Showing 57001 words to 60000 words out of 152254 words
jakarta ta yi, ta fita bayan da saƙon barrister Habib ya shiga wayarta.
Ba ta wani sha wahala ba zuwa kotun da ya bata adress ɗin, tun da dama sananniyar magistrate court ce a kano.
Ofishin rijistra ta je, suka gaisa da mutanen wurin, sannan ta tambayi office ɗin mutumin da barrister Habib ya gaya mata.
Aka yi mata iso, sannan ta gabatarwa da mutumin kanta, da wanda ya turo ta.
Ya karɓeta da mutuntawa sannan ya ce "Baiwar Allah, gaskiya ta in da ki ka biyo, babu yadda za ayi na kasa yi miki alfarma, amma riƙe file ɗin nan, tamkar saka hannu ne ki ɗaukko ƙarfen da yake cikin wuta ne, dan Allah kar ki je ki yi wani abu da bai kamata ba, tun kan ki zo aka yi waya, aka ce a baki idan kin zo"
Nabila ta ce "In sha Allah, babu wani abu da zan yi, ina ɗan yi wani bincike ne kawai".
Ya ja ta suka tafi wani wuri a cikin kotun, suka shiga can wani office, da ba zaka ce akwai mutane a wurin ba, sai da suka shiga can ciki, suka iske wani mutum yana ta aiki a computer.
Suka gaisa, wanda ya rakota ya ce "Oga, ga baƙuwa mun yi, Barrister Habib ne ya aikota, shi kuma daga top oga, ya ce a kawo ta file ɗin Al'amin viper zaka ɗaukko mata"
Shiru mutumin yayi yana kallon ta sannan ya ce "Ya sunanki?"
"Nabila yusuf maitama"
"Me za ki yi da file ɗin?"
Ta ɗan rausayar da kai ta ce "Wani bincike nake yi ne"
Ya mayar da hankalin sa kan mutumin da ya rakota ya ce "Ka gaya mata illar da ke cikin hakan?"
"Na gaya mata, ko ma dai menene na gaya maka wanda ya ce a ba ta ai"
Yayi ajiyar zuciya yana cigaba da yi wa Nabila kallon tuhuma, ya tashi ya shiga wani wuri.
Ta kalli mutumin da ya rakota ta ce "Yallaɓai, meyasa file ɗin yake da hatsari har haka?"
Yayi murmushi ya yi ƙasa da muryarsa ya ce "Yana da alaƙa da rashin gaskiya"
Mutumin ya fito ɗauke da file ɗin, duk ya yi ƙura, hannu na rawa ta karɓa ta ja kujera ta zauna, ta fara dubawa.
Sannu a hankali ta din ga bin bayanan ciki, da binciken rahoton ƴan sanda a kai, sai dai komai ba straight forward aka yi shi ba, gaba ɗaya kanta ya kulle, ba ta fuskanci wani abun kirki a ciki ba.
"Amma sir, ina ƙarshen shari'ar, ai wannan ba a yanke hukunci ba, ranar ƙarshe da aka ɗaga shari'ar an ce sati uku za a sake zama, yanzu kusan shekara biyar, ba a sake rubuta komai ba"
Mutumin ya ce "Eh yadda ki ka gani a haka yake"
Cike da mamaki ta ce "Dan Allah wane alƙalin ne ya yi masa shari'ar?"
"Yana abuja" suka bata amsa a taƙaice.
"Wannan documentation ɗin, sam ba a yi shi ma yadda za a fahimta ba, amma dan Allah....
Wanda ya ɗauko mata File ɗin ya ce "Mu fa babu abun da za mu iya sake gaya miki, ba wanda yake da damar zuwa wurin nan sai staff ɗinmu, dan haka ki tashi ki tafi".
Ta miƙe tsaye ta ce "Na gode sosai"
Ta fito daga office ɗin tana mamaki, ta ja ta tsaya tana kallon office ɗin, a abun da ta fuskanta wuri ne da ake ɓoye files na musamman.
"Yayi kisan kai!" Ta faɗa a fili.
"Ba abun mamaki bane ba, da gani zai aikata abun da ya fi kisan kai, amma menene dalilin ajiye shi shekara biyar, ba ayi masa shari'a ba, an ɓoye file ɗin sa a wuri na musamman, ya shekara biyar a prison, kuma kwatsam an sake shi, babu document na wanke shi aka yi daga laifin ko kuwa, duk da an rubuta ya amsa laifin, amma wane hukuncin aka yanke masa? Wayyo Allah kaina zai fashe" ta yi maganar tana dafe kanta, da ya yi mata nauyi.
