Showing 114001 words to 117000 words out of 152254 words

Chapter 39 - ?arfe A Wuta Book 1 Hausa Novel Complete

15 Dec 2024

352

a kan gaɓa, amma ba zan gaya miki ba, in je zaƙin soyayya ya ja ki ki gaya masa ba idan ya fito, ki haddasa husuma, baban abokin nawa yayi magana, sun ce ayi haƙuri ya ƙarasa wata ɗaya, kotu za ta wanke shi ya fito, ashirin da biyu ga watan gobe za a sake shi"

"Wayyo Allah, yaya saifu kusan watanni uku fa kenan zai yi a prison?"

"Au baki gode ba kenan?"

Jiki a sanyaye ta ce "A'a na gode sosai yayana, Ubangiji Allah ya saka maka da gidan aljanna, to zaka kai ni na ganshi?"

Ya ce "Amin ya rabb, yana prison na ciki gari, kuma ban ce ki je ba, kar ki kuskura ki je, kin ji na gaya miki"

"Amma yaya meyasa?"

Saifu ya ce "Saboda haka na ce miki, kuma ke ma kin ce ya ce kar ki je, kar kuma gaya wa wani gashi zai fito shi ma bai sani ba".

Jauhar ta ce "To shikenan, na gode Allah ya saka maka da mafificin alkhairi"

"Amin ki koma gida, ki cigaba da exams ɗinki, idan da wani abu, ki neme ni a waya, kar ma ki sake zuwa gidan nan da wani batu a kan aurenki, tun da ki na son abun ki ki yi zamanki"

Tayi murmushi ta ce "Ban san menene son ba dai yaya, ban san me ake ji ba, da farko dai na san ina jin tsoronsa sosai, amma yanzu kuma tausayin sa nake ji"

Yayi murmushi ya ce "Ga kuɗin mota, ki sauka lafiya, yau ba zan je gidanki ba"

Ta karɓa cikin murna tayi masa godiya, ta tafi gida.

Ta ji sanyi a ranta jin cewar zai fito, sai dai tana cikin damuwa na rashin sanin halin da yake ciki, ya ji sauƙi ko kuwa, yana samun abinci ko kuwa?"

Da ta samu kuɗi, take yin sayayya, ta ari waya ta kira walid, ya zo ya karɓa ya kai masa.

Sana'a tuƙuru jauhar kamar tayi ƙwace, dama ga azumi yana gabatowa, ana samun ɗinkuna, dan haka tana samun aikin stone da beads, sai dai ba ta iya sakin jiki ta kashe kuɗin, saboda akwai abun da take son yi.

Ita ce mayafai, har da su kantu da aya,  haka take saya ta soya ta ɗaura a leda yara na saya.

Har guga take karɓar kayan maman halimatu, ta ta da ta yara tayi mata, ta biyata.

Sana'oi kamar zata yi ƙwace, duk da ana yi mata mugunta a kan wasu abubuwan, mussman gidan mai ɗinki, da take yi mata aikin stone ta fara yi mata mugunta.

Ta ƙara tsananta addu'a, da roƙon Allah, a kan Allah ya kuɓutar mata da mijinta, ya shirya mata shi.

Rana ba ta ƙarya, sai dai uwar ɗiya ta ji kunya, saura kwanaki biyu Al'amin ya fito, jauhar ta yi ta gyaran gida, ta ƙara gyara masa ɗakinsa.

Ranar da zai fito ɗin, ta yi girki, sai dai kuɗin hannunta ba su da yawa, duk mutane sun riƙe mata kuɗi, dan muɗin hannunta ba za su ishe su kuɗin mota ba ita da shi.

Ta dafa ruwa ta zuba a flask, ta shirya tun ƙarfe tara, ta tafi prison ɗin, gashi damuna ta ja baya, an fara wani irin sanyi mai ratsa jiki.

Ta nemi shiga cikin prsion ɗin, aka ce mata a waje za ta jira, idan yau za a sake shi, za ta ganshi ya fito.

Tana nan zaune, wasu suna ta fitowa, 'yan uwansu suna ta murna, sai dai shiru-shiru ba ta ganshi ba.

Nan hankalinta ya tashi, ta sake nufar wurin masu gadin ta ce "Wai haryanzu ban ganshi ba, kuma yau aka ce mini za a sake shi"

"Waye ya ce miki za a sake shi?" Wani gandiroba ya tambayeta.

