Showing 66001 words to 69000 words out of 152254 words

Chapter 23 - ?arfe A Wuta Book 1 Hausa Novel Complete

15 Dec 2024

338

oho masa, ni sonake ya bar gidan nan, kar ya hana mini ƴaƴa auruwa, ko ya illata wani, dan Abba da ki ke gani ɓaras ya karya mini ɗa kamar kara.
Kina kallon halin da muke ciki, yanzu babu bushasha kamar da, ɗan abun da ta bari ya gada, ubansa ya fito da shi, ya ƙara jari, yaƙi wai ba zai taɓa masa kaya ba, kin ga da zai bar gida a neme shi a rasa ai ma samu mu ci, babu irin korar da ban saka ya yi masa ba, amma yaƙi tafiya".

Haka suka cigaba da hirarraki, wadda galibi a kan rayuwar makaranta da suka yi, sai na iyalinsu hirrar take.

Kusan sati biyu, da maganar da baba yayi, a kan wanda ya zo wurinsa a kan jauhar, yayi shiru da maganar kamar ta wuce, ya dawo da yamma, kasancewar juma'a ce, jauhar ta duƙufa tana ta shirin dutse. Kuɗinta da suka taru ba ta samu ta sai pad ba, sai ta sayo riɗi, ta ce zata soya ta juya kuɗin, idan suka taru ta saya da wuri.

A tsakar gida baba ya tsaya, ya ƙwala mata kira, ta amsa ta fito ta tsuguna.

Ya kalleta ya ce "Ki shirya, ki je ga baƙonki can a waje ya zo ku gaisa".

Ji tayi kamar ta fyalla da gudu, ta tsaya da saurayi, ya ce mata me, ko ta ce masa me?

Amma ta amsa masa, ta tashi ta shiga ɗakinta, jikinta duk yayi sanyi.

Sajida ta shiga falo in da su surayya ke kallon Bollywood.

"Kai kuna nan kuna kallo, baba fa da gaske yake auren jauhar zai yi muna zaune"

Surayya ta ce "Kamar yaya?"

"Kamar yadda na gaya muku, wallahi wai wani ne wai yake son ta"

Hafsa ta ce "Da yardar Allah ba za ta yi aure ta barmu ba".

Jauhar kuwa turus ta yi, tana kallon ƙatuwar motar da ke ƙofar gate ɗin gidan an yi parking ɗin ta.

Zura kai ta yi tana lelleƙawa ta ga waye baƙon.

Ya buɗe ƙofar motar ya fito, yana murmushi.

Turus ta yi tana kallonsa, ya yi murmushi ya ƙaraso ya jingina da jikin motar, ya ce "Mayar da idon mana, kin yi mamakin ganina ko?"

Da sauri ta durƙusa ta ce "Ina wuni?"

"Lafiya ƙalau Faɗimatul Jauhar"

Ya ɗan gyara tsayuwarsa ya ce "Na san dole zaki yi mamakin ganina, zuwa na yi na sake bayar da haƙuri, a kan incident ɗin da ya faru, na tsorata ki da na yi, na kusa buge ki da mota"

Jauhar ta ce "Ai bakomai ya wuce, na ma manta"

"Ai ni ban manta ba, dan sai da na koma wurin da muka haɗu, na tambayi ina ne gidanku, na samu baba muka yi magana, hankalina ba zai kwanta ba, har sai na aure ki, na kai ki gidana, na rarrasheki da kyau"

Jauhar ta sunkuyar da kanta, tana jin abun wani banbarakwai. Ita gaba ɗaya ma ji take yi ya takurata.

"Jauhar"

"Na'am" ta amsa tana kallonsa da idanunta da suke farare tas, sai dai ba manya ne can ba.

"Me ki ka ce? Ni aurenki nake son na yi, kuma nan kusa wallahi ba da nisa ba, na yaba da tarbiyarki fiye da yadda ki ke tunani".

Kamar za ta yi kuka ta ce "Ai ban gama makaranta ba, ni yarinya ce kai kuma babba ne"

Dariya yayi ya ce "Wow, ashe shagwaɓaɓɓiya ce har haka? To dan ni babba ne ba za a aure ni ba? Kar ki ce haka, zaɓin Allah ake nema kin ji sweetheart, ki yi ta addu'a Allah ya tabattar mana da alkhairi. Ina da mata ɗaya da yara biyar kacal, yaro ne ni haryanzu" yayi mata maganar yana kashe mata ido ɗaya.

