Showing 117001 words to 120000 words out of 152254 words
ɗora tea, kasancewar da wuta ta ɗora a heater.
Tana cikin kwashe tea ɗin, ya fito ya je ya karɓo kayan shayin, ya ajiye mata a ƙofar kitchen.
Ta ce "To, Allah ya saka da alkhairi"
Ta ɗauka ta dudduba, da yabi ta ita, iya buredi da sugan ya isa, sauran kuɗin ko taliya sa saya, ta ɗauka ta soya ƙwan, ta kawo kayan karin.
Shikaɗai ta haɗawa ta koma gefe, ta cigaba da shirinta.
"Wannan shirirtar ta fi ki karya kumallo?"
Ta girgiza kai ta ce "Ba na jin yunwa ne, zan karya amma".
Gaba ɗaya ba ta walwala, duk surutun nan ma da take yi masa, yau bakinta shiru, ta kunna mp ɗin ta, ta ajiye a gefe, tana saurar radio, ana ta zancen za a tafi yajin aiki, saboda tsadar rayuwa da rashin ingantacciyar rayuwa ga ma'aikata.
"Amm Angela ki ke ko?"
Tayi murmushi ta ce "Ko 'yar madara ba" tayi maganar cikin ƙoƙarin ɓoye damuwar da take ciki.
"Koma dai wanne ne, magana ce da ni"
Ta ce "To" ta ajiye kayan abun da take yi, ta fuskance shi, amma ba ta yadda sun haɗa ido ba.
"Kalleni, idan ina magana na fi son ki kalleni, ki daina sunkuyar da kai"
Kallo ɗaya tayi masa ta sake sunkuyar da kai ta ce "Ba zan iya ba ne, wani abu nake gani a cikin idon naka da yake bani tsoro"
"Kin kusa daina gani, wata shawara na yanke a kan zamanmu, ni wannan yawan koke-koken da ki ke yi, da wahalar da ki ke sha ba na so, jin sa nake yi kamar wani nauyi a kaina, kuma ni gaskiya ba zan iya daina wasu abubuwan ba, ina saka ki a damuwa da matsala sosai, ga rayuwar ki a cikin hatsari, duk saboda ni.
Kina takura rayuwata sosai da sosai, nima kuma ma san ina takura ki dan haka na yanke shawarar kawai na sauwwaƙe miki, ki koma gida Allah ya baki wani mijin ki yi aure, ni ba na buƙatar mace a cikin rayuwata".
Tun da ya fara maganar, ta ji kamar an jona mata shocking, zuciyarta ta din ga bugawa da wani irin sauri, ta rasa me ma za ta ce.
Sai da ya kammala tsaf, sannan cikin ƙarfin hali ta kalleshi ta kawar da mai ta ce "Wannan ne tukuicina kenan? Baka buƙatar mace a rayuwarka, nima ƙaddara ce ta kawo ni in da ka ke, na zata idan na jure na cigaba da yi wa baba biyayya, na yi biyayyar aure, komai zai wuce, zan ci riba, amma yanzu na fuskanci ni ce mara sa'ar, ko ina ba a buƙata ta, yanzu tozarta maraicina shi ne ka ga ya dace da ni, har ya sanya ka ce ba zaka yafe mini ba jiya? shikenan ka bani a rubuce na kai wa baban, na gode master, amma duniya da ba a yafiya da mu zo i yanzu ba, na san nayi maka kuskure amma na baka haƙuri, amma ka sani idan ka sake ni, ka tozarta maraici" ji tayi numfashinta ya yi wa ƙirjinta nauyi, kawai ta tashi jikinta na rawa.
Tsananin fargaba da tashin hankalin maganar da ya gaya mata, ya sanya period ya zo mata ba shiri, har jikinta ya ɓaci, dama sauran kwana ɗaya ya zo.
Har tayi maganar ta gama, ba ta kalleshi ba ko sau ɗaya.
A ransa ya din ga maimaita ;idan ka sake ni, ka tozarta maraicina. Ita a tunaninta abun da ya faru ne ya sanya ya ce zai rabu da ita? Marainiya ce kenan? Ya tambayi kansa a lokaci ɗaya ya bawa kansa amsa da no wonder.
Sai kuma jikinsa yayi sanyi, shi wannan wahalar da take sha, ya ɗauka za ta yi murna da abun da ya ce, kawai ya basar ya kwanta.
