Showing 126001 words to 129000 words out of 152254 words

Chapter 43 - ?arfe A Wuta Book 1 Hausa Novel Complete

15 Dec 2024

337

dan Allah dan Annabi ka yi haƙuri ka yafe mini, abubuwan da na yi maka kwanan nan ban kyauta ba, dan Allah ka yi haƙuri ba zan sake ba, wallahi ni ba mara kunya ba ce, kawai na rasa ya zan yi da wasu abubuwan ne, damuwa tayi mini yawa, dan Allah ka yi haƙuri idan ka sakenin ma, ka yi haƙuri ka mayar da ni" tayi maganar cikin rauni.

Ya lumshe idanunsa ya ce "Bani wuri zan kunna hayaƙi"

Ta marairaice ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri master, ka yafe wa 'yar madara ɓacin rai ne ba zan sake ba, na san ban kyauta ba, dan Allah ka yi haƙuri"

"Sai fa kin tafi, kin isheni ne kawai takura mini ki ke yi"

"Dan Allah ka yi haƙuri, na daina takura maka, har cincin na yi maka jiya, in kawo maka?"

"Eh ki kawo mini, sai fa kintafi"

"Da ka san abun da hakan ka iya haifar wa rayuwata, da baka sake ni ba, dan ka ga ina ta roƙonka shikenan, duk ranar da ka bari na bar rayuwarka na bar ta har abada lokacin da zaka so ka ganni da kuɗi ba zaka ganni ba".

"Eh na ji, kafin ki fara ɗaukar makami, gara mu rabu, ungo takardarki tafi da ita" yayi maganar yana danƙa mata takardar da ya warware. Ta rintse idanunta, tuni ta fara kuka, ta buɗe idanunta ta sauke a kan kyakkyawan rubutunsa, dan ganin saki nawa ya yi mata.

*Ba zan dawo da wuri ba, na bar kuɗi a kan katifata ki sai wani abun ki ci*

Wata irin ajiyar zuciya ta sauke, ta ce "Shi ne ka yi ta wahalar da ni? Dama ba sakina ka yi ba, ka sakani kuka?"

Hamma yayi, yayi shiru ta ce "A'uzibillah" duk gurbin da ya yi wani abu, yakamata ya yi addu'a bai yi ba, sai tayi masa.

Ta ce "Aishikenan amma dan Allah ka yi haƙuri abubuwan da na yi maka ka yafe mini"

"To, ki bani wuri zan sha abu"

Ta ce "To bani wayar da ka bani jiya" gefen katifarsa ya nuna mata, ta tashi ta ɗaukkota a kwali.

Ta kalleshi ta ce "Yanzu dan Allah wannan ta wa ce master? To kai ina taka?" Ya nuna mata keypad ɗin sa.

"Wallahi ko a mafarki ban taɓa tunanin riƙe waya ba, yaya saifu ya taɓa bani keypad mama ta ƙwace, Allah ya saka maka da alkhairi ya saka ka a aljanna, Allah ya nuna mini ranar da zaka daina shan komai, ka zama limami saboda salihancinka, Na gode master na gode sosai da sosai" tayi maganar tana tattaɓa wayar.

"To excuse me, ina son yin caji"

"To yi mana"

Ya ce "Ki fita ki bani wuri dai, kar ki sume mini yau bani da kuɗin zuwa asibiti"

Maƙale kafaɗa tayi, ta ce "Master, wai yaushe zaka kai ni na gaida mama ne? Da wurin hajiya ma?".

"Wace maman?"

"Mamanka mana, bamu taɓa zuwa ba, na san wadda na gani a gidanku ba ita ce mamanka ba"

"In ji wa?"

Jauhar ta ce "Babu uwar da zata zauna hankalinta a kwance, alhali an yi wa ɗanta sharri an tsare shi".

"Mama ta mutu" ji tayi kamar ya soka mata mashi, ta kalleshi ta ce "Kai ma ka san pain ɗin master? Ka girma da ita ka santa?" Ya jinjina mata kai alamar eh.

