, na fuskanci duk lokacin da magana irin wannan ta tashi, sai ka nuna kamar bana ƙoƙari a kan riƙonta, kamar zaluntar ta nake ko?"

Kamar yaronta ya ce "A'a bance ba"

"To wallahi ba za ayi wa jauhar aure ba, ga su Sajida ba, wannan ai cin mutunci ne".

Yayi mata shiru, bai sake cewa komai ba, ya ƙuduri aniyar, aurar da jauhar ko ba ta so.

***
A tsakar gida ta tsaya tana ta kwaɗa sallama, daga cikin falon aka amsa mata, wata matashiyar mata ta fito.

Suna ganin juna suka rungume juna, suna murna.

"Zakiyya Bala, yau ke ce a gari?"

"Wallahi kuwa Rahila".

"Ya aka yi ki ka gane gidan nan? Kin san lambarki na rasa".

Zakiyya ta ce "Ke wayata aka sace mini, tun da na canza layi na rasa lambarki nima, ai da Abba na haɗu a bakin titi, ya ce mini ai kun jima da dawowa unguwar nan, bamu da wani nisa bamu sani ba".

Rahila ta ce "Allah sarki, shigo daga ciki, shegiyar ƙawata, na yi missing ɗinki fa" suka shiga suna dariya.

Ta kawo mata ruwa da lemo ta ajiye, Zakiyya ta kalli gidan ta ce "Ikon Allah, nan ku ka dawo kenan?"

"Wallahi kuwa, ai yanzu ba abun, tun da aka damfare shi ɗin nan, lamuran sai godiyar Allah, amma a hakan ma ai bamu tagayyara ba"

Zakiyya ta ce "Gasakiya ne, Allah ya ƙara rufa asiri, ina su kursum?"

"Duk suna makaranta, kin san tana level 3 ita yanzu, ina su hafsa, haryanzu babu labarin aure ko?"

"Haba Rahila, yaushe za ayi auren su Hafsa ba ki ji labari ba, wallahi babu shiru, abu kamar saka hannu, har na fara zargin uwargidana, sai na ga ita ma ga nata nan biyu, Sajida da surayya, suma babu ana ta shige-shige shiru, dan ma ni da ita kar ta san kar ce, an daɗe ana gogawa taga babu riba, na sha gabanta shi ne ta sarara mini".

Rahila ta ce "Subhanallah, kin ga nima ana ta fama, duk wanda ya zo kamar walƙiyya sai ya tafi, ni kuma ba zan bawa talaka aure ba wallahi"

"Ba ke kaɗai ba Rahila, kin ga yaran nan, har mai suka shafa, sun yi ɗas sun zama farare, kwalliyar nan, supplements ɗin nan, na gyara dai, amma ba tsayayye duk sai shirmanmu"

"Ki daina damuwa fa, lokaci ne"

"Wallahi haka ne, ba ki san wani abun takaici ba, wai sai yarinyar nan, ƙanwar bayansu, jauhar ƴar bafulatanar nan da ya taɓa aura kwanaki, aka rabu tsiya-tsiya ƴar da ta mutu ta bari, wai ita wani ya ce yana so da aure, yarinyar nan sai da Laɗifa ta shiga ta fita, ko suturar kirki ba ta sakawa, wai amma a haka wani ya gani yake so, kin san ita ya bawa riƙonta"

Rahila ta kwashe da dariya ta ce "Ai wasu lokutan maza ƴan wahala ne, ga in da ya dace su je, amma wani wurin suke kai kan su. Ni kaina ga nawa ɗan riƙon ya sani a gaba, ɗan gidan zahra'u tsinannen yaron da asiri baya cin sa, babu irin kurciyar dan ban saka ayi masa ba, amma abu ya gagara".

Zakiyya ta gyara zama ta ce "Ke haba? Al'amin ko"

"Shi, ai ya zame mini bala'i Zakiyya, ya zama riƙaƙƙen ɗan daba da shaye-shaye, za ki ji matasa suna mai dogon zamani shi ne fa"

Zakiyya ta dafe kai ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ke ina jin labarinsa har a radio, dama shi ne, amma lokacin kina amarya kamar a nutse yake"

"Ke rabu da ni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login