Showing 3001 words to 6000 words out of 152254 words

Chapter 2 - ?arfe A Wuta Book 1 Hausa Novel Complete

15 Dec 2024

321

sai ƴan iska. Sai dai duk wanda ya zo hannuna sai na ci rabona ayi baran-baran. Na daina wahalar son mutum, daga ƙarshe yayi breaking heart ɗina, ya ci bulus. And also haryanzu ban samu spec ɗi na ba kin dai gane"

Sumayya ta ce "Au ke yanzu har wane zaɓe-zaɓe ki ke yi?"

Nabila ta ce "To ana raba mai rai da motsi ne? Iya wuya akwai abun da zuciya take so, kuma ni na fi son namiji mai kumari sosai. Irin wanda zaki ganshi ingarman namiji mai cikar zati. Beside fuskar namiji ba gemu, ai sunansa sumayya, ni kuma daga dattijai, sai marasa gemu, sai kuma ƴan wahala, ni matashi nake so, ba kuma yaro ba"

Sumayya ta ce "Au sunana ne ma abun kwatancen iya shegenki ko, to ki je dan kanki. Mai napep zan sauka a nan, za ta baka kuɗin"

Nabila ta ce "Ke uban waye ya ce miki ina da kuɗi?" Tuni Sumayya ta sauka, ta bar Nabila.

Nabila ta yi ƙwafa ta ce "Zamu haɗu ne, zaki ga wulaƙanci".

***
A hankali yake buɗe jajayen idanunsa, a lokaci guda kuma yana lumshe su, tamkar mai shirin yin bacci. Sai mirgina kansa yake yi, yana sake lumshe manyan idanunsa da suka koma jajaye matuƙa.

Tamkar an jefo shi, haka ya faɗo ɗakin, yana rarraba ido.

A hankali ya ɗaga kai ya kalli wanda ya shigo ɗin, ya mayar da kansa ƙasa ya sunkuyar.

"Allah ya taimaki oga..." Bai amsa ba kawai ya buɗe tafin hannunsa ya miƙa masa.

Wata baƙar leda ya ciro, ya ɗora masa a hannun, sannan ya ce "Sai dai Oga ba a samu da yawa ba, ƴar kaɗan ce, cinnaku sun yi wa kasuwar ƙawanya, shiga da fitar kaya na bayar da wahala, da ƙyar na samu wannan wurin wani ɗan inyamura, ina ga wuri zan canza, saboda kamar ana son yi mini cune".

Bai ce masa uffan ba, ya kwance ledar, ya fito da kwalin wata allura pack guda, mai ɗauke da ampoule na allura guda goma.

Sirinji lamba biyar ya ɗauka, ya din ga fasa alluran yana zuƙa, sai da ya cika sirinjin, sannan ya miƙe hannunsa.

Ya ɗaga kansa ya kalli matashin da ya kawo masa allurar, bai ce masa komai ba, matashin ya bar ɗakin.

Ya mayar da idonsa kan hannunsa, ya yana kallon jijiyoyin da suka kwanta ɗoɗar a ƙarƙashin fatarsa, suka yi ruɗu-ruɗu, manya da ƙanana.

Ya dubi guda ɗaya, ya huda ta da sirinjin hannunsa, ya fara bawa kansa allurar sannu a hankali. Sai da ya zuba ta duka, sannan ya yi jifa da sirinjin, ya sunkuyar da kansa ya na jiran Sakamakon hukuncin da ya ɗauka.

Sai dai kusan mintuna goma sha biyar, bai ji abun da yake so ba, sai wani irin nauyi da kansa ya ƙara, idonsa ya din ga yi masa yaji, ya rintse idanunsa amma bai ji alamar abun da yake so ba.
Abu kamar wasa kansa ya din ga wani irin sarawa, ƙirjinsa yana zafi. Ya dafe kansa da hannunsa bibbiyu yana jujjuyawa tare da rufe idanunsa.

Ihu ya fara yi iya ƙarfin sa yana taƙarƙrewa, yana girgiza kansa, saboda yadda yake jin kansa tamkar zai yi bindiga.

Da gudu suka shiga ɗakin, suka fara ƙoƙarin danne shi, amma ya yi ihu ya watsar da su baki ɗaya ya cigaba da kururuwa.