"Yayana ne"

"Yayan naki alƙali ne? Ko shi ya kawo shi nan ɗin, wanda zamu saki kenan yau sun gama fitowa"

"Innalillahi na shiga uku" ta faɗa a raunane.


Ayshercool
08081012143

🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724



https://chat.whatsapp.com/E3bH5OKBh9jH2aYygj0ArA




Kina bukatar kaya masu kyau da inganci??

Kina bukatar kayan kitchen wnd suke available ba order ba??

Kina bukatar adashin gata wnd zaki dauki kaya kamar kyauta??

Kiyi joining wnn group din namu insha Allah xakiji dadin kasancewa a ciki.

Muna da kaya available masu kyau da rahusa💃🏾💃🏾
Ko kimin mgn ta👇🏽👇🏽
08093932955





Da kallo suka bi jauhar, ganin yadda take yi musu kuka wiwi, wani gandiroba ya ce "Koma tsallake, idan ki ka gama kukan, sai ki tafi".

Ta juya ta kama hanyar tafiya, tana ji a ranta kamar duk duniya, babu wanda ya kaita rashin sa'a.

Sannu a hankali yake tunkaro gate ɗin fitowar, zuciyarsa cike da mamakin yadda aka sake shi, dan bai san ma zai fita ba, sai yau ɗin.

Tsayawa yayi bayan ya fito daga cikin gate ɗin, ya lumshe idanunsa sakamakon hasken ranar da ya ji ya yi wa idanuwansa yawa, sannu a hankali ya cigaba da buɗe su, har ya ji hasken yayi dai dai da abun da idon nasa yake buƙata.

Kamar an kira sunanta ta waiwayo, ta hangoshi a tsaye, shi ma ita yake kallo da mamaki, ba ƙaramin kashedi ya yi wa su liti ba, a kan kar su kuma ɗaukarta su kaita in da yake.

Da sauri ta nufo shi, ta kasa tsayar da hawayenta ta na wata irin ajiyar zuciya ta ce "Har na ji daɗi, da suka ce mini, ba za su sake ka yau ba"

Yayi shiru yana kallon ta.

Ƙare masa kallo take yi, an yi masa aski an aske masa sajensa da gemunsa, sai ɗan kaɗan da ya fara fitowa, idanunsa sun washe yayi haske, saboda babu kayan shaye-shaye a nan, sai dai ya rame sosai.

Kallonta kawai yake yi, kamar wata baƙuwar halitta, sai dai bai yi mata magana ba.

Tayi ajiyar zuciya ta ce "Mu tafi?" Ya jinjina mata kai yayi gaba.

Ta ɗaga ƙafarta kenan takalminta ya tsinke, ta durƙusa ta cire takalmin ta ce "Takalmina ya tsinke" ya kalli ƙafarta sannan ya dubeta, ƙafarta busu-busu, duk yadda ya santa da gayu, ko ba ta gaya masa ba, ya san tafiyar ƙafa ta yi.

Ta tsayar musu da abun hawa suka hau, sai dai har suka je in da za su sauka, duk surutun da take yi, ko sau ɗaya bai tanka mata ba.

A titi suka sauka, saboda kuɗin motar ba zai isa a shiga da su har ƙofar layin ba, har ta yi gaba, ya janyota ya cire mata takalmansa ba tare da ya ce komai ba.

Ta ce "A'a ka saka kar ka taka wani abun".

Kallon da yayi mata, ya sanya ta yin shiru, ta saka takalman kamar zata tashi sama a kansu suka shiga layinsu, kamar ta taka rawa, master ya fito.

A falo ya zauna, ya kashingiɗa ya lumshe idanunsa, ta shiga banɗakinsa, ta haɗa masa ruwa mai zafi, ta ce "Master ga ruwan wanka na kai maka" bai yi mata musu ba, ya tashi ya tafi, kafin ya fito ta jera abinci a falo, ya yi wankan ya fito falo, ya tarar da abinci, yanayin yadda yake cin abincin ya tabattar mata da yana jin yunwa sosai duk da dama can acici ne.

Yana so yayi mata magana, amma ya rasa me zai ce mata ma, ya gama ci ya tafi ɗakinsa ya kwanta, dan surutunta ya fara takura shi, duk da yayi kewar abubuwa da yawa a tare da ita, sai dai yadda yake jin zuciyarsa a cunkushe babu daɗi, ya sanya shi jin surutunta ya gundure shi.

