Showing 147001 words to 150000 words out of 152254 words

Chapter 50 - ?arfe A Wuta Book 1 Hausa Novel Complete

15 Dec 2024

363

ta kwanta da wuri ba, ta daɗe tana salloli, da karatun Alqur'ani, a kan Allah ya shirya Al'amin, ya sanya tarayyar ta da shi, ta zama sanadin shiriyarsa.

Sai da tayi sallar asuba, sannan ta kwanta, dan haka wani irin nannauyan bacci ya ɗauke ta.

Sama-sama ta ji muryar Al'amin, yana faɗa da boti, ya zo tashinta yana jin yunwa, ya ga boti ya lafe a jikinta, shi ma yana tashi.
Ya danƙo shi ya jefa ƙasa ya ce "Ware ka bar nan wurin dan ubanka"
Boti ya tsaya, yana kallon Al'amin yana kuka.

Al'amin ya mayar da idonsa kanta, bacci take sosai, shi kuma yunwa ta ishe shi, dan yayi shaye-shaye.

Dukan katifar gadon yake yi a hankali, ta motsa kaɗan ta cigaba da bacci.

Yaye bargon yayi gaba ɗaya, daga ita sai vest da gajeren wando, a razane ta tashi zaune tana kare jikinta.

Ya riƙe bargon ya ce "Ki na ji na ki ka yi mini shiru? Ina son na karya na sha magani, kin ɗauki wancan abun kin kwanta kina bacci da shi".

Cikin muryar bacci, mai haɗe da tsoro, ta ce "Na ji, amma ka bani bargon zan fito yanzu".

Ya ce "In tafi ki cigaba da baccin, tashi mu je"

To ka je ka jira ni, zan saka kaya.

Taɓe baki ya yi ya ce "Da kin kwantar da hankalinki, ba na jin komai, ba abun da zan yi miki" ya miƙe yana ajiye mata bargon ta, ya danƙo kan boti ya yi waje da shi.

A jejjere ta din ga ajiyar zuciya, tana maimaita maganarsa shi ba ya jin komai.

Da ta fito kasa haɗa ido tayi da shi, ya kwanta ruf da ciki saboda raunin bayansa, yana jiran abinci.

Bayan ya karya, ta ce "To wanka fa?"

"Ba yanzu ba, gasa mini ciwon nan kai"

Ta haɗo ruwan ɗumi, ta gasa masa, ciwon, tana yi yana raki, saboda yadda ya ga tana damuwa sosai, wai da zafi.

Wayarsa ta fara ringing, ta hana shi ɗagawa, har ta katse, ta sake fara ringing, ta ɗaga ta ce "Assalamu alaikum, ba shi da lafiya bacci yake"

"Ya jikin nasa?"

Ta ce "Da sauƙi"

"Masha Allah, ke ce matar ta sa? Al'amin ya karɓe wayar ya kasheta gaba ɗaya ya kalleta ya ce "Meyasa ki ka tsaya kina magana da wani?"

"Na zata su yaya walid ne, yi haƙuri, amma yakamata ka kira shi ka ji, ko an sako shi"

Al'amin ya haɗe ce "Wai ke kowa ma damuwa ki ke da shi ne?"

"To ai gani nayi saboda mu ya shiga matsala, aka kama shi"

"To ba ruwanki, da ni kawai zaki din ga damuwa" ta kwashe da dariya ta ce "To shugaba, in sha Allah. Juya in shafa maka man zafin a wurin" ya juya tana shafa masa a hankali, dan kar ya ji zafi.
Wayarta ce ta fara ringing, ta ɗauka ta duba
Ta ga lambar mama ce, ta ɗaga suka gaisa, ta ce "Yauwwa, dama kiranki na yi, ana ta shirin bikin hafsa, tun saura sati ɗaya biki yakamata ki dawo gida, akwai aikace-aikace da za ayi, saboda bikin.

Ta ce "To shikenan mama, Allah ya kaimu lafiya"

"Amin" ta kaste wayar.

"Ba in da zaki" ya faɗa dai-dai lokacin da ta ajiye wayar.

"Master meyasa, bikin Yaya hafsa ne fa"

"Ko bikin wacece, ba zaki ba? Idan akwai mai neman dalili, sai a tuntuɓe ni".

Jauhar ta ce "Master za su ga kamar wulaƙanci ne, ko baƙin ciki, ko ba zan yi satin ba, dan Allah ka bari na je bikin"

Ya girgiza kai ya ce "No, bayan bikin kya je gidanta".

