Showing 108001 words to 111000 words out of 152254 words
ya motsi, balle yayi magana haka Al'amin yayi kirim a wurin.
"Dalla malam ka yi musu bayani, ka gaya musu ba ka ta'amalli da ita kar su yi ta tila maka na jaki a banza su nakasa ka" Walid yayi maganar cikin ƙunar rai, dan ya san ƙage kawai aka yi wa Al'amin.
Liti ya ce "Kai ma ka san ba zai yi ba, wasu lokutan zuciya in dai irin ta shi ce ba ta yi ba"
Jauhar ta riƙe hannunsa za ta yi magana, sai dai jikinsa kamar wuta Saboda zafi, sai yanzu ta tuna bai gama warkewa ba aka kama shi, durƙushewa tayi a gabansa ta cigaba da kuka.
"Lokacinku yayi, zaku iya tafiya"
Liti ya ce "Ko ba ku ce ba zamu tafi, kowa yayi na gari dai kansa ya yi wa"
Al'amin ya miƙe tsaye, ya saka hannu ɗaya ya ɗagata daga durƙushen da take, ya juya zai koma, ta saka ƙarfinta ta rirriƙe shi tana kuka.
"Ke wai meye haka, da ki ka samu aka bari ki ka ganshi" ɗan sandan ya daka mata tsawa.
"Wallahi sai dai ku rufe mu tare, ni ba zan tafi ba, wai ya ake so na yi ne? Ya zan yi ko ina babu daɗi, ni komai nawa ba sa'a. Na gaya muku ba shi da laifi, amma dukansa ku ke yi, tayaya hankalina zai kwanta idan na tafi? Ba laifinsa ba ne wallahi, laifina ne na karɓi abu daga hannun wanda ban sani ba dan Allah ku ƙyale shi"
Matsanancin tausayin da jauhar ta bawa liti, ya sanya ya fice ya bar wurin, kuka take iya ƙarfinta, Al'amin har mamaki yake yi, tsakaninsa da ita ba wata shaƙuwa ko kulawa ta musamman amma idan abu ya same shi, gaba ɗaya sai ta rikice.
Walid tsayawa yayi ya ga viper zai rarrasheta ko kuma ƙasaitar zai tsaya ya cigaba, da kuwa ko 'yan sandan za su rufe shi, sai ya zage shi.
Ɗaya daga jami'an tsaron yayo kan jauhar, da nufin ya ɓanɓareta ta ƙarfin tsiya, su mayar da Viper, cikin hanzari ya ja baya da ita a jikinsa, ya ɗaga masa hannu yana ƙara tsuke fuska.
Ya saka hannu, ya ɓanɓareta daga jikinsa, ya riƙe hannayenta, gaba ɗaya kammnin fuskarta sun canza saboda idanunta sun kumbura sosai ta koma pink saboda kuka.
Ya sunkuyo dai-dai fuskarta ya ce "Kin kusa fara exam, ki yi karatu sosai, kar ki zauna zaman shiriritar nan, ki yi ƙoƙari ki yi karatu ki zama lawyer ko likita, ko dan saboda fitinannen mijinki, ki gaida mini da kwaɗinki da ƙadangaru idan kin koma gida" tana jin yadda jikinsa yake fitar da hucin zafi da warin datti, kwana bakwan nan babu alamar wanka ko wadataccen abinci a tare da shi.
Ya kama kafaɗarta, ya saita ta hanyar fita ya ce "Kar ki sake zuwa wurin nan saboda ni" ya kalli walid ya nuna masa Jauhar, ya yi masa wata inkiya, ya juya suka mayar da shi.
Suka fito tana kuka, liti ya girgiza kai ya ce "Wallahi Mutanen nan 'yan wuta ne"
Walid ya ce "Kai wannan hurumin Ubangiji ne, amma ko dan hakkin yarinyar nan Allah sai ya kama su, a gidan uwasu zai ga cocaine ɗin, wallahi ƙila su suka zo da abar su suka saka masa"
"Zasu aikata ai ba tsoron Allah suke yi ba" sun yi gaba suna ta surutu suna zage-zage da tsine-tsine.
Suka nemi jauhar suka rasa, suka waiwaya, tana bakin ƙofar in da suka baro, ta zauna dirshan tana matsar hawaye.