Ayshercool.
08081012143
[7/16, 1:53 PM] null:          






⚔️*ƘARFE A WUTA*⚔️

MALLAKAR AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION

*BRIGHT PENS SECOND BATCH*

https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

Arewabooks ayshercool7724
Watpad ayshercool7724

2

A ƙalla sun kai ƙarti uku majiya ƙarfi, suka riƙe shi, amma sai ƙoƙarin watsar da su yake yi, ga wani irin gurnani yana yi, kamar mahaukacin zaki.

Da ƙyar suka haɗu suka kai shi ƙasa, suka daddane shi yana cigaba da ƙoƙarin watsar da su ya tashi.

Ɗaya daga cikinsu da yanayin kamanninsa ya bayyana, ƙarara shaye-shaye ya huda shi, saboda yadda laɓɓansa suke baƙi ƙirin, ga wani irin ƙaton tabo a gefen fuskarsa.
A hankali yake ɗan dukan bayansa cikin sigar rarrashi yana faɗin "Easy maza, easy, mun san ka na cikin damuwa da raɗaɗi, amma hakan ba mafita bane ba, ka yi haƙuri muna tare da kai ɗari bisa ɗari iya wuya" ya cigaba da maganar yana rarrashin sa.

A hankali jikinsa ya saki, ya daina gurnanin da yake yi, ya lumshe idanunsa, ya rufe su, tamkar mai bacci. Sai da suka tabattar ya yi relaxing, sannan suka ɗaga shi.

Major ne tsaye a gaban mudubi, yana ƙara kintsa jikinsa kamar wani matashi, ba dattijo ba, uwargidan sa na gefensa tana taimaka masa yana shiryawa, Ba tare da ya kalle ta ba ya ce "Arfa kuwa ta tafi aikin?".

Ta yamutsa fuska ta ce "Ta ga dama ta tafi"

Ya jinjina kai ya ce "Punishment ɗin da na yi mata jiya, shi ya hana ta zo ta gaishe ni yau kenan,'? zan gamu da ita ne idan ta dawo".

"Dan girman Allah major ka ƙyale sabgar yarinyar nan, sai ka ce itakaɗai ce ƴa a gidan nan, komai ita su duk sauran ba ƴaƴa bane ba, da ba ka damu da lamarinsu ba?" Kallon da yayi mata ne ya sanya ta yin shiru, tare da sunkuyar da kai, bai sake ce mata komai ba, ya ɗauki mukullin motarsa ya fice.

Cike da takaici ta sauka daga benen, ta fito main falon gidan tana mita.

"Yaya ya dai? Meyafaru ne?" Duk da ba ta kasance mai sakarwa abokan zamanta fuska ba, amma haka kurum ta tsinci kanta da gaya mata abun da ya faru saboda takaici.

"Major ne mana, gaba ɗaya ya tattara hankalinsa a kan yarinyar nan, kamar itakaɗai ce ƴa a cikin gidan nan, jiya kwana na ne, amma a barandarsa ya ƙare kwanan jiya, wai yana gadinta, abubuwan nan sun fara isata"

Ɗayar ta taɓe baki ta ce "Ai ni na gaji, na zuba ido su ƙarata, abun da ba jiya aka fara ba, ba yau ba".

Anty, wadda take ta uku, da take karyawa, duk da ba da ita suke ba ta ce "Amma dai an yi abun kunya, kishi zan ce ko baƙin ciki da ƴar cikinku"

A fusace Uwargidan major, da ake cewa Mama ta ce "Asiya, da ni ki ke ko wa?"

Anty ta ce "Duk wanda ya tsargu, sai menene dan ya nuna mata kulawa ta musamman, duk kulawar da yake bawa sauran yaran bai isa ba? Ƴaƴa nawa ne a gidan nan, kowanne ya na bashi kulawa dai-dai da buƙatarsa ne, amma da yake kishi ya zame muku bala'i, mussaman ma ke, da kowa ma yi ki ke, kin fi mu daɗewa da shi, amma haryanzu ba ki san halinsa ba"

Mama ta ce "Ba zan yi musayar yawu da ke ba ƙanwar bayana, dan ba ki isa ba, da wanda ya ajiye ki zan yi".

Anty ta ce "Idan ma ƴar cikinki ce, matsayinmu ɗaya matan major, kuma ni gaskiya nake faɗa" haka suka cigaba da ƴan faɗace-faɗacen su na kishi.

Nabila kuwa da wasu lokutan a kan yi mata laƙabi da Arfat, tana zaune a katafaren office, itakaɗai sai aikin danna waya take yi, cikin nishaɗi kamar babu wani abu da yake damunta.

