Showing 150001 words to 152254 words out of 152254 words

Chapter 51 - ?arfe A Wuta Book 1 Hausa Novel Complete

15 Dec 2024

343

master magiyar, ya taimaka ya bari ta je gidan hafsa tun da an yi bikin, kuma ta na son ta je gida ta gaida baba, ta bashi gudunmawar biki.

"Ni fa nayi miki alƙawarin zuwa gidan yayrki, amma amarya ce, ya zaki je musu gida sati ɗaya da biki?"

Cikin rashin fahimta ta ce "To ba a zuwa?"

"Eh, idan sun shirya samun zuriya su, ai ba za so ki dame su ba, idan lokaci yayi zan kai ki".

Anty da Rahila suka cigaba da yawon bin bokaye, ƙauye-ƙauye, dan su sake kama Alhaji mu'azzam, kuma ya saurari hafsa.

Komai na buƙata gashi nan a zube, amma miji ya gagareta sai dai ta ganshi daga nesa.

Tayi iya ƙoƙarinta, duk wanda ya zo, ba ta bari ya fuskanci tana cikin damuwa, ta baka abinci ka ci ka sha, idan zaka tafi ta baka na mota mai yawa, tayi ta hura hanci, saboda tana cikin gida na alfarma ga motoci a parking lot.

Jauhar ta gaji da yi wa Al'amin magiya, ta ƙyale shi, dan kansa ya ce ta shirya, shi zai kaita gidan hafsan, su gaisa ya dawo da ita.

Ta din ga murna tana yi masa godiya, amma ta ce "Dan Allah master a sakawa baburin nan salansar sa, idan muka fita fa saboda ƙarar da yake yi, sai kowa ya waiwayo ya kallemu".

Ya ce "Ni fa na fi son abuna a haka"

Ta kwantar da murya ta ce "Na sani, amma a taimaka mini, ko so kake kowa sai ya ɗaga kai ya kalli babyn robar taka?"

"Zan duba"

"Yauwwa master na"

Yayi murmushi ya ce "Naki, waye ya baki?"

Ta ce "Allah ne ya bani, kuma na karɓa hannu bibbiyu ina yi masa godiya"

Ta kira hafsa a waya, hafsa ta ɗaga da ƙyar tana cika tana batsewa, Jauhar ta ce "Anty hafsa ina wuni, ina ta kiranki ba kya ɗagawa"

"Bana kusa ne, shiyasa"

"Adress ɗin gidan zaki bani, gobe in Allah ya kaimu zan zo in sha Allah"

Kamar hafsa ta ce mata ba ta so, b tare da la'akari da su ba su taɓa taka gidan jauhar ba, amma sai ta ga ya dace jauhar ta zo ta ga daular da take ciki, dan haka ta bata adress ɗin.

Bayan ta gama wayar, ta ce "Master ta bani adress ɗin, babu wuya ma gane gidan nata. Zo mu yi kallo a wayata" ta yi maganar tana zama a kusa da shi.

"Ni kallon nan gajiyar da ni yake yi"

Ta ce "Ahh haba dai, ko kaɗan nan, yana da kyau ka samu abubuwan da za su din ga ɗebe maka kewa"

Al'amin ya ce "To zaɓi ɗaya, ko dai ki sauke wannan abun, ko kuma a haƙura da kallon" yayi maganar yana nuna boti, da yayi ɗare-ɗare a kan cinyar jauhar.

Jauhar ta kwashe da dariya ta ce "Boti master ya ce ka tashi daga cinyar matarsa" kwanciya magen ya ƙara yi, yana lafewa.

"Ban taɓa ganin abun da ya raina ni ba, kamar ke da magen nan ba"

Jauhar ta din ga dariya, ita yadda ba sa ga maciji da botin ma dariya yake bata.

Ta zauna a kusa da shi, tayi connecting da mp, ta saka musu film.

Ta kalleshi ta ce "Ka ji ko? Baby ake cewa mace, kai baka yi mini irin wannan kalar soyayyar, sai zare mini ido da sakani kuka"

Yayi murmushi bai ce mata komai ba, sai dai ta ji ya saka hannayensa ya riƙe nata. Mintuna goma da ta ɗaga kai ta ga yayi bacci. Ta zuba masa ido yana bacci, a ranta ta cigaba da yi masa addu'a.