Liti ya ce "Taɓ lallai sabga da mata sai haƙuri, wannan ko mutuwa yayi abun da za ta yi kenan"
Walid ya ce "Sai an yi mata uzuri, ba ta saba ganin wannan tashin hankalin ba, ina zuwa".
Ya koma da baya wurinta, ya zauna ya din ga rarrashinta, tare da ba ta tabbacin Aminu zai fita.
Cikin kuka ta ce "Ba ma fa shi da lafiya, zazzaɓi ne a jikinsa"
"Ki yi haƙuri, Allah zai bashi lafiya"
Ta sake cewa "To yanzu daga nan me za su yi masa?"
"Wallahi ba mu sani ba, amma zamu cigaba da bibiya in sha Allah, sai mun ga abun da ya ture wa buzu naɗi" da ƙyar ta taso, suka kaita har gida, Walid ya ba ta kuɗi, ta ce ba zata karɓa ba, sai da ya ce mata Al'amin ne ya ce ya bata sannan ta karɓa.
Har ta shiga falo, aka buga mata ƙofa, ta dawo ta buɗe, ta ga Malam lawan baban su halimatu a tsaye.
Ta durƙusa ta gaishe shi, ya ce "Wato duk na san ke da mijinki, kuna jin haushina, amma ni duk in da gaskiya take sai na faɗa. Ke yanzu ki ji da halin da mijinki yake ciki, amma kin zo kina tara mana maza a layi, kusan kullum sai sun zo, shi fa aure abu ne mai daraja da muhimmanci".
Jiki a sanyaye ta ce "Tara maza kuma?"
"Eh mana, wannan da ku ke fita tare da su ku dawo, muharraminki ne?"
Kalmar ta yi mata nauyi sosai, amma ta dake ta ce "Aboknsa ne, su ne suke taimaka mini a kan case ɗin sa"
"To ke me yayi miko zafi? Ki koma gidanku mana, idan ya fito kya dawo, ko ma ki haƙura da auren, da kyanki da ƙuruciyarki nan da nan wani zai aureki, shi kuma ya cigaba da shashancinsa".
Ta ce "To na gode sosai"
"Ai gara dai ki san abun yi, ni Allah ya sa ma ba iyayenki ki ka bujirewa a kansa ba, Allah yake jarabatarki ba" gaba ɗaya sai ta ji kimarsa ta zube a idonta.
Jauhar ta kama Alƙur'ani da da carbi, tayi ta Addu'a tana gaya wa Allah.
Aka sake shafe kwana biyar, su liti suna yi mata yawo da hankali, suka kuma hanata komawa wurinsa, sai su ce mata sun je yana lafiya yana gaisheta.
Haka kurum ta ji a ranta ƙarya suke yi mata, ba tare da sun sani ba, ta sake ɗaukar ƙafa ta tafi wurin 'yan sanda, har da abincinta ta tafi da shi, sai dai suka tabbatar mata sun kai shi kotu, har alƙali ya aike da shi gidan gyaran hali, zuwa lokacin da za a cigaba da shari'a.
Cikin tashin hankali ta tambaye su, zuwa yaushe zai fito.
Suka ce mata ta tafi kotun ta tambaya, suka din ga yi mata wasa da hankali, har da wanda suka biyota da maganar lalata.
A ƙofar gida, ta tarar da su walid, sai jan ƙafa take da ƙyar, ta ƙarasa.
Walid ya ce "Madam ina ki ka tafi ne, mun zo ba kya nan?"
Ta kalleshi cike da karaya ta ce "Dama an kai shi prison ba ku gaya mini ba?"
Liti ya ce "Komawa ki ka yi kenan, ke ana ta ɓoye miki, dan kar ki tayar da hankalinki, shi muka zo gaya miki, sai da muka tsara yadda zamu gaya miki, yadda ba zaki damu ba, amma kin tashi kin tafi kin jiyo wa kanki damuwa"
Ta ce "To ya zan yi, na kasa jurewa".
Walid ya ce "Yanzu dai tun da kin riga kin je kin ji da kanki, shikenan amma ki yi haƙuri zamu nemo wata hanyar mijinki zai fito in sha Allah"
Jinjina musu kai kawai tayi, ta shiga gida. tuna da liti yayi mata kwatancen gidan su Al'amin, kamar korarriya, ta sake ɗaukar hanya, ta tafi unguwar su Al'amin tare da fatan Allah ya sa idan ta je gidan su Allah ya sa a dace a samu hanyar fitar da shi.