Sosai ta din ga kuka, a ɗakinta, tana tunanin wane irin baƙin jini ne da ita haka? Duk yadda take haƙuri tana lallaɓa auren nan, amma ya yi mata wannan sakayyar, take ta fara tunanin wane irin zama zata koma ta yi a wannan gidan na su, da suke nuna mata ƙiyayyarsu a fili?
Da ƙyar ta shiga banɗaki ta gyara jikinta, ta fito zauna a ƙasa ta cigaba da kuka.
Bayan ya gama abun da yake yi, ya fice ya bar gidan.
Kanta ne ya fara ciwo, ga numfashinta da yake ta barazanar ɗaukewa, ga wani irin azababben ciwon mara da yazo mata da zazzaɓi duk a sanadin tashin hankalin maganganun Al'amin.
Yaya saifu kuwa tun da ya dinga bibiya, aka tabattar masa da an saki Al'amin, hankalinsa ya kwanta, ya so ya je gidan nata ya tabattar amma har ga Allah ba ya ƙaunar shi, duk da sau ɗaya ya taɓa ganinsa, ranar ɗaurin auren a masallaci, kawai a jikinsa yake jin azabatar da jauhar yake yi, dan ba zata faɗa bane kawai.
Al'amin kuwa, su walid suna ta hirar irin tashin hankalin da matarsa ta shiga, da aka kai shi prison, da irin aiken da ta din ga yi masa da kayan amfani yana prison.
Gaba daya sai ya tafi lissafin yanzu idan ya saketa, to abinci fa? Amma shi duk da haka gani yake hakan ne mafita, wannan tashin hankalin da take shiga idan ya shiga cakwakiya, sai ya ga kamar yana shiga hakkinta da yawa, kuma a idonta yake ganin damuwa idan ta ganshi a halin maye.
Da daddare da ya dawo, yadda ya fita ya bar kayan karin kumallo, haka ya dawo ya tarar da su, ba ta taɓa ba, sai yayi tunanin ko wani abun ta ci, dan haka ya ƙarasa hallake buredin da ƙwan, ya shige ɗakinsa ya cigaba da busa hayaƙi cikin nishaɗi.
Washegari ya din ga zaman jira, ya ga ta fito ta yi abun karyawa, amma shiru, gashi bayan sallar asuba ya yi shaye-shaye dan haka yunwa yake ji sosai.
Ganin har sha ɗaya ba ta fito ba, ya sanya ya fice, sai dai kuma yajin aiki ake yi, da ƙafarsa ya tafi unguwar su, wurin su Walid.
Yau ko tsintsiya jauhar bata ɗauka ba, tana ta fama da kanta, da la'asar ya dawo, ya sake tarar da gidan yadda ya bar shi.
Gaba ɗaya sai gidan yayi masa wani iri, ya kwashe kwanukan da ya karya da su jiya, ya fara tunanin ko fushi tayi, shi ne ya sanya taƙi yin shara a gidan.
Yana tsaye yana kallon falon, ya ɗaga kai ya ga ta fito daga ɗakinta, kamar fuskarta ta kumbura.
Ya tsaya yana kallonta, ya ga tana ɗaga ƙafa da kyar a hankali.
Kawai ta yanke jiki ta faɗi a wurin, a sukwane ya yo kanta, ya ɗagata.
ta motsa da ƙyar, hannu ya saka ya juyota jikinsa sosai, wani irin hucin zafi jikinta yake fitarwa, ta ɗaga idonta da ƙyar ta kalle shi, idanunta sun yi ja sosai da sosai ta mayar da su ta lumshe.
Hankali tashe ya ce "Menene?"
"Kaina ne zai fashe" tayi maganar hawaye na bin gefen fuskarta, kafin yayi magana, jikinta ya hau karkarwa, haƙoranta na karo da juna, idonta na neman juyewa saboda zafin zazzaɓi da matsanancin ciwon kai.
Ɗagota yayi sosai ya ce "Ki na ji na?" Ta ɗaga masa kai da ƙyar.
"Zan je in samo abun hawa, mu je asibiti"
"Yajin aiki ake yi, ka manta?" tayi maganar a galabaice.
Sai yanzu ya tuna, dan da ƙafa ya je yawonsa ya dawo, ƙungiyar ƙwadago na jagorantar yajin aiki da kuma zanga-zanga domin janyo hankalin gwamnati a kan wasu haƙƙoƙin 'yan ƙasa.