***
A tsaye yake a kanta yana ƙare mata kallo, yanayin yadda take a kwance ya tabbatar masa da salla ta yi.
Ruwan robar hannunsa ya fara zuba mata a Jikinta, hakan ya razanata ta tashi a gigice.
Ya watsa mata sabulu da soso a jiki ya ce "Ki tashi ki je ki yi wanka, ba na son ƙazanta, kar ki haifar mini ɗa mai dauɗa"
Ta yinƙura ta tashi da kyar, tana jiri, ga yunwa ga zazzaɓi ga kwana da ta yi amai, ta din ga bin bango, har ta isa banɗaki.
Ta daɗe a banɗakin tana kuka, sannan ta yi wankan ta fito, ta tarar da shi a kan gado a zaune yana danna waya.
Ya ɗaga kai ya kalleta ya ce "Dalla cire wannan kayan, ƙazamar banza da wofi, har amai ki ka yi a jikin kayan amma ki ka mayar da su jikinki" kallonsa take yi, to tsirara yake son ta zauna?
Ya buɗe wardrobe ɗin da ke ɗakin, duk kayansa ne a ciki, ya jefa mata wata shirt, ya ce ta ɗauka ta saka.
Banza ta yi masa, ta kawar da kanta gefe, wanda hakan ya hasala shi, yana zuwa gabanta ya kwasheta da mari, abunka da jiki babu ƙwari, take ta faɗi ƙasa, ta riƙe fuskarta.
"Ke kin isa ina magana ki yi mini banza, ƴar wahala mara amfani, ɗauki ki saka kan na tattakaki"
Ramma ba ta ƙaunar duk da abun da zai taɓa lafiyar jikinta, haka ta zura rigar nan, ta zo mata har gwiwa, sai rufe jikinta take yi.
Ya danƙota, ya fita falo da ita.
A falon ya haɗa mata baƙin shayi, sai soyayyen dankali da ketchup ya ce ta ci.
Gaba ɗaya a tsorace take, saboda kar ya kuma dukanta, haka ta din ga tsakura tana ci tana hawaye.
Ta gama ci, ya ɗaukko alluran zazzaɓi da yake yi mata yayi mata.
Ta lura yana da mai aiki a gidan namiji, har girki da gyaran gidan shi ne yake yi masa su.
Ya kashingiɗa yana kallon tv, ita kuma tana gefensa a ɗarare, sai mutsu-mustu take yi tana share hawaye.
Sahidar yatsunsa ya gani kwance a fuskarta, har ya ɗaga ya basar ya cigaba da kallonsa yana kaɗa ƙafa.
***
"Allah ya taimaki maigida"
"Menene labari?"
"Na samu kiran waya ɗazu, wata yarinya ta je an kaita har ofishin secret files, an ɗaukko mata file ɗin viper ta duba"
"Wacece ita?"
"Yarinyar da ka ce ayi amfani da ita a kama Viper"
Da sauri ya ce "What? Ya aka yi ta san da file ɗin ta je? Waye ya ce a bata?"
"Wallahi ban sani ba, amma an tabattar mini da ga sama su ma aka ba su umarnin ba ta"
"Sama ina, waye ya bayar da umarnin?"
"Ban sani ba wallahi, kuma da gaske lawyer ce, idan kuwa haka ne, za ta iya yiwuwa da gaske ta haɗu da Viper, ƴar jaridar nan raina mana hankali ta yi"
Indabo ya numfasa ya ce "Kar ku yi gaggawa, kar ta san mu na bibiyarta, ka bi ta hannun ƙawarta, ku samo me take son samu a kansa, idan ta ƙi, ku kamata ku azabtar da ita".
Ya amsa da "Ok sir".
Daga kotun, gida arfa ta tafi, tun daga shigarta, Sauda ta fara tsokanarta da faɗa, amma ba ta ita take ba, ɗakinta tafi ta cigaba da tunani da lissafi.
Kamar wadda aka zungura, ta ɗaukko wayarta ta kira Nasir.
Murya ƙasa-ƙasa ya ce "Arfa ya dai? Mun shiga meeting ne"
Kamar za ta yi kuka ta ce "Yaushe za ka dawo?"