Allah ya taimaketa, ya wuni a ɗaki, bai fita ko ina ba, tun da ya dawo.


Hafsa kuwa ta samu abun yi, dan tun da Allah ya sa ta mallaki lambar wayar Alhaji mu'azzam, take kiransa a waya, da sunan rarrashin sa a kan rashin jauhar, tare da ƙoƙarin sake ɓata jauhar ɗin a wurinsa.
Mahaifiyarta ta sake miƙewa wurin shige-shige a kan Allah ya tabattar da lamarin aure tsakanin hafsa da Alhaji mu'azzam.
Cikin ikon Allah, idan ta kira shi, yana amsawa ba ya yi mata wulaƙanci ko makamancin haka, hakan ya sa ta cigaba da ƙoƙarin cusa kanta cikin hikima da kissa.
Sannan suka yi ƙoƙarin rufe wa mama duk wani abu da yake faruwa, ba ta san halin da ake ciki ba.

Kasancewar Al'amin ya fito ya dawo gida, ya sanya jauhar yin isashshen baccin da rabonta da shi, tun kan a rufe shi, dan bayan sallar asuba da ta kwanta, ba ta farka ba sai goma saura.

Ta fito tsakar gida da sauri, ta fara aikace-aikace, ta dafa tea ta soya dankalin hausa.

Ta dafawa Al'amin ruwa a heater, ta je ƙofar ɗakin ta tsaya tana sallama.

Ƙasa-ƙasa ya amsa, ban da yana da buɗaɗɗiyar murya ma ba za ta ji ba, ta shiga tana sake yin wata ta ce "Ina kwana master"

"Lafiya ƙalau"

"Ban san ka tashi ba, yau na makara da na fara kawo maka ruwan wankan ai, bari na haɗa maka" ta haɗa masa, yanzu ma bai yi musun yin wankan ba, ya tashi ya shiga banɗakin.

Ɗakin fes yake, amma ta din da karkaɗe karkaɗe, da goge-goge, ta kunna turaren wuta, ta fito masa da kaya ta saka musu turare.

Ya gama ya fito, jikinsa yana ɗigar da ruwan wanka, ya ɗauki dogon wando ya saka, ya zube mata wanda ya cire a kan katifa ya fito.

Kallo ɗaya tayi masa ta kawar da kanta gefe ta ce "Ba ka saka rigar ba, na fito maka da ita ma".

"Ba na buƙata, wandon ya isheni".

Jauhar ta ce "To ai kar ayi sallama, a ganka a haka".

"Ki koma ɗaki idan ba zaki iya kallona a haka ba" yayi maganar yana zama.

Ya kalleta ita ma yau ba hijjabi a jikinta, doguwar rigar material ta saka, mamaki yake yi, yadda ta yi duhu, ga wani uban ƙashin wuya da ya fito mata, tayi rama sosai da sosai, ashe jiya dan ya ganta a cikin hijjabi ne ya sanya bai gane ba, sai ya ji ransa babu daɗi.

Ta haɗa masa abincin ta miƙa masa, ya ɗauka zai kai baki ta ce "Bisimillah" a zuciyarsa ya maimaita sannan ya fara ci.

"Askin nan da aka yi maka, ka yi kyau, sai dai ban so aka aske gemun ba gaba ɗaya"
Idan ba gizo idanunta suka so yi mata ba, da murmushi zai yi ya shanye abun sa.

Ta tanƙwashe ƙafarta ta sake cewa "Sannu master, a prison ɗin ma duka ake yi, na ga bayanka duk shaidar duka. Wallahi ba zan taɓa yafewa wanda suka yi maka sharri ba, ban taɓa shiga tashin hankalin da na shiga ba, na san baka ta'mali da wannan abar, sauran ma zaka daina wataran in sha Allah" tayi maganar hawaye na cika mata ido.

"Kun kusa gama exams ko?"

Jin yayi magana ya sanya ta saurin ce wa "Eh, cikin azumi zamu gama in sha Allah"

"Allah ya taimaka"

"Amin na gode, baka tambayeni kwaɗinka da ƙadangaru ba?"

Ya rausayar da kai ya ce "Ai naki ne ba nawa ba" hakan yayi da kammala cin abincin.

Ta ce "Alhamdilillahilazi aɗa'amana haza, warazaƙatana min gairi haulin minni wala ƙuwwa, Ubangiji Allah ya ciyar da mu na anjima" tayi maganar tana tattare kwanukan.