Jauhar ta marairaice za ta yi masa magiya ya buga mata tsawa ya ce "Ina magana kina mayar mini, ba zaki je ba na ce" a razane ta ja da baya, ta sunkuyar da kai ta yi shiru, ya tashi ya bar mata falon.

Yana ƙwafe da wayar da suka yi, aka ce ba zata iya sayen anko ba, yanzu kuma an ce ta zo ayi aiki, saboda baiwar su ce ita, ita kuma gaba ɗaya hakan bai dameta ba, wasu lokutan kamar ba ta da zuciya sam.

Tun da Indabo ya ajiye wayar, yake jujjuyata yana jin yadda muryar jauhar, ke kai komo a cikin kwanyarsa, kana jin muryar ka san ta yarinya ce, haka kurum ya ji ya kwaɗaitu da son ganinta.

Ayshercool
08081012143
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724

https://chat.whatsapp.com/E3bH5OKBh9jH2aYygj0ArA

Kina bukatar kaya masu kyau da inganci??

    Kina bukatar kayan kitchen wnd suke available ba order ba??

    Kina bukatar adashin gata wnd zaki dauki kaya kamar kyauta??

    Kiyi joining wnn group din namu insha Allah xakiji dadin kasancewa a ciki.

     Muna da kaya available masu kyau da rahusa💃🏾💃🏾
Ko kimin mgn ta👇🏽👇🏽
08093932955 da


Indabo ya cigaba da jujjuya wayar yana kallonta.

Sosai jauhar ta ji babu daɗi, hanata zuwa bikin da Al'amin yayi, ba ta san dalilin sa na yin hakan ba, kuma bai gaya mata ba, ba ta san me za ta ce wa su mama ba, su yarda da ita.

Kuma yayi fuska, ya hau hura hanci yana wani basar da ita, dan ma kar ta ce zata yi fushi da maganar hanata zuwa bikin da yayi, shiyasa yayi sauri ya rigata fara fushin.

Haka ta wuni, idan ta tuna abun sai ta ji ba daɗi, da duk in da za ta je, ba ruwansa, amma yau bikin 'yar uwatta, ya ce ba zata je ba, Al'amin kenan.

Sai dai tayi iya ƙoƙarinta, ta danne fushinta, ba ta canza masa ba, amma yanayinta kallo ɗaya yayi mata ya gane, a cikin damuwa take, kuma ya san hakan yana da nasaba da hanata zuwa biki da yayi.

Can gidansu amarya hafsa, ana ta rawar kai, an sha gyaran jiki, magungunan mata kuwa ba a magana, fatar nan ta ƙara ɗashewa, tayi fara ƙal kamar aljana.

Sai hura hanci ake yi, za a auri mai kuɗi, mama kuma sai yi musu lumbu-lumbu, kamar tana tare da su a komai.

Suka din ga karɓar kuɗi a wurin Alhaji mu'azzam kamar ba gobe. Shi kuma duk abun da suka nema, haka zai ba su.

Zakiyya ta saka hafsa ta tambaye shi, wai a ina za su je honeymoon. Murmushi ya yi da ta tambaye shi ya ce "Hafsa yawon ƙasashen duniya har sai kin gaji, dai ƙasar da ki ke so zamu je" hakan ya ƙara fasa mata kai, ta din ga jin cewa ta gama dacewa.

Al'amin ciwonsa ya fara warkewa, kasancewar ba shi da ƙan jiki, ga kulawa da Jauhar take yi da shi sosai da shan magani.

Ta ɗaura aniyar, fara ɗora Al'amin a turbar tafiya masallaci kuma, ya din ga salla a cikin jama'a, kamar yadda Annabi Sallallahu alaihi Wasallam, ya kwaɗaitar da al'ummarsa, mussaman da ciwonsa ya kame, dan ya fara saka riga ya fita ma.

Sai dai fa aikin ba na wasa bane ba, dan wasu lokutan idan ta tashe shi sallar, har a idar tana fama da shi bai tashi ba, mussman idan a cake yake, idan ta yi alwala kuwa ta zo tashinsa, ƙarshe sai ta ta alwalar ta karye, shi kuma bai yi ba.