"Zamu yi waya an jima, ki yi haƙuri"
"Kar ka kashe mana dan Allah, ni ina cikin damuwa magana nake son mu yi, wani abu zan baka"
Ya ce "Wani abu me?"
"Abu ne mai muhimmanci a kan viper, amma sai ka yi mini alƙawarin ba zaka yi mini faɗa ba ko ka gayawa abba ba"
Tattara nutsuwarsa ya yi ya ce "I hope, ba wata kasadar ki ka je ki ka aikata ba"
Ta girgiza kai ta ce "Ba wata kasada da na yi, ni dai ka yi ka dawo, kan na mutu"
A rikice ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, menene ki gaya mini"
"Ka kwantar da hankalinka, kawai dai ka yi ka dawo, abun yana da muhimmanci, na san yadda zaka same shi kai tsaye"
"Kin ga ba zan iya jira ba, gaya mini menene sai na aika su Mu'azzam, dama wanda aka kama ɗin nan ya ƙi magana"
"Sai ka dawo gaskiya" ta kashe wayar gaba ki ɗaya, dan kar ya biyo ta, ta sake dafe kanta.
Sumayya na news room, tana jiran lokaci ya cika, ta gabatar aka turo ƙofar aka shigo. Sak tayi tana kallon mai shigowar.
Mutumin da honorable ya saka ya karɓi wayarta ne, ranar da ta je gidansa.
Ya ja kujera yana kallonta, ya ce "Ya dai, kin yi mamakin ganina ne? Mintuna goma sha biyar suka rage miki, kan ki fara karanta labaran, zaki yi mini aiki".
Ta zuba masa ido, amma ba ta ce uffan ba.
"Meyasa ki ke yi mana ƙarya a aikinmu? Da gaske ƙawarki ta haɗu da Viper?"
Cikin ɓacin rai Sumayya ta ce "Na gaji da amsa wannan tambayar, idan ba ku yadda da ni ba, ku nemeta ta amsa muku mana"
Ya shafi sajensa ya ce "Zamu gani ai, yau ta je court ɗin da aka yi wa Viper shari'a, ta karɓi secret file ɗin sa ta duba, zaki kira ta, ki ji dalilin zuwan ta, da kuma abun da za ta yi da file ɗin"
Sumayya ta girgiza kai ta ce "Nabila ba wani abu da za ta amfana muku, kawai na san ƴar rigima ce, so take ta yi suna ta ɗaukaka ta taimakawa yayanta shikenan"
Yayi dariya ya ce "Za mu gani, daga yanzu zuwa azahar ɗin gobe, idan baki kawo rahoton dalilin bin diddigin shari'ar Viper da take yi ba, abun da ba kya zato zai faru" ya miƙe tsaye ya ce "lokaci ya cika, ki gabatar da aikinki"
Sumayya ta dafe kai cikin matsananciyar damuwa, tana tunanin wannan wace irin rayuwa ce.
Murtala ne ya shigo yana faɗin "Afuwan sisyna, mamager ya kira ni ne, na saita komai ki fara".
"Ba ka ga mutumin da ya fita yanzu ba?"
Ya kalli ƙofar ya ce "Ban ga kowa ba"
Tayi ajiyar zuciya ta ce "Shikenan mu fara".
***
Ƙaramar wayarta ce isheta da vibration a ƙasan pillow, ta ɗaga ta ce "Bacci fa nake ki ke ta kiran wayata".
"Haka dai, daga bacci sai kwalliya da cin abinci, ke har kin koma gida kin kwanta, ni tun 9 gani har 5 ban tashi ba"
Nabila ta ce "Ke ba na samun bacci a ƴan kwankin nan wallahi"
"Meyasa?"
"Wallahi a tsorace nake, ba na iya bacci, gani nake kowane lokaci viper zai kashe ni, cewa yayi fa sai ya kashe ni, sonake Yaya ya dawo na danƙa masa wayar nan, na huta, wai da wayar wa ki ka kira ni ne?"
Sumayya ta ce "Wayata ce ta ɗauke, ina ki ka je ne yau?"
"Wurin aiki mana, amma da labari sosai, mu haɗu gobe in Allah ya kaimu"
"Yakamata mu haɗu kam, dan na ga mutuniyarki bunkure, a gidan honorable Indabo"
Daga kan gadon da Nabila take ta miƙe tsaye ta ce "Amma ba ki gaya mini ba sai yau?"
