Showing 60001 words to 63000 words out of 152254 words

Chapter 21 - ?arfe A Wuta Book 1 Hausa Novel Complete

15 Dec 2024

340

babu a cikin file ɗin nasa ma"

Ya ce "Nabila cases irin wannan ai da yawa, sai fatan Allah ya kyauta"

Ta amsa da "Amin, yanzu saura alƙalin da ya yi masa shari'a, na ga an rubuta justice zakariyya, amma babu surname ɗin sa"

Barrister Habib ya yi murmushi ya ce "Shi kuma me zaki yi masa?"

"Kawai so nake na sani"

"Ai an yi masa transfer ma daga kano, bama ya ƙasar ya je ƙaro karatu"

Nabila ta ce "Kuma duk hakan yana da alaƙa da case ɗin viper?"

"A'a ba na ce ba, na dai san shi ne before, bani da tabbacin yanzu"

Ta ce "Na fahimta, na gode sosai da sosai, bari na je zan ga Sumayya, yanzu zan dawo, na yi mata alƙawarin haɗuwa da ita yau"

Ya ce "Ok, Allah ya tsare"

Ta tashi ta fita, dan kuwa yau ba ta da aiki sosai.

Sosai take son ganin sumayya, domin ta ba ta labarin halin da ake ciki, a kan binciken da take yi a kan viper.

Ta kira sumayya ta ce mata za ta shiga gidan radiyonsu, su haɗu a can.

Tana fitowa daga gate ɗin, ta tarar da wani mai napep a tsaye, ta ce "Malam tafiya zaka yi?"

Ya ce mata "Eh"

"Yauwwa, mu je" ta kama adaidaita sahun ta shiga, tana ƙoƙarin ɗaga kiran da yake shigowa wayarta.

Sai dai ba ta kai ga hakan ba, wasu matasa suka shigo napep ɗin, suka zauna a gefe da gefenta, suka rufe mata baki da ido, mai adaidaita sahun ya ɗauke kan babbar hanya ya yi wani wurin.

Kusan awanni biyar, ramma ta ɗan samu ƙwarin jikinta, har ta samu ta yi wanka, sai dai ta kasa cin komai, ya sake ba ta wasu kayan a cikin nasa, duk da sun yi mata yawa, ta karɓa ta saka, ya ja hannunta zuwa falo.

Solomon ya kawo abinci, da fruit, Abdul ya kalleta ya ce "Me zaki ci a nan?"

Ta girgiza kai alamar a'a.

"Wallahi ko ki ci abinci, ko na sake yi miki tsinannnen duka a wurin nan, bana son shashanci bar ganin ina lallaɓa ki"

Cikin tsoro ta din ga cakalar abincin, tana ci tana kuka.

"Ke, meye sunanki ne ma?"

Jiki a sanyaye ta ce "Ramma"

Ya yatsine fuska ya ce "Meye wani ramma, ba rahama ba?"

"Eh rahama"ta amsa tana sunkuyar da kai.

"Meye yake yi miki ciwo yanzu?"

Ta ja majinar da take shirin zubo mata, ta goge hawayenta ta ce "Duka jikina"

"Dukan da na yi miki ne, gama mu koma ɗaki, sai na yi miki tausa"

Manyan idanunta ta kafa masa, tana kallonsa.

"Ki daina kallona da wannan ƙwala-ƙwalan idanun naki, idan ba haka ba, na fita sai kin ganni".

Ta din ga wasa da doyar, ta kasa ci, ta kuma rasa abun yi.

Shiru-shiru sumayya ta din ga kiran wayar Nabila, ga wayar na shiga, amma ta ƙi ɗagawa har ranta ya fara ɓaci, gefe guda kuma ga mutanen honorable na ta kiranta su ji, yaya suka yi me Nabila ta yi da file ɗin viper da ta je nema.

Nabila ta na ji aka sauko da ita daga cikin adaidaita sahun, bayan shafe lokaci ana tafiya.

Babu bakin magana, an rufe mata baki, an ɗaure mata ido, sai addu'a kawai take yi a zuciyarta.

Kwance mata idanu suka yi, ta yi tozali da Walid a gabanta yana yi mata wani irin mugun kallo, sai da hantar cikinta ta kaɗa.

Wurin da suke kamar jeji, babu gida gaba babu a baya, sai shi da ƴan daban da suka kawota, ashe mai napep ɗin nan ma duk set up ne.

