Showing 81001 words to 84000 words out of 152254 words

Chapter 28 - ?arfe A Wuta Book 1 Hausa Novel Complete

15 Dec 2024

628

dan ta ganshi? Ya basar ya shiga ya yi abun da zai yi ya fice.

Sai a yanzu ta fara gazgata lallai wannan ne mai gidan, shi ne mijin da aka aura mata.

Cikin kuka ta ce "Allah komai ka yi dai-dai ne, Allah ka sanya shi ne mafi alkhairin da nake ta fata". Ta sanya wa zuciyarta za ta yi ƙoƙarin, danne tsoronsa da take ji, amma abun da ba ta gane na shi ne, ba iya abun da ya faru waccan ranar ne kawai yake ba ta tsoro ba, tsananin kwarjinin sa ne ke ƙara rikita ta.

Suna dabarsu, Al'amin yana ta shan sigari, Walid ya ce "Maza, gaskiya abun da ka ke yi baya dacewa, an kai maka mata, amma kullum kana nan kana cakewa, akwai matsala ne?".

Al'amin ya rausayar da kai ya ce "Yarinyar Mahaukaciya ce ashe"

Cikin rashin fahimta ya ce "Mahaukaciya kamar yaya?".

"Kamar yadda na gaya maka, ihu take yi itakaɗai"

Walid ya ce "Ko dai tsorata ta ka ke yi? Ki tsaya kun yi magana kun gaisa?"

Aminu ya ce "Da wa?"

"Da amaryar mana" ya ja tsaki, yana mayar da sigari bakinsa.

"Wallahi Aminu da ni aka yi wa auren gatan da aka yi maka da na more, haba baka kyautawa gaskiya "

Yayi masa shiru, yaƙi ko kallonsa, dan ko zancen auren ba ya son ji, haka kurum ji yake yi kamar an yi masa dabaibayi.

Saifu kuwa yanzu ban da gaisuwa, babu abin da yake haɗa shi da da mama da Baba, dama Babar su hafsa Zakkyya ba shiri suke yi ba, ko kallo ba ta ishe shi ba.

Sai dai sun fara zancen a kawo 'yar aiki, dan duk yawan 'yan matan gidan nan, ba sa iya aikin gidan, girki sai dai a jagwalgwala, wani ya ciwu wani ba zai ciwu ba, gidan nan kuwa wasu lokutan kamar fadar mahaukaciya, dama jauhar ce ana ɓatawa tana gyarawa, yara na cire kaya suna zubarwa tana kwashewa, amma yanzu bata nan babu mai gyarawa.

Baba kuwa ƙasan zuciyarsa yana nadamar auren da ya yi wa jauhar, amma ba zai iya nuna hakan ba, ya duƙufa yana yi mata addu'ar samun kwanciyar hankali a gidan aurenta.

Cikin dare da ya dawo, ya ji gidan a rufe, bai tsaya jiran komai ba, ya kama katanga ya dira kamar ɓarawo.

Gaba ɗaya jauhar a zatonta, itakaɗai ta kwana a gidan, saboda ba ta ji bugun ƙofa ba, ta fito tana ta share-sharenta, ta ɗora ruwan zafin dafa makaroni, saboda su yaya saifu ya sayo mata, taliya makaroni, mai maggi sugar da sauransu.
Ta fara bin ɗakunan tana gyarawa. Sai dai ta din ga jin warin taba, ta rasa daga ina take jin warin.

Kawai ta nufi ɗakin da yake ciki, ba tare da ta san yana ciki ba, ta afka, a zatonta ita kaɗaice a gidan.

Yana kashingiɗe yana zaune yana kaɗa ƙafa yana shan tabarsa, ya zazzage kayansa a kan katifar ɗakin, ghana must go ɗin, ya cillar da ita a tsakar ɗakin. Har da takalma a kan katifar, soson wanka da brush duk suna kan katifar.

Ba wannan ba kawai, har da ledoji da kwalayen taba, ga tokar maganin sauro ko ina.

Kamar mahaukaciya haka ta juya, ta ɗiba da gudu, sai dai a wannan karon, rufa mata baya ya yi, ya cimmata, tana ƙoƙarin rufe ƙofar ɗakin da ta shiga, ya hankaɗa ƙofar ta faɗi jikinta na wata irin tsuma.

Ya zuba mata ido, wanda ya haddasa mata tsuma da karkarwa cikin razani da matsanancin tsoro.