Sai dai ta tsananta addu'a da gaya wa Allah. "Ya Allah ga bawanka Al'amin, kai ka halicce shi, ka shirya wanda suka aikata laifuka fiye da nasa, Ubangiji Allah ka shirya mini shi. Allah ka sa ya shiryu a sanadin zamana da shi, Allah kar ka saka na ƙosa ko na gaji, Allah ka dubi niyyata ta son zama da shi da yin biyayyar aure kamar yadda ka umarta, Allah dan kunfayanunka ka shiryi wannan bawa naka"

Duk in da jauhar ta ji Addu'ar biyan buƙata, irin su salatul haja, salla raka'a biyu, fatiha da sura, idan ta idar ta mayar da goshinta ƙasa, ta karanta la'ila ha illa ant subhanaka inni kunt mina zalimin. Ƙafa arba'in  da ɗaya, ba ta ɗagowa sai ta gaya wa Allah buƙatunta.
Salatul tasbih, da sauran tasbihai haka take yi, tana yi wa Allah magiya da yin tawassuli da su, ta roƙi Allah ya shirya mata mijinta, ya haɗa kan su su zauna lafiya.

Yau ta samu yayi sallar asuba ƙarfe shida saura da ƙyar, ta dawo dan ta saka shi yayi azkar, ta tarar har ya kunna sigari daga idar da sallar.

Bai yi tsammanin za ta dawo ɗakin ba, kawai ya ji sallamarta ta shigo. Kamar yadda tayi tsammani, bai daina sha ba, kuma ya tsuke fuska.

Ta ƙarasa gabansa ta zauna, ta zuba masa ido.

"Kin san an hanaki shaƙar hayaƙi ko? Kin san ba cikakkiyar lafiya ce da ke ba"

"Kai ma bai dace da kai ba, ina gaya maka ina son lafiyarka, su kan su masu kamfanin abar sun yi gargaɗi a kan haka, dan Allah ka ajiye magana zamu yi".

Bai ajiye ba, yayi mata shiru yana cigaba da fesar da hayaƙin wani wurin daban.

Tashi tayi ta zagaya, in da yake fesar da hayaƙin tana kallonsa.

"Meye haka ne wai?"

"Dan Allah ka ajiye mu yi magana"

"Ina jinki ai" wani abu mai ɗaci ta haɗiye, kawai ta tashi ta bar masa ɗakin.

Ta koma ɗakinta ta tsaya, kuka ya ƙwace mata, sai ta fara saito abubuwa, sai Al'amin ya sake burkice mata, tun da suka yi aure take yi masa addu'a, amma abun nasa sai a hankali.

"Kul jauhar, kar ki yi saɓo, ko ki yi wa Allah butulci, Allah sami'ul alim ne, idan ka roƙa baka ga tasirin abun ba, lokacin ne bai yi ba, tun da shi ya ce mu roƙa zai amsa, kuma Allah ba ya sabon aiki' wata zuciyar ta gargaɗe ta.

Istigfari ta cigaba da yi, ta nemi wuri ta zauna a tsakiyar gadonta, tana cigaba da tasbihi.

Sai da gari yayi haske sosai, ta fita tana aiki, ya fito cikin takun ƙasaita, ya nemi wuri ya kame a kan kujera.

Sai da ta kai zuciyarta, sanna ta iya ce masa "Ina kwana?"

"Lafiya ƙalau" a ranta ta ce 'Ka yi laifi, kuma ka maze kana hura mini hanci, da ni ka ke zancen'.

Ta ajiye masa karin kumallonsa, ta koma ɗakinsa, ta na gyarawa, yanzu ya rage watso mata kaya daga wardrobe, sai dai ya tara mata kayan wanki, a kan katifarsa.

Tsayawa yayi a bakin ƙofa, yana kallonta.

Yayi gyaran murya ya ce "Kin ce zamu yi magana, ta menene?"

Ta kalleshi ta ce "Ka manta kawai" ta ƙarasa maganar tana kwaso kayan wankin za ta fita.

Har ta gota shi, ya janyo ta kamar wata 'yar tsana, ya tsuke fuska ya ce "Gaya mini menene?"

Ta sunkuyar da kanta, hawaye ya fara zubowa daga idonta, wani na bin wani.

"Menene kuma yanzu?"

Cikin rauni ta ce "Kai ne"

"Na yi me?"

"Kusan kullum sai ka sakani kuka mussaman kwanan nan, na ce dan Allah ka daina shan komai ka ƙi dainawa, haba master wane irin uba ka ke son ka zama idan Allah ya bamu zuriya? Ina son in ga ka daina shan komai ka daina abun da ka ke yi. Amma ƙir-ƙiri ɗazu ka ƙi daina sha".