Jiki a sanyaye ta ce "Ni ban ma santa ba, ina yawan takura ƙwaƙwalwata, dan na tunota, da rayuwar da muka yi tare, amma bana iyawa, baba ne yake da hotonta, nayi-nayi ya bani, ya hanani, idan na shiga ɗakinsa zan gyara masa, sai na ɗauki hoton in yi ta kallo ina jin daɗi, duk da ina jin kewarta, ina son in san yaya take ya halinta yake, yadda su mama suke faɗa ne ko akasin haka? Kawai saboda Baba ya saka hoton a cikin wallet ɗin sa, ya ce zai kai a wanko wani ya saka a yi enlarging ɗin sa ya bani, mama ta ɗauki hoton ta yayyaga, ta watsar wallahi ji na yi kamar ta yaga zuciyata, bana riƙo idan an yi mini laifi mantawa nake yi, ana yawan cewa bani da zuciya amma haryanzu a raina, na kasa jin cewa na yafe wa mama abun da ta yi mini.
Da farko da na taso, na zata mama ce ta haife ni, daga baya na gane ba ita haife ni ba, sai na fara tunanin ko kawai faɗowa na yi ko tsinto ni aka yi, kowa yana da uwa ban da ni, wataƙila a haka aka haifeni, daga baya na yi tunanin ko kawai 'yar aiki ce ni, na zata 'yan aiki duk ba su da iyaye. Daga baya na gane baba ne babana, uwa ce bani da ita, sannu a hankali kuma na gane ina da uwa amma bata duniyar.
Sai dai ba na jin daɗin irin yadda su mama ke aibata mamana, duk da ba ta raye ban san ta ba, har suna cewa mayya ce ta taɓa kama su ma, amma baba yana faɗar cewa mamana mutuniyar kirki ce, irin halina ɗaya da ita, haka yaya saifu ma yana faɗa.
Mama ce mariƙiyata, na so in tashi kamar ita ce wadda ta haife ni, amma ƙiriƙiri sai ta nuna mini banbanci ba ita ta haife ni ba. Ta saka aka cire ni daga makarantar kuɗi, aka mayar da ni ta gwamnati wai ba na gane karatu ni daƙiƙiya ce, kuma ni babu mai kula da ni, ko koya mini assignment komai ni nake yi wa kaina gashi baba ba ya iya magana a kan abun da ake yi mini.
Ita kuma anty Zakiyya cin zali na zahiri, na daku a wurinta, duk ba wannan ba ni ya riga ya wuce, kawai haryanzu ina jin zafin yaga mini hoton uwata da mama tayi, da ƙazafin nan da suka yi mini, na fanɗarewa, na san zan yafe musu wataran amma ba yanzu ba.
Ina son in ga mutum yana hira da mamansa, ko suna wasa irin na ɗa da uwa, abun yana burgeni, ko mutum ya din ga gaya wa mamansa damuwarsa da daɗi master, wataƙila kai ka samu wannan damar ni kuwa ban samu ba, maybe da mamanka ta yi tsawon rai wannan rayuwar za ta zo maka da sauƙi". Tana gaya masa raɗaɗin abun da take ji a zuciyarta yana raguwa, duk da kuka take yi.

Ya ce "You are missing her?" Yayi maganar yana kallonta.

Ta jinjina masa kai ta ce "So badly"

"Ki yi mata addu'a" ta jinjina masa kai tana goge hawayenta, a take shi kuma ya tuna irin tasa rayuwar, duk da lokuta da dama idan ka haɗu da wanda ku ke da irin matsala ɗaya ku ka yi sharing ana samun releif, amma yanzu shi ba ya son doguwar magana idan ya fara ma gajiya zai yi, duk da kwanan nan jauhar na isarsa da saka shi magana, kuma muddin ya gaya mata shi nasa labarin, zata shiga damuwa dan haka ya ƙyaleta.

Duk da kuka take yi, ta fara ɗaukarsa a hoto tana murmushi ta ce "Kai zan fara yi wa hoto da wayar nan, haryanzu mamaki nake yi, wai master ne ya saya mini waya, Allah dai ya sanya mini kai a cikin aljanna ya jiƙan mama, ya ja da ran wanda suka rage mana, Allah ya goyi bayanka ya yi maka jagora a cikin lamuranka. Kai master na rasa wace addu'ar ma zan yi maka, na rasa wace irin godiya zan yi maka ma"

Har cikin ransa ya ji daɗin Addu'ar da take yi masa.

Ya kuma amsa da Amin.

"To mun gama ki tafi"

"To me na yi maka ka ke korata?"

