Showing 24001 words to 27000 words out of 152254 words

Chapter 9 - ?arfe A Wuta Book 1 Hausa Novel Complete

15 Dec 2024

329

yaron nan, dama mugu shi ya san makwantar mugu ai"

Madaki ya sauke numfashi ya ce "Zan shirya gagarumar ɗaukar fansa kan mai uwa da wabi a unguwar su, jinin yarana da suka zubar ba zai tafi a banza ba, dan shammatar su ka yi, suka mamaye su ba na nan"

"Wannan ku ta shafa, ni babban burina shi ne Aminu, muddin yaron nan yana numfashi, kamar sarƙa ce a wuyana, dole a kawar da shi".

Madaki ya ce "Ba kai kaɗai ba, ko kuma in ce da ni da kai kusan abu ɗaya ne a wurinsa, nima ka san akwai tawa ni da shi, tsohuwar gaba ce ta tsawon shekaru, wanda a kanta unguwanninmu suka kasa zaman lafiya har yau, ga kuma wannan al'amari da ya faru. Muddin ban kashe Aminu ba, ni zai kasheni"

Ya jinjina kai ya ce "Ai Viper na fuskanci ƙarfe ne a wuta, ya fi ƙarfin ɗauka da hannu, sai dai da ɗan uwansa ƙarfe, kai kaɗai zaka iya maganinsa"

"Ka bani lokaci kawai, zan kuma ƙoƙartawa, matsalar ko yaransa ba kowa ne ya san in da yake ba, amma na san dole Walid ya san in da yake, amma shi ma Walid ba lafiya ba ne taɓa shi, ka dai bani lokaci"

"Babu isasshen lokaci, ka yi huɓɓasa kawai"

Madaki ya jinjina kai.

Mutumin ya ɗebo kuɗi ya bashi, ya sallame su, suka juya suka fita da shi da yaransa.

Nasir ne tsaye a office ɗin sa, ya kalli matashin da yake zaune, da aƙalla zai yi sa'ansa ya ce "Mu'azzam lamarin ƙasarmu sai Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ka san da ƙyar na gano station ɗin da yaran nan suke, ba ma ta yankin da abun ya faru ba ce?"

Mu'azzam ya yi murmushi ya ce "Haka ka ce mini"

"Gaba ɗaya yaran under age ne, kuma duk cikinsu babu yaran Aminu, dan tuni an sake su, sai wani wai madaki, na ce dai a ajiye mini su, da yiwuwar mu kama madakin, zai iya sanin in da Aminun yake,tun da abokin faɗansa ne, amma da na yi magana da DPO ɗin division ɗin yankin, ya ce shi ma madakin ba ya kamuwa, kuma ya addabi yankin yana da yara sosai da sosai. Abun takaicin ma ba unguwar su ɗaya da Aminun ba, amma suke cigaba da tayarwa da mutane tarzoma"

Mu'azzam ya ce "Harkar nan tamu sai fa Innalillahi wa Innalillahi raji'un, muna tufka manyanmu na warwarewa"

Nasir ya ce "Bari kawai, zan yi iya ƙoƙarin da zan yi, ni zan kama Madakin, Arfa har asibitin da aka kai waɗanda aka yi wa rauni ta je, muka yi waya kafin na je wai an kwashe su, an bar asibitin da su, na fara zargin anya ba jami'an mu ne aka samu bara gurbin da suke mara masa baya ba"

Mu'azzam ya ce "Ba abun mamaki bane ba, amma meya kawo Arfa cikin wannan lamari, ta bar aikin lawyern ne?"

Yayi murmushi ya ce "Rigima mana, yarinyar nan ta zarce tunaninka, ba ta wasa da duk abun da ya shafe ni ko cigaba na"

"Hmm Nasir kenan, wai yaushe zaka gayyacemu sabgar nan ne? Shekarun ka fa suna ja"

Nasir ya rausayar da kai ya ce "Mama ce ta hana, ta nuna ba ta so, ban taɓa gaya mata ba, saboda tun kafin na furta maman ta gargaɗe ni a kan haka, kuma haryanzu ni ban ji ina son kowace yarinya ba, ita ɗin dai nake so. Ban san adadin samarinta da na kora ba saboda kishi. Yadda take son abun da nake so da son cigabana, na san da zan furta ina sonta, ba zata ƙi ba, amma na rasa yadda zan yi da mama".