Jikinta ya hau tsuma, sai dai ta kasa magana, amma duk da haka godewa Allah take yi, da ba wurin Viper suka kaita ba.

"Yanzu abun da ki ka yi kin kyauta kenan?" Walid ya yi maganar yana tsareta da idanunsa.

Ta sunkuyar da kai, ya daka mata tsawa ya ce "Tambayar ki nake yi, da ki ka saka a ka kama liti shi laifin me yayi miki, ina har in da Vipern yake kin sani, kuma kin je, meya hana ki tura kai tsaye a kama shi?
Yanzu gashi ina ta fama da shi, ya ce lallai zai miƙa kansa ga hukuma, saboda a saki liti, ba zai sake bari wani ya wahala saboda laifinsa ba"

Cikin dakiya Nabila ta ce "Dama haka ne ya dace da shi ai, mutumin da yayi kisan kai aka sake shi, kuma yake zubar da jinin mutane ai hakan yakamata yayi, ta haka ne zai wanke nauyin laifukan da ya aikata"

Walid ya ce "Haka ki ka ce? Da ya yi kisan kai wa ya kashe?"

Ɗaya daga cikin su ya ce "Me gida, ka bari mu cire mata ta yatsu ko za ta dawo hayyacinta, ji fa maganganun da take faɗa a kan master".

Ya ɗaga musu hannu, ya dube ta ya ce "Shikenan, kin yi gaskiya yayi kisan kai, zan bar Al'amin ya miƙa kansa ga hukuma, amma ki sani duk hukuncin da aka yi masa, ke zaki ɗauki nauyin alhakinsa, idan ma amfani ake da ke dan cimma wata manufa a kansa, wanda suke amfanin da ke sun bar ki a duhu, amma kafin nan yakamata ki san waye Al'amin, meyafaru da shi, daga nan kuma duk abun da ki ka yanke ya rage naki!!!.

GUNDARIN LABARIN.

Tsaki yake tayi a jejjere, yana kaiwa yana komowa a matsakaicin falon, yana sauke numfashi.

Matar da ke zaune a kan kujera ta kalleshi ta ce "Wai yanzu dan Allah wannan sintirin ne zai baka mafita?"

Kamar mai jiran ƙiris ya ce "To yaya zan yi? Magana fa ake ta makomar siyasata, idan muka faɗi zaɓen nan akwai matsala, kuma malamin nan ya tabattar mini da na cika kowane sharaɗi, sai zubar da jini ranar zaɓe, kuma alamu sun nuna gwamnati da gaske take, za a tsaurara tsaro sosai da sosai a wurin zaɓen nan, kuma idan ba a cika wannan sharaɗin ba, komai fa ya rushe"

Matar ta numfasa ta ce "Duk ina yaranka marasa jin nan ne, da suke yi maka aiki?"

"Bilki duk suna hannu, kuma babu wani cikakken jan wuya da zai iya tarar aradu da kan nan, idan aka kama mutum da tayar da tarzoma a wurin, shekara sha biyar ne a gidan yari".

"To sai me, kai zaka yi, ka biya su su yi aiki kawai".

"To ai ki gane, duk sun tsorata da hukuncin ne"

Bilki tayi murmushi ta ce "Ka fito da mai dogon zamani mana, kai ka san zai iya, Al'amin ba"

Ya kalleta sannan ya nemi wuri ya zauna ya ce "Kuma fa kin kawo shawara, sai dai yaron ne hukuma ne sai da rarrash, ban taɓa ganin ɗan iska mai mulkin tsiya ba sai shi, tsaf zai ƙi yi, saboda kusan watanni shida yana tsare ban fito da shi ba"

Ta ce "Amma ai yana jin maganar ka, zai yi ba ni da wata tantama"

Ya jinjina kai ya ce "Hakan za ayi, zan saka a fito da shi"

***
Sanye take da dogon hijjabi launin maroon, har ƙafarta hijjabin ya ɗauki guga, ƙafarta sanye da safa baƙa, sai sauri take yi tana ratsa lunguna har ta iso ƙofar gate ɗin makarantar islamiyyar. Sai dai duk wannan saurin da take yi, an riga an fara tarar makara, wanda idan da abun da ta tsana, shi ne a taɓa lafiyar jikinta.