Ita kam gabanta ne ma ya faɗi, yara biyar ne kacal, ita duk wata harka da za ace kishiya, tsoronta take ji.

"Kar in cika ki da surutu, bani lambar wayarki, a hankali zamu saba, kin shiga raina sosai, zan yi iya ƙoƙarina na baki kulawa dai-dai iyawa ta, kuma karatunki, in sha Allah sai kin ce kin gaji dan kanki" yayi maganar yana miƙa mata wayar ta saka masa lambarta.

"Bani da waya ai"

Ya ce "Ohh, ashe fa ƴar baby ce, ba ta isa riƙe waya ba, zan kawo waya in sha Allah"

"A'a dan Allah kar ka kawo mini, ba ma za a bari na riƙe ba"

"To ikon Allah, to ta ina zan din ga jin muryarki? Amma shikenan bai kamata na karya dokar gidanku ba, zan san abun yi na nemi iznin baba na kawo wayar. Amma baki tambayi sunana ba"

Ita dai tayi shiru, tana mamakin yadda babban mutum kamar wannan, yake ta kashe mata murya.

"Sunana Alhaji Mu'azzam. Ina dillancin kayan sawa, mussaman na mata, ina shigo da kaya daga ƙasashe daban-daban, kuma ni ɗan siyasa ne, yanzu haka ina da muƙmi a gwamanati, amma ba dai wannan ba, ni amincewarki nake nema, kar ki yi saurin rejecting ɗina ki yi mana addu'a kin ji zahrana"

Jauhar dai ta yi gum, ita wannan tsayuwar ma kawai, kunya take bata kamar ta falfala da gudu.

Haka ya gama surutansa, ba komai take fahimta ba, lissafi kawai take a zuciyarta, saura dozen nawa ta gama shirin dutse, ta kai ta karɓo kuɗin, ta cika ta soya riɗi.

Kuɗin da ya miƙo mata, ya sanya ta ja da baya, tana girgiza kai. Ya kaɗa ya raya, amma fafur ta ƙi karɓa, sai haƙura yayi.

Haka yayi mata sallama ya tafi, da sauri ta shiga gida, dan kuwa Alhaji mu'azzam duk ya cinye mata lokaci, ba ta ƙarasa shirinta ba, mugun kallon da ta tarar da ƴan matan gidan na yi mata a tsakar gida, ya sanya ta shan jinin jikinta, dan kuwa tuni yaran gidan suka kawo musu tsegumin irin motar da aka zo wurin Jauhar da ita.

Sai jikinta yayi sanyi, ta hau tunanin laifin me tayi? Jiki a sanyaye ta ɗaukko aikinta ta cigaba.

Sai dai suka din ga zaginta babu dalili, hafsa ta saka ƙafa tayi fatali da ɗan plate ɗin jauhar da take zuba dusten.

Hankali a tashe ta ɗaukko tsintsiya tana tattarewa, ba tare da ta damu da son sanin dalilin da ya sa hafsan tayi mata haka ba, domin kuwa idan da sabo ta saba.

Yaya saifu da ya fito daga banɗaki ne, ya ɗurawa Hafsa ashar, saboda ya ga abun da ta yi hafsa.

Babarta ce ta fito tana yi masa masifa, tana kare hafsa, da mayar masa da zagin da yake yi mata.

Aikuwa mama ma ta fito ta haushi da bala'in menene ruwansa da shiga abun da babu ruwansa, nan faɗa ya harƙe, sum-sum jauhar ta ja jikinta ta koma ɗaki.

Da daddare bayan sallar isha'i, baba ya kira jauhar ɗakinsa, ya tambaye ta yaya suka yi da baƙonta, amma ta kasa magana, sai duƙunƙuna hannunta da ta din ga yi a hijjabi.

"Jauhar"

Kanta a sunkuye ta ce "Na'am baba".

"Ba zan yi miki dole ba, ban bawa mutumin nan damar zuwa wurinki ba, sai da na yi bincike a kansa, na san makarantar ki ke tunani, ina mai tabbatar miki ya tabattar mini zai bari ki cigaba. Bana jin daɗin irin rayuwar da ki ke yi a cikin gidan nan, babu yadda zan yi ne. Amma idan ba kya son sa, ba zan yi miki dole ba, ki bi komai a sannu, ki yi istikhara da addu'a, na san ke mai yawan addu'a ce, da miƙa lamuranta ga Allah, ki ƙara dagewa sosai da sosai, ki nemi zaɓin Allah"

"To Baba in sha Allah"

"Yauwwa yarinyar kirki, Allah ya yi miki albarka, ya sa naga jikokina ƴan farare masu kyau kamar jauhar ɗina" rufe fuska tayi ta ƙunshe fuskarta tana murmushi.