"Na san halinki ne, uzzura mini zaki yi, ke bari na tafi gida ma yi magana"
Ta kashe wayar, ta kaiwa murtala wayarsa, dan ta fuskanci mutanen honorable na bibiyar kiran wayar da take yi.
Wuni guda ramma ba ta sake saka Abdul a idonta ba, sai dai kukunsa idan ya kammala girki, ya ƙwanƙwasa mata ƙofa ya ajiye mata abinci.
Tayi kuka har ta gaji, ta koma addu'a, tare da fatan Allah ya kuɓutar da ita daga sharrin zaluncin Abdul.
Tana zaune a ƙasan carfet, har wurin sha biyu na dare, ya shigo yana kokawa da ƙofar ɗakin, saboda a buge yake.
Ta tashi tsaye cikin tsoro, sai dai ba tare da ta yi masa laifin komai ba, ya hau ta duka, ya din ga ball da ita yana taka ta da ƙafarsa, tun tana kururwa har ta kasa sai ajiyar zuciya, ko ƙwaƙwƙwaran motsi ba ta iya yi.
Tamkar dabba haka ya afka mata, ba tare da la'akari da ƙarancin shekarunta ba, kodayeke ina tunani ga wanda hankalinsa ya gushe?.
Bai farka ba sai kusan tara na safe, yayi miƙa ya tashi yana kallon ɗakin, da sauri ya kalli gadon bai ganta ba, ya kalli jikinsa, ya tashi yana mayar da kayansa, kawai ya ga jini a gefensa, har zuwa banɗaki, cikin hanzari ya nufi banɗakin, ƙofar tana buɗe dan haka ya shiga, ya tarar da ita a zaune ta jingina da jikin bath jini yana ta zuba daga jikinta, ga jikinta duk a kumbure saboda duka, idonta a rufe.
Ya ƙarasa ya durƙusa ya ɗaga hannunta ya saki, ya ga ya koma babu alamar numfashi a tare da ita, rigarsa dake jikinta, tayi sharkaf da jini.
Dafe kansa yayi yana tuna abun da ya faru jiya, kamar mafarki.
🔞*PAID BOOK NE, ₦500 BOOK1-3 VIA 0009450228, AISHA ADAM JAIZ BANK, SAI SHAIDAR BIYA TA 08081012143*
16
Shi gashi ko sunanta ma bai sani ba, ya sake ɗaga hannunta, amma hannun ya sake dawowa ƙasa.
Ya kai hannunsa hancinta, ya ji tana numfashi kaɗan-kaɗan.
Ya haɗa ruwa a bath ɗin mai ɗumi, ya cire rigar jikinta ya ajiye a gefe.
Ya ƙarewa jikinta kallo, ko ina shatin duka ne da ya yi mata, take wani abu mai kama da tausayinta ya ɗarsu a ransa, ya ɗaga ta, ya sakata a cikin bath ɗin, ga abun da ta yi ɓari nan daga cikinta a ƙarƙashin ta.
Duk da ƙyanƙyaminsa, da yadda ƙarnin jinin yake hawar masa ka, haka ya din ga tarar ruwa, yana kwarawa a banɗakin, ita kuma ya din ga canza ruwan da take ciki, saboda yadda yake ɓaci da jini.
Rigarta kuwa, wuri guda ya ware ta, dan kuwa yarwa zai yi, bai san yadda zai yi da ita ba.
Ya fita da sauri, ya kira mai aikinsa solomon, ya rubuta masa abubuwan da yake buƙata ya ce ya sayo masa.
Har solomon ya je ya dawo, yana ta ƙoƙarin ganin ya tsayar da jinin da take zubarwa.
Ya ɗauke ta zuwa kan gado ya kwantar da ita kamar gawa, ya sake ɗiban jininta, ya yi bawa solomon ya ce ya kai kowane lap ne, idan ya kai ya kira shi a waya.
Ya saka mata drip hannu biyu, ya sake su, yana yi yana duba vitals ɗin ta.
Ƙofar ɗakin ake ta bubbugawa, ya tashi ya buɗe, ya ga saif a tsaye.
Saif ya kalleshi ya ce "Ya na ganka kamar mara gaskiya? Lafiya kuwa?"
Ya girgiza kai ya ce "Ina fa lafiya, yarinyar nan ce tayi miscarriage"
Saif ya ce "Shi ne me to? Dama ba haka kake so ba, na ga ma fa kasheta za ka yi ka bar ta"
Abdul ya ce "Haka ne, jiya daka sauke ni bayan ka tafi, ka san a buge nake, na dake ta sosai"
"Lallai Abdul, yau ka fara yi wa mata haka to?"
