Showing 45001 words to 48000 words out of 152254 words
da Nabila ta gaya mata, a kanta, ya sanya ta tashi da sauri tana murmushi ta ce "Barrister Naja'atu Bunkure, baya goya marayu, dama zan ganki ido da ido?" Sumayya ta yi maganar tana murmushi.
Kamar ta ga kashi, ta yatsuna fuska ta ce "Sannu".
Sumayya ta maze ta ce "Na tsinci dami a kala yau, ni ƴar jarida ce, a cikin ayyukan da ki ke gudanarwa, zan so yi miki tambaya ɗaya zuwa biyu, na san masu sauraronmu, za su ji daɗin hakan, kasancewar ki abar so da koyi ga al'ummar mu, mussaman mata. Dan akwai sister na, die hard fan ɗin ki ce, ita ma lawyer ce.
Cikin fusata Naja'atu ta ce "Ke saurara mana, daga ganina sai tsare ni ki hau zuba dan kina ƴar jarida, who permits you to do that?"
Sumayya ta dake ta ce "No, barrister, ba as ƴar jarida ba kawai, as a woman and one of your fans, ko ƙorafi ne da ni, ta yaya zan same ki ki tsaya mini, atleast ko mintuna uku ki bani mana, dan Allah. Na san ƴan jarida wasu lokutan mu na da zaƙewa amma a duba roƙona" kamar ta zagi Sumayya, ta tsani baƙin naci irin na ƴan jarida, amma sanin halin su na yanzu sai su samu abun ɗorarwa ta ɓata mata career ya sanya ta danne ta ce "Ina jin ki"
Fitowar honorable, ta sanya ta yin shiru, ya kalli sumayya ya ce "Mu je in da zaki ɗauki program ɗin"
Tana ji tana gani, Naja'atu ta tafi.
Can wani surƙuƙi ya ja ta, da sai da ta fara jin tsoro, sai dai duk in da suka ratsa, akwai ma'aikata.
Sumayya ta sha mamakin, irin dukiyar da aka yi ɓarna, wurin gida wannan gida da kamar ba za a mutu a bar shi ba.
Daga ita sai shi a ƙaton falon, mai ɗauke da ɓangarori daban-daban.
Yayi mata iznin zama, yana ƙureta da idonsa, ta fito da kayan aikinta, ta fara saitawa, tana ta addu'a a zuciyarta, dan kaɗaicewar nan ta su kawai, hankalinta a tashe yake.
Nabila kuwa, Walid sakata yayi a gaba, har suka zo ƙofar wani gida, a can bayan kamfanunukan nan, babu kowa a wurin, ba gida gaba babu a baya, sai ma wani uban dutse idan ka yi tafiya can gaban gidan, ba ta taɓa zaton akwai irin wannan wurin a kano ba.
Ya kalleta ya ce ta shiga.
Jikinta yana rawa ta ce ba zata shiga ba, sai dai ya kira wo mata shi nan waje, wanda har a lokacin idan ta ganshin, ba ta san me za ta ce masa ba, tsabar fitina ce da son ta ɗaukaka ko ta halin ƙaƙa ya sanya take wautar.
Wani makami ya zare mata, mai kama da kibiya ya buga mata tsawa ya ce "Ki shiga na ce" sai a lokacin ta tabattar da ta tafka babban kuskure, haɗi da wauta mara amfani, idan suka illata ni fa?" Ta tambayi kanta cikin tashin hankali, haka ta shiga, yana bin ta da wuƙa.
Ɗan mama yana ɗan matsakaicin tsakar gidan, yana wankin kayansu, jin kukan mace ya sanya shi ɗaga ido, cikin tsananin mamaki.
Sai dai yayi wata irin zabura ya ja da baya, yana bin su da kallo.
Yana cikin ɗaki a tsaye ƙyam, kamar an gina shi, ya bawa ƙofar baya, yana kallon bango. Ya sha ya bugu, amma bai samu yadda yake so ba, tunanin da yake son dainawa ya kasa, dan haka yana tsaye, yana ta nazarin abubuwa daban-daban a cikin ransa.
Ɗan mama biyo su yayi, yana bin Nabila da kallo.
Turus Nabila ta yi, duk da ba ta ga fuskarsa ba, amma yanayin suffar jikinsa, sai da ta ji tamkar ta zunduma ihu, kallo ɗaya zaka yi masa ka san madakin maza ne, ingarman namiji ne, da Allah ya yi shi da tsawo da kuma kakkauran jiki.