"Na sani, yanzu zan dawo"
Ba tare da ya san in da zai nufa ba, ya kwantar da ita kawai ya fita, a ransa yake jin idan ya bar yarinyar nan da ciwo, bai yi wa kansa adalci ba.
A titin unguwar, ya ga wani ɗan adaidaita sahu, ya tsayar da shi ya ce "Malam mara lafiya zaka ɗaukar mini"
Mai baburin ya ce "A'a yi haƙuri ba aiki na fito ba, ba ka san ana yajin aiki ba ne maigida?"
"Ana yajin aikin amma ka fito da babur?"
"Eh na yi wani uzuri ne, gida zan koma".
A ɗan hasale ya ce "Mara lafiya zaka ɗaukar mini"
Shi ma a hasale mai baburin ya ce "Na ce ba zani ba, ana dole ne? Ka nemi wani mana"
A fusace ya daki tayar gaban adaidaita sahun, mai napep ya waro ido ya ce "Malam meye haka?"
Kawai ya shiga bayan adaidaita sahun, ya zare wuƙa ya ce "Bi cikin layin nan, ko na zaro hanjinka yanzun nan da russia" tsit mai ɗan sahun yayi, ya bi layin tare da yin sarandar ƙwace masa baburin ma zai yi.
A ƙofar gidan ya saka shi yayi parking, ya sauka ya ƙwace mukullin babur ɗin, ya shiga cikin gidan da shi.
Ya ɗauko hijjabinta ya saka mata.
"Master"
Ya kalleta ba tare da ya amsa ba, ta ce "Yi haƙuri, na saka wahala"
"Ki yi mini shiru"
Ta ce "To" ya ɗaukkota kamar matacciya, ya shiga da ita napep ɗin.
Ya ciro mukullin ya miƙa wa mai baburin ya karɓa yana cunkusa fuska ya ce "Megida amma ka san yajin aiki ake yi, ina zan kai ku? asibitin gwamnati babu aiki".
Al'amin ya ce "Ko ma wane asibitin ne mu je"
Kamar wata 'yar kyanwa, haka ta kwanta luf a jikinsa, da suka hau kwalta, sai sanyin da take ji ya ƙaru, dan haka ta ƙara shigewa jikinsa, jikinta na ta rawa.
Wani Asibitin kuɗi ya kai su a gadon ƙaya, Al'amin ya cilla masa dubu ɗaya, ya rungumi jauhar ya shiga da ita.
Ba a taɓa ta ba, sai da ya biya kuɗin file da komai, sannan aka fara yi mata abun da yakamata.
suka shiga wurin likita, aka tambayi sunanta, ya manta surname ɗin ta da ya gani a invitation ɗin su, dan haka ya ce a saka mata Zahra Al'amin, shekaru ya ce bai sani ba, sai kintata akayi, aka tura su yin gwaje-gwaje.
Bayan sun dawo,ikitan da ya duba ta, yayi ta mita malaria tayi mata mummunan kamu, ga ulcer kuma ga jininta ya hau.
Al'amin ya ce "Malam ba lissafi ko masifa zaka yi mini ba, ayi mata abun da yakamata kawai" yanayin yadda yayi maganar, ya sanya likitan gane waye shi.
Sai dai Al'amin yayi mamakin jin an ce jininta ya hau.
Likitan ya ce "Tana da aure ne?".
"Eh"
Likitan ya ce "Ayi gwajin ciki, kar mu yi treatment da ka".
Al'amin ya ce "Babu ciki"
Likitan yayi saroro yana kallonsa.
"Malam ni ne mijinta, babu wani ciki, ka yi sauri a fara yi mata abun da yakamata, tana ta murƙususun ciwo. Ko ba ka yadda ba? Al'ada take yi, ko kuna ganin cikin kwana ɗaya ne ko biyu?"
Likitan ya ce "Ikon Allah"
Jauhar duk da tana fama da kanta, wata irin kunya ta rufeta, ya aka yi ya san tana period ma.
Tana ta yinƙurin amai, sai dai babu komai a cikinta, aka ce ya samo mata wani abun ta ci, kafin a fara treatment.
Ya fita ya sayo uwar gurasa mai nama, da ruwa ya kawo mata.
Ya zo ya tarar, an saka mata ruwa, da allurai.
Ya kalli fuskarta, bacci take yi sosai, tana iya ƙoƙarin ta a kan sauro, kar ya cije ta, ba ita ba har shi, da magariba ta yi za ta hau rufe ko ina tana kunna maganin sauro.