"A'a Nasir, dan Allah kar ka zalunci yarinya, haka zaku zauna shekaru na tafiya, kai baka aureta ba, kuma ba ka bari wani ya aura ba? Wannan ai mugunta ce, ka yi magana da Abba mana".

Nasir ya girgiza kai ya ce "Manta kawai, abun ya wuce yadda ka ke tunani".

***
Arfa na kitchen tana taya baba magajiya aiki, suna hira tana tambayar baba magajiya kwatancen cikin unguwar ƙofar na'isa, dan zuwa aiken barrister Habib, dan ita ba zuwa ta taɓa yi ba.

Baba magajiya na girki, ita kuma tana wanke-wanke a sink.

Siyama da take ƴa ta uku ga mama ce ta shigo kitchen ɗin, ta jefawa Nabila kwanukan hannunta maimakon ta ajiye.

Nabila ta yi shiru, ta cigaba aikinta suna hira, duk da abun ya ɓata mata rai.

Amfani ta kuma yi da kofi, ta wurgowa Nabila cikin sink, cikin zafin nama da masifa, Nabila ta ɗauki kofin ta jefa mata a fuska ta ce "Ai ba baiwar ubanki ba ce ni, da zaki din ga jifana da kwanuka"

"Nabila ni ki ka daka?"

"An dake ki ɗin?"

Baba magajiya ce ke ƙoƙarin basu haƙuri, amma siyama ta shaƙe Nabila, Nabila ta rarumo wani kwano ta buga mata, dambe ya kacame.

Baba uwani ta yi ƙoƙarin raba su, amma abu ya gagara.

Ta fito falo da gudu, tana neman taimako.

Dambe tun daga kitchen har falo, duk abun da Nabila ta rarumo sai ta kwaɗa mata, kamar wasu kuraye.

"Mahaukaciyar ina ce ke? Ke kullum haka zaki ƙare ki zagi wannan ki ci mutuncin ƴaƴan gida kina ƴar karere"

Cikin baƙin ciki Nabila take kallon mama, tana iya ƙoƙarinta wurin danne abubuwan da mama take yi mata, duk faɗanta da tashin hankalin ita da yaran gidan suke yi, amma sai mama ta shiga ta zaƙe ta shigarwa yaranta.

Anty ta ce "gaskiya maman Sauda wannan ba girmanki bane ba, maimakon ki yi musu nasiha, sai ki din ga aibata Arfa, ai ba a haka"

Siyama ta din ga zagin Nabila, zagi na cin mutunci, tsawar da Abba ya yi musu ne, ya sanya duk suka ɗago cikin tsuma.

Ya nuna nabila ya ce "Arfa, ban isa na saka doka ki bi ba ko? Siyama ba gaba take da ke ba? Nake jiyo muryarki tun daga waje kina zaginta?"

Arfa ta buɗe baki zata yi magana, amma ya daka mata tsawa ya ce ta yi masa shiru.

Siyama kuma ta fashe da kuka tana gaya masa har dukanta arfa tayi.

Aikuwa ta in da ya shiga ba ta nan yake fita ba, ya hana kowa magana ya yi wa arfa kaca-kaca saboda sanin ba ta ji, ga rashin haƙuri da taurin kai.

Da sauri ta tafi ɗakinsu tana wani irin kuka, ta je ta faɗa kan gadonta, jikinta har rawa yake yi saboda baƙin ciki takaici ta din ga kuka.

Cikin kuka ta ce "Ya Allah ka bani miji kowane iri ne, in dai zai zama alkhairi a gare ni, na tafi na bar gidan nan, na gaji Allah ka amsa mini dan girmanka, kowane iri ne zan iya zama da shi".

Can falo kuma, jikin Abba ne yayi sanyi, ganin arfa na kuka ya san akwai wani abu a ƙasa, dan idan tayi laifi, wataran ko kasheta zai yi ba zata yi kuka ba, duk da tana da saurin kukan.

Ya kalli Anty ya ce "Zainab je ki duba yarinyar nan, kar ciwonta ya tashi"

Anty ta jinjina kai, ta bi bayan arfa.

Mama kuwa a sashinta take yi wa Siyama mitar meyasa ba ta yi wa Nabila dukan da za ta kasa tashi ba.