Bai ce mata komai ba, sai cigaba da kallonta da yake yi.

"Dan Allah ka yi haƙuri, wallahi ban gayawa kowa ka kashe shi ba, dan Allah ka yi haƙuri, ni matar aure ce, ka daina shigo mini gida" tayi maganar wani irin gumi na tsatstsafowa daga fuskarta.

Ya sunkuyo saitinta, warin sigarin da ya sha, tana dukan hancinta, sai a lokacin ya gane ta, ya gene a in da ya taɓa ganinta.

"Kin ganni na kashe shi?"

Ta jinjina kai alamar eh.

"Mahaukaciya ce ke? Ki na da taɓun hankali ne?" Ta girgiza masa kai alamar a'a, tana ja da baya.

"Idan ki ka kuma ganina, ki ka gudu kina ihu" ya zaro wuƙa a ƙugunsa, ya nuna mata. Sannan ya ce "Sai na yi miki abun da ki ka ga na yi wa wancan mutumin, wato in kashe ki"

Ta girgiza kai ta ce "In sha Allah ba zan sake ba" ya miƙe, ya mayar da wuƙarsa ya fita ya bar ta.

Wani irin numfashi ta din ga saukewa, cike da tsoro, ta ƙara gazgata cewar, shi ɗin ne dai mijinta ba wani ba.

Ta jima a wurin tana kuka, sannan ta tashi a hankali, ta sake komawa ɗakin da ta gano shi.

Ɗakin yana nan, kamar mahaukaciya ta buɗe dealer, ya watsar da komai, sai warin sigari ɗakin yake yi.

Ta ɗaɗɗaga labulaye, ta zo ta durƙusa ta fara ware kayansa, wankakku da masu datti, ta kwashe takalmansa, ta jera masa a bayan ƙofa, wankakkun kayansa, ta shirya su a cikin wardrobe, marasa wankin ta fita da su, ta share ɗakin tsaf, ta ɗauki brush ɗin sa da toothpaste, ta kai masa banɗakin cikin ɗakin, da bokiti da buta.

Kayanta akwai turarukan wuta, da aka bata na gudunmuwa, sai dai ba ta da gawayi, dan haka ta kunna na tsinke, ta sassaka a ko ina, saboda korar warin sigarin nan. A cikin kayan sa ta ga wata Mp, ta ɗauki mp ta kunna ta ji tana yi, ta kunna radion jiki, ta ji tana yi, ta fita tsakar gida da ita, tana ta aikace-aikace, da zummar kan ya dawo ta kashe ta ajiye masa, ta ɗan ɗebe mata kewa, ta manta ko sallama baya yi kafin ya bayyana.

Gidan su jauhar, akwai maƙwabciyar su Anty lubabatu, tana tausayinta sosai, suna mutunci da juahar, dan idan ta haihu, jauhar ta yi ta zuwa gidanta, dan ta ɗauki yaranta, ita ce ta haɗata da 'yan gidan su, take karɓar shirin dutse tana yi.

Tun washegarin kai jauhar, ta shiga gidan ta ce wa su mama, a bata mutum ɗaya ya rakata gidan jauhar, amma suka ce ba wanda ma ya san gidan.

Jauhar kuwa, ta gama aikinta tayi wanka, gidan babu komai na abinci, sai taliyar nan da macaroni da yaya saifu ya saya mata, gashi sun isheta, sai dai babban abun da yake yi mata daɗi, tana da damar ta dafa ta ci yadda take so, saɓanin idan a gida ta girka, sai ta gama wahalar a sanmata.

Tunani take yi, idan ta dafa taliya yau ma ko zai ci, tana tunanin ko shi ma sun fara isar shi. "Karfa ya ce ko ban iya girki bane, shiyasa kullum nake dafa taliya. To ai gidan bakomai sai su"

Ta ɗan yi shiru, tana tunanin yau bari ta aika a sayo mata kayan miya, tayi da miya, so take ma ta nuna masa kuɗin da kakarshi ta ba ta, amma tsoronsa take ji.

Tana ta tunani, ta ji ana buga ƙofa, cikin murna ta tashi, ta san baƙi tayi sa ɗebe mata kewa.

Anty lubabtu ta gani, maƙwabciyar su, da ƙanwarta wadda take karɓar shirin dutse a gidanta, cikin murna tayi musu maraba.

Allah ya sa tana da ruwan pure water, ta basu.