Knocking ɗin ƙofar office ɗin aka yi, ta bayar da izinin a shigo.

Nabila suka gaisa da matar ta ce "Nabila ko?"

Nabila ta jinjina kai ta ce "Eh"

"Ki zo Barrister yana kiranki"

"Wane barrister?"

Matar ta ce "Director. Dama ina son in yi miki magana. Kin ga wurin nan babbar organization ce, da muke dealing da mutane daban-daban, especially manyan mutane. Yana da kyau ki jajirce director baya son ragwanci ko harkar ko in kula da aiki, sai ku samu saɓani"

Nabila ta yi murmushi ta ce "Na gane, na kuma fahimta na gode sosai" matar ta jinjina kai ta fita.

Nabila ma tashi ta yi, ta fita ta tafi office ɗin da ake nemanta.

Ta tarar da shi da wani babban mutum a zaune a office ɗin sa, ta gaishe su cikin girmamawa sannan ta kalli Director ta ce "Sir gani"

Ya kashingiɗa ya ƙare mata kallo sannan ya ce "Nabila, what is actually wrong with you ne?"

Cikin mamaki ta ce "Ni kuma? Me na yi sir?"

Ya gyara zamansa ya ce "Anya ke ki ke son zama lawyer ko choice ɗin major ne? Tun da ki ka zo wurin nan you don't care, sai dai ki zauna ki danna waya, ki yi ciye-ciye, sai kwalliya. Bama kya shiga cikin ma'aikatan ki ga yadda ake aiki, balle mu ga gogewarki, mu faa tura ki trials, dama zuba miki ido na yi amma na ga baki san zuru ba" Nabila ta yi shiru ta sunkuyar da kanta ƙasa.

"Ina buƙatar ganin canji a tare da ke, idan ba haka ba na fara kai ƙarar ki wurin Major, yanzu muna da client da yake son yin apeal, a kan wata shari'a da wasu mutane suka kai ƙararsa. Ki je na saka ki a team ɗin su barrister Habib, ki je ku tattauna yadda za ayi handling case ɗin. Effort ɗinki shi zai sanya na baki manyan cases to help your career"

Ta risunar da kai ta ce "Ok sir" ta juya ta fara tafiya, sai dai mutumin da tarar a office ɗin, ya bi bayanta da kallo yadda ƙugunta ke juyawa, cikin skirt ɗin kayan jikinta.

Office ɗin Barrister Habib ta je, aka sanar da ita suna ɗakin sirri, dan haka kai tsaye can ta wuce.

Ta tura ƙofar ta yi sallama, suka amsa mata, ta nemi wuri ta zauna.

Barrister Habib ya ce "Kin ga damar zuwa kenan?" Wani irin kallo ta yi masa, amma ba ta ce komai ba, su kuma suka cigaba da abun da suke yi.

Shari'a ce a kan wani attajirin mutumin ya karɓe gonakin wasu ƴan ƙauye, ya basu diyya ya fara ginin kamfanin sarrafa shinkafa, sai dai suka yi ƙararsa diyyar da ya biya su, ta saɓawa yarjejeniyar da suka yi da shi, dan sam bai kai darajar gonakinsu ba. Ganin ba su da galihu, ya sanya bai damu da ƙarar da suka kai shi ba, sai da aka yanke hukuncin ya biya su, sannan ya ce zai yi apeal.

Mamaki ya cika Nabila, irin maƙudan kuɗin da ya biya law firm ɗin su, a bashi lawyoyi su kare shi, ya isa ya ƙarawa mutanen nan, ya biya su haƙƙoƙin su.

Nabila dai ta yi zuru da ido, tana kallon yadda ake harhaɗa hujjoji na halal da na haram, domin mutumin yayi nasara a kotu.

Baƙin ciki da takaici suka isheta, sunan ƙauyen da abun ya faru kawai ya isa ka gane cewar masu ƙaramin ƙarfi ne. Dan galibi mutanen karaka da Allah suka dogara, da harkar noma suka dogara.

Tashi ta yi tsaye ta ce "Excuse me please, na fara jin yunwa lokacin cin abincina yayi"

Duka lawyoyin da shi kansa client ɗin suka ɗago suka kalleta.

Habib ya ce "Ana tsaka da aikin?"