"Mama kin san yarinyar nan har aljanu take yi, haka kurum su tashi ni ta kashe ni, komai ta rarumo buga mini take yi, ba ki ji kafaɗuna ba"

Mama ta yi ƙwafa ta ce "Na rasa yadda zan yi maganin yarinyar nan, wallahi bana sonta ba na ƙaunarta, gaba ɗaya ba kwa gaban mahaifinku sai ita, in sha Allah sai ta zame masa masifar da ba zai iya shawo kanta ba, sai ta kwaso abun kunyar da za ta kunya ta shi a idon duniya".

Nabila kuwa ƙin saurar anty ta yi, ta sha uban kuka, Anty ta sanarwa Major kukan da take yi, ya basar kamar bai damu ba, amma ƙasan zuciyarsa sam babu daɗi.

Tsakar dare suke waya da sumayya, take gaya mata abun da ya faru.

Sumayya ta ce "Arfa, ke rashin haƙuri ne yake janyo miki wasu abubuwan, da kin yi haƙuri ba ki tanka mata ba, dama neman magana ta zo yi".

"Sumayya kin san ba zan iya ba, ni ina wulaƙanta mutane ne?"

Sumayya ta ce "A'a idan na ce kina da wulaƙanci Nabila na yi miki sharri, sai dai masifa da rashin haƙuri, ga jarababben taurin kai ba a gaya miki ki ji ko kaɗan"

Nabila ta ce "Sai dai ayi haƙuri da ni a yadda nake, ni ba zan yadda da wulaƙanci ba"

"Aikuwa zaki yi ta shan wahala dan ubanki"

Nabila ba ta damu da zagin da sumayya ta yi mata ba, domin idan da sabo ta saba, dan wasu lokutan sumayya playing role take yi kamar na uwa a rayuwarta, ta kan ji maganarta idan ta ga dama.

"Sumayya dan Allah ki yi mini addu'a, Allah ya bani miji kowane iri ne, in dai zai zame mini alkhairi a shekarar nan na bar gidan nan na huta"

Sumayya ta ce "Ba ki da hankali, kowane iri fa ki ka ce"

"Eh, wallahi idan ba haka ba, zan gudu na bar garin nan, na bar musu gidan, sumayya baki san me suke yi mini ba na gaji" ta ƙarasa maganar cikin shagwaɓa tana kuka.

Sumayya ta san komai, dan haka cikin rarrashi, ta kwantar da murya, ta din ga yi wa Nabila nasiha, da rarrashin ta, har ta sassauta kukan da take yi.

Da haka suka yi sallama, ta kwanta bacci.

Sai dai ta kasa baccin, saboda yadda zuciyarta take zafi, ta rasa me ta tsarewa maman su Sauda a rayuwa, da ita da yaranta suka tsaneta haka, Nasir ne kawai suke ɗasawa da shi, da ƙyar bacci ya kwashe ta.

Da safe ta shirya cikin wata abaya baƙa, tayi kyau ko karyawa ba ta tsaya yi ba, ta fito falo fuskarta babu walwala.

Kallo ɗaya zaka yi mata, ka san ba ta samu isasshen bacci ba.

Da kamar ta yi fuska tayi tafiyarta, amma ta haura benan Abba ta je ta gaishe shi, sai dai fuskarta babu annuri, babu raha da ta saba yi idan ta je gaishe shi.

Ya ƙura mata ido ya ce "Kin karya kuwa?" Ta ce "Idan na tsaya karyawa zan makara, zan karya a wurin aiki"

"Dan zaki makara sai ki fita ba ki karya ba, yaushe ki ka fara tsoron makara? Menene ma ya hana ki tashi da wuri?"

Tayi shiru tana wasa da yatsun hannunta, idonta yana cika da hawaye.

Ya saka hannu a aljihunsa, ya ciro kuɗi masu yawa, ya miƙa mata ya ce "Ga wannan na san wata yayi nisa, babu lallai ki na da kuɗi a hannunki, ki sai wani abun idan kin je ki karya, saura ki sai abun da zai ɓata miki ciki, ko ya cutar da lafiyar ki"

Kamar ta ce ya bar su, amma ta saka hannu biyu ta karɓa, ta ce ta gode, yanayin yadda take tafiya kawai, zai tabattar mata da tana cikin damuwa ko rashin lafiya.

Gaba ɗaya jikin Abba ya yi sanyi, a tsakiyar zuciyarsa yake jin zafi, idan ya ga Nabila a cikin damuwa, shiyasa wasu lokutan baya iya jure yi mata hukunci yake kawar da kai a kanta.