Idonta ya sauka a kan miyagun makaman da suke ɗakin, kamar za aje yaƙin duniya, gefen katifar da take ɗakin kuma, sirinjai ne, da kwalaban allura a wurin, sai kuma satchets na magunguna da kwalabe da kwalayen sigari. Ban da warin sigari, da wani irin ƙauri da ba ta gama tantance ko na menene ba, babu abun da yake tashi.
Tirƙashi! Ai ko lokacin da aka rufta ta, aka turata dabar madaki, ba ta ga abun da ya razanata ba, kamar yanzu ba, dan tarin ƴan dabar da ta tarar na su wasa ne, ba su firgita ta ba, tun da ta samu ƙwarin gwiwar yi musu magana.
"Boss, ga ta na kawo maka ita, sai ka ji dalilin da ya sa take nemanka"
Babban abun da ya ƙular da Viper, bai wuce watsi da umarninsa, da Walid yayi ba, tun da fari ya gargaɗe shi, a kan kawo masa wata mace, dan ba shi da alaƙa da su, amma ya yi burus da maganar sa.
Kasancewar ya sha sai dai buguwar ta gagara yadda yake so, ya sanya ƙwayoyin suka taimaka wurin tunzura shi, ya waiwayo a fusace domin ya sauke wa Walid rashin mutunci.
Sai dai gabansa yayi wata irin mummunar faɗuwa, adadin bugun zuciyar sa ya ƙaru da sauri da sauri, wani irin gumi ya fara tsatstsafowa ta kafafen gashin sa, jijiyoyin jikinsa suka kukkumbura.
Shi dai ya san a farke yake, ba iya bacci yake mai nauyin da zai ɗauke shi, har ya sa shi mafarki yake, balle ya ce mafarki ne, kuma ya san a hayyacinsa yake, domin kuwa bai yi buguwar da hankalinsa zai gushe ba.
Sai dai a zahiri, sam yanayin sa bai nuna irin halin da ya shiga ba, dan babu abun da ya canza a tattare da shi, ya zuba mata manya-manyan jajayen idanunsa.
Tirƙashi! Jin ka ya fi ganinka! Nabila za ta iya cewa, tun da Allah ya sa ta buɗi ido a duniya, ba ta taɓa ganin mutum mai kwarjini da razanarwa kamarsa ba, kodayake ai ya wuce ta kira shi kwarjini, sai dai mai ban tsoro.
Yadda ake faɗarsa a baki kawai, ta ɗauka wani ƙaramin alhaki ne kawai, sai dai yanzu ta tabattar da ya wuce duk yadda ta yi tsammanin ganinsa sa.
Ashe waɗanda take gani ƙaryar daba suke yi, ga ɗan daba na gaske yau ta gani,kamar ta fashe da kuka a cikin zuciyarta ta ce "Na shiga uku, wani tsautsayin ne ya kawo ni? Daga ni sai su idan suka kashe ni fa? Na san ko gawata ba za a gani ba, balle ayi mini salla, kamar yadda addini ya tanada"
So take ta ɗaga ido ta kalle shi, amma abu ya gagara, saboda daga kallo ɗayan da ta yi masa, ba ta fatan sake yi masa na biyu, duk da zuciyarta na azalzalar ta, ta sake yin hakan, ba zata iya tantance abun da take gani a cikin idanuwanta ba, da kuma ma'anar irin kallon da yake yi mata ba.
Ƙoƙarin sake satar kallonsa tayi, amma suka yi ido huɗu, tayi saurin sunkuyar da kanta ƙasa, saboda mummunar faɗuwar gaban da ta ziyarci zuciyarta, tabbas cikakken mashayi ne duba da yadda launin idanunsa suke, sai dai Allah ya yi shi da siffar girma da cikar zati, ya isa a kira shi da cikakken namiji.
"Shi kuwa wannan meya haɗa shi da aikin daba, a irin ƙira da Allah ya yi masa, da aikin office ya dace, ko na tsaro, ya ɓata wayonsa, da ya ƙare a shaye-shaye da daba.
Duk da ta sunkuyar da kanta, a tsakiyar ƙirjinta take jin kallon da yake yi mata.
Walid ya zagaya saitin kunnensa ya ce "Ka ga abun da nake gaya maka?"
Jinjina masa kai kawai yayi, taku ɗaya yayi, ba tare da Nabila ta ankara ba ya danƙi wuyanta.