Ta basar ta ce"Am sorry, am having a chronic ulcer, za a iya samun matsala, idan na cigaba da zama" daga haka ta ɗauki jakarta ta fice, tana mitar ba zata zauna a ƙulla wannan sharrin da ita ba, ranar lahira ta shiga uku.

Ta koma office ɗin ta, ta yi alwala tayi sallar azahar, ta je ta samu Director ta sanar masa da tana da uzuri ta na son ta tafi, yayi mata iznin hakan.

A hanya ta tsayar da mai napep, suka ɗauki sumayya, sannan suka tafi.

Ta kalli Sumayya ta ce "Sumy, meyafaru ne? Na ga kina wani ɓata rai"

Sumayya ta yi tsaki ta ce "Haushin kaina nake ji, da na karanci aikin jarida Arfa"

Cikin mamaki ta ce "Amma meyasa, na ga shi ne zaɓinki?"

"Wallahi duk ya fita daga kaina, hira aka yi da honorable Indabo, wai an yi borehole a ƙananan Hukumomin da yake wakilta, an raba kayan makaranta ga ɗalibai. An kai bencina makarantun firamare da na islamiyyu. Last week aka ce na je na tattauna da al'umman local government ɗin, na je ni ban ga ayyukan da aka yi ba, na tattauna da mutanen ƙananan hukumomin, sun ce ba ayi musu ba. Na kai recording ɗin, aka saka, wai lawisa ba ta tantance shirin ba, ba ta sani ba aka saka, kin ga cin mutuncin da aka yi mini, wai zan lalata musu business wai sai na je na samo mutanen da zan yi hira da su, su ce eh an yi ayyukan su yi godiya alhalin ba ayi ba. Na zama maƙaryaciya kenan me zan ce wa Allah? Wai har da idan ban yi wasa ba, sai honorable ya saka an ɗaure ni"

Nabila ta ce "Ikon Allah, ashe duk kanwar ja ce sumy, yo nima hakan take ai, wani tasonon Alhaji ne ya zo yayi kirim a kan kujera kamar damin doya, ya biya uban kuɗi wai za a kare shi, ya cuci talakawa ko kunya bai ji ba, kuma director ya sakani a team ɗin lauyoyin, ni dai ba zan yi ba wallahi, sai dai ya yi ta gaya wa Abban. Haka kurum a cuci mutane ka je ka cewa Allah me?"

"Wallahi Nabila, ba ki ji zuciyata ba, yanzu sai dai na je na tara maƙwabta na yi hirar ƙarya da su, a zo a sake sakawa, kuma wai sai na rubuta takardar ban haƙuri, ki ji fa"

Nabila ta ce "Tirƙashi, wai ya ɗaure ki, to ya ɗaure ki shi ma ya hau da ɗaurin Allah " Haka suka cigaba da tattaunawa, har suka isa in da sumayya za ta sauka.

***

Cikin tsananin tashin hankali, yake magana, kallo ɗaya zaka yi masa ka san hankalinsa a matuƙar tashe yake.

Ya daki teburi ya ce "Kwamishina, dole fa ku nemo yaron nan, dole ku mayar da hankali a nemo shi a duk in da yake a ƙasar nan"

Mutumin da yake zaune cikin kakin ƴan sanda ya ce "Honorable, ka kwantar da hankalinka, aikinmu baya buƙatar garaje da gaggawa, sai mun bi a sannu"

"Haba Cp, wane irin bi a sannu? Rayuwata na cikin hatsari, yayi iƙirarin kashe ni, dole fa a nemo yaron nan, ko be kashe ni ba, idan ya buɗe bakinsa yayi wata magana a kaina kashina fa ya riga ya gama bushewa, na san fa waye yaron nan ciki da bai"

Cp ya gyara zamansa ya ce "Amma honorable, wace irin yadda ko alaƙa ce tsakanin ka da yaron nan, da har ya sanka haka, zamansa a gari yake barazana a gareka"

Tsaki mutumin yayi ya ce "Kai har ka tambayi alaƙar da ke tsakanin ɗan siyasa, da tantirin ɗan daba, ɗan iska? Ku nemo shi dillalin wiwi ne, da hard drugs. Da kun ganshi ma kawai a harbe shi, kuma a tuhumi controllern gidan yari, a kan dalilin sakinsa, bayan ko shari'a ba ayi masa ba tsawon lokaci"

Ɗan sandan ya jinjina kai ya ce "Shi controller ya ce court order ya karɓa"

"Ni dai ka yi mini wannan taimakon a nemo shi da gaggawa, dan yana cikin garin nan, tun da ga ayyukan ta'addanci yana ta yi yadda ya ga dama".