Abun da bai sani ba, tsananin damuwar da ta shiga bayan kama shi, da maganganun da ya gaya mata jiya ne suka haifar mata da ciwon.
Sai dai babbar damuwarsa, hawan jinin da aka ambata.
Sai wajejen magariba, ta ɗan samu afuwa.
Wajen isha'i aka sallame su, suka yi mata wasu allauran, aka ce masa maza ya kaita gida, alluran suna kashe jiki.
Duk kuɗin jikinsa sai da suka ƙare, suna fitowa harabar asibitin, jikinta ya saki ta tafi zata faɗi, ya riƙeta da ƙyar suka fita, sai dai gaba ɗaya titin babu ababen hawa.
Ganin sai tangaɗi take yi, kuma bashi da wata dabara ya sanya, ya ɗaure ledar magungunan ta, ya ɗaga ta ya saɓa a bayansa, ya ɗauki takalmanta ya riƙe a hannunsa, ya zagaya ya bi lunguna.
A din ga yi ana sauke hakki, idan baki saya ba 0009450228
Aisha Adam jaiz bank
Ayshercool
08081012143
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
Arewabooks ayshercool7724
https://chat.whatsapp.com/E3bH5OKBh9jH2aYygj0ArA
Kina bukatar kaya masu kyau da inganci??
Kina bukatar kayan kitchen wnd suke available ba order ba??
Kina bukatar adashin gata wnd zaki dauki kaya kamar kyauta??
Kiyi joining wnn group din namu insha Allah xakiji dadin kasancewa a ciki.
Muna da kaya available masu kyau da rahusa💃🏾💃🏾
Ko kimin mgn ta👇🏽👇🏽
08093932955
A ƙalla ya kai awa ɗaya da mintuna talatin, yana tafiya da ƙafa, bayansa ɗauke da jauhar, wani wurin idan da mutane, ayi ta kallonsa, tun da sauran sahun mutane, har ya zama saura ɗai-ɗai.
A haka ya isa gida, ya buɗe gidan, ya shiga da ita ɗakinta ya kwantar da ita, zazzaɓin jikinta ya sauka, sai dai gaba ɗaya jikin nata ya saki.
Ya kunna fitilar wayarsa yana haskata.
Surutai take yi, wanda tun suna hanya take yi, sai dai ba ya gane me take faɗa sai yanzu.
"Allah ka shirya mini mijina, Allah ka sa ya daina abun da yake yi. Ya Allah, Allah ka sa ya shiryu.
Allah na san ba zaka kunyata ni ba, Allahumma inni as'alukal jannata wa na uzubika mina narr. Rabbana hablana min azwajina, wa zuriyyatuna ƙurattu a'ayunun waja'alna lil muttaƙina imama. Rabbigfir ummi wa abi, warahamhuma, kama rabba ya ni sagira" ta ƙarasa tana shafar fuskarta, da tafukan hannayenta, hakan ya tabattar masa da addu'aoin ta ne na salla, take maimaitawa.
Ya lulluɓeta, ya tashi ya sake fita, sai dai abubuwa daban-daban suna ta cigaba da kai komo a zuciyarsa, ya ji ƙwarai yana son sanin wacece yake zaune da ita a matsayin mata, shi dai ya san ba shi da nagartar da uban kirki zai bashi auren 'ya, idan ba da wata a ƙasa ba.
Cikin gari ya sake ninkawa ya tafi, bai zarce ko ina ba sai gidansu, ya tarar har sun rufe ƙofa.
Bugawa ya fara yi iya ƙarfinsa, Abba ya zo ya buɗe, yana ganin Al'amin ya ruga da gudu ya koma, saboda yana bala'in tsoronsa.
Ba tare da ya kula kowa ba, ya shiga kitchen, ya dudduba babu komai sun cinye abincin.
Rahila ta fito, ta ce "Kai Aminu lafiya ka zo mana a wannan daren? Yaushe aka sako ka?"
"Shahida" ya ƙwala mata kira, kasancewar ya hangota a falo.
Cikin hanzari, ta fito ta ce "Gani yaya"
Yayi mata alama ta shiga kitchen, ta shiga ya bi bayanta, ya ce "Dafa mini shayi cikin flask ɗin nan" yayi maganar yana nuna mata flask ɗin shayinsu, family size.