Sai da ta haɗa da tambaya, sai dai gidan na su ba ɓoyayye bane ba, mussaman ma sunansa da ya riga ya shahara sosai.
Sau biyu tana sallama aka amsa, mata wata matashiyar budurwa, da zata girme mata ta leƙo ta amsa.
Ta ce "Ya aka yi?"
Jauhar ta yi murmushi ta ce "Baƙuwa ce"
Amira ta ce "Baƙuwa daga ina?"
Rahila ta ce "Amira ki bari ta shigo mana"
Ta bawa jauhar hanya, ta ƙarasa ta shiga falon da sallama.
Rahila na ganinta ta washe baki, cike da duniyanci ta ce "Amrya ba kya laifi, ko kin kashe ɗan masu gida" jauhar ta zube har ƙasa ta gaisheta.
"Lafiya ƙalau, zauna a kan kujera mana jauhar" ta sunkuyar da kai tare da girgizawa ta ce "Nan ma ya isa"
"Amira matar Aminu ce fa, kawo mata ruwa dan Allah" kallon banza ta yi wa jauhar, ta gyara zamanta ta cigaba da danna waya.
Rahila ta ce "Ke fa 'yar wulaƙanci ce amira".
Jauhar ta ce "Ai a ƙoshe ma nake"
"Allah sarki, ya mijin naki, tun da aka yi auren ba ki zo mana ba" tayi shiru tare da sunkuyar da kai tana murmushi.
"Bari yanzu babansu zai shigo, sai ku gaisa".
Amira ta saci kallon jauhar, kyakywar bafulatanar yarinya, daga muryarta kawai zaka san ba ta da hayaniya, ita aka aurawa Al'amin.
Abbu ne yayi sallama suka amsa masa gaba ɗaya, ko da ya shigo sau ɗaya jauhar ta kalle shi ta mayar da kanta ƙasa, babu in da Al'amin ya bar kamanin mahaifinsa.
"Abbu ga 'yar ka fa, sirikarka matar Aminu"
Ya ce "Subhanallah" ya zauna yana faɗin "Yarinyar kirki, tuba nake yi yakamata ace na zo gidan naku, tafiya ta kama ni ne, ina ga yau kwanana huɗu da dawowa, kuma ina maganarku sosai wallahi, dan Allah ki yi haƙuri"
"A'a babu komai, ai mu ne masu laifi, tuntuni yakamata ace mun zo, ban san gidan nan ba ne shiyasa shi kuma bai kawo ni ba"
Rahila ta ce "Hmm, dama ya za ayi ya kawo ki, ai ko za a shekara sai idan rashin mutuncin sa ne ya kawo shi" yanayin maganganun da rahila tayi, ya tabattar mata da ba ita ce mahaifiyar Al'amin ba.
Abbu ya ce "Ina fatan dai ba wata matsala, ba yayi miki wani abu na rashin kyautatawa?"
Tayi ajiyar zuciya ta ce "Ba ya yi mini sai dai.." sai kuma ta yi shiru.
Rahila ta yi farat ta ce "Sai dai me, ki faɗa ba wani abu, ai mu duk iyayenku ne".
"Ƴan sanda ne suka zo mana cikin dare, suka kama shi suka tafi da shi, naje na kuma zuwa anƙi sakinsa, wai suna zarginsa da ta'amalli da hodar iblis".
Rahila ta ce "Taɓ! Ki ce shi likkafa ce ta cigaba a harkar shaye-shayen har ya kai wannan matakin?"
Jauhar ta ce "A'a ba ya amfani da ita, wani ne ya kawo ya ce a ajiye masa, ban san kowaye ba, su kuma suka zo amma wallahi ba shi da laifi, shi ne na ce bari na zo, dan Allah baba ko da hanyar da za a bi a sako shi, ba ma shi da lafiya wallahi, da na je dukansa suke yi, jikinsa duk shaidar duka" ta ƙarasa maganar tana kuka, duk yadda ta so riƙe hawayen amma abu ya gagara.
Rahila ta ce "Au dama shi ne dalilin zuwan naki? Sai da matsala ta afku ki ka nemi gidan ubansa, in dai wannan ne ya saba, kina zaune 'yan iskan da suke bashi goyon bayan yin rashin mutunci za su saka a sake shi".