CP ya ce "In sha Allah, ka kwantar da hankalinka za ayi duk mai yiwuwa, zan nemi zaƙaƙurai daga cikin mutanenmu, da suke dealing da criminal cases, very soon zai zo hannu, DSP Nasir na san zai yi abun da ya dace in sha Allah"

"Yauwwa to shikenan, ko dai sanarwa za ku yi, ace duk in da aka gano shi a kamo shi, an sake shi ba bisa ƙa'ida ba"

Da sauri ya ce "No ai ba haka aikin tsaro yake ba, ai wannan abun kunya ne ga hukumominmu, yanzu sanin in da yake shi ne babban target ɗinmu, dan yaron yana da wayo sosai, na bibiyi record ɗin sa, sai an yi taka tsantsan sosai wurin kama shi, sai an yi amfani da dabarun aiki, hatsabibi ne sosai"

"To ayi ƙoƙarin hakan dan Allah".

***
Gudu-gudu sauri-sauri ta ƙarasa gida, saboda azababben fitsarin da ya cika mata mararta, tana zuwa ɗaki ta watsar da komai a kan gadonta, ta shiga banɗaki.
Sai da ta gama fitsarin, ta ji iska na shigarta, tayi wanka ta fito, ta tattare kayan da ta watsar, ta samu riga ta shan iska ta saka, ta shafa turare ta fita.

Kitchen ta shiga dan zuba abinci, ta ci karo da fate-faten wake a cikin food flask ɗin ta. A ƙule ta ja uban tsaki, ta fito babban falo kamar ta fashe da kuka, ta hau ƙwalawa mai aikinsu kira.

"Baba magajiya!"

Daga can wani sashen ta amsa da "Na'am, Arfa gani nan"

"Na ga faten wake yau?"

"Eh, umarnin Hajiya babba ne, ita ta ce ayi faten wake".

Cikin ɗaga murya arfa ta ce "Amma dai an san ba na ci ko? Kin dafa mini wani abun ne?"

Magajiya ta ce "Wallahi har na ɗaukko doya na fara frayewa, na ɗan dafa miki, na soya miki miya, aka kuma sakani aiki".

Nabila cikin kwakwazo take masifa "Saboda tsabar an tsane ni, so ake na mutu a huta, in je aiki in dawo a kasa ajiye mini abinci, sai a dafa abun da ba na so"

"Ke Nabila meye haka ne, hajiya ce ta bayar da umarnin hakan, ki shiga kitchen ki dafa wani abun mana" Nabila ta kalli Yaya Sauda ta ce "In je in dawo yanzu, sannan in shiga kitchen in hau girki, bari in je in sha faten waken, duk abun da ya same ni, ku kuka kasheni, ai kun san likita ya hana ni cin wake"

"To ki je ki ci ɗin mana, idan kin mutun sai ne? Banda gulma amma ai ki na cin ƙosai da shinkafa da wake, ko duk su ba waken bane ba"

Kamar ƴar goye, Nabila ta din ga zirarar da hawaye ta na bala'i.

"Kar Allah ya sa ki ci abun da aka dafa, kya mutu da yunwa agola ƴar wahala".

Cikin tsananin fusata Nabila ta ce "Tun da dai ba shegiya ba ce ni da ubana, ai da sauƙi"

Cikin son kunna Nabila, Sauda ta ce "Meye marabarki da mara uban?"

Baba magajiya da ke tsaye ta ce "A'a Sauda, dan Allah kar ayi haka, ke fa babbace"

Sauda ta ɗaga mata hannu tare da cewa "Babu ruwanki, ki wuce ki ƙarasawa mama aikinta. Ke kuma ki tsaya ki cigaba da hauka, banda samun wuri ina na taɓa ganin agola da miƙe ƙafa".

"Ai gara ni, agolar ce, kuma iya wuya ni ƴar gari ce, ba baƙuwar haure ba, jikar yarabawa. Kuma ni ba dan albarkacin ubana ba, wallahi da na daɗe da barin gidan nan, gara na je na kama gida na yi zaman kaina, iyaka ace ina zaman kaina, ba ɗan iskan da zai takura mini"

Sauda ta tsaya ta ce "To

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login