Showing 33001 words to 36000 words out of 152254 words

Chapter 12 - ?arfe A Wuta Book 1 Hausa Novel Complete

15 Dec 2024

331

yana rawa, taga ya fara tunkaro ta.

Ta ja da baya ta miƙa masa ruwan, amma ya haɗa da hannunta ya riƙe.

"Dan Allah ka sakeni, in ƙarasa aikina"

Babu tausayi ko imani, ya ce "Nawa aikin zaki fara yi tukuna, kafin nata"

Ganin akwai alamun ƙarfi a tare da ita, ba zata tsaya ba, ya sanya ya gaura mata wani lafiyayyen mari. A take hancinta ya fara zubar da jini.

Ta ƙwala ihu, ya sake buga kanta da cabinet na kitchen, goshinta ya fashe, nan ma jini ya hau zuba, ga goshi ga hanci, dan haka ta kasa magana, jikinta ya saki.

Haka ya keta mata haddi, ta hanya mai muni da rashin tausayi ya tashi ya fice ya barta.

Idonta biyu, amma ta kasa taɓuka komai, ko ɗaga hannunta ta kasa yi.

Zulai ce ta dawo ta tarar da ita cikin mummunan yanayi, a rikice ta fita ta kira ɗaya daga cikin masu gadin gidan, suka ɗauke ta suka kaita Asibiti.

Aka ƙi karɓar su, sai da aka kira matar gidan aka sanar mata, suka yi magana da likitoci ta waya.
Sai dai duk abun nan, ramma ba ta san ko sunansa ba, balle ta san ɗan waye shi.

Kafin matar gidan ta dawo, ta aiko a bawa ramma kuɗi, a bata haƙuri su koma ƙauye, ko warkewa ba ta yi ba aka sallame su, shi ne mamanta ta ɗauke ta suka tafi gidan radiyo.

Ramma ta bawa barrister labarin komai, tana kuka mai taɓa zuciya, goshinta ga ɗinkin da aka yi mata a asibiti, ga na ƙasanta da yake addabarta da raɗaɗi.

Tayi ajiyar zuciya ta ce wa mahaifiyar ramma ta shigo.

Bayan ta shigo ta zauna, ta kalle su ta ce "Baiwar Allah, dan cuta na san an cutar da ku, amma za ki sake jefa kanki a halaka, gara ku yarda ayi masalaha.
Babu wata kotu, ko wani alƙali, da zai tsaya miki ya ƙwato muku hakkinku, saboda yaron nan ɗan gata ne gaba da baya, ubansa suke da ƙasar.
Dan haka ki yi haƙuri, a baku wani abun, ki samu ku sai abinci, a kuma kaita asibiti, idan ta warware ta koma makaranta.

A take ramma ta fashe da kuka, mahaifiyarta ta ce "Haba baiwar Allah, shikenan bawa dan talaka ne, ba zai samu adalci ba, kuɗi zasu ƙare, mutuncin ƴa ta fa? ni gaskiya so nake a karɓa mata hakkinta".

Barrister tayi shiru tana zancen zuci "Ko yaushe mutumin ƙauye ya wani san ƴancinsa? Da matar nan take zaƙewa?'

"Naira miliyan uku za a baku, kuɗi hannu, ki yi tunani zan sake dawowa. Idan kuma kun ƙi, zan cire hannuna, duk matakin da uban yaron ya ɗauka a kanku babu ruwana, ina sake gargaɗinki, babu ke babu magana da wani ɗan jarida ko makamancin haka, idan kunne ya ji jiki ya tsira" ta ciro kuɗi a jakarta, ta ajiye musu, ta tashi ta fice.

***
Kamar zai tashi sama, saboda tsananin tashin takaici da haushi, ya ce "Madaki, wace irin shiririta ce wannan ku ka yi, ta yaya zaku bari, jami'an tsaro su sake kamaku?"

