Showing 102001 words to 105000 words out of 152254 words
wai wuri ɗaya suke kwana?.
Jauhar ta kwashe da dariya ta ce "To zai kwana a waje ne yana da mata?".
Surayya ta ce "Iyee zama da maɗaukin kanwa, wato har bakinki ma ya buɗe haka?"
Jauhar ta yi dariya ta ce "Kai Anty surayya tambayata fa tayi, bari na ƙarasa na je gida ma na yi girki, kar ya dawo".
A tunaninsu za su ga jauhar cikin mawuyacin hali, amma sam ba su ga alamar hakan ba.
Ta shiga suka gaisa da anty lubabatu,ta din ga murna yadda ta ga jauhar, babu alamar wahala a tare da ita, ta aika 'ya'yan anty lubabatu su je gidan kakannin su, su karɓo mata shirin dutse a wurin ƙanwar anty lubabatu. Da yake duk a unguwar ne.
Anty lubabtu har da harhaɗawa jauhar 'yan kayan gyaran aure na mata, ita dai ba ta ce komai ba, ta karɓa ta ce ta gode.
Da ta fito daga gidan, ta lura da wasu matasa da ba ta san suwaye ba, a layin amma ba ta damu ba ta shige gida.
Walida ta tare ta ta ce "Me Anty lubabatun ta baki?" Suka karɓi ledar hannunta, suka ga kayan mata da turarukan wuta da humra masu kyau da ƙamshi.
Suka din ga yi mata dariya cikin izgilanci surayya ta ce "Wai nan ba ki yadda ba ke matar aure ko jauhar? Dan Allah ya ki ke yi ke kuwa da shi, ga 'yan shaye-shaye da ƙazanta, kuma har kiss ku ke yi?"
Jauhar ta yi wani irin murmushi ta ce "Yaya surayya kenan"
"Gaya mana man"
"To ni me zan ce? Annabi ya hana faɗa, sirrinmu ne ai"
Surayya ta ce "Lallai, yau na ga illar ƙani ya rigaka aure, ni ki ke gaya wa baƙar magana jauhar?
"A'a ki yi haƙuri, ba baƙar magana ba ce"
Ta karɓe kayanta, ta saka a jakarta, ta cigaba da aikinta.
Ta zauna tana yanka salak, sai mita take yi ba ta haɗu da yaya saifu ba, kuma baba ma baya nan"
Tijjani ya fito yana ɗan tattakawa, ta din ga yi masa sannu.
Tun da ya shigo layin yake ganin yaran madaki tsilla-tsilla, alla-alla yake yi ya ƙarasa ya tabattar da abun da madaki ya faɗa gaske ne ko akasin haka, idan gaske ne bai san iya adadin haukan da zai yi masa ba.
Walid ya ce "Ga gidan nan" dai-dai lokacin ɗan gidan anty lubabatu ya zo zai shiga gidan su jauhar, hannunsa riƙe da ledar viva, an zubo mata dutsen shiri da kayan yi kala-kala, babar anty lubabatu ta ce a bata kyauta a matsayin jari, shi ne gudunmawarta na biki.
"Kai shiga nan gidan ka ce.... Sai kuma ya yi shiru dan ya manta sunanta, sai Fatima yake iya tunawa.
Walid ya ce "Ka faɗa masa sunan"
Tsaki yayi ya ce "Na manta sunan, sunan wani iri ne dai haka kamar Angela"
Walid ya ce "Amma kuwa ka yi asara"
Al'amin ya ce "Ka ce 'yar madara ta zo in ji Master"
Walid na son yin magana, ya maze ya ce "Na san ƙarya fa madaki dama yake yi bai kasheta ba".
Yaron ya shiga ya fara ba ta saƙon hajiya kakarsa, na bata kyautar dutse, ta karɓa tana murna da godiya, sannan ya ce "Wani a waje ya ce wai 'yar madara ta zo" take gaban Jauhar ya faɗi.
Walida ta ce "Wace wata 'yar madara, babu ita a gidan nan, in ji wa ya ce maka?"
Yaron ya ce "Wai in ji Master "
Jauhar ta ce "Na shiga uku, master ne, ban gaya masa zan zo nan ba, waye ya gaya masa?".
Ta ce "Bari na ɗaukko jakata"
Anty ta fito ta ce "wannan aikin kuma wa zai ƙarasa shi? Ai sai yayi haƙuri ta gama, kai je ka ka ce masa aiki take yi, ya dawo an jima"
Buɗe baki jauhar ta yi ta ce "A'a anty kar ya gaya masa haka, kaga haidar ka ce masa...