Abbu ya ce "Ya isa haka rahila" ya kalli Jauhar ya ce "Ki daina kuka yarinyar kirki, case da ya haɗa da irin wannan case ne babba ba ƙarami ba, Al'amin ba ya jin magana ko kaɗan".
"Wallahi baba ba shi ya kawo su ba, ban taɓa ganinsa da ita ba".
"Idan ma yana ta'amalli da ita, ba gaya miki zai yi ba ai"
Abbu ya ce "Ki kwantar da hankalinki, idan da wata matsala ki koma gidanku, zuwa lokacin da komai zai daidaita, zan je na ga abun yi"
"Abbu ka san cocaine kuwa? Wallahi ka je suka fuskanci belinsa ka ke son yi, za su iya haɗawa da kai, ka dai koma gefe ka taya su da addu'a, duk masifar da ya janyo ta ƙare masa a kansa idan yana da rabo ya fito, idan babu ya ƙarata a can".
Kalaman rahila suka yi wa jauhar zafi da nauyi, ba shiri ta tashi ta ce "To bari na tafi sai anjima".
Rahila ta ce "Ki je gida ki yi ta addu'a, idan babu dama ki koma gida, amma shigar mahaifinsa wannan case ɗin ba mafita bane ba, kina zaune za a sako shi".
Abbu ya ce "Ki yi haƙuri kin ji, zai fito in sha Allah, zan san abun yi"
"Ka daina saka mata rai da zaka yi wani abu fa, haka kurum wani abu ya sameka gani ga 'ya'ya ka barmu"
Bayan tafiyar jauhar, Abbu ya ce "Rahila, anya ban yi wauta ba da na biye miki aka aura wa yarinyar mutane Al'amin ba, kalli yadda take cikin tashin hankali da damuwa fa".
"Wannan yarinyar fa da ka ke gani, ba a bar tausayi ba ce ba, ko ka manta kangarewa iyayenta ta yi suka nemi maraba da ita?"
"Duk da haka rahila, ni fa tantama nake yi a kan maganar nan, gaskiya ina ga zan jagoranci raba auren nan, Al'amin ba zai yi hankali ba"
"Abbu ina ruwanka, dan Allah ka bar maganar yaran nan"
Jauhar kuwa bayan ta fita, ba tare da tunanin komai ba, ta nufi unguwar su, ta je ta samu baba, ko da wani abu da zai iya taimaka mata, ba tare da tuna haɗarin da hakan ka iya haifarwa ba, kodayeke wanda yake cikin ruwa ko takobi ka miƙa masa kamawa zai yi.
Ayshercool
08081012143
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
Arewabooks ayshercool7724
https://chat.whatsapp.com/E3bH5OKBh9jH2aYygj0ArA
Kina bukatar kaya masu kyau da inganci??
Kina bukatar kayan kitchen wnd suke available ba order ba??
Kina bukatar adashin gata wnd zaki dauki kaya kamar kyauta??
Kiyi joining wnn group din namu insha Allah xakiji dadin kasancewa a ciki.
Muna da kaya available masu kyau da rahusa💃🏾💃🏾
Ko kimin mgn ta👇🏽👇🏽
08093932955
Sosai take sauri, tare da fatan Allah ya sa baba yana nan.
Sai dai tayi iya ƙoƙarinta wurin daidaita nutsuwarta, kafin ta ƙarasa gidan.
Yamma ta fara yi, yaran gidan sun dawo, sun yi kaca-kaca da shi, duk sun zubar da kayan makarantar su ko ina, ga uban wanke-wanke da aka rasa mai zaman kawar da shi daga wurin.
'yan ƙananan yaran gidan ne suka fara murnar ga jauhar, ɗakin mama ta shiga suka gaisa, ta kalleta ta ce "Lafiya na ganki yanzu? Wani abun ne?"
Jauhar ta ce "Lafiya ƙalau wurin baba na zo".
"In ce ko dai lafiya, kuma ya san kin zo? Ki tashi ki tafi kar ki saka makakken mijinki ya zo yayi mana tijara da tashin hankali"
Anty ce ta leƙo falon ta ce "Jauhar ashe abun da ya faru kenan?"
Jauhar ta kalleta ta ce "Anty dama kina nan ina wuni?"
"Lafiya ƙalau, ashe kuma kama mijinki aka yi da hodar iblis, abu bai yi daɗi ba".
Dammm! Ƙirjin jauhar ya buga, yaya aka yi anty ta san wannan zancen, mama ta ce "Kamar yaya?"
