Showing 15001 words to 18000 words out of 152254 words

Chapter 6 - ?arfe A Wuta Book 1 Hausa Novel Complete

15 Dec 2024

328

Amma ina roƙon Allah, in sha Allah tana raye, sai na ɗaukaka fiye da tunaninta, kuma bibiyarta zan din ga yi, da bibiyar duk wani abu da ya shafe ta, sai na rama abun da ta yi mini. I will do a background check on her"

"Ke fa baki iya ɗaukar