Anty ta katse ta ta ce "Fita ka je ka gaya masa haka, waye shi ba gidan sirikansa ba ne ba".
Gaban Jauhar ya tsananta faɗuwa, ba ta san me hakan ka iya haifarwa ba.
Mama ma fitowa ta yi ta ce "Ba zaki zauna ki cigaba da aikin ba"
Viper kuwa wani marurun takaici ne ya ƙule masa a wuya, jin irin saƙon da aka aiko masa da shi, kamar shi za a aikowa da wannan banzar maganar. kawai ya sai kai zai shiga gidan, walid ya riƙe shi ya ce "Mai zamani gidan sirikanka ne fa, dan Allah kar yi wani abu mara daɗi, ka zubar mata da mutunci"
"Tun da suka zaɓi su aura mini ita, sai na tabattar musu da maganata ce gaba da ta su a yanzu" kawai ya saka kai cikin gidan.
Cak ta tsaya, jikinta yana tsuma, ganinsa ya shigo yana wannan takun nasa, ya ƙureta da ido, tun kafin ya ƙaraso.
Tsit suka yi suna kallon ikon Allah, ya ƙaraso, ta wutsiyar ido ya kalli yaya tijjani da ke zaune a kan farar kujera, ya sauke idonsa a kan mama, su surayya sannan Anty Zakiyya ta ƙarshe.
Yana ganinta ya ƙara tabattar da Rahila ce ta saka aka yi masa aure, bai ga alamar akwai mahaifiyar jauhar a cikin su ba.
Ya kalli Jauhar ya ce "Ni na aiko ki zo ki ka ce mini ba zaki zo ba?"
Ta ce "Dan Allah Master ka yi haƙuri"
"Shut up!" Yayi maganar cikin ƙaraji, tare da ball da bokitin da aka kawo markaɗe, da kwanon salak ɗin duk suka tarwatse a wurin, ta zabura ta ƙanƙame jikinta. Ai ba ita ba, har sauran matan gidan da 'yan matan.
Tijjani kuwa ɗimaucewa yayi, dan kuwa ba zai manta muryar nan ba, duk da yana tantama amma kamar muryar wanda suka yi ma aika-aika.
"Dama mun yi da ke zaki zo nan? Kin zata ƙarya suke yi da suka ce za su saraki idan suka kuma ganinki a unguwar nan?" Ɗago ido ta yi cikin tsoro tana kallonsa.
Ganin yadda duk ta rikice ya sanya ya saki muryarsa ya ce "Zo ki wuce mu tafi"
Ta ce "Bari na ɗakko hijjabina"
Mayar da idonsa yayi kan Anty Zakiyya, ko ƙiftawa ba ya yi, babu shiri ta juya da sauri ta shige ɗaki.
Jauhar ta fito, da jakarta da ledojinta, ya danƙi hannunta, suka yi waje.
Suna fita Surayya ta ce "Bala'i dama wannan ne mai dogon zamanin? Jaraba jauhara na cikin bala'i".
Hafsa ta ce "Ni kuma abun da na gani daban, kut wallahi na ɗauka zan ga wani gardin mummuna, ji mutum hanci har baka, kai amma yayi kalar tsoro da yawa, haka yake yi mata wannan tijara"
Mama ta ce "Dalla ku yi mana shiru, kalli asarar da ya yi mana, abincin ranarmu ya mayar da mu baya" mama tayi maganar a ƙule.
"To mama aikin gama ai ya riga ya gama, ni wallahi na zata dukanta zai yi ma. Anty har an gudu ɗaki, bayan ita ta bayar da saƙon da aka gaya masa"
Daga ɗaki ta ce "Haka kurum in tsaya ya kasheni a banza, kin ga wani huci da yake yi kamar kumurci, gashi sai kallona yake yi, ya ƙara girma fiye da yadda na san shi".
Jauhar kuwa suna fita, walid ya rufa musu baya, Viper ya din ga jan ta, gashi saurinsa ya ninka nata, kamar ta hantsila, Alla-Alla yake yi su ƙarasa titi ya saka ta a abun hawa, sai dai suka yi karo da madaki da yaransa.