Ta ce "Anty lubabatu shi ne sai yau zaku zo ko? An barni nikaɗai, ba wanda yake leƙo ni".

"Ki yi haƙuri jauhar, tun washegarin kawo ki, nake sintirin neman mai rako ni a gidanku, wallahi fafur 'yan gidanku da 'yan tsukin nan aka rasa masu zuwa su rako mu, wai tsoro suke ji, 'yan gidanku ma wai ba za su rakomu ba, mijinki ɗan daba ne, ni kuwa na ce ko menene zamu zo, sai kwatance suka yi mana".

Ta ɗan rausayar da kai ta ce "Shikenan bakomai, yaya saifu ma ya zo, daga ni sai yaran maƙwabta, ni kaɗai nake wuni".

Samira ta ce 'Allah sarki, mma dai jauhar ba wata matsala dai ko?"

Tayi murmushi ta ce "Babu anty samira, ya shiri kin zo mini da shi?"

"Taɓ kina amarya, kawai sai na kawo miki shiri?"

Jauhar ta ce "Eh mana, zai din ga ɗebe mini kewa ai, dan Allah idan an samu mai zuwa, ki bayar da yawa a kawo mini, na din ga yi"

Anty lubabtu ta ce "Jauhar iyayen neman kuɗi".

Samira ta ce "Bar ta ta nema, rayuwar nan ba a zama haka"

Miya lubabatu ta soyawa jauhar, mai yawa ta sha naman kaji, da shinkafa da 'yan kayan buƙatu.

Jauhar ta ji daɗin hakan sosai da sosai, ta din ga murna, suka wuni tare har la'asar, sannan suka tafi.

Suna tafiya ta aiki almajiri, ya sayo mata salak da kayan haɗin sa, ta zauna ta shirya salak ɗin nan, ta juye miyar a tukunya, ta ƙara soyata tayi mata gyare-gyare ta ƙara mata su maggi da kayan ƙamshi ta kammala komai.

Ta ɗebarwa yaran da suke shigo mata abincin ta basu, ta ɗebe wani ta rufe, dan abincin da yawa, ta sake turara shinkafar ta zuba a wani flask mai kyau kamar a lokacin ta dafa ta.

Tana aikinta, tana jin radiyo a mp.

Ta bawa yara kuɗi, suka sayo mata ruwa da lemo mai sanyi.

Ta gama aikin, ta share kitchen ɗin, ta kwaso sharar abun da ta ɓata, ta fito kawai ta ga Al'amin a tsakar gida, aikuwa ta razana ta saki abun kwashe sharar tana ihu, ta zubar da sharar a wurin, har zata gudu sai kuma ta tuna kashedin da yayi mata, ta tsaya jikinta yana rawa ta ce "Yi haƙuri, tsorata nayi, ban san ka shigo ba" tayi maganar tana kare jikinta, saboda babu hijjabi a jikinta, bai jira ta gama maganar ba ma, ya shige falo.

Ta daɗe a tsakar gida, ta kasa shiga falon ma, ta lallaɓa ta shiga zuciyarta na bugawa da sauri-sauri, gaba ɗaya falon ya gauraye da warin wiwin da yake yi.

Ba ya falo, ta shiga ɗaki ta sako hijjabi ta fito, sai dai ta kasa zuwa ɗakin da yake.

Wanka yayi ya fito, ya tarar ta ajiye masa sabulun wanka, a cikin wanda ta zo da shi, banɗakin ta kai mas bokiti da ruwa, ga buta ita ma cike da ruwa.
Ya gama wankan, ya ɗora soson a kan sabulun yayi fitowarsa, da zai canza kaya kuwa, duddubawa ya din ga yi, da ya gan su a cikin wardrobe, sai da ya watso su gaba ɗaya ƙasa, sannan ya zaɓi wanda zai saka, ya bar su a wurin ba tare da ya gyara ba.

'yar siririyar muryata ya ji a bakin ƙofar ɗakinsa, tana ta sallama.

A fusace ya ce "Meye ne?".

Ta razana ta ɗan shigo daga bakin ƙofa ta tsuguna, ta ce "Dama tun washegarin kawo ni, wasu sun zo, da kakarka hajiya da wasu, suna nemanka na ce baka nan, suka bani kaya da kuɗi dubu goma, amma na sai maggi da ashana da omo, a ciki baka zama a gida, ban nuna maka ba, shi ne na kawo maka"

Ɗan shiru ya yi, jin ta ce hajiya ta zo, ya ji babu daɗi da bai haɗu da hajiyar ba, dan rabon da yaje ya ganta har ya manta.