Cikin muryarsa da ta riga ta fashe irin ta mashaya ya ce "Kai ka san ba laifinmu ba ne ba, wani banzan bakware aka kawo mana, kai zaka tsawatar, ka saka a sake su, dan idan babu su babu aikin nan"

"Shikenan, na ji, ka saurare ni da kyau, zuwa hankali ya riga ya kwanta, mutane sun manta da abun da ya faru watan baya, ina son a cigaba da yi mini aikina, amma a wannan karon yankin yamma da gari zaku je, yaron kar ya wuce ɗan shekaru goma zuwa sha biyar, jininsa nake buƙata, a zuba a babban dam ɗin da yake rarraba ruwa a yankina, tun daga mazaɓata, sai ku kawo mini ƴan marainan yaron, da hanjinsa. Sa'ar aikin ranar laraba ce bayan al'muru. Idan kujerata ta cigaba da tabattuwa kuma zaku mora"

Madaki ya ce "Wannan ba zai yi wahala ba, ka huta kawai, kujerar nan ko an so ko an ƙi, mai hawanta sai bayan ka mutu honorable"

"Eh, amma ba yanzu zan mutun ba ai, sai an kwana biyu tukuna, zan aiko maka kuɗi, ayi abun da yakamata larabar tsakiyar wata za ayi, yaranka kuma za a sake su"

"Sai da kai honorable, ka ci dubu sai ceto"

"Yauwa yayi".

Nabila kuwa sannu aka din ga yi mata a wurin aiki, ana tambayarta yaya jiki, ta din ga amsa musu da yauwwa.

Ofishin barrister Habib ta je, ta gaya masa yadda suka yi da matar, da duk abun da ta yi documenting.

Ya karɓa ya duba sannan ya kalleta ya ce "Yayi, amma me ki ke gani a kan case ɗin? Do you have interest on it?"

Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Wani case na jiyo, na wata yarinya da aka yi wa fyaɗe,amma ana ta ɓoye abun, amma na ji an ce su barrister Naja'atu sun shiga case ɗin, hankalina ya fi karkata a can".

"Wai ke menene haɗinki da wannan naja'atun ne? Ki kiyayi kanki da lamarin matar nan,tun da sun shiga case ɗin, ki ƙyale su, case ɗin wannan hajiyar ki tsaya ki mayar da hankali a kai ki yi"

Ta marairaice ta ce "Amma barrister menene aibun hakan, tun da class mate ɗin ka ce, ka haɗa ni da ita dan Allah, ina son irin aikace-aikacenta na jin ƙai"

Ya cire medical glass ɗin sa ya kalleta ya ce "Wai ke meyasa ki ke da taurin kai ne? Ke ma ki kafa naki harkar jin ƙan marasa gatan mana, dole sai kin zama ita, ke kin san wacece Naja'atu kuwa? Zahirinta ki ka sani, baki san baɗininta ba, go and work on this case now".

Tsatstsare fuskar Barrister ta yi da kallo, a ranta ta ce "An zo gaɓar da nake so, hasashena ya tabbata, zan cigaba da matsa ka, har sai ka amayar da abun da ka ke ɓoye mini"

A fusace ya ce "Ba zaki tashi ba, ki ka tsare ni da ido?"

Miƙewa tayi tana zumɓura baki, ta ɗauki file ɗin ta fice.

***

Kaiwa yake ta yi yana komowa, a katafaren office ɗin sa, hannunsa riƙe da waya a kunnesa, yana jiran a ɗauka.

Har fitar da ran za a ɗauka, aka ɗaga. Cikin harshen turanci ya ce "Haba sir, kai fa nake jira kayan nan su iso, almost 2weeks, ayi ta ga kaya nan amma shiru, ni na riga na gama clearing road, a yankinmu na arewa, ka hanzarta na fara jin ƙishin-ƙishin canjin controllers na coustom, bana son a kawo waɗanda za mu yi ta fama"

Daga cikin wayar mutumin ya ce"Sai fa ka yi haƙuri, kayan ne ba a gama loda su ba, kuma nima dole sai na gama da controllers ɗinmu na nan, kuma ka daina ɗaga hankalinka, babu wani wanda ya isa a ƙasar nan, ya sha abun da ba mu muka dama ba, ranar laraba kaya za su shigo, amma sample ce allurar, ba a shigo da ita da yawa ba, sai an ga yanayin aikinta tukuna, har da tablet ma"

"To na ji, amma ka tabattar ranar larabar za su iso?"

"Ko tantama babu"

"To shikenan, godiya nake"ya katse wayar, cikin shauƙin irin ribar da zai mayar idan kayan suka tsira.

Zaune take a ƙasaitaccen ɗakin baccinta, jikinta sanye da riga da wando na nylon, masu sauƙin zafi.