Ta kashe wayar ta ce "Master ka tashi ka je ka kwanta tun da kallon ne ba ka so"
Yayi shiru bai motsa ba. "Master"

"Mmm" ya amsa ba tare da ya buɗe idonsa ba.

"Mu je na yi maka addu'a ka kwanta"

Ya ce "Ɗauke ni, na gaji"

Ta ce "Na ɗauke ka, ai kuwa da sai dai wata ba ni ba, aikin me ka yi ka gaji har haka?"

"Ƙasa muka kwashe tifa biyar, ban sha komai ba kuma na yi aikin, ni da su Walid"

Jikinta a sanyaye ta ce "Har tifa biyar master. Baka gaya mini ba sannu, amma dai sun biya ku ko?"

Ya tashi zaune ya ce "Eh, har na kai wa mai solar kuɗin, ya zo ya saka miki solar, ya kawo miki fankar solar zafi ya fara yawa kuma ba wuta".

"Solar kuma master? Da mun sai kayan abinci, zafi lokaci ne zai wuce, solar fa da tsada".

"An ce masu asma, ba sa son zafi" ya yi maganar yana tashi tsaye, tashi ta yi ita ma, sai ta rasa me za ta ce masa, ya nufi ɗakinsa, ta rasa ta ina yakamata ta fara ma. Akwai abubuwa masu muhimmanci da yakamata ace yana yi da kuɗi, da solar da ya saya, kamata yayi ace ya sai musu kayan abinci, ya ɗinka sutura da ko ɗan takalmi ne mai kyau na kwalliya. Duk in da ya kwashi taklminsa soso haka yake ƙarawa gaba da su, kayansa ma ita ta ware masu kyan ta kai ɗakinta, sai idan za shi wani wuri na musamman ko juma'a ta bashi ya saka. Sai dai ta san bai kyautu, ta nuna ba ta ji daɗin abun da yayi ba, domin ko ba komai, yayi ne dan ya kyautata mata.

Ya nemi wuri ya kwanta, ta zauna a kan katifar, ta ɗora hannunta a kansa, tare da karanto masa addu'oin kwanciya bacci.

Abun da jauhar ba ta sani ba, bayan ciyar da shi da ta din ga yi farkon auren su, Addu'ar da ya ji tana yi masa cikin magagin ciwo, tayi matukar tasiri a zuciyarsa, Addu'a ce da idan ba uwa ba, ba kowa zai yi maka ba. Addu'oin da take yi masa idan yayi mata wani abu na kyautatawa ma, ba ƙaramin daɗi yake ji ba. Ga uwa uba kirarin da take yi masa wasu lokutan, da suke fasa masa kai. Duk wani abu da zai yi baya manta tarin alkhairin ta.

"Allah ya saka maka da alkhairi, ya buɗa arzikin ka, ya wadata mu da halal ya nesanta mu da haramun. Na gode sosai da sosai Allah ya biya ka da gidan aljanna, ya jiƙan iyayenmu"

Idonsa a lumshe ya ce "Amin 'yar aljanna, addu'ar ta yi daɗi" tayi murmushi ta tashi.

Washegari da wuri ta shirya, tana ta murna za ta je gidan hafsa, ta wanke laifinta na rashin zuwa biki.

Shi kuma ya ce zai kaita, amma ya din ga yanƙwanata.

Ba su fita ba sai sha ɗaya saura, tiryan-tiryan, har gidan hafsa.

Gida ne babba na gaske, Al'amin ya ce "Ba daɗewa zaki yi ba, da wuri zan dawo mu tafi"

"To Allah ya dawo da kai lafiya, take care".

Ya ce "To, ki shiga, sai na tafi"

"Saboda kar in gudu?"

"Idan kin gudu ma zaki dawo" yayi maganar yana tayar da babur ɗin sa.

Juahar ta shiga har falon Hafsat, ta din ga bata haƙuri na rashin zuwanta bikin nan ta ce "Kin san halik maza wasu lokutan sai a hankali, babu yadda ban yi ba, amma ya hana, ba shi da lafiya lokacin" Hafsa sai ɗan fizgar kai take yi, wai ita dole ga matar mai kuɗi.