"Yanzu muka yi waya da rahila, ta ce bata daɗe da barin gidan ba, ta je musu wai an kama shi".
Wani abu ɗaci ya tsaye wa jauhar, kamar ta fashe da kuka, ta ce "Ba ya ta'amalli da hodar iblis, rigima ce kawai ta haɗa su da wasu, shi ne dai na je na sanar musu, kar ya zamana ba su sani ba"
"Dan ubanki ni zaki yi wa ƙarya dan ki kare mijinki, ai rahila ba zata yi miki ƙarya ba"
Walida ta ce "Taɓ, Allah ya kiyashemu taɓewa, hodar iblis abun ba arziki ai na zata a sara suka kawai ya tsaya ashe babban kai ne"
Duk yadda ta so ta riƙe hawayenta ta kasa, ta fashe da kuka, suka din ga aibata Al'amin, gashi ba ta tarar da baba a gida ba, babu alamar za su tausaya mata, ko su rarrasheta, kawai ta tashi ta ɗauki jakarta tana kuka, ta fice.
Hafsa ta ce "Allah sarki jauhara da tuni ana china ko gidan Alhaji mu'azzam ana shan A.C" suka din ga dariya.
Ta kwashi ƙafa ta nufi gida, tare da ƙudirce wa ranta da yardar Allah, babu abin da zai saka ta sake zuwa gidan nan da matsalarta, ƙarshen ƙiyayya da tsana dai ana nuna mata a gidan nan.
Kamar daga sama ta ji an buga mata tsawa "Ke bamu hana ki shigowa unguwar nan ba?"
Sai a lokacin ta tuna abun da ya faru, cikin tsoro ta kalli mai yi mata tsawar, sai dai ta kasa magana, ta bishi da ido.
"Ba magana nake yi ba"
"Nawa ubanka ya bayar aka shimfiɗa unguwar da za a hanata shigowa mahaifarta?" Ta ji wata muryar daban.
Ta kalli matashin yaron, guduma kenan ɗan gidan mai unguwa, da su Walid suka bawa ragamar kula da gidan Al'amin da shige da ficen jauhar, har ta je gidan su Al'amin ta taho nasu gidan yana biye da ita.
Saroro ta yi tana kallonsa, dan ba ta san shi ba.
"Waye kai? Meya kawo ka unguwar nan?"
Guduma ya nuna masa Jauhar, ya ce "Wannan, wallahi kana taɓa ta zamu ɓalla ƙarfe a wurin nan, mu rabu salin alin" ɗayan ya ja da baya ya basu hanya, guduma ya ce wa jauhar "Mu je"
Ita dai ba ta iya yi masa magana ba, ta cigaba da tafiya ita yanzu gaba ɗaya hankalinta da lissafinta yana kan halin da take ciki a yanzu.
Misalin ƙarfe uku da rabi na dare, jirginsu ya sauka malam Aminu Kano international airport, direba ya zo ɗaukarsa.
Duk da a gajiye yake, saboda doguwar tafiyar da ya yi, hankalinsa da lissafin sa yana kan, ya ƙarasa gida garin Allah ya waye, ya je ya ji ba'asin dalilin fasa aurensa da yarinyar da ya ƙallafa rai a kanta, kullum cikin tunanin ta yake, kuma tun da aka ce, an fasa bashi ita, ya ji ya ƙara ƙaunarta, ta shiga ransa fiye da yadda yake tunani.
***
Kwanaki kaɗan ya rage jauhar ta fara jarrabawa, amma ba ta iya karanta komai, ga uniform ɗin ta, ga litattafanta sai dai ba ta da nutsuwar da za ta yi karatu, duk ta ƙare tayi rama ga rashin abinci dama damuwar da take ciki ba ta barinta ta ci abincin.
Walid sai da yayi mata faɗa a kan zuwanta gidansu ba tare da saninsu ba, tare da jaddada mata mugunta da gaba mai tsanani da take tsakaninsa da Al'amin.
Tana kwance a falo, maman halimatu ta shigo gidan, ta tarar da ita a kwance cikin damuwa ta ce "Jauhar, rayuwa za ta yiwu a haka kuwa? Yanzu da mutuwa yayi ba dole ki yi haƙuri ba, kin addabi kanki, kamar ko abinci ma fa ba kya ci" kamar ta soso mata wurin da yake yi mata ƙaiƙayi, ta