Wata irin muguwar dariya madaki yayi, wadda ta ƙara fito da ainihin muninsa, baƙi ne wuluk kuma gabjeje, yana da jajayen idanuwa, wanda yake rambaɗa musu farin kwalli, ga wani ƙaton sara a fuskarsa a kaikaice da ya raba fuskar in to two equal parts.
Sai ta ga Al'amin ɗin ta nutsatstse ne mai kyan gani, a kan madaki, ta san gidansu ta san sunansa a unguwar su, amma ba ta sanshi a fuska ba.
Jikinta ya hau tsuma, Al'amin ya sakata a bayansa, ya tsaya yana fuskantar madaki, Walid ya tsaya a gefensa.
"Tun da aka gaya mini matarka ta shigo unguwar nan, na ce bari in auna adadin son da ka ke yi mata. Ka san bikin ma bana nan aka yi, labari na samu ban haɗu da kai na yi maka Allah ya sanya alkhairi ba. Ƙarfin halinka ya kai, tun da ka iya ratso cikin unguwarmu ka auri 'ya. Shiyasa na so ka zama ɗaya daga yarana tun a wancan lokacin amma ka ƙi.
Ya leƙa ya kalli fuskar jauhar ya ce "Ashe 'yar gidan Alhaji faruku ce, rabona da ita tun tana 'yar mitsitsiya, ashe haka ta girma ta ƙara kyau, ka bani kunya ma, wannan ai ba ta wani gama nuna ba, wannan ai ka yi mata girma, kodayeke ba a nan take ba an danne bodari ta ka, bakinta mai kyau ɗan ƙarami zai yi daɗin sha, anya wannan ba....
Wani wawan mari Al'amin ya ɗauke madaki da shi yana huci, Walid ya riƙe shi ya ce "Viper ka san me ka yi kuwa?"
Al'amin ya hankaɗe shi, ya kalli madaki cikin ido ya ce "Ka daɗe da kashe Al'amin ɗin da ka raina, ka mayar abun nishaɗinka, Kar ka sake ka shiga shingena, duk wala-walar da zaka yi, kar ka ƙetare iyaka".
Yaran madaki suka yinƙuro, Madaki ya ɗaga musu hannu, ya ciro wata muguwar wuƙa a jikinsa, ya ce "Bari in nu na wa duniya kai rago ne, a gaban matar taka, da ka yi dan ka burgeta"
Wani irin ihu jauhar ta ƙwala, ta rirriƙe Al'amin tana kuka ta ce "Dan Allah kar ka caka masa, zaka kashe shi idan ka caka masa, dan Allah ka yi haƙuri kar ka kashe shi".
Viper ya ce "Kafin ɗayanmu ya bar duniya, za a ga waye ragon, ƙazamin kare kawai"
Ya sake danƙar hannun jauhar, ya keta ta tsakanin yaran madaki yayi gaba, walid kuma ya tsaya a kan hanyar yana kallonsu, dan kar wani ya bi bayansu ya illata su.
Madaki ya bi bayansu da kallo, ya din ga kallon wuƙar hannunsa yana murmushi, lallai yayi sake ɗan zaki ya girma, ya fara zama barazana a gare shi.
Babban abun da ya ƙular da Al'amin, bai wuce yadda jauhar take ta rusa masa uban kuka ba a cikin a daidaita sahu, bayan koma menene ita ya janyo, kamar ya cillata kan titi ya huce, yana zaman zamansa an ƙaƙaba masa ita, yanzu dole duk in da zai yi sai yana tunanin kar a cutar da ita.
Bai kulata ba har suka je gida,ga wani irin ciwo da kansa yake yi, ga zazzaɓi tun a hanya ya rufe shi.
Suna zuwa gida, ya wuce ɗakinsa ya bar ta.
Bin bayansa ta yi, cikin marairaicewa ta ce "Dan Allah Master ka yi haƙuri, ban san haka za ta faru ba, nayi niyyar gaya maka dama idan na dawo, dan Allah ka yi haƙuri"
Banza yayi mata, ya rufe idanunsa, saboda yadda sanyi yake ratsa shi, ga wani abu mai ɗaci da ya tsaya masa, ya ƙi wucewa, saboda yadda abubuwan da suka wakana a rayuwar sa, suke dawo masa cikin kansa a yanzu. Idan ya tuna abun da madaki ya faɗa a kanta, sai ya ji kamar ya kurma ihu, ya gama cutarsa, ko shi jai tsaya ya ƙare mata kallo, ya ga bakin nata ba sai shi.