"Ga kuɗin" muryarta ta dawo da shi daga tunanin da yake yi.

"Bar nan wurin kafin na yi ball da ke, ba ruwanki da shiga sabgata na gaya miki, tashi ki ware" ta tashi ta ce "Kuɗin fa" banza ya yi mata, ya tsaya yana kallon fuskarsa a mudubin ɗakin.

Ganin ba zai kulata ba, ya sanya ta ajiye masa kuɗin, ta tashi za ta tafi, cikin tsawa ya ce "Ke!" A razane ta waiwayo.

"Kwashe kuɗin nan ki bar nan" jiki na rawa, ta ɗauka ta ce "To bar mini ka yi" mugun kallon da ya yi mata ya sanya, ta juya da sauri ta bar ɗakin.

Ta je kitchen, ta shiryo masa kwanukan abinci a kan tray, amma ta tsaya tana wasi-wasi, kar ta kai masa ya kuma korarta, ta shiga falon tana taradaddi.

Ta na shigowa yana fitowa daga ɗakin, take hannunta ya hau rawa, ta ji tana neman ta saki farantin da kwanukan, ta ƙarasa tsakiyar falon, ta ajiye ta ce "Fita zaka yi, ga abinci" ta juya ta koma kitchen ta ɗaukko ruwan roba da lemo, da ta saya masa ta ɗora a kan wani plate ɗin ta kawo. Tana zuwa taga ya zauna ya kame zai ci abincin, kasancewar yana girmama cikinsa, Al'amin yana son abinci, dan haka ba kowane tayi yake wucewa ba.

Maimakon ya ɗebi abincin, ya zuba a plate, kawai ya buɗe flask ɗin, ya juye salad ɗin a ciki, ya ɗaga flask ɗin miyar ya girgije a kai, ko kallon cokalin bai yi ba, ya zura hannu ya kama kai loma.

Duk da wani irin mugun tsoronsa take ji, amma haka cikin tsoron, ta tsiyaya masa lemo a kofi ɗaya, ɗaya kuma ta zuba masa ruwa.

Satar kallonta ya yi, yadda take komai a nutse, sai dai hannunta rawa yake yi, saboda tsoro, mamaki yake yadda take wani zuba masa ruwa kamar ya sakata.

Ya din ga tunanin ita kuwa wani zunubi ta aikatawa 'yan gidansu, suka zaɓa su aurar da ita ga shi? Gaba ɗaya yanayinta kalar 'ya'yan hutu ce, irin wanda ba sa son wahalar nan.

Sai dai yadda yake auna loma, yana basarwa ba zaka ce, ita yake satar kallo ba.

Ta koma can gefen kujera ta zauna ta yi tsuru, gabanta na cigaba da faɗuwa da zarar ta kalleshi, sai dai duk da haka, a ranta ta ji tana son yi masa magana a kan kakarsa, da sauran tambayoyi, duk da miskila ce, amma idan ta samu wuri akwai hira. Sai dai ko kusa ko alama, ba ta ga wannan fuskar ba.

Kan ta ankara ta gama zancen zucin, ya kawar da abincin cikin kula 'yar tsakiya, shanye ruwansa da lemo tsaf, ta zuba masa ido, duk da ba abun mamaki bane ba, ta saba ganin maza da shegen cin tsiya, dan tsaf Yaya Saifu zai iya cinye cikin babban flask, dan akwai ranar da suka din ga musu da surayya, ya ce zai iya cinye shinkafa rabin kwano a zama ɗaya, dama taliya leda guda yake cinyewa.
Dan haka ba ta yi mamakin yadda ya cinye abincin ba, ya dubi carfet ɗin ta, milk mai haske, ya goge hannunsa a kai ya tashi tsam ya bar mata wurin da kwanukanta a wurin.

A hankali ta ce "Na shiga uku, miya a kan carfet ɗina" da sauri ta kwashe kwanukan, ta ɗebo ruwa da omo, ta goge wurin da ya goge mata hannu a carfet, ta koma ɗakinsa, ta sake kwashe kayan da ya zubar.

Ya watso su duka gaba ɗaya, ya cire na jikinsa duk ya watsar ya ƙara gaba.

Ta sake gyara masa, ta kwaso wanda ya cire, da wanda ta kwashe na wanki ɗazu, ta fito ta jiƙa su zata wanke.