Kafin ta dawo ya ɗauki pillown kujera ya kwanta.

Ta je gabansa, ta durƙusa ta kai hannunta goshinsa ta ce "Wai haryanzu kana zazzaɓin ne?"

Ya girgiza kai alamar a'a.

"Master duk ka yi wani iri kamar an canza mini kai" duk lokacin da ta danganta shi da ita, sai ya ji wani abu a ransa da bai san Menene ba.

Yana daga kwance ya din ga miƙa, yana ɗan banƙare kafaɗunsa zuwa bayansa.

"Ciwo bayanka yake yi ne?"

Ya gyaɗa mata kai alamar eh.

"Bari na ɗaukko man zafi na shafa maka zaka ji daɗi, naga wani raunin bai gama warkewa ba". Ya jinjina mata kai, sai dai bai buɗe idonsa ba.

Ta je ta ɗauko man, ta dawo ta zauna a bayansa, tana shafa masa a hankali.

Ta ce "Juyo" ya gyara kwanciyar sa a hankali, jikinsa wasu wuraren duk shaidar yankan wuƙa, bayan tabon duka.
Haka kurum zuciyarta ke raya mata, kai hannu kan gashin da yake kwance a ƙirjinsa, da sauri ta rintse idanunta ta kawar da wannan tunanin ta kira sunansa.

"Master"

"Mmm?" Ya amsa idonsa a rufe.

Ta ce "Ka na jina?"

"Mmm"

A ɗan shagwaɓe ta ce "To ka kalle ni, magana zamu yi fa"

Ya buɗe idanunsa a kanta, take ta sunkuyar da kanta, saboda wani irin nauyi da kwarjinin da idanun nasa suka yi mata, a tunaninta ta daina jin tsoron sa, ashe haryanzu da sauran rina a kaba, yayi mata shiru yana kallonta yana jiran tayi maganar, sai dai ta kasa.
Gaba ɗaya sai ta diririce, ta kasa maganar sai cigaba da shafa masa man zafi a wuri ɗaya a kafaɗarsa.

Hannunsa ya saka ya cire nata, ya karɓi man zafin ya ajiye, ya ce "Ya aka yi?"

"Dama sonake na ce dan Allah ka yi haƙuri ka yafe mini, na yi sanadiyar shigarka wahala, duk laifina ne da ban gaya maka an kawo maka saƙo ba, ka yi haƙuri mantawa na yi ka yafe mini dan Allah"

"Idan naƙi fa" yayi maganar very serious.

Cikin damuwa ta ce "Please dan Allah ka yi haƙuri"

"Zan duba, ki je ki yi karatunki saboda exams" ta jinjina kai ta tashi, tsakar gida ta fita ta hau wanke-wanke, ta ɗaukko kayansa da ya cire, da wanda ya dawo da su daga prison, ta jiƙa su dan ta wanke.

Wasila maƙwabciyarta ce tayi sallama, kasancewar ƙofar ba a rufe take ba, jauhar ta ce "Anty wasila sannu da zuwa ga kujera"

"Yauwwa jauhara, ashe mai house ya dawo, jiya na ji halimatu ta ce ta ganku, na zata sharrinta ne ma, na zo ɗazu tun takwas da rabi, na yi ta bugu baki buɗe ba na ce bari na tafi, su jauhar ana can jikin miji an liƙe ba a tashi ba"

Jauhar kawai ta yi murmushi tana fatan Allah ya sa bai jiyo ba, tun da yana falo a kwance.

Ta ce "Jiyan ya fito, ban samu na shigo na gaya muku ba ke da maman halimatu".

"Allah sarki jauhar, kin sha wahala shikenan kuka ya ƙare, ki daina anty wasila ba ki san me nake ji ba, zuciyata kamar ciwo take, Allah dai ya bar wannan ƙauna, zuciyar ya daina ciwo ko?"

Dariya kawai jauhar take yi ta ce "Ta daina"

"To ai da kamata yayi, da ki ka san zai fito, ki yi magana ayi gyare-gyare a gyara masa turaka, ki zo na baki kayan maman nihal Anty maryam, na sanmiki kayanta ki gwada ki ji, ai ba kya yi shiru ki zauna haka ba" (Ga mai buƙatar jarraba kayan maman neehal sai ya tuntuɓeta ta wannan lambar 0706 677 4630).