Tun da ya shigo layin, wasu daga matasan layin ke darewa, suna ɓuya, ko a jikinsa, tafiyarsa yake yi cikin hanzari da ƙasaita, sumar sa ta cika masa kai, ya aske wani wurin ya bar wani, irin cikakken mara jin nan.

Kai tsaye ya buɗe ƙofar gidan, ya kunna kai cikin gidan.

Babu sallama ba komai, ya kutsa cikin falon in da suke zaune suna karyawa.

Abbu ya ɗaga kai ya kalle shi, ya ce "Uban me ka zo yi mini gida? Me na gaya maka a kan zuwar mini gida?".

Ya sunkuyar da kai ya ce "Ganinka na zo na yi na gaisheka"

"Ba na buƙatar gaisuwarka Al'amin, ai tun da ka zaɓi watsewa a duniya, ka yi fatali da tarbiyarka nima na sallamaka, ka koma wurin abokanka ƴan wiwi da suka fi ni a wurinka. Kalli tsinannen askin da yake kanka, ka zo mini banda warin wiwi babu abun da ka ke yi, sanna ka ce ka zo gaishe ni? Ai ni na barwa duniya kai ka tashi ka bar mini gida"

Yayi shiru yaƙi tashi, kuma ya ƙi magana, sai murza zoben azurfar hannunsa da ƙarfi da yake yi, zuciyarsa na zafi.

Rahila ta ce "Dan Allah ka fita Aminu, wannan warin da ka ke yi, zan iya amai wallahi, kuma ni idan ina ganinka tsoro nake ji wallahi, tun da kullum a buge ka ke kar ka illatani ko yarana a banza" tamkar tana magana da dutse, haka yiyin gingirin gim, bai motsa ba.

"Ba magana ake yi maka ba?" Yayi masa maganar cikin tsawa.

Al'amin ya ɗaga idanunsa, da suka yi ja fiye da lokacin da ya shigo, ya ƙara matsawa kusa da mahaifiyar, ya zuba masa ido sannan ya ce "Na san ina wari, na san kullum a buge nake, a kowane lokaci zan iya ɗaukar makami na hallaka duk wanda ya yi gaba da gaba da ni, ko wanda bai ji ba bai gani ba. Wasu lokutan ma banbancina da mara hankali kaɗan ne, na san ba na jin magana ko kaɗan, bana tsoro ko shakkae aikata duk wani abu da zuciyata ta raya mini, amma idan ban zo wurinka ba wurin wa zan je? Da haka nake? haryanzu ban san laifina a wurinka ba Abbu, zan yi ƙoƙarin daina zuwa gidan nan kamar yadda ka buƙata, ko aka ce maka ana buƙata, amma idan na daina na daina kenan har abada wallahi! Ka huta lafiya" yayi maganar yana shafar saman hannun mahaifinsa.

Yana miƙewa zai wuce, yayi ball da flask ɗin ruwan zafin da yake tsakiyar wurin, da kwanukan. Gaba sai da suka razana.

Ta ce "Ka gani ko?"

Shiru mahaifin Al'amin yayi, ya tashi da sauri ya bi bayansa, sai dai yana fitowa daga falon, ya ga an jefo Abba, babban ɗan Rahil, ƙaton saurayi amma kamar an watso shara.

Ko ba a gaya masa waye ba, ya san aikin Al'amin ne, Abba kuwa bajewa yayi, ko shurawa ba ya yi, rahila ta fito tana kururwa.

Abbu ya leƙa waje da sauri, a can ƙarshen layi, ya hango Al'amin, ya zare wuƙa yana ta zuba sauri.

Ya rufa masa baya, yana ƙwala masa kira, amma ya ƙara sauri har da gudu, ya bar layin.

Ayshercool
08081012143

🔞*PAID BOOK NE, ₦500 BOOK1-3 VIA 0009450228, AISHA ADAM JAIZ BANK, SAI SHAIDAR BIYA TA 08081012143*

Ganin Aminu ya ɓace masa, ya sanya ya koma gida da sauri, rahila sai kururwa  take yi, tana jijjiga Abba.