Duk iya ƙoƙarin da Nasir yake yi, a kan yaƙi da harkar daba, abu ya ci tura, dan yaran da aka kama ya koma ya tarar da wai an yi umarni daga sama a sake su, abun ya ɓata masa rai sosai da sosai.

*****
A farfajiyar wata bishiya suke zazzaune, suna ta shaye-shayen kayan maye, duk sun cika wurin da ƙaurin hayaƙi.

Madaki ya karta wuƙa a ƙasa, ya kalli tarin matasan da sun fi ashirin a gabansa ya ce "Babu rangwame ko sassauci, babu mace babu namiji, ko babba yaro ko tsoho, duk wanda aka samu idan aka shiga operation ɗin nan a farmasa, ayi ɓarna ayi ta'adi a ɗauki fansar abun da Aminu yayi mana, jini ya din ga gudana ko ta ina, duk shagon wanda aka samu a fasa ku kwashi ganima, na yarje muku.
Haka zalika duk wanda ya gano in da Viper yake, muddin ya kawo mini shi, a mace ko a raye, akwai tukuici mai tsoka"

Suka fara shewa cike da maye, ɗaya daga cikin su ya ce "Aminu fa ƙarfe ne a wuta, duk wannan shewar kama shi ba abu ne mai sauƙi ba, da mai sauƙi ne na san da ka riga mu kama shi"

Madaki ya ce "Rufe mini baki, ko na yi gunduwa-gunduwa da namanka, dole ne a kama shi, kai gobe duk wanda aka gani daga tsallaken unguwar su, ya shigo unguwar nan ma a sara mini shi kawai, a ɗauki fansa mafi muni na abun da ya yi mana, zan ga da ni da shi, waye zai sarara waye gaba da wani"

Cikin haɗa baki suka dinga faɗin "An gama oga, gobe akwai ƙaramin yaƙi"

misalin ƙarfe sha ɗaya da rabi na safe, a sannu take tafiya a cikin unguwar, tana duba kwatancen da barrister Habib ya tura mata.

Kasa ganewa tayi, ta tsaya a wurin wani mai kanti, ta sayi ruwa ta sha, kuma tambaye shi.

Tana tsaye tana duba wayarta a cikin shagon provision ɗin, wani matashi ya shigo, suka gaisa da mai kantin ya ce "Bani ƙulli biyu da ruwa uku"

Mai kantin ya ce "Amma ka san ina binka sauran kuɗi ko?"

"Zan biyaka, wannan yawa ne, ka bani na ware mana, caji zan yi kaina gaba ɗaya babu network,aljihuna kuma yayi gobara"

"Ba zan bayar ba" mai shagon yayi maganar yana miƙawa Nabila ruwan roba.

Nabila ta din ga satar kallon matashin, yadda bakinsa ya karkace saboda shaye-shaye take kallo, laɓɓansa duk sun zazzago.

Tayi gyaran murya ta ce "Ɗan uwa ka bashi mana, tun da ya haɗaka da Allah, in sha Allah zai kawo maka, tun da ya yi alƙawari"

"Rabu da shi, ba ya biyan bashi"

Nabila ta yi murmushi ta ce "Nawa ne kuɗin nasa?"

Mai kantin ya ce "Dubu biyu nake bin sa"

Ta yi murmushi, tare da ciro kuɗi a jakarta ta ce "Dubu biyu ai babu yawa, Ga dubu uku, na biya masa kuɗin da ka ke bin sa, ka bashi wani bashin, ni kuma ka ɗauki kuɗin sayayyata"

Matashin ya kalleta ya ce "Sai kin yi babbar yaya, Allah ya ƙara arziki"

Ta amsa da "Amin ɗan uwa na gode sosai".

Wani abu ta ga an bashi a nannaɗe a leda, da ruwa ya sake yi mata godiya, ya fice.
Yana fita ta ce "Malam dan Allah menene wannan ya saya?"

Mutumin yayi murmushi ya ce "Ƙanwata wiwi ce" waro ido ta yi ta ce "Wiwi kuma, ka ke sayarwa? Amma na ga kai kamar ba ka sha ko?"

"Ki yi ƙasa da muryarki mana, ya zamu yi sana'a ce, ni ba abun da nake sha. ga canjinki"

Cikin mamaki ta ce "Meyasa ka ke sayar da abun da ba ka sha?"