Ya ce "Ke, wai an gaya miki daina shaye-shaye kamar daina cin tuwo ne? Ina ƙoƙartawa fa, duk kin addaba mini, ina ji ina gani, asuba ina shan kara biyar zuwa sama, amma ɗazu uku kawai na sha amma ba kya gani, kuma yaushe na ganki, balle a tara wata zuriya? Shiyasa ma ban bari sun ƙaraso ba tukuna sai na gama abun da nake yi. yayi maganar yana basarwa.

Wata irin kunya ta kama ta, jin abun da ya mayar da maganar.

"Ki daina damuwa, ina ƙoƙari sosai, ba zan iya dainawa ba, sai na cika burina, mutum ɗaya kawai zan kashe, shikenan"

Jauhar ta kalleshi ta ce "Kisa kuma? Ana ga ƙura kana ga yaƙi, idan an yi nan sai ka yi can"

Dogon harshensa ya zaro mata, yayi wani irin murmushi, sai ta ga kamar ya canza gaba ɗaya, ya dafo kafaɗarta kamar ƙawarsa ya ce "Bar wankin, zan yi ki haɗo da naki ma, idan na gama zan yi gyaran kwatar layin nan, duk an bari ta cushe da shara, me zaki dafa mana da rana?"

"Master ba ka da aiki sai zancen abinci ne?"

"To idan ban yi zancen abinci ba zancenki zan yi babyn roba"

"Saura ta katako, rana zata yi mini, ko wankin ka saɓa sai na yi mana ɗauraya"

Al'amin ya ce "A'a ki yi aikin ki zan wanke" yayi maganar yana yi mata wani irin kallo tare da murmushi.

Ita ma murmushin ta yi masa ta ce "Harshenka dogo ne, meyasa ka ke fito da harshe ne?"

Ya ce "Rantsuwa ce, kowane specie ɗinmu, akwai irin ta su".

Jauhar ta yi dariya ta ce "Wai specie kamar a biology?"

"To in ce kowane ɗan daba?"

Ta yi saurin girgiza kai ta ce "A'a ba na son wannan kalmar, babu daɗin ji"

Ba tare da ta gane ba, yayi mata wayo, ta daina fushin da take yi, dan babban burinta ya kula ta, ya sakar mata fuska.

Aka shiga satin bikin Hafsa, Anty Zakiyya ta kira Jauhar ta ce "Jauhar wai yaushe zaki zo ne? Ayyuka sun kacame, ko dai baƙin ciki ki ke yi da lamarin nan ne?"

Jauhar ta ce "Haba Anty, ba haka bane wallahi. Kin ga maigidan ne ba ya jin daɗi, idan na taho babu mai kula da shi".

"Kamar yaya? Au mijinki ya fi 'yar uwakki, kamar wani mijin kirki, da waye yake kula da shi idan ba shi da lafiyar?"

"A'a Anty, ai miji duk in da yake miji ne, yana buƙatar kulawa ne, ba dan....

"Dalla yi mini shiru, har wani tinƙaho ki ke yi da wannan abun? Makakken ɗan wiwi.

Ba tare da Anty ta sani ba, tuni ya karɓi wayar daga hannun jauhar, ya saka a kunnensa tana ta masifa "To ki zauna sai yadda yayi da ke, ai mutumin kirki mai kuɗi shi yake saka doka a bi, ba irin mijinki ba da har ki ke gaya mini wai ai miji miji ne ba".

"Makakken ɗan wiwi yana godiya, kuma kun san da makakken ne, ku ka aura mata ni. Ni na hanata zuwa matata ba baiwa ba ce, ta zo ta yi muku bauta, ba zata zo ba, idan kun ga dama ku bar bikin kar ku yi" Jauhar tana girgiza masa kai, amma sai da ya gama maganar ya jefar da wayar.

"Master, iyayena fa, ba a haka yakamata a gaya musu ba, da ka bi a hankali, na san yadda zan gaya musu".