Ta koma ta sake sharo falon, sai dai ta ga leda a in da Ya tashi, ta ɗauki ledar, ta taɓa ta buɗe, tana tunanin ko ita ta ajiye wani abun, amma ta ga wani abu kamar ganye a ciki, ta sinsuna ta kasa gane ko menene, kuma a iya tunanin ta, ba ta ajiye ba. Ta samu wani wurin ta ajiye, ta cigaba da aikinta.

Sallama aka din ga rangaɗawa a ƙofar gida, ta wanke hannunta ta ce "Waye"

Ya amsa da "Ni ne" ta saka mayafi, ta fita ta leƙa.

Wani jibgegen ƙato ta gani, jiki duk a murɗe, duk bai kai girman Al'amin ba ba.

A ɗan tsorace ta ce "Sannu"

Ya ce "Yauwwa, matar gidan tana ciki ne?"

Ta ce "Eh meyafaru?"

"Ɗan je ki ce mata ana sallama da Boss"

Ta yatsuna fuska ta ce "Waye hakan?"

"Mai dogon zamani nake nufi, ba shi ne maigidan ba?"

Jauhar ta ce "Ba wani mai irin sunan nan a gidan nan, ba sunansa kenan ba"

Ya ce "Kee, ni fa nake rako shi har gidan nan, ki ce mini ba sunansa kenan ba?"

Ta tsuke fuska ta ce "To shikenan idan ba ka yadda ba"ta mayar da ƙofa ta rufe.

Walid ya koma gefe ya kira Al'amin ya ɗaga ya ce "Ya mai laya".

Walid ya ce "Na kiyayi mai zamani, maza na zo gidanka wata 'yar cika, ta leƙo ta raina mini hankali, na kusa kwarfeta, na ƙyaleta ne kar na kwafsa"

"Wacece ya aka yi?"

"Kai na zo nema, ina ta jiranka, yaran nan za su karɓi kaya su rarraba, ba ka zo ba, na biyo ka gida, wata jar yarinya nunar rana mai kama da 'yan china ta ce mini wai ba mai irin sunanka a gidan, na ce mata mai zamani wai ba gidan ba ne"

Al'amin ya ce "Ita ce matar gidan fa"

"Kai haba maza, wannan ɗin?"

"Yarinyar da ta suma, na ce ka saka a kaita Asibiti"

Walid ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, maza ka sha kwana wallahi, dama ita ce, kaga rabo, wata 'yar caras beauty ka ji muryarta".

"Kai dalla malam, ka buga mata ƙofa, ka ce ta duba in da na tashi, na bar leda ta baka, ka tsaya shirme".

Walid ya ce "To meye na yi mini masifa kuma, na ga dai auren dole aka yi maka" katse wayar walid ya yi, yayi ashar ya ce "Ina da wannan, ai kan a ganni a ƙofar gida, sai an sha wuya, kai Aminu kamar ba biladam ba" yayi maganar yana bubbuga ƙofar gidan.

Kamar ba zata buɗe ba, ta sake buɗewa cikin mamaki ta ce "Malam lafiya?"

"Ya ce ki duba in da ya tashi, ya manta leda ki bani"

"Shi wa?"

Cikin mamakin yadda take neman raina masa hankali ya ce "Maigidan"

"Dan Allah ka yi haƙuri, bai bar mini wannan sallahun ba"

Ya ce "Saboda bai bar miki sallahu ba, ba zaki bayar ba?"

Ta marairaice ta ce "Idan na baka ya dawo, ya ce mini ba shi ya aikoka ba, kaga bani da abun da zan ce masa".

Ya ce "Gaskiya ne, shikenan" ya juya ya tafi, ta mayar da ƙofar ta rufe.

Duk da kayan suna da nauyi, haka ta zage ƙarfinta a kan kayan nan, ta wanke su.

Sai a lokacin ta kalli window, ta ga mpn da ta ɗaukko masa ta ce "Na shiga uku, da ya ganta fa me zan ce masa?" Ta ɗauka ta mayar masa ɗakinsa

Al'amin kuwa duk in da ya juya, sai dai ya yi gyatsa saboda yadda ya ƙoshi.

Walid ya je ya samu Al'amin, ya  din ga yi masa mitar yadda jauhar fafur ta hana shi saƙon nan. Yayi ya gama, bai ce masa komai ba, sai sakace da yake yi, yana cigaba da jin ƙamshin miyar da ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login