A marairaice ta ce "Master, Yaya Al'amin dan Allah ka yi mini magana, ka yi haƙuri ka yafe mini dan Allah, na san koma menene ni ce sila".
"Get out from sight, ki tashi ki fita kafin ni na sassaraki a wurin nan" a tsorace ta tashi ta fita, tana waiwayen sa.
Tana fita ya riƙe kansa, saboda yadda ya yi masa nauyi.
Anty Zakiyya kuwa, Rahila ta kira a waya, bayan sun gaisa ta ce 'Ƙawata yau na ga tsiya da wasali"
"Bani na sha meyafaru?"
"Yau ɗanki ya zo gidan nan ai"
"Wa kenan"
"Sirikinmu mana, wai ashe yaran madaki ɗan dabar nan na unguwarmu sun ce idan ta sake zuwa unguwar nan, sai sun sassarata, ta zo gidan nan bai sani ba, a sukwane ya taho, yau mun ga bala'i, kin ga tijarar da ya yi ya ja hannunta suka tafi?"
Rahila ta ce "Zai aikata fiye da haka ma, in dai Aminu ne ɗan banzan bawa kenan ake gaya miki"
"Taɓ amma anya ba son yarinyar nan yake yi ba? Kin ga a yadda ya zo kuwa?".
"To ke ina ruwanki, dama dai ba burinki ita wannan ta bar miki gida ba, shi ya sani ba mace ba ce ba? Luf zai yi ai, ni fa tun da aka yi auren ba mu sa shi a idonmu ba, na ce can ya ƙarata"
Suka kwashe da dariya, Zakiyya ta ce "Taɓ amma ƙato ne, sai ka ce ɗan dambe, kuma wallahi ba wani abun gyara da muka yi mata, yau ne ma da ta zo maƙwabciyarmu ta bata, amma haka nan muka kaita"
"Oho musu, in dai buƙata ta biya, ba shikenan ba, su ƙarata"
Suka kwashe da dariya gaba ɗaya.
Jauhar ta kasa zaune ta kasa tsaye, master ya ɗau fushi da ita, gashi ya ƙi fitowa, kuma ya korota daga ɗakinsa.
Da canjin hannunta, ta haɗa ta sayo fulawa, ta kwaɓa alkubus, da wata irin miya ya 'yan dabaru, sai dai har ta yi ta gama bai fito ba.
Sai ta kasa ci, ta sake lallaɓawa ta leƙa ɗakinsa, ta ga yana banɗaki, ta cigaba da tsayuwa ya fito, ta tsaya tana sallama a bakin ƙofa.
"Idan ki ka bari na zo na sameki a wurin nan, sai na ɓata miki rai"
Ta marairaice ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri master, na tuba ba zan sake ba"
Kwanciya ya sake yi, ya juyawa ƙofar baya.
"To in kawo maka abinci?"
Kamar ya ce eh, amma yayi mata shiru.
Abun da ya ɗaure mata kai, bai wuce har dare kwanciya yake yi ba, yaƙi fitowa, cikin tsananin fargaba ta shiga da kwanukan abinci ta ajiye masa.
Ƙamshin miyar da ya cika masa hanci, ya sanya ya buɗe idonsa.
Gwiwoyinta ta saka a ƙasa ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri, ni ko wani hukuncin ka yi mini dan Allah ka daina yin fushi da ni, bana son na ga na yi laifi dan Allah" hawayenta ne yake ɗiga a kan katifarsa, ya gyara kwanciyar sa ya juya mata baya.
Ya tsani kuka, ba ta san ƙara ƙular da shi take yi ba.
Tashi ta yi ta sake zagayawa kamar mayya, tana yi masa magiya.
Ya buɗe jajayen idanunsa yana kallonta, sai dai yaƙi magana.
Yarrrr haka ta ji tsigar jikinta tana tashi, ba ta san kallon ma yake yi mata ba.
"Ka yi magana Please, ka ce ka haƙura" tayi maganar tana jan majina.
Ƙafarsa ya ɗora ɗaya kan ɗaya yana kaɗawa, saboda ciwon da kansa yake yi, amma a zahiri abun da yake yin, kamar yana yi ne da gayya da nuna mata iko da izza irin ta ɗa namiji.
"Kin cika mini kunne" yayi maganar a hankali, duk da buɗɗaɗiyar murya ce da shi irin ta jaruman maza.