Ya girgiza kai ya ce "No, kawai su sauran su ne suke kawo mini kansu, shiyasa ban taɓa jin komai ba a kan abun da nake aikatawa, sai ta ji sauƙi sosai, zan kasheta na huta"
Saif ya ce "Well mu je in ga jikin nata"
Abdul ya tsaya a gaban ƙofar ya ce "No, ba zaka shiga ba"
Cikin mamaki ya kalli Abdul ya ce "Lafiyarka kuwa?"
"Ras nake, ba zaka shiga bane kawai"
"Ka kashetan kenan?"
"Idan na kasheta, zan kasa gaya maka ne, ko tsoronka nake ji?"
Suna haka solomon ya kira shi, ya haɗa su da masu lap, ya gaya musu gwaje-gwajen da yake so a yi wa jinin ramma da ya bayar aka kai.
Ya koma ɗakin da take, ya rufe ya saka mumulli, ta ciki, ya sake nufar gadon, ya hau yana tattaɓata ya ga ko ta na da rai.
Ambaton Allah ya ji tana yi, tare da kiran sunan mama ƙasa-ƙasa, sai dai bai ma san sunanta ba balle ya kira sunan.
A hankali ta buɗe idonta a kansa, ta yinƙura za ta tashi, amma ta kasa, duk jikinta ciwo yake yi, mararta ma wani irin ciwo take yi mata.
Ya riƙe hannunta, yana tsareta da idanunsa ya ce "Sannu"
Hawaye ya shiga ziraro mata ta gefen idonta ta ce "Me na yi maka jiya ka dake ni?"
Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "A buge nake ne ba abun da ki ka yi mini"
Cikin ƙarfin hali ta ce "Allah ya saka mini, na barka da Allah"
Ya amsa da "Tom"
Ta sake yinƙurawa za ta tashi, amma ya riƙeta ya ce "Ina zaki?"
"Salla zan yi"
Abdul ya ce "Ki na zubar da jinin zaki yi salla?"
Ta ɗan gyara kwanciyar ta, cike da takaicin yanayin da take ciki, da kuma kallon da yake yi mata, cikin marairaicewa ta ce "Dan Allah ka rufe mini jikina, ka daina kallona".
Da idanunsa ya tsatstsareta, yana yi mata wani irin kallo, da ya ƙara ɓata mata rai, ta ɗaga hannunta da kyar, za ta ja zanin gado da ya rufe mata ƙafa, ta rufe jikinta da ko arzikin vest babu, amma ya riƙe hannunta, ya mayar ya ajiye wuri guda.
Ya ce "Idan ruwan nan ya goce, mutuwa zaki yi, dan kin zubar da jini sosai, kuma bana fatan ki mutu yanzu, sai kin samu ciki, kin haifa mini ɗa, saboda zuciyata ta so abun da yake cikinki, ya zube".
A hankali ta cigaba da sheshsheƙar kuka, tare da fatan ta mutu ta huta da wannan bayahudiyar rayuwar da ta faɗa, duk a silar talauci da rashin galihu, ta san Allah kaɗai ya san halin da mahaifiyar ta take ciki, na tashin hankalin rashin sanin in da take.
Idonsa ya sauka a kan taruwar jinin da ya kwanta a gefen wuyanta, ya ƙara tabattar da ba ƙaramin duka ya yi mata ba.
A karo na farko da ya ji waji abu mai kama da tausayin wani ya shiga ransa, she look very innocent and calm.
***
Tun da Nabila ta shiga office ɗin Barrister Habib, take murmushi, shi ma murmushin ya yi mata ya ce "Ya ake ciki ke ƴar ƙwalisa"
Ta zauna tare da faɗin "Godiya nake barrister, jiya ai na je, an bani duk abun da na buƙata, na gode sosai da sosai Allah ya saka da alkhairi"
Barrister Habib ya amsa da "Amin ya rabb, ina fatan babu wani abun?"
Ta ce "Akwai, abubuwan da na gani sun ɗaure mini kai, ashe kisan kai yayi"
"Ba abun mamaki bane ba, dan mutum irin wannan ya yi kisan kai ai".
Ta ce "Haka ne, amma shekara biyar ya yi ba a yi masa shari'a, kuma aka sake shi, ba tare da wani cikakken dalili ba, gaba ɗaya ma akwai abubuwan da