Ba wani riƙon kirki yayi mata ba, amma idanuwanta suka yo waje, jikinta ya hau kyarma, tamkar ana kaɗa mata gangi.
Ta saka hannunta ta riƙe nasa, numfashinta na fita da sauri da sauri, cike da tsoro take ta gwagwarmayar ƙwatar numfashinta, saboda yadda take jin yana barazanar barin ƙirjinta.
Ba ta ƙara tsinkewa da lamarin ba, sai da ta ji tsini a cikinta, ga wani irin azababben zafi da ya ratsa fatar cikinta.
Ba ta san bata tsorata ba, sai da ya buɗe baki yayi magana.
"Wacece ke? Me ki ke nema a wurina?!!"
Numfashinsa ya sauka a fuskarta, warin sigari ya daki hancinta, jikinta ya hau tsuma.
A rikice Walid ya ce "Boss zaka kashe ta fa, ka kalli abun da ka ke yi"
Bai saurari walid ba, ya sake buga mata tsawa, tare da ƙara nutsa wuƙar da ya saita a cikinta.
"Viper, jini ya fara zuba daga cikinta, ka dawo hayyacinka mana" yayi maganar yana ƙoƙarin kai hannu ya ƙwace wuƙar hannunsa.
Idan ka taɓa ni, kai zan cakawa!" Yayi maganar yana kallon idon Nabila da suka yo waje, ga jikinta ya saki, sai numfashi da take yi da kyar.
Buɗe baki tayi, da niyyar ta yi magana, amma jikinta ya saki, ta daina ganin komai sai duhu.
"Viper kar ka kashe yarinyar nan" Amma kan walid ya yi wani yinƙuri, Viper ya watsar da ita a wurin, ta faɗi sumammiya.
Ayshercool
08081012143
*ƘARFE A WUTA*
AISHA ADAM AYSHERCOOL
Arewabooks : ayshercool7724
Watpad: ayshercool7724
What's app :08081012143
What's app channel
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
Paid book ne ₦500 via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda ba ss som group akwai special 1k.
13
Cike da takaici Walid ya nufeta da sauri, ya kalli Viper ya ce "Amma meyasa zaka yi haka? Da ka kasheta fa?"
Aminu ya kalli saman tsinin wuƙarsa da take ɗauke da jinin Nabila, bai kalli Walid ba ya ce "Ban gaya maka kar ka kawo mini kowa ba?"
Walid ya ce "Ka gaya mini, amma na tabatta ka ga abun da nake son ka gani, ai ko?"
"And so, me hakan zai amafana mini? Ka ƙaddara ban ga komai ba, kuma gargaɗi na yi mata a kaina, dole na san tana da manufar son haɗuwa da ni, wataƙila wata ƙulalliyar ce, sai dai amafani da mace ba zai hana in illata ta ba, idan ta shiga gonata"
Walid ya ce "Yanzu abun da ka gani, ba shi da muhimmanci kenan?"
"Ko kaɗan" ya bashi amsa kai tsaye.
Walid ya tsuguna a kanta, amma ya rasa abun da yakamata yayi.
Wani irin numfashi Nabila ta fara fitarwa, mai sauti wanda hakan yake tabattar da, numfashin yana ba ta wahala.
Ɗan mama ya ce "Mun shiga uku, wane irin numfashi ne wannan,ko mutuwa za ta yi ne?" Walid ya sake dirircewa ya rasa abun yi.
Viper ya goge jinin Nabila da ke jikin wuƙarsa, a jikin rigarsa.
Ya ɗaga kai, yana kallon yadda take jujjuya kanta, tana neman iska.
Wata drower ya saka mukulli ya buɗe, ya ɗaukko wata ƴar ƙaramar akwati, ya ajiye, ya ƙarasa ya ɗauki jakar Nabila, ya zazzageta yana neman inhaler, amma bai gani ba, ya ja uban tsaki ya tashi, ya sake buɗe wardrobe, ya ɗaukko inhaler, sai dai sai da ya tsaya yayi ta kallon inhaler, yana kallon Nabila, sannan ya ƙarasa kanta, ya tsaya, ya ɗagota ya fesa mata a cikin bakinta.
Kamar zata haɗiye inhaler, haka take sake buɗe bakinta, ya mayar da ita ya kwantar, ya ɗaga gefen rigarta, da wuƙarsa ta huda, ya saka auduga da spirit, ya goge jinin tsaf, ba wata huda ce ta kirki ba, kawai dai ta zubar da jini ne sosai.