Ƙannensa mata su azima, suka kewaye shi suka hau kuka.

Abbu ya ɗebo ruwa, ya din ga zubawa Abba, har Allah ya sa ya buɗe ido.

Cikin kuka take cewa "Ka gani ko? Ba zaka taɓa yadda da ta'addancin ɗanka ba, har sai ranar da ya kashe mini ƴaƴa, me yayi masa zai yi masa wannan ɗibar karan mahaukaciyar ya watsar? Wallahi na gaji, ina ga tafiya zan yi na bar maka gidan nan kai da ɗanka, na rasa uban me yaron nan yayi masa, ko dan ba kai ka haifi abba ba, ya tsane shi daga shi har nazifi ni ban sani ba. Ni ba abun na kai shi ƙara wurin hukuma ba, ba sa yi masa komai sai dai a sako shi, ni na gaji".

Abbu ya ce "Dan Allah ki daina wannan maganganun, bari na samo mota, mu kai shi asibiti"

Abba kuwa ko magana ya kasa, Nazifi ne ya taimaka aka fita da Abba zuwa mota.

Al'amin kuwa da ya tabattar da ya tserewa Abbu, ya samu wani lungu, ya jefar da wuƙar hannunsa, ya samu wuri ya zauna, yana ƙoƙarin haɗiye wani abu mai tsananin ɗaci da zafi a maƙogwaronsa, ji yake kamar numfashin sa zai ɗauke, babu abun da zuciyar sa ke raya masa, banda ya kashe matar Abbu wato rahila ya huta.

***
Gidan babu kowa, duk yaran sun tafi makaranta, mama tayi sallama a falon zakiyya.
Ta amsa tare da fitowa daga bedroom ɗin, tayi miƙa ta ce "Lafiya kuwa?"

"Au bacci ma ki ke yi? Lallai kam, to magana na zo mu yi"

Zakiyya ta ce "Ok, bisimillah zauna mana"

Ta nemi wuri ta zauna, ita ma ta zauna.

Mama ta kalleta ta ce "Kin san waye yake son Jauhar kuwa?"

"A'a sai kin faɗa".

"Ɗan familyn mai atamfa ne"

Waro ido Zakiyya ta yi, har tana neman faɗowa daga kan kujera, ta ce "Wani mai atamfar?"

"Waɗanda dai ki ka sani,ba ma wannan ba shi zai tsaya takarar majalissar tarayya a yankinsu, jiya na tutsuye shi, yake gaya mini, ga kasuwancin atamfofi da lesuna da yake sayarwa, daga ƙasashe daban-daban yake order kaya, na din ga bugun cikinsa yana gaya mini, wai zata yi karatu idan tana so, idan business take so zai ba ta jari, idan ma zaman gida take so, ayi din ga yi mata komai, duk zai iya kuma nan kusa yake son ayi auren".

"Bantan uba, namu ƴaƴan suna zaune za ayi hakan, muna me?"

Mama ta ce "Hmm, ni fa na daɗe ina hana faruwar wasu abubuwan, rannan daga aikenta gidan Hajiyar lamin, wai ɗan wan maigidan ya ganta, ya ce ayi masa hanyar aurenta, uban yaron fa sanata ne a Adamawa, hauka nake? Na toshe na hana, na din ga aika su surayya, da walida amma ko kare a familyn babu wanda ya sinsuna su.
Lokacin da suka yi sauka ma, babu kunya wai chairman yana son ta, tun ba ta kai haka ba ma, na ce ba za a lalata mata tunani ba, karatu take yarinya ce, na rasa wannan masifar".

"Mun shiga uku, meyasa kowa sai ita? Kuma duk masu kuɗi, namu yaran fa?".

Mama ta ce "Wannan shegiyar farar fatar suke yi wa ai"

"Wace farar fatar? Su ma duk ba suna shafa mai ba, manyan zaratan ƴan mata, sun sha mai da kwalliya amma ace su duk shiru sai ita?"

"Shiyasa tun jiya ban yi bacci ba wallahi, na saƙa wannan na kwance wancan, dole fa a rusa wannan maganar ma"

Zakiyya ta ce "To yanzu menene shawara? Wallahi na rasa abun cewa, ko malamai zamu shiga ne?".