Kusan mintuna goma ya ƙara, bai shiga ajin ba domin yi musu ƙari, yana jira ya ga ta ina za ta ɓullo, yana ofishin malamai, yake hango yadda malam hamza ya zage ƙarfin sa, yana shimfiɗa mata murtukekiyar dorina a jikinta, sai kuka take tana bashi haƙuri.

Sam bai ga fa'idar duka a cikin ladabtar da ɗalibai ba, mussaman mata, macen ma mai rauni kamar wannan baiwar Allah.

Litattafan sa ya kwasa, ya tafi ajin nasu, malam Jamil kenan, ba ya duka ba ya zagi da cin mutuncin ɗalibi, amma ɗalibai na ganin girmansa da mutuntashi.

Ana tsaka da tilawa ta shigo ajin, ta nemi wuri ta rakuɓe a gefe, ɗaya bayan ɗaya ɗaliban suke tasowa, suna zuwa gabansa da littafi, suna bayar da haddar Alqur'ani mai girma, idan ya kammala ji, ya rubuta maka making haddarka, sauran ɗalibai kuma na cigaba da tilawa, sai dai fiye da rabin hankalinsa yana kanta.

A haka har aka zo kanta, ta tashi jiki babu ƙwari, ta je gabansa ta zauna, ta miƙa masa littafinta, ya karɓa yana dubawa, ba bu in da take da maki ƙasa da casa'in da biyar.

Tayi bisimillah, ta fara karanto wurin haddarta, sai dai ba aje ko ina ba, muryarta ta fara rawa, kuka ya ƙwace mata, bai ce mata uffan ba, ya cigaba da kallon ɗaliban, tamkar haddarta yake ji.

Sai da tayi sosai, sannan ta cigaba da karatun, tana yi tana share hawaye.

"Ba kya son duka meyasa ki ka makara?" Maimakon ta bashi amsa, sai ta sake fashewa da kuka.

"Kin ci abinci ne?"

Ta ɗaga masa kai alamar eh.

"Wani abun suka yi miki a gidan" ta girgiza kai alamar a'a.

"To ni wannan haddar taki, ban ji ta sosai ba, dan haka sai kin sake wata, je ki zauna, kuma ki daina wannan kukan" ta jinjina masa kai, ta share hawayenta.

Sai dai zamanta ke da wuya, sai ga malam hamza ya shigo da dogon littafi, yana muzurai.

Yayi wa malam Jamil magana sannan ya ce "Duk wanda ya ji sunansa, ya tashi ya je gida, kar ya sake zuwa sai ya biya kuɗin term, tun da ba da yawun bakinmu zamu biya malamai ba, tun da iyayenku ba sanin darajar malaman addini suka yi ba, da dai na boko ne.
Sunan farko sunanta ya fara kira, ya ce "Ke waliyiyya, duk term sai an kore ki, sai an yi ta artabu kan ki biya kuɗin term, duk wannan uban shirgegen gidan naku, dubu uku a wata uku sai an yi ta fama, tafi gida idan kin karɓo kuɗin kya dawo".

Ba wannan ne karon farko da aka koreta saboda kuɗin makaranta ba, sai dai a duk lokacin da aka koretan, ta kan ji ta muzanta ainun.

Haka nan ta ɗauki jakarta ta tafi gida, tana zuwa gidan ta tarar da wata babbar mace ta shirya za ta fita unguwa, ita da wata budurwa.

"Me kuma ki ka dawo yi, an tashi ne?"

"A'a mama, wai kuɗin makaranta aka turo ni na karɓa"

Matar ta kwaɓe baki ta ce "Uban naki bayanan ai, tun da kin dawo dama unguwa zan je, maza ki ɗora girkin dare, bana son yin daren girkin nan" ta amsa da to.

Budurwar ta ce "Yauwwa Jauhar, akwai kayana a kan gado, dama jibi zan koma school, tun safe nake jiran mai wanki, ya zo ashe ya tafi gida, kya wanke mini, har bedsheets ɗi na, bargona kuma na jiƙa shi, yana baya, idan ya so kan mu dawo idan sun bushe, ko gugar kya rage mini ki goge su".

Ta sake amsawa da "To, sai kun dawo"

Ta ƙarasa ɗakin da take kwana, ta hau cire uniform, ranta babu daɗi, duk ƴan gidan suna makarantun islamiyyar su, ita kuwa an korota daga ta su, kullum sai an kai ruwa rana kan a biya mata kuɗin makaranta, alhalin sauran har na term uku ana biya musu.