"To ka ce ka haƙura mana" tayi maganar cikin shagwaɓar da ba ta san ta yi ba.
"Kai mini ruwa zan yi wanka" cikin sauri ta ce "To"
Tunani yake yi daban-daban a ransa, ya ma rasa wanne zai yi, yana shiga wankan, ta sake gyara shimfiɗar katifarsa, ya yi wanka ya fito yanzu ma jikinsa babu riga, yana ƙoƙarin mayar da kayan da ya cire, da sauri ta ce "Ai kana da wankakkun kaya, na wanke maka ka saka wannan" ta yi maganar tana miƙo masa kayan da ta ciro masa.
"Ɓace zan canza kaya" ta fita da sauri,mintuna goma da ta dawo, tuni ya kusa rabin abincinsa.
Garin ta miƙa hannu ta ɗauki jug ta zuba masa ruwa, hannunta ya taɓa ƙafarsa ta ji zafi sosai, ta kalleshi ta sake kai hannunta ƙafarsa. "Master zazzaɓi ka ke yi?"
Lomarsa ya cigaba da yi, cikin tsoro ta sake kai bayan hannunta ta taɓa hannunsa.
"Na shiga uku ba ka da lafiya ai, duk ni na janyo ko?"
Ya karɓi jug ɗin hannunta, ya cire murfin, ya kafa kai ya sha fiye da rabin ruwan, sai ka ce tsohon raƙumi.
Ya gama ya jingina da jikin bango ya sake lumshe ido.
"Master, akwai allurar nan da ka sayo mini ba ayi mini ba, mu je in raka ka ayi maka to"
Gyatsa ya saki, maimakon ya yi hamdala, sai ita ta ce "Alhamdilillahilazi aɗa'amana haza, Ubangiji Allah ya ciyar da mu kullum, ya bawa wanda bai samu ba"
"Amin" ya faɗa ƙasa-ƙasa zai kwanta, a sukwane ta ce "Dan Allah kar ka kwanta, mu je a duba ka, kar ka sha wahala, sauro ne yayi yawa a unguwar nan shiyasa muke ta zazzaɓi, dan Allah ka zo mu je a duba ka"
"Kai wallahi kina addaba mini, kin dame ni"
Jauhar ta kwantar da murya cikin sigar rarrashi ta ce "To na sani, amma ka yi haƙuri, na daina, dan Allah mu je a dubaka ka ji Mijin 'yar madara, ba ka ji yadda jikinka yayi zafi ba?"
Ya kalli yadda ta dafe kafaɗarsa, tayi saurin sakinsa, ya ce "Sai an yi sallar magariba"
"To mu koma falo, sai na saka maka maganin sauro a ɗakin, idan ka cigaba da kwanciyar jikinka mutuwa zai yi"
Da ƙyar ta lallaɓo shi, suka dawo falo, ta kunna maganin sauro.
Ana idar da sallar magariba, ta ɗaukko allurar, ta ce su tafi, ya ce ya fasa zuwa, shi ba zai iya tafiya ba.
Da ƙyar sai ka ce ɗan goye, ta lallaɓa shi suka fita.
Ta rufe ƙofar gidan, ta riƙe hannunsa ta ce "To mu je, kar ka ji jiri idan ka gaji ka yi mini magana sai mu tsaya ka huta".
Kallonta kawai yake yi, ɗan hannun nata ɗan mitsitsi a cikin nasa.
Suna tafe tana ƙara ba shi haƙuri, a kan laifin da ta yi.
Nasiru mai chemist na ganinsu ya ce "A'a jauhar, kin warware shi ne shi ma ya kwanta" tayi murmushi ta ce "Allura na kawo shi, ayi masa mai sanyi dan Allah"
Da jauhar ta san yadda yake ji a zuciyarsa idan ya ga tana tankawa mai chemist da ba ta yi ba, sai dai bai san dalilin hakan ba, kawai ba ya son ya ga wani yana kulata.
Aka gama yi masa suka fito za su tafi, ta tsaya tambayar mai ɗanyen dankali nawa kwano.
Al'amin ya zaro kuɗin ya bayar, suna tafe tana godiyar dankali.
Da safe ta soya musu dankali da tea, ya gama karyawa, ya kalleta ya ce "Wannan matar da na gani a gidanku wacece?"
Ta ce "Wacce?"
"Mai baƙaƙen kayan nan"
"Anty zakiyya ce, matar Baba ce" ya jinjina kai bai sake cewa