Ya ce "Sigari zan sha"

Ta ɓata fuska ta ce "Da sassafen nan ba ka ci komai ba, sai ka fara da hayaƙi, haba mai babban suna, idan a baya babu wanda ya damu da lafiyarka, ni ina son ka yi lafiya, ka rayu saboda ka ajiye 'yar madara, yau dai ɗaya ayi haƙuri dan Allah a ɗaga ƙafa kar a sha da sassafen nan" kamar shashasha haka yake bin ta da kallo, ta karɓe lighter da sigarin hannunsa, har da ta gefe ta cikin kwali ta tattaresu.

"Bari na dafa mana shayi, cincin na yi jiya, amma na kasa ci saboda damuwa, ka yi brush sai ka fito ka karya, kuma zan din ga leƙowa saura na ga mutum ya sha wani abu"

Sunkuyar da kai ya yi, yana murmushi da gefen bakinsa.

Jauhar ta samu na yi, lambar baba ta kira, yana ɗagawa ko gaisawa ba su yi ba ta ce "Baba na yi waya"

Baba ya ce "Masha Allah Alhamdilillah, ina tayaki murna waliyya"

"Ka hau what's app mu yi video call"

Baba ya ce "To shikenan waliyya" Al'amin ya kalleta ya maimaita waliyya a ransa, lallai ta ci sunan da mahaifinta ya kirata da shi.

"Master, nan ne wurin video call ɗin ko?" Ya jinjina mata kai alamar eh.

Tana kira baba ya ɗaga fuskarsa ta Bayyana a screen ɗin wayar.

"Baba wayata touch screen ce mai kyau".

Baba yayi dariya ya ce "Masha Allah, Allah ya sanya alkhairi."

"Amin, ina su yaya saifu su mama da Anty?"

"Duk suna nan lafiya, baba dan Allah kowa da kowa a turo mini lambarsa, duk zan yi musu magana ta what's app, zan din ga kiran su kuma a waya"

"To shikenan, a ina ki ka samu waya ne?"

"Master ne ya saya mini" sai kuma ta ce "Au amm maigidan ne ya sai mini"

Wani irin sanyi ya ratsa zuciyar baba, ya ce "Allah ya saka masa da alkhairi, ya yi muku albarka baki ɗaya"

"Amin baba" ta kaste wayar.

"Master " ya ɗago ya kalleta.

"Na gode sosai" ya ɗan tsuke fuska ya ce "Kin faɗa kin sake, ya isa haka"

"Bar ni na yi yabon gwani ya zama dole".

Tana cikin maganar hankalinta ya kai kan labarin da ake yi a radio, wata mata ce take kuka, take roƙon gwamna, sarki da kuma jami'an tsaro su kama Aminu mai dogon zamani bisa karya mata ɗa da yayi, ya soke shi da wuƙa, an kai shi asibiti rai a hannun Allah gashi ba ta da ƙarfi, tana neman a bi wa ɗanta hakkinsa.

Cikin tsananin tashin hankali, jauhar ta kalli Al'amin, tamkar bai ji me aka faɗa a radiyon ba, sai tauna cin-cin yake yi ƙururus ƙurus ko a jikinsa an mari dutse.

Ayshercool
08081012143

🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724

https://chat.whatsapp.com/E3bH5OKBh9jH2aYygj0ArA


Kina bukatar kaya masu kyau da inganci??

    Kina bukatar kayan kitchen wnd suke available ba order ba??

    Kina bukatar adashin gata wnd zaki dauki kaya kamar kyauta??

    Kiyi joining wnn group din namu insha Allah xakiji dadin kasancewa a ciki.

     Muna da kaya available masu kyau da rahusa💃🏾💃🏾
Ko kimin mgn ta👇🏽👇🏽
08093932955


Jinjina kai indabo yayi, ya ce "Za ayi ba zai gagara ba, zamu dawo idan an kammala aikin, kuma wa'adin da aka ɗibar mana ya cika".

"Shikenan, nasara tana tare da kai, ba yaƙini muke da shi ba, tabbaci nake bakaz duk da akwai ƙalubale a gaba, sai da ba za su gagara ayi maganin ƙalubalen ba, amma a gaba kaɗan ɗin akwai dutse, da zaka yi karo da shi, na buga na duba, duk babu hanyar maganin dutsen nan, sai dai ayi ragas, ko ka kar dutsen ko ya kar ka"

P.A ya ce "Kuma babu yadda za ayi da dutsen? Ko wata mafitar?"