Ta zauna ta nutsu, ta zubawa kayan kan table ɗin gabanta ido, tana ta saƙe-saƙe a kan ta sha ko kuma kar ta sha.

Kwalabe ne na magunguna, da ƙwayoyi haɗi da allurai.

Wata matashiyar mace ce tayi sallama, ta amsa mata, ta ƙaraso hannunta riƙe da cup ta na shan wani abu.

"Sweetheart, ya dai na ga kin saka kayan nan a gaba kina kallo?"

Tayi ajiyar zuciya ta ce "Tunani nake yi da zuciyata, in sha ko kar in sha"

"So you are going to quit abusing drugs?"

Ta girgiza kai ta ce "Is not that easy dear, jikina is resisting it, ba sa ɗauka ta sai na sha su in a very high doses, ba na son su huda ni, a fara ganewa. Mun yi magana da honorable a kan sabuwar allurar da suka yi order daga Mexico yana ta yi mini yawo da hankali"

"Haba barrister, ke fa ta hannun daman honorable ce, ba zai yi miki yawo da hankali ba. An samu wani zazzafan malami fa"

Ta ɗago idanunta ta kalleta ta ce "Wow, are you serious?"

"Yes of course, aikinsa tested and trusted ne, amma kafin muje a kan buƙatarki, anya ba zaki duba a manyan mutanen nan, mu kai wani ba, ki yi aure yadda zai zama backup kar abubuwa su zo su taɓarɓare fa, ko ki samu wani kamar tsohon mijinki, ki aura"

Ta taɓe baki ta ce "Ba zan iya aure ba, na riga na saba da rayuwar ƴanci, ba zan yi aure in zauna ƙarƙashin wani yana juya ni yadda yake so ba. Ai tun da na yi joining organization ɗin nan kin san in da na dosa".

Ta ce "Na sani dear, amma duk da haka, religion da tradition yana da tasiri sosai da sosai a arewacin najeriya, ba na son wani ya gano wani lagonki, ayi amfani da shi wurin yaƙarki"

Ta girgiza kai ta ce "Muddin ba zan samu wanda zan gindayawa sharuɗa ya bi ba, zan iya zamana a haka, i have so many ways to satisfy my feelings, when i need it, ba dai duk su ake yi wa a auren ba? Kin san komai ai ke.
Ki saka mana time, mu je wurin mutumin, ba na son sunana ya ɓace, har sai na cika burina, na kammala aikin da na karɓo a wurin shugabannina, sai na tabattar da samun daidaituwar jinsi a tsakanin mutanenmu na arewa"

Badi'a ta yi dariya ta ce "Ki huta baby, ki ɗan yi caji, sai ki kwanta, ko in fita da ke ne?"

"No, ba na son na yi bacci da yawa, zan sake komawa wurin matar nan, a kan case ɗin ɗan gidan honorable, naga alamar za ta yi taurin kai, idan taƙi yadda kawai mu bi hanyar da muka saba bi"

"Hmm, talaka akwai ƙi faɗi, kuɗin ne ba zata karɓa ba kenan? Sa yi biyu babu kuwa"

"Manta da su, idan ki yi waya da journalist ɗin nan, manta sunasa nake yi, ki tura masa kuɗi, a cigaba da ɓoye wanda ya yi laifin, a sanarwa da duniya na shiga case ɗin, a sassaka a social media ma, a dai yi ƙoƙarin ɗauke hankalin mutane daga kai" ta ƙarasa maganar tana tuttula ruwan maganin da ke cikin wata ƙatuwar kwalba tana lumshe ido.

Yau Abba kamar ya san Nabila so take ta lallaɓa ta fita, ya zauna a gida bai fita ko ina ba.
Tayi iya tunanin ƙaryar da zata sharara masa, ta fita amma ta kasa tunawa, dan idan ya tsitiyeta zai gane ƙarya take yi, gashi weekends ne babu aiki.

Cikin ikon Allah, aka samu tarzomar su madaki da Viper ta ɗan lafa, saboda an jibge jami'an tsaro a unguwannin.

Nabila har alla-alla take yi, ranar Monday tayi ta fita aiki, daga nan ta tafi nata wuri.

Ranar Litinin tun sassafe wasu daga cikin iyaye mata, suka fara sintirin karɓar belin ƴaƴan su da aka kama, a ofishin su DSP Nasir.

Nasir yana zuwa ya tarar da su, an ce musu su jira sai ya zo.