Al'amin ya ce "Kin san bani da tarbiyya, ban iya magana da manya ba"

"A'a ba haka nake nufi ba"

"Idan ma dai hakan ki ke nufi, idan kuma ban isa ba, ki shirya ki tafi "

Jauhar ta ce "A'a ka ma isa, ai na fasa zuwan, amma ai ka yi mini alƙawarin zaka kai ni gidanta bayan bikin ko?" Tausayinta ne ya kama shi, ba dan haka ba da gidan hafsan ma ba zai bari ta je ba, amma ya tuna ɗan uwa duk in da yake daɗi ne da shi, kuma bai kamata ya hanata zuwa wurin 'yar uwatta ba, amma kamar ko a jikinsa ya ce "Zan yi shawara"

Anty Zakiyya kuwa, sai da kayan cikinta suka yanutsa, saboda tashin hankali da ta ji muryar Al'amin a waya.

Sai dai jauhar ta sha zagi a gidan, ana cewa baƙin ciki ne da hassada ya sanya ba zata zo ba.

Yaya saifu ya ce 'm"Jauhara ba ta da irin wannan zuciyar, hankalinta na kan mijinta, wannan aure dai, in dai dan cin amana aka yi shi, ba in da zai je zai watse".

A fusace Anty ta ce wa mama "Ki ja wa ɗanki kunne, kar ya sake aibata mini auren 'ya"

An kai kwanaki huɗu ana events kala-kala na auren Hafsa, jauhar sai kallo da ta din ga yi, tana murmushi tare da jin babu daɗi rashin halartar auren yayarta, ga 'yan uwa da abokan arziki duk an taru.
Ita ma ta ɗora hotunan, tana yi wa hafsan fatan alkhairi.

Aka gama biki, aka kai hafsa gidanta, wanda suke haɗe da uwar gidansa, kowacce part ɗin ta daban.

Aka yi sayen baki aka watse, ya tara su yayi musu nasiha, bayan Uwargidan ta fita, Alhaji mu'azzam ya ce "Bari na je na ɗan ƙara rarrashinta, na san tana cikin damuwa" haushi ya kama hafsa, dan a zatonta yana zumuɗinta, ba zai saurari uwar gidan ba.

Sai dai har ɗaya na dare bai dawo ba, ta kira wayarsa a kashe, tun tana saka ran ya dawo, har ta gaji, bacci yayi awon gaba da ita.

Da safe ma, ga yunwa ga gajiya, amma ba ta ganshi ba, sai sha ɗaya na safe.

Ya ce "Jauhar am sorry please" ta kalle shi cikin takaici ta ce "Jauhar kuma?"

"Afuwan Hafsat, wallahi madam ce nayi  ta faman rarrashinta, taƙi yin shiru kin san kishi babu daɗi, shiyasa na zauna da safen nan ma da ƙyar na fito, duk a cikin damuwa ta ke, yanzu haka kanta ciwo yake saboda kuka, ina ga da kaina zan fita nema mata magani"

Tamkar hafsa ta zabga masa mari haka ta kalleshi ta ce "Ni bana buƙatar kulawarka kenan sai ita?"

Ya ce "No ba haka bane ba? Ai ke sabuwa ce, sai ta fiki shiga damuwa, bari na je na sayo mata maganin na kai mata, na yi ordern abinci, idan ban dawo da wuri ba ki karya kawai.

Abu kamar wasa, har wurin kwanaki uku, bai saurari hafsa ba, wai uwargidansa ba ta da lafiya, har ma ya ɗauki fushi da ita, wai ba ta je ta yi mata sannu ba, ta ɗauki waya tana kuka ta sanar da Anty, Hankalin Anty ya tashi, ta ce ta je ta dubata ɗin, za su sake shiri su ma.

Baya nan hafsa ta shiga duba ta,  ta ce "Na ji an ce baki da lafiya, na zo duba ki"

Ta ce "Ko ɗaya, lafiyata ras, kawai ina ƙoƙarin nuna miki ƙarfin ikon da nake da shi a cikin gidana da irin gangancin da ki ka aikata na shigo mini gida"

Hafsa ta ce "Shigowar ai ita ce mai wuyar, tun da an ce hanawa ki ke yi, ni kuma na yi nasara na shigo, mu zuba da ni dake".

"Lallai yaro bai san wuta ba sai ya taka, ga fili ga mai doki".

Har hafsa ta kwana bakwai a gidan nan, ba su haɗa shimfiɗa da Alhaji mu'zzam ba, duk ɗokin amarcin da take yi, komai ya fita daga kanta, ta rasa abun da yake yi mata daɗi, ƙiri-ƙiri yake nuna mata shi ta matarsa yake yi ba ita ba, saɓanin abun da ya nuna mata a waje.

Jauhar kuwa ta cigaba da yi wa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login