"Wai Aminu me ka ke yi haka, dan me zaka sakata girki a wannan tsohon daren?"
Bai kulata ba, ya kwaso ƙwai ya zube mata ya ce "Ki soya mini wannan ma".
Rahila ta koma bedroom ta taso Abbu ta ce "Ta so, ga ɗanka can ya zo a wannan tsohon daren, kar ya yi mana ɓarna".
Abbu ya taso ya fito, dan ya fara bacci ma.
Ya fito yana faɗin "Kai Al'amin lafiya, ka zo mana a daren nan? Ina matar taka ina gidan naka?".
Shahida ta ce "Abbu ka koma ka kwanta, ba wani abu, girki kawai ya ce na yi masa".
"Kuma a daren nan, ina matar ta sa?".
Abbu yana ta ɓaɓatu, Amma Al'amin bai kula shi ba, sai ma ɗaukko ledar viva, ya buɗe fridge ya kwashe lemon ɓawo ya zuba a ciki, kankana da sauran abubuwan da ya gani a ciki har da su madarar ruwa.
"Ka yi masa magana, wannan kayan da yake ɗiba ina zai kai su?".
Al'amin ya kalli rahila ya ce "Da kuka aura mini 'yar mutane, ai kun san bani da abun yi, in bari yunwa ta kasheta ko na fara satar kayan mutane ne na kula da ita? Ba ta da lafiya dan haka dole na fito na nemi abun da zan kai mata ta ci".
"Da can kai da me ka ke riƙe kanka, ba sai ka nema ba, kuma saboda lalacewa da abun kunya, daga gidanku ne za a ciyar maka da mata?
Al'amin ya waiwayo a fusace, ya nunata da yatsa ya ce "Ki kiyayi lokacin da haƙurina zai ƙare a kanki"
Shahida ta ce "Yaya gashi na gama, ka ga akwai su maggi ma a nan, tayi maganar tana buɗe drower tana ɗaukkowa. Ta buɗe wata ta ɗebo su taliya da macaroni ta ce "Ka haɗa da su"ya girgiza kai ya ce "Ban da wannan, wannan sun isa"
Ta sake cewa "Yaushe zan zo gidanka, ina son kan na koma school na zo muku ziyara, tun da ba ma nan aka yi bikinka, samu zo mu dubata"
A taƙaice ya ce "Sai kin zo".
Ta ce "Wannan ɗin sun isa, ko kuna buƙatar wani abun?"
Ya ce "A'a, sun isa. zo ki rufe muku gidan" ya ƙarasa maganar yana kwasar kayan, ya nufi hanyar ficewa.
"Al'amin" Abbu ya kira sunansa, ya tsya cak bai waiwayo ba.
"A tunanin auren nan da aka yi maka nutsuwa zaka yi, ka daina wasu abubuwan da ka ke aikatawa, amma abu ya ci tura, ka sanya 'yar mutane a tasku da tashin hankali, meya kai ka ta'amalli da hodar iblis?.
Lokaci yayi da yakamata ka daina wasu abubuwan, ko dan kare mutuncinka da na iyalinka. Ko dan ka ga ka sameta a ɓagas ka ke nema ka wahalar da rayuwarta"
"Kaga Abbu dan Allah ka daina jan maganar nan, ya tafi kawai su je can su ƙarata, dama ai ba ji take ba ita ma, daidai da ita ne"
Wani abu mai nauyi ya haɗiye, ya saka kai ya fice, ba tare da ya sake cewa uffan ba.
Bayan ya tafi, Shaida ta ce "Mama dan Allah ki daina tayar da hankalinki a kan yaya, idan yana wannan abubuwan ki zuba masa ido, tun da ba kullum yake zuwa ya yi ba. Abu ɗaya kawai yake buƙata yayi iko da kayan mahaifinsa a matsayin sa na ɗa, kamar yadda muke yi, kin san fa ke da shi, ba kwa jituwa ki din ga kawar da kai a wasu abubuwan da yake yi, yana ɗaga miki ƙafa fa kar yayi miki wata illar".
Abbu ajiyar zuciya ya yi, maganganun shahida gaskiya ne, amma shi babban takaicin sa, Al'amin ba ɗan da za a haɗu a rufawa kai asiri bane ba, miyagun halayensa ya sanya ba ya son ya zo ko in da yake. Gaba ɗaya auren da aka yi masa bai sanya ya nutsu ba, kodayeke da sauƙi tun da ya san ya fito ya nemi abun