"A yanzu dai babu,

Suka tashi suka fito, suna tafe a hanya Indabo ya ce "P.A"

"Na'am honorable"

"Bokan nan kullum cikin faɗin ayyuka masu hatsarin gaske yake, ina tsoron tonuwar asirina, kar mu je in sake janyo wa kaina jagwal kana kallon yadda yarinyar nan Naja'atu ta zame mini alaƙaƙai"

"Mu bi komai a sannu sir, zamu yi nasara kuma samo yarinya ba zai gagara ba, ko cikin ƙauyukan nan aka bincika za a samu, ko kuma Naja'atu ta samo a irin mutanen da ke hulɗa da su" yayi ajiyar zuciya ya ce "Ba zan so ce a samo ta ɓangaren ta ba, amma kai na ɗora maka ragamar samowar"

"Za a bincika in sha Allah sir"

"Yayi, ina jiranka, ka ga idan lokaci ya ƙure, aikin da muka yi ya koma baya"

"Haka ne, da yardar Allah ka ci kujerar nan ka gama, mu je injiniyoyin suna can gida suna jiranka, aje ayi lissafi"

"Ok to, Aminu haryanzu ya ƙi zuwa ko?"

"Wallahi yaƙi, Allah da wani wanda zai iya yi mana irin kasadar da yake ɗauka, da mun canza shi, ɗan rainin hankali ne, ko fushi yake saboda wannan karon ba ka fito da shi ba?"

"Da fushi yake yi, ba zai ɗauki wayata ba, kuma ina son aiki da shi, ba ya jin kasada komai zafinta kuma ba shi da mgana ko kisan kai zaka yi a gaban sa, sai ya ga dama zai ɗaga kai, balle ka ji zancen a waje. Sannan babban abun shi ne, bokan nan ya ce nasarata tana tattare da wanda yake zubar mini da jini, na riƙe shi sosai, shiyas nake shanye iskancin sa".

P. A ya ce "haka ne ya na da amana, ba shi da magana sam, amma shi ya san da hakan ne?".

"Haba dai, hauka nake yi na bari ya sani, ba abun da ya sani, kawai aiki yake yi mini"

Misalin ƙarfe huɗu da rabi na yamma, manyan injiniyoyi ne zaune a falon indabo, suna ta lissafin ginin plazarsa.
Ga wanda zai tattauna da su a kan harkar yaƙin neman zaɓensa, suma su na jiransa.

Al'amin yana cikin falon, ana ta lissafi, shikuwa yana hakimce yana kallon tv.

Sai da aka gama lissafi, za ayi total ɗin kuɗi, Al'amin ya kalli shugaban engeneers ɗin ya ce "Kayi plusing da kuɗin siminti buhu shida, da tiles carton biyar"

Ya ce "Na menene?"

"Ina ruwanka, ka saka kawai".

Injiniya ya kalli Indabo, Indabo ya ce "Kuɗi ka ke buƙata ne na baka?"

"Gyaran gidana zan yi nima"

Indabo ya ce "Engeneer a rubuta, a bashi"

Al'amin ya sake cewa "Akwai yarana mutum biyar, da nake son a saka mini su a cikin aikin ginin nan, su yi su ma a sallame su"

P.A ya ce "An gama mai dogon zamani"

"Zamu zo tare da su, ni ne cikon na shida, da ni za ayi aikin a biyani"

P.A ya sake cewa "Ba ka da matsala"

Aka gama aka sallami injiniyoyi, 'yan jami'iyya suka shigo, duk yana zaune, aka gama meeting.

Duk sai da suka gama, sannan Indabo ya mayar da hankalinsa da Al'amin ya ce "Mai zamani" ya ɗaga ido ya kalli indabo.

"Akwai tafiya da zan yi ƙaddamar da takarata, a yammacin garin nan, ina buƙatar tawagar ka kai da mutanen ka, saboda ban san ya zata kaya a wurin ba, 'yan sandan nan gaibu ne wasu lokutan".

"Yaushe ne?"

"Nan da kwana goma"

"Cikin azumi kenan?"

Indabo ya ce "Eh"

"Allah ya kaimu, baka da matsala"

P.A ya ce "Allah ya ƙara maka nisan zango mahadi mai dogon zamani. Ina matarka kuwa?"

Da sauri ya kalli P.A ya ce "Kamar ya ina matata, meye haɗinka da ita?"