Har la'asar tana gidan hafsa, bayan ta gama shan ƙamshin, ta saki jiki kuma suka hau hira, da yake ita ce sakuwar jauhar, daga ita sai jauhar.

Ta din ga koɗa mata irin son da Alhaji mu'zzam yake yi mata, dan ta tura mata haushi. Jauhar kuwa ko a jikinta, ta ce "Wallahi yaya hafsa idan Allah ya baka miji mai sonka tsakani da Allah, duk wani ƙalubale mai sauƙi ne"

Ta ce "Aikuwa shiyasa nake tausyinki, aure ba soyayya, ga miji sai a hankali"

Jauhar ta ce "Aikuwa ke da ki ka yi na soyayyar ma, ba ki fi ni samun kulawa ba, da farko a tsorace nake da shi, tun da muka saba Alhamdilillah"

"Taɓ, haryanzu yana safarar cocaine ɗin?"

Duk da jauhar ta ji haushin maganar ta ce "Da safarar cocaine yake, ai mun girmi zaman Kano sai Abuja"

Al'amin ya kira jauhar, ya ce ya zo ta fito su tafi.

Ta leƙa ta window falo ta hango shi, a cikin harabar gidan.

Ta ce "Ɗago kanka sama ka ga" ya ɗaga kai, ya hangota.

"To ka tafi, ba yau zan dawo gida ba, sai gobe"

"Wallahi idan ba ki fito ba, zan shigo har ciki"

"Kaikaikai, gidan mutanen za ka shigo?"

"Sai na shigo ɗin tukuna kenan?"

Tayi dariya ta ce "A'a, rufa mini asiri, kar ka saka da ni da kai a zanemu, gani nan"

Hafsa ta yi ƙuri da ido, tana kallon jauhar, tana leƙen Al'amin kuma suna waya, tana ta dariya.

"Yaya hafsa, bari na tafi"

Hafsa ta tashi ta ce "Mu je na raka ki".

Suka fito harabar gidan tare, yanayin Al'amin a yanzu, akwai nutsuwa a tare da shi, ba kamar lokacin da ya je gidan su ya ɗauki jauhar ba.

Hafsa ta ce masa "Ina wuni?"

"Lafiya ƙalau" ya amsa idonsa a kan jauhar.

"Ya ka ke hararata ne, ba gani na fito ba"

Ya ce "Zaki yi bayani" motar Alhaji mu'azzam ce ta shigo gidan, yana hangen jauhar, ya ci wani irin wawan burki ya buɗe motar ya fito.

Ya ƙaraso ya kalli Jauhar ya ce "Jauhar, dama kina nan?"

Tayi murmushi ta ce masa "Eh, ina wuni?"

"Lafiya ƙalau jauhar, sai dawowa na yi aka ce mini kin yi aure, na ce ko wani laifin na yi miki? Hafsa ta ce mini dama akwai wanda ki ke so, shi ki ka aura, ni kuma baki gaya mini ba lokacin da nake neman aurenki"

Kallo ɗaya jauhar ta yi wa Al'amin, ta ga ya murtuke fuska, idonsa ya fara kaɗawa zuwa ja.

Ta ce "Eh, gashi nan a gabanka mijin nawa, Allah dama ya ƙaddara yayata zaka aura. Yaya hafsa sai anjima".

Ya ce "Tsaya na baki na mota" ya saka hannu a aljihunsa ya ɗebo kuɗin da bai san yawan su ba, ya miƙa mata ta girgiza kai ta ce "A'a na gode"

Hafsa ta ce "Baby kawo ka ga" ta karɓi kuɗin ta turawa jauhar a jakarta, ta ce ba a mayar da kyautar manya, ku gaida gida. Tuni Al'amin ya juya ya fice, idan ya cigaba da tsayuwa, zai iya yi wa Alhaji mu'azzam illa, da wuƙar da take cikin rigarsa a soke.

Tun da suka tafi hanya, bai ce mata uffan ba, hakan ya sanya ta cikin matsanancin tashin hankali.

Da ya ajiyeta a gidan ma, tafiyar sa yayi, bai ko shiga gidan ba.