Tsakanin iyaye da ƴaƴa sai Allah, amma wannan rashin juriyar yana ɗaya daga abun da yake taka rawa, wurin sake sangarta yaran.

Bayan sun gaisa da su, ya ce "Da farko ina mai baku haƙuri, domin kuwa ba za mu bayar da belin yaran nan ba, sai mun kai su gaban alƙali tukuna. Yaran nan ku kanku sun fi ƙarfin ku, ba kwa iya tsawatar musu, suna barazana ga zaman lafiyar al'umma, dan haka ku yi haƙuri a wannan karon babu sabo babu ɗaga ƙafa, sai dai na yi muku alƙawarin duk wanda muka kama ba shi da laifi, zamu sake shi, masu laifi kwai zamu kai gaban hukuma".

Bai tsaya jin mai zasu ce ba, ya wuce office ɗin sa.

Koke-koke wasu daga cikinsu suka fara, yayin da wasu suka din ga janyo masa jafa'i kala-kala, wai an zalunce su, an rufe musu ƴaƴa.

A cikin office ɗin sa ya karya, kasancewar ya makara, bayan ya kammala, ya je in da ake tsare da yaran, tare da taimakon wasu daga cikin jami'an tsaro, ya fara tuhumar su, da ƙoƙarin zurfafa bincike akan su gaya masa in da viper yake.

Wanda aka ritsa ɗin ana tuhuma ya ce "Wallahi Yallaɓai, da ne dai kafin ya je prison, na san in da yake, har gidansu na sani, muna yi masa aiki sosai da sosai, amma tun da ya fito bamu sake ganinsa ba, su Walid da tarago ne suka san in da yake, tarago kuma madaki ya kashe shi, walid kuma wallahi shima ba a ganinsa, muna yi masa aiki amma bamu san in da yake ba".

Nasir ya ce "Ta yaya ku ke karɓar order daga wurinsa?"

"Randomly, suke zaɓar mutum ɗaya su kai masa takarda, ko aje a ajiye takardar a in da muke taruwa shikenan"

Nasir zai sake magana, wayarsa ta fara ruri, ya zura hannu a aljihunsa ya ɗaukkota, ya ɗaga ya saka a kunne, tare da yin sallama.

"Kana ina ne?"

"Na shiga wurin aiki sir"

"Yaran nan da ka kama, ka sake su, kowa ya tafi, kuma ka janye jami'an tsaron da ka jibge a unguwar" cikin tsananin mamaki ya tashi tsaye ya ce "Sir, yarane da suke ɓarna fa, har kisan kai aka yi a ranar, yaya zamu....

"This is an order from higher up Nasir, ka saki yaran nan, nima umarni aka bani daga sama, Aminu Viper muka ce ka kamo mana, ba yaran unguwa ba"

Ya taune lips ɗin sa na ƙasa cikin ɗacin rai ya ce "Amma sir, muna kan binciken wanda suka yi kisan kan ne".

"Ka sake su nace, is an order"

Nasir ya ce "Ok sir, as you wish"ya kashe wayarsa, jikinsa yana wata irin tsuma, ya tuna yadda a garin kamo yaran, sai da suka kusa kashe shi, a artabun da suka yi, ga kisan kai, ga miyagun makamai da suka kama yaran da su, amma an bashi order ya sake su, anya kuwa ana son kawo gyara da matsalar tsaro a ƙasar nan!?

Ƙarfe a wuta paid book ne, few pages zan bayar free, masu buƙata za su iya contacting ɗi na, su fara subscribing, miƙaƙƙiyar tafiya ce, mai cike da sarƙaƙiya da ban al'ajabi.




Ayshercool
08081012143
[7/24, 1:44 PM] null: *ƘARFE A WUTA*


AISHA ADAM (AYSHERCOOL)


Ku yi following channel ɗin nan, domin samun littatafan autar manya.
https://whatsapp.com/channel/0029VakTcGc5Ejy40GSTWA0h


Masu son ƙarfe a wuta daga farko, ku bi link ɗin nan ku yi joining channel ɗin
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g



10

Gaba ɗaya zuciyarsa ta cunkushe, ya rasa me ma Yakamata yayi.

Ya daɗe a zaune kafin ya tashi ya fita reception ɗin.