"Kar ki tsananta bincike malama" yayi maganar yana haɗe rai. Ta jinjina kai ta ce "To Allah ya taimaka"

Fitowa ta yi daga shagon, ta hangi matashin yayi nisa, ta rufa masa baya ta bishi da sauri.

"Bawan Allah ɗan tsaya dan Allah" ta ƙarasa tana haki.

Ya tsaya yana kallonta ya ce "Ya dai?"

"Abu zan tambaye ka, amma kafin nan ka san abun da ka saya ɗin nan, yana da illa ga lafiyarka?"

Tsayawa yayi yana kallon ta, tayi saurin cewa "Dan Allah taimako nake nema, wani gida nake nema, amma na kasa gane layin, ko zaka taimaka mini?"

"Ina ne?"

Ta gaya masa ya ce "Na san gidan, amma ba hanyar ki ka biyo ba nan"

"Dan Allah kwatanta mini"

"Mu je na kai ki bakin layin"

Ta ce "Yauwa ɗan uwa, dan Allah mu yi wata magana mana, ka san wani mutum Aminu Viper?" Wani irin burki ya ci yana kallonta.

"Yi haƙuri idan na ɓata maka rai, ɗan uwana ne shi, tun da Allah ya sa ya bar gidan yari, bamu sake ganinsa ba, kuma na ji an ce yaransa sun tayar da tarzoma a unguwar nan a satin nan, dan har asibitin da aka kai waɗanda aka yi wa rauni na je, na zaci zan ganshi, amma ban tarar da shi ba"

Ya ware mata jajayen idanunsa ya ce "Ki ka ce ɗan uwanki ne?"

Cikin ƙarfin hali ta ce "Eh, ina da alaƙa da shi"

Ya ce "Na san shi, na kuma san in da yake"

Da sauri ta ce "Dan Allah ka taimaka mini a ina zan ganshi?"

Ya ƙare mata kallo ya ce, idan kin tashi, ki tambayi ina ne layin iraƙi a unguwar nan, idan ki ka je akwai wata babbar bishiya zaki ga wasu a zazzaune a wurin, ki tambaye su, za su nuna miki shi.

Cikin tsananin farin ciki, ta din ga yi masa addu'a. Amma fa sai dai ta kasa tantance irin kallon da yake yi mata, hakan bai dame ta ba.

Har ƙofar gidan matar ya rakata, ta kuma yi masa godiya, ta ciro kuɗi ta bashi, sannan ta shiga gidan matar.

Matar ta karɓi Nabila hannu bibbiyu, bayan da Nabilan ta yi mata bayanin barrister Habib ne ya turo ta.

Ta bawa Nabila duk wani information da take buƙata, tana gama abun da take yi ta tashi ta ce tafiya za ta yi.

Babu yadda matar ba ta yi da ita ba, a kan ta zauna ta ci abinci ta yi salla, amma taƙi, ta tashi ta tafi.

Babu tunanin komai, tana fita, ta tambayi wasu yara, ina ne layin iraƙi?.

Duk sai da suka kalleta, ganin tana mace tana tambayar wannan layin da ƴan daba suka mayar mallakinsu, abunka da yara, babu tunanin komai suka sakata a hanya, ta yi musu godiya ta nufi kwatancen.

Tana ta addu'a Allah ya sanya ta dace, duk tana da burin cikar nata muardin, amma za ta yi farinciki sosai idan aka ce Nasir ne yayi nasarar kama Aminu, koba komai likkafarsa za ta sake ɗagawa, ta nufi layin ba tare da ta san idan ta ganshin me za ta ce masa ba.

Layin shiru babu kowa, babu gina-ginan kirki, sai kangwaye, sai da ta je tsakiyar layin, ta hango wata ƙatuwar bishiya, da mutane.

Kamar ba mace ba, babu razani ko fargaba ta tunkari bishiyar.

Gaba ɗaya suka zuba mata ido, har ta ƙaraso.

Wiwi kawai suke busawa, ta ɗan tsaya nesa kaɗan da su, saboda hayaƙi.

"Ina wuninku"

Suka amsa mata da lafiya ƙalau, suna mamakin ganin mace a wannan chamber.

"Dan Allah tambaya nake yi, wani nake nema, aka yi mini kwatancen nan aka ce zan sameshi".

Ɗaya daga cikin su ya ce "Waye shi?"

Ta ce "Amm, sunansa Al'amin, amma ana ce masa Aminu Viper, tun da ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login