Ta din ga addu'a Allah ya sanyaya masa zuciyarsa. Duk yadda ya so ya sarrafa kansa ya kasa, sai da yayi shaye-shaye, domin rage raɗaɗin abun da yake ji, dan zuciyarsa har wani tururi take yi.

Har sha biyun dare, idonta biyu tana zaune, tana jiran dawowarsa, ya koma mata Al'amin ɗin sa, dan ko sallama bai yi ba ya shigo, ya wuceta ya tafi ɗakinsa.

Cikin fargaba, tana addu'a, ta bi bayansa, warin wiwi duk ya cik wurin.

"Sannu da zuwa, nan zan kawo maka abincin?"

"Fita ki bani wuri, kafin na kakkaryaki na zubar. Idan ba kya son zama da ni, ba sai kin wulaƙanta ni, ta hanyar kai ni wurin tsohon saurayinki ba, shiyasa nake ta baki zaɓi tuntuni a kan zama da ni, ba dan na sarrafa zuciyata ba, sai na kashe mutumin nan har lahira yau, fita ki bani wuri, bana ƙaunar ganinki ma".

Ta marairaice ta ce "Dan girman Allah ka yi haƙuri, wallahi da na san zamu ganshi da ba mu je ba, ni saboda 'yar uwata na je".

"Saboda 'yar uwakki, ko kuma saboda ki ganshi?"

"Ya za ayi na je ganin wani, alhalin ina ɗauke da igiyar aurenka a kaina"

"Ki daina wani kwantar da murya, na riga na gane abun da ki ke nufi, da in da ki ka dosa, if you still loves him zan iya sakin ki, ki iya koma wurinsa, tun kafin na illata ki, ba zan juri wannan cin fuskar ba, nan gaba ban san me zaki aikata ba"

Cikin tsananin ɓacin rai ta ce "Idan ka sake ni, hakan baya nufin rayuwata ta zo ƙarshe, jaririn da ya zo duniya ma Allah ya na iya karɓar rayuwar mahaifiyar sa, kuma ya raya mata shi. Ka yi mini duk hukuncin da ka ga shi ya dace ni" ta fice daga ɗakin, cikin tsananin ɓacin rai da damuwa.

Ransa yayi matuƙar ɓaci, jin yadda ta gaya masa maganganu, gashi dama a cake yake, ya nemi wata ƙwaya ya haɗiya ya kwanta, dan kar ayi ɓatacciya. Da asuba ya farka, ya saba ta zo tayi ta fama ta tashe shi, amma yau taƙi zuwa.

Yayi sallar asuba, gari yayi haske ya fito, amma ba ta fito ba, ya gaji da zama ya fita.
Da azahar ma, abincinsa ta ajiye masa ta yi zamanta a ɗaki, idan yana falo tana ɗakinta, idan yana ɗaki sannan zata fito.

Ya shareta shi ma, yana jiran ta zo ta bashi haƙuri kamar yadda ta saba, amma taƙi, sai ya ji gidan yayi masa duhu babu daɗi. Kusan kwanaki uku, ba wanda yake shiga harkar wani.

Yau har ya cire kaya ya kwanta, ya tashi ya zauna yayi shiru yana tariyo maganganun da ya gaggaya mata, sai ya ji sun ɗan yi nauyi da yawa.

Ya tashi ya tafi ɗakinta, kasancewar babu wuta, ya kunna fitilar wayarsa, ya shiga.

Tana banɗaki tana wanka, ta jingina fitilarta a kan mudubi, tana haska mata cikin toilet ɗin.

Ya ƙarasa gaban mudubin, ya ɗauki wayar ya kashe fitilar.

"Waye a nan?" Tayi maganar cikin tsoro, dan ba ta san ma ya dawo ba.

"Waye?" Yayi shiru bai yi magana ba.

Da sauri ta gama kwara ruwan a jikinta, ta fito sai dai ɗakin yayi duhu, ba ta ganin komai.

"Wai waye ne?" Tayi maganar tana laluba hanya.

Direction ɗin da yake ta nufo, cikin tsoro, kawai ta ji ya zaunar da ita a kan cinyarsa. Cikin tsananin tsoro ta ware baki za ta yi ihu ya tsohe mata baki ya ce "Shhhhh, Al'min ne"

Ayshercool
08081012143


Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login