Wasila ta din ga sakin layi, sai da jauhar ta ce "Anty wasila yana nan fa, yana falo yana jinki"

Tayi ƙasa da muryarta ta ce "Na shiga uku, kuma ki ka bar ni nake ta zuba, amma baki kyauta mini ba".

Ta durƙusa ta kwashi takalmanta cikin sanɗa, ta fice, jauhar ta din ga dariya, ta rufe ƙofarta, sai dai ita ma shiga falon ya gagareta, saboda kunyar abun da wasila ta din ga faɗa, dan ta san halinsa, sai ta sakankance, bacci yake yi, ta ga idonsa biyu.

Ta jima tana raɓe-raɓe kafin ta shiga ɗakin, baccinsa yake yi, sosai take jin tausayinsa, yanayin yadda yake miƙa ma, kawai ya tabbatar mata da zaman gidan kaso bai yi masa daɗi ba.

Tana ta dirzar kayansa, ta ji an yi wani irin fito a waje, sannan aka buga mata gate, ta saka hijjabi ta buɗe ta ga su walid.

Ta ce "Yaya walid, ina wuni"

"Madam dama mutumin nan ya fito baki sanar mana ba? Sai yaran da muka saka gadinki ne suka faɗa mana".

"Dan Allah ku yi haƙuri, na san zai neme ku, bacci yake yi ne".

Liti ya ce "Ko dai ki ka ɓoye shi ki ka hana shi fitowa"

Ta ce "A'a na isa? Ban hana shi fitowa ba, ina dai roƙon Allah ku bar mini shi, na san dole dai zai zo in da ku ke".

Walid ya sake wani irin fito, tana waiwayawa ta ga har ya zira riga ya fito.

Saroro ta yi ta tsaya tana kallon sa, ya ƙaraso, zai raɓata ya wuce.

Jiki a sanyaye ta ce "Fita zaka yi? Ban gama ganinka ba fa"

Kallonta ya yi, ya raɓa zai wuce ta ce "Dan Allah Master kar ka sha komai, ko ka je in da ake aikata laifi, dan Allah" maganar da tayi, har hawaye ya cika mata ido.

Bai kulata ba ya fita, gaba ɗaya sai ta ji garin yayi mata babu daɗi, duk da tana cikin shauƙi, da farincikin dawowarsa.

Tana jin shewar su walid, da suka ganshi, ta ja jikinta, ta koma ɗaki, aikin ma ta kasa cigaba, kawai ta saka kuka, kasancewar shi ne kaɗai abun da take yi, ta rage damuwarta, sai kuma tsananta ambaton Allah.

Tun wannan fitar da yayi, tun tana saka ran dawowarsa, har ta cire rai, dan har magariba ba ta kuma saka shi a idonta ba.

Tayi ta addu'a a ranta, Allah ya sa yana lafiya.

Har bayan goma na dare, ta kasa kwanciya, sai sha ɗaya da wani abu, ta ji yana rufe ƙofa, ta fito falo da sauri, ya shigo yana haska fitilar wayarsa, gaba ɗaya falon ya gauraye da warin wiwin da yake yi, jikinta yayi sanyi ta kasa yi masa magana, yadda yake tafiya ya tabattar mata da a buge yake, ya wuce ta ya tafi ɗakinsa.

Ta nemi wuri ta zauna a wurin, ta haɗa kai da gwiwa, ta din ga kuka ƙasa-ƙasa, ta tashi ta nufi ƙofar ɗakinsa ta leƙa, ɗakin duhu, sai dai tana hango hasken wutar jikin sigarinsa, ta juya ta koma ɗakinta, ta ji tana neman sarewa, kamar Allah ba zai karɓi addu'arta a kan sa ba, da sauri ta din ga istigfari, ta nemi wuri ta kwanta.

Da safe da ta tashi, ba ta ko nufi ƙofar ɗakinsa ba, sai da ya fito ya tarar da ita a falo, tana shirin dutse.

Cikin girmamawa ta ce "Ina kwana"

"Lafiya ƙalau" ya zauna a kan doguwar kujera, ta ce "Afuwan kar ka ga ban kawo komai ba, wallahi ba kuɗi a hannuna ban girka komai ba"

Bai yi magana ba, sai kamar bayan mintuna goma, ya ɗauki wayarsa ya ɗan danna ya saka a kunnensa.

"Kawo mini bredi da lipton, kayan tea dai na dubu biyu, kawo mini gida ka karɓi kuɗin". Ya ajiye wayar.

Jin wayar da ya yi ya sanya ta tashi ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login