Gaba ɗaya suka zuba masa ido, ya zuba iodine a jikin audugar, ya saka a kan cikin nata, ya kawo plasta, ya saka.
Dama ya saba yi musu dressing, idan suka je aka sare su, a wurin rashin jin su.
Ya mayar da akwatin in da take, ya koma gefe ya kunna sigari. Mamaki yake da tunanin, uban me take nema a wurinsa, sai dai ya fi yarda da cewa, tarko ce ake son yi masa da ita.
"Amma ya aka yi, aka samu wannan coincidence ɗin?" Ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa.
Duk suka koma gefe, suka zubawa sarautar Allah ido.
Tari ta fara yi, ta yinƙura ta tashi zaune, ta kalli kayan cikin jakarta, da suke a watse, ta fara tattara abun ta, sai kuma ta dawo hayyacinta,bayan da suka yi ido huɗu da shi.
A rikice tayi jifa da jakar, ta ƙwala wani uban ihu, nan take mafarkin da ta taɓa yi ya dawo mata, tabbas sai yanzu ta fuskanci inuwarsa take gani a mafarki.
Ƙoƙarin tashi take ta gudu, cikin zafin nama, ya bar in da yake ya cafkota.
Tausayinta ya kama Walid, tare da dana sanin kawo wa Viper ita, ko haɗa bakin aka yi da ita a cutar da shi, atleast ita macece ya ɗaga mata ƙafa, amma ya san in da ya matsa, sai Viper ya illata ta fiye da yanzu.
"Waye ya aiko ki?" Yayi maganar a kausashe.
Ta girgiza kai, amma ta kasa magana.
"Waye ya turo ki na ce?" Yayi mata tsawa.
A rikice ta ce "Wallahi ba kowa" tayi maganar tana zubar da hawayen tsoro.
"Me ki ke nema a wurina?"
"Dan Allah ka yi mini rai, na tuba na bi Allah, ba zan sake ba, dan Allah kar ka kasheni, wallahi ni marainiya ce, tayi maganar tana kawar da kanta gefe, ta kasa kallonsa, sai azabar bugu da zuciyar ta take yi, cikin tsoro da fargaba.
"Look up kalleni" muryarsa ba a iya kunnuwanta take jin ta ba, a tsakiyar zuciyarta take yi mata amsa kuwwa, gashi ya matso daf da ita, warin sigarin da yake yi, ya fara hautsina mata ciki.
"Kalleni" ya sake maimaitawa.
Ɗan mama ya ce "Ki bi umarninsa, ba ya maimaita magana, kan ki farka a lahira".
Cikin karkarwa, ta ɗaga kanta, da gefen idonta kawai ta kalleshi, amma ta fashe da kuka "Wallahi tsoronka nake ji, ba zan iya kallonka ba, idonka tsoro yake bani, dan Allah ka yi haƙuri kar......
Tsit tayi, ta haɗiye wani irin mugun yawu, da ta ji tamkar ta haɗiyi wuta, biyo bayan ganin ya saita kaifin wuƙa a kwaroron maƙogwaronta.
"Idan ki ka bari, na sake ganin fuskarki, ko a kan hanya, Wallahi sai na kashe ki!"
Nabila ta gama saddaƙar da gumin da yake bin ƙafafuwanta, fitsari ne ba gumi ba, gashi tun daga goshinta, har cikin jikinta gumi ne kawai yake yanko mata ko ta ina.
Ta jinjina masa kai, ya ja da baya, ya kalli Walid ya ce "Ta ƙara mintuna biyar a gabana, sai dai ka fita da gawarta"
Walid ya kalleta ya ce "Zo in fitar da ke hanya"
"To in ɗauki jakata?" Tayi maganar cikin tsoro.
Walid ya ce "Hanzarta ki kwashe kayanki mu tafi"
Sai dai ta kasa motsawar, ta ƙame a jikin bangon ɗakin, jikinta sai tsuma yake yi.
A fusace Walid ya ce "Ki tattaro mu tafi mana"
Nabila ta fashe da kuka, ta ce "Wallahi tsoro nake ji, kar in durƙusa ya kashe ni, dan Allah ka bashi haƙuri, kar mu haɗu a wani wurin ban sani ba ya kasheni, ya rantse sai ya kasheni".