Ta canza kayanta zuwa na gida, ta shiga kitchen ta kunna gas, ta tarar ya ƙare, ba ta jira komai ba ta ɗebi itace, ta fita garejin gidan, ta tayar da wuta ta ɗora girki.

Ba ta fi shekara goma sha shida ba, amma yadda take sarrafa jikinta tana aiki, kamar wata babba.

Tana girki tana wanki, a haka ƴan islamiyya suka dawo, kowa ya watsar da jakarsa, da uniform ɗin sa, masu ball suka tafi, masu wasa suka fita, duk suka sake ɓata gidan, ta bi ta sake tattarewa, ta haɗo kan kayan da suka watsar su ma ta zuba ruwa za ta wanke.

***
Fuskarsa murtuk, kamar bai taɓa dariya ba, haka ya tunkari ƙofar gidan, yana wata irin tafiya, mai kama da ta ƙasaita, maimakon ya saka hannu ya buɗe ƙofar gidan, wani irin duka ya yi mata da ƙafarsa, ya shiga ba tare da ko sallama ba.

"Wane mara hankalin ne yake dukar mana ƙofa haka, sai ya karya..... Shiru ta yi ta haɗiye sauran maganar, ganin wanda yake tsaye ƙerere a gabanta.

"Yaushe ka fito? Ko in ce waye ya fito da kai?" Ko kallonta bai yi ba, ya cigaba da takun ƙasaita, ya je ya tura ƙofar wani ɗaki, ya shiga sai dai babu kowa a ciki, dan haka ya fito ya nufi kitchen.

"Al'amin kar ka shigar mini kitchen, ban dafa komai da kai ba, na ga lokacin fitowarka daga prison ma bai yi ba, wannan jaraba da masifa Allah ya yi mini maganinka" ba ta gama maganar ba, ya fito daga kitchen ɗin, da kulolin abinci.

Shan gabansa tayi ta ce "Kar ka taɓa mini abinci, abincin ƴaƴana ne da na mijina, bana son tashin hankali Aminu, ka je ka ajiye mini"

Take ya juya idanunsa yayi mata wani irin kallo, a take ta ja da baya ta koma gefe, tana bin fulasan hannunsa da kallo.

Wani irin fito ya yi, wani daga waje ya amsa masa da fiton, ya fita da fulasan abincin ba tare da ya amsa ko ɗaya daga maganganun da matar ke ta yi masa ba.

Jauhar kuwa, kafin magariba ta kammala girkin nan, ta kawwame a flask, sai gyara gidan take yaran suna ɓatawa, da masu hankalik cikinsu da marasa hankalin duk babu mai taimakawa a gyara. Ta ɗauki abincin maigidan ta kai masa ɗakinsa.

Tana idar da sallar magariba, ta shirya ta ɗauki jakarta, dan tafiya makarantar dare.

Tana fita maigidan yana dawowa, yayi parking ya sauke glashin motar ya ce "Waliyiyya an fito?"

Murmushi ta yi, sai da fararen haƙoranta suka bayyana ta ce  "Baba kai ma waliyiyyar zaka ce mini?"

"Eh mana, ba haka malamanku suke ce miki ba, za a tafi makarantar ne?"

Ji tayi kamar tayi masa maganar kuɗin term ɗin ta na islamiyya, amma ta kasa, mussaman da tuna gargaɗin mama da tayi mata.

Ta ce "Eh baba, sannu da zuwa, na kai maka abincinka ɗaki ma, kana zuwa sai dai ka ci"

Yayi murmushi ya ce "To Allah ya yi albarka, a kula sosai ayi karatu da kyau"

Ta ce "In sha Allah" ta wuce makaranta shi kuma ya gyara parking.

Gudun kar ta makara a makarantar dare, ya sanya ta fita ba ta ci abinci ba, duk da yunwar da take ji, ta ce idan ta dawo sai ta ci.

Sai dai bayan dawowartata, ta tarar da an cinye komai.

Cikin girmamawa ta ce "Mama an cinye abinci ne?"

Mama ta kalleta ta ce "Au ba ki ci ba dama?".

"Eh, na rana ma ban samu ba, na rufe nawa saboda kar na makara na tafi makarantar dare".