"Babu lallai yayi tasiri, na fuskanci ƙashin masu arziki ne da ita, amma mu cigaba da shawara kafin faruwar abun".

Zakiyya ta ce "In sha Allah "

Mama ta miƙe ta ce "Sai na ji ki".

***
Cikin ikon Allah Abba ya warware, babu abun da ya same shi, sai dai ya bugu, ya yi ta fama da jiri, sai da ya kwana uku a asibiti, aka sallame shi.

Rahila ta cigaba da ɗagawa Abbu hankali a kan Al'amin, a kan lallai ya kai shi wurin hukuma, a san yadda za ayi da shi, kafin ya yi mata kisan gilla ita da yaranta.

Gaba ɗaya maganganun Al'amin sun yi tasiri a zuciyarsa, amma kuma wani ɓangaren, Rahila tana da gaskiya, al'amin barazana ne a gare su, saboda yadda sunan mai dogon zamani, yayi ƙaurin suna a bakin mutanen unguwa, ba iya unguwar ba, har gidajen radiyo, duk wani faɗan daba da zai tashi a arear rukunin unguwannin to sai an ambaci mai dogon zamani wato Al'amin.
Ƴan sanda har sun gaji da kama shi, idan an kama shi ma, ƴan siyasa sai sun saka an sako shi, daɗinta ɗaya ba ruwansa da taɓa kowa ko kayan kowa, sai ƴan daba da jami'an tsaro da su yake faɗansa.

Bayan Jauhar ta dawo daga makaranta, mama da Anty suka sakata a gaba, suna sake yi mata tambayoyi a kan Alhaji mu'azzam, Jauhar ta rasa me za ta ce musu, dan ita ba komai ta sani a kansa ba, dan tun da ya zo sau ɗaya, bai sake zuwa ba, dan haka ta din ga ce musu ba ta sani ba.
Aikuwa suka din ga zaginta, tare da kiranta munafuka.

Suka gama zaginta, ta cigaba da sabgoginta.

Yaya tijjani ya shigo, wanda shi ne babba a gidan, ya shiga wurin mama, jauhar ba ta san hawa ba, ba ta san sauka ba, ya kamata ya zane a yammacin nan, wai an ce masa kule-kulen maza take yi.

Ihun jauhar ne ya sanya yaya saifu shigowa, ya tarar TJ yana mata bala'i, wai tana kula maza.

"Haba yaya TJ, idan ba ta kula maza ba, kai za ta kula? Ko za a jiƙata a ruwa a sha ne? Da iznin baba fa ya zo wurinta idan ma a kan wannan mutumin nan"

Mama ta ce "Rufe mini baki, kai da ba ka san me duniyar take ciki ba, yadda maza ke lalata yaran mutane yanzu, idan aka sake lalata ta kawai zai yi ya gudu, kuma fuska ya gani shiyasa ya biyota har gida, da ba ta bashi fuska ba ba zai zo ba. Idan da gaske yake auren zai yi, duk ga mata nan da suka fita komai sai ita.

Saifu kawai ya girgiza kai ya fice, ransa ba ya yi masa daɗi, da irin riƙon da ake yi wa ƙanwarsa a gidan nan, shikenan maraici sai ha zama makamin cutar da bawa?.

Har jauhar ta gama girkin dare, kuka take yi, dan ta daku sosai da sosai, fatarta duk tayi ja.

Baba da ya dawo, bai san me aka yi ba, na dukan Jauhar.

Ɗan autansu ne wato amir, ya shigo ya ce "Jauhar ana kiranki a waje, in ji wannan mai motar, kin ga har ya bani kuɗi dubu biyu".

Anty ta ce "Ba zata je ba, je ka ce ba ta nan, ki mayar da kai ki gama sauran aikace-aikacen ki, idan kuma baki da abun yi, ki zo ina da shi ki yi mini".

Baba ya fito da kansa ya ce "Amir, je ka ka ce tana zuwa, Waliyiyya, ajiye duk abun da ki ke yi, ki je ki sallami baƙonki".

"Amma Alhaji.....

"Amma me? A kan me zaku hana yarinya zance, maganar aurensu fa za a fara kwanan nan, da yaya za su fahimci juna?".

Jauhar kamar ta ce wa Baba ba zata je ba, dan tana tsoron a sake saka yaya TJ ya dake ta.

Amma ta kasa magana, ta zura hijjabinta, ta fita.

Tun kan ta fita ta fara jiyo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login