Walid ya ce "Na ji zan bashi, taho mu tafi"
"Wallahi na kasa motsi" tayi maganar hawaye na cigaba da zuba daga idonta.
Gaban wardrobe ya je ya tsaya, ya juya musu baya, ya saka hannayensa, ya kama ƙasan rigarsa zai cire ya canza wata, kamar wadda ya kwance daga ɗauri, dama idanunsa ne igiyoyin da suka ɗaureta, ta durƙusa ta kwashi kayan jakarta, da jakar ta fita da gudu, ta kwashi takalmanta, ta fyalla a guje, ta bar gidan.
Dariya ɗan mama ya ƙyaleƙyale da ita, ya yi wata irin ashariya ya buga ƙafa, sannan ya je gaban Viper yayi wata irin kururwa, cikin sara masa tare da kambama shi ya ce "Maza gumbar dutse, ina gwanin wani ga nawa, gaba salamun baya salamun mutumina, zaki ka ke sarki a gida sarki a dawa, ina mazan suke, ga fa uban ɗakina wanda ake kira namijin gaske. Sun buga da kai sun barka mutumina, Allah ya baka duniya lahirar ma ka samu in sha Allah. Mahadi mai dogon zamani. Kai idan ba namijin gaske ba, kalli yadda ka mayar da mai hankali zararre cikin ƙanƙanin lokaci, kalli yadda yarinyar nan ta firgice ta koma zararriya lokaci ɗaya, ba gaba da gaba ba ko ta baya sai an shirya tararka uban gidana, mahadinmu mai dogon zamani, Allah ya baka tsawon rai, ya kaimu ranar da zamu ba da jininmu domin ɗaukar maka fansa"
Geɓare baki Viper yayi kamar zai yi murmushi, dan kirarin ya tuna masa wasu abubuwa da dama da suka shuɗe.
Walid kuwa gaba ɗaya daga Viper har ɗan mama haushi suka bashi, kamar ya ɗura musu ashar, Nabila ko da cunen aka yi musu da iya, shi yaƙi ai ɗan zamba ne, kuma ko ba komai mace ce, bai kamata ya razanata har haka ba, tun da ya san mazan ma razana su yake yi.
Takalmansa ya saka, ya bi bayan Nabila, dan yadda ta fita a burkicen nan, komai zai iya faruwa, gashi ga dukkan alamu, ba ta da cikakkiyar lafiyar numfashi.
Viper kuwa, rigar jikinsa ya canza, Ɗan mama ya ce "Boss, wai ka taɓa karatun likita ne? Na san dai ka iya wankin ciwo, to kuma na ga yau kayi aikin likita".
Al'amin ya girgiza kai ya ce "Ko ɗaya, na zauna da mai irin ciwon ta ne"
Ɗan mama ya ce "Na fahimta, amma dai ba fita zaka yi ba ko?"
"Zaka hana ni ne?"
Da sauri ya ce "A'a wane ni, ka san idan wannan jarababben ya dawo, ya tarar ka fita, masifa zai ta yi mini" bai saurari ɗin mama ba, ya bi ƙofa ya fita.
Nabila kuwa tun da ta fita da gudu, ba ta tsaya a ko ina ba, sai da ta fita titi, shi ma babu ababen hawa, haka ta cigaba da tafiya tana waige-waige, sai a lokacin ta ji gefen cikinta, yana ta yi mata zugi, ta ɗaga rigarta ta ga plasta.
Ga jikin rigarta da jini, a hankali ta furta "Na shiga uku"
Addu'a ta din ga yi, tana cigaba da tafiya, cikin ikon Allah, Allah ya kawo mai a daidaita sahu, ta kama ta shiga, tana ta haki.
Sumayya tamkar yau ta shiga harkar aikin jarida, haka tattaunawar ta su da honorable Indabo take kasancewa, saboda yadda ya tsatstsareta da manya-manyan jajayen idanunsa, yana yi mata wani irin kallo, gashi daga shi sai ita a wurin.
Ajiyar zuciya ya yi ya ce "Meyake damunki ne? Ki nutsu mana"
Ta jinjina masa ta kai, ta cigaba da yi masa tambayoyin da su aka yarje mata ta yi masa.
Sai dai ita kanta ta san amsoshin da yake bayarwa, na son zuciyarsa ne kawai, ba wani abu ba.
Jin ta yi shiru, ya sanya ya kalleta ya ce "Ya dai?"
Cikin girmamawa ta