Sai dai yana zuwa ya tarar da wani mutum a tsaye, baƙi ƙirin da shi, ya ɗaura ɗan kwali a kansa, ga wasu wulaƙantattun kaya a jikinsa kamar mahaukaci, idanuwansa jawur kamar an rina masa.

Nasir ya ce "Lafiya kuwa? Wannan fa?"

Ya dube shi ya ce "Kai ne Nasir ko?" Yayi maganar yana shagiɗe kafaɗa irin na cikakkun mashaya.

Nasir ya ce "Ya aka yi?".

"Na san ka samu saƙon ka sakar mini yarana, na zo na tafi da su ne"

Wani irin ƙululun takaici ya tokare zuciyar Nasir, yayi ajiyar zuciya ya ce "Kai ne wa?".

Yayi wani irin ihu, ya jinjina kai ya ce "Madaki nake, gumbar dutse, na san ko bamu yi gaba da gaba da kai ba, ka san labarina, ina son wannan ya zama gargaɗina da kai na farko na ƙarshe, babu kai babu shiga harkata da yarana, idan ba haka ba" Nasir ya tsare shi da ido, ban da lalacewa ace ɗan ta'adda ne zai shigo har office yana yi wa jami'in tsaro kashedi, saboda wasu masu faɗa a ji sun tsaya masa.

Yayi murmushi mai ciwo ya ce sergent Iliya, ka fito da yaran nan gaba ɗayansu"

Ya amsa masa da "Ok sir"

Nasir ya zagaya, ya kama gefen rigar madaki, suka fita waje, ya kalle shi ya ce "Wanene Aminu? Ina zan same shi?"

Madaki ya ce "Wane Aminun?"

"Viper, na san ka san shi, tun da an ce abokin rigimarka ne"

Madaki ya buɗe wawaken bakinsa, da wiwi duk ta dafar da haƙoran, laɓaɓansa sun zama manya, sun yi baƙi saboda taba, ya kwashe da dariya ya ce "Tabbas! Na san shi, ɗan zaki ne, da na yi sake ya girma yake neman gagarar kundila, dan da na kashe shi tun a wancan shekarun da haka ba ta faru ba. Nima neman sa nake yi ruwa a jallo, ko a raye ko a mace, dan haka idan ka same shi, ka sadani da shi.
Sai dai ka bi a hankali wurin neman sa, jami'anku su suka masa sunan Viper, kumurci ne mai hatsari da idan ya sareka zai kashe ka"

A dai-dai lokacin matasan suka fito harabar station ɗin suna ihu, suna sarawa madaki, wasu daga cikinsu kuma da ba yaran madaki bane ba suka fice.

Nasir ba ya tunanin tun da ya fara aiki, ya taɓa cin karo da abun da ya ɓata masa rai kamar wannan, sai ya ji gaba ɗaya aikin ya fita daga kansa.

Haka ya ja tawagar matasan suka bar harabar station ɗin suna iface-iface.

Duk yadda Nabila ta so ta samu damar guduwa, daga wurin aiki yau, ta kasa samun dama, dan haka ba ta tashi ba sai ƙarfe uku, a lokacin ba ta da wani kuzarin kirki, babu abun da take buƙata wanda ya wuce ta tafi gida.

Ba ta fi mintuna ashirin da shiga gida ba, Nasir ya dawo.

Bayan sallar la'asar ya kirata a waya, ya ce ta fito yana son ganinta.

Ba ta ɗauki lokaci ba, ta fita harabar gidan, wajen parking space akwai fararen kujeru.

A can ta tarar da shi, sai dai yanayinsa ya tabbatar mata akwai damuwa "DSP, yana ga kamar ranka a ɓace ne?" Tayi maganar tana zama.

"Damuwa kam akwaita, gagaruma kuwa arfa"

Ta girgiza kai ta ce "Subhanallah, meyafaru yayana?"

Nasir ya ce "An saki yaran nan fa, da muka kama shekaranjiya"

Ta waro ido ta ce "Saboda me?"

Ya ɗan ɗage kafaɗa ya ce "Saboda yaran ƴan siyasa ne, ina zuwa office aka kira ni daga sama, wai suma umarni aka yi musu, kar in sake kama yaran, aikin neman Aminu aka saka ni ba wannan ba, na daɗe ba ayi mini abun da ya ɓata mini rai irin wannan ba, kamar ni wai ni ɗan daba ya kalleni a cikin kakina, yake yi mini kashedi a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login