"Eh to ai yayi kyau, al huda huda ina da littafi, to an cinye ki zuba ki ci kan ki tafi ba zaki iya ba, duk salon ace zaluntarki ake yi ba a baki abinci, kin wa kanki ai, ni ki hanzarta ki yi wa yara gugar uniform, tun da ga wuta, kar a ɗauke"

Ran jauhar ya sosu rashin samun abincin nan, dan har ga Allah tana jin yunwa sosai da sosai, sai dai babu yadda ta iya, dole ta shiga ta kwaso tulin guga ta hau yi.

Tana gugar nan zabga-zabgan ƴan matan gidan suna kawo mata karon nasu, har wurin sha biyu na dare tana abu ɗaya, ga cikinta sai ƙara yake yi tana hamma, ga bacci da gajiya, ga kuma yunwa.

Bayan ta kammala guga, ta bi manyan ɗakunansu ta ba su, ta kai na sauran yaran ɗakin iyayensu, sannan ta koma ɗakinta, ta yi alwala tayi sallar isha'i, ta yi shafa'i da wuturi, ta nemi ta kwanta. Ba ta yi mintuna goma sha biyu da kwanciyar ba, ta jiyo ana ƙwala mata kira a tsakar gida.

Haka ta sake yinƙurawa, ta fito matashin saurayi ne, tsaye hannunsa riƙe da leda ya kalleta ya ce "Kin fara bacci ne?"

Ta ce "A'a yaya, idona biyu"

"To ga indomie nan, faka-faka dafa mini dahuwar nan taki, mai muslmin daɗi, akwai gasashshiyar hanta a ciki da ƙwai, na san akwai attaruhu da alabasa a gidan, tayi yaji fa sosai"

Ta karɓa ta ce "amma yaya da daddare nan ka ci yaji ka kwanta, ulcer fa"

Zare mata ido yayi ya ce "Sai kin saka an yi mini faɗa ko, maza dafota ƙwan nan fa ya soyu shi ma"

Tayi murmushi ta koma ta sake gangamin haɗa wutar da ƙanan itace, dan kuwa, ta riga ta kashe murhun, kuma ba ayi refilling ba.

Kasancewar a gareji take girkin, sauro yayi mata rubdugu da cizo, sai da wutar ta kama sosai, hayaƙi ya kore su.

Sai da ta gama tana juye masa, sai gashi ya shigo, hannunsa da leda ɗauke da lemon roba mai sanyin gaske.

"Yauwwa waliyiyya, Allah dai ya tuttula miki albarka, ya baki miji nagari" ta sunkuyar da kai cikin jin kunya.

Ya samu wuri ya zauna, ya ce "Samo plate ki ɗiba, sai ki jiye mini sauran"

"A'a ni fa a ƙoshe nake, ka bari na lashe tukunya, ka san ina son romon indomie"

Yayi murmushi ya ce "Ke ce romon ai"

Ya zuba mata a tukunyar, ya datsar mata ƙwan, jikinta har tsuma yake yi, tana hannu baka hannu ƙwarya, ba tare da ta san tana hakan ba.

Yadda ya lura tana ta suɗar kwanon, ya san babu lallai ta ci abinci yau, dan haka ya sake tura mata ta gabansa ya ce "Ungo na ƙoshi"

Ta ɗan yi saroro ta ce "Yaya Saifu ba daɗi ne?"

"Ina fa, ke kin san duk duniya, babu wanda ya kai ki iya dahuwar indomie, ƙoshi nayi kawai, ki hanzarta ki gama ki je ki kwanta, dare yayi"

Ta karɓa ta yi masa godiya.

Sai dai tana gama ci, wani matashin da zai girmewa saifu ya fito, ya zube mata kayansa na ƙwallon ƙafa, har da takalmi, sai tsamin rana da warin hammata suke yi, ya ce ta wanke masa kafin ta kwanta. Kamar saifu yayi magana, amma yayi shiru ya fasa.

Ƙarshe ba ta kwanta ba, sai ɗaya da rabi na dare, shi ma ko da ta tuna, kwanaki kaɗan suka rage mata jinin al'ada ya zo mata, gashi ba ta da audugar tare jini, ga kuma kuɗin makarantar islamiyyarta, babu shiri ta fasa kwanciyar, ta ɗaukko kwanon da take zuba dutsen da take shiri da shi, ana biyanta, tana tara ƴan kuɗi, duk da shirin ba wata riba ce da shi ba, amma yana taimaka mata sosai.

Tamkar mai shirin hawan aljanu, haka ta haƙiƙance, tana zuba masa bala'i, "Wallahi ba zai yiwu ba, dole ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login