"A'a babu komai, lokacin da kana tsare ne, ta zo ita da Walid, ko da yadda za ayi ka fito, lokacin honorable baya nan"
Viper ya yi shiru bai sake cewa komai ba.

Wata ƙatuwar mage ce ta shigo, da matasan 'ya'yanta, fara tas kana ganinta ka san 'yar waje ce.

Al'amin ya tashi ya nufi in da take, ya saka hannu ya ɗauki guda ɗaya ya ce wa P.A "Wannan mace ne ko namiji?"

"Namiji ne"

"Zan tafi da shi"

P.A ya ve "Ka san kuɗin abun nan kuwa? Ya kai dubu ɗari shida fa, wannan ƙaramin".

"Da gold aka yi shi ne?" Yayi maganar yana nuna ɗan muzurun da yake ta ihu saboda ya ji matsa.

Indabo ya ce "A'a ɗan Germany ne"

"Tun da ba daga aljanna ya zo ba shikenan, kai kawo leda na saka shi" yayi maganar yana kallon mai goge-goge.

"P.A ya ce wace irin leda kamar zaka ɗauki masara, kwando dai za a baka.

Yayi ƙerere, aka kawo masa kwando, ya saka muzurun ƙato da shi fari, jikinsa cunkushe da gashi mai kyau.

Ya kalli Indabo ya ce "Zan tafi"

Indabo ya yi murmushi ya ce "Ga abun kuɗi nan ka ɗauka a hannunka, ai ba sai an sallameka ba"

"Za a sallame ni ko in tafi?"

"P.A sallame shi"

P.A ya buɗe jaka, ya ɗebo kuɗi ya miƙawa Viper.

Al'amin yayi masa wani mugun kallo, indabo ya ce "Ƙara masa"

"Ya ƙara ɗebowa, ya ƙara masa"

Ya karɓa ya ce "Na karya wani yaro, yana emergency, babar yaron tayi maganar a kamani, a bi wa ɗanta hakkinsa, yana can a emergency asibitin tsakiyar gari, a kashe wutar, ko ta ƙone yiwuwar aikinka, hankakin nan suka yi ram da ni, ba zan yi aikinka ba" daga haka ya fice daga falon.

P.A ya ce "Kai, honorable Mai zamani yana hawa kanmu da yawa wallahi, wai sai abun da yake so za a din ga yi yayi ta yi wa mutane tunƙaho?"

Indabo yayi murmushi ya ce "Rabu da shi lokaci ne, bari a ci zaɓen, ai ka ga mutumin can ya ce akwai nasarar mu a tattare da shi, yanzu abun da za ayi, ka koma ka yi waya, ka saka a haɗa wata tawagar ta 'yan daba, da zasu far mana a wurin taron, yadda za a samu a zubar da jinin shi ma a can. Sannan ka tara mana 'yan media, idan hakan ta faru a ce abokan adawa ne suka yo hayar 'yan daba suka far mana".

"An gama honorable, yanzu kuwa zan je na tara su na sanar musu tun yanzu"

"Yauwwa, idan ka gama da su, a hanzarta ko aike ka yi wurin wanda ya karya ɗin, a rufe bakin babarsa"

"Ok sir"

***
Al'amin ya koma gida, ya tarar da Jauhar da maƙwabta, tana yi musu kitso.
Yana shigowa hannunsa riƙe da ledoji, ta tashi tana murmushi, suka gaishe shi, babu wanda ya amsa sai sannu zuwan da tayi masa ya amsa.

Ta miƙe hannu za ta karɓi kwandon, ya ce "Banda wannan" ya shiga falo da shi.

Ta dudduba kayan, kayan abinci ne wata irin ajiyar zuciya ta sauke, tare da yi wa Allah godiya.

Allah ya sa ta gama kitson, ta sallame su suka tafi, ta shiga falon hannunta riƙe da cup ta risuna ta miƙa masa. Ya karɓa ya ga zoɓo mai sanyi, sai ƙamshi yake yi. Ya kafa kai ya zuƙe ya miƙa mata kofin ta ce "Ba ka ce ba"

Ya ce "Alhamdilillah" tayi murmushi ta ce "Sannu da zuwa" ya jinjina kai ta ajiye kofin, ya jefo mata muzurun nan a jiki, ta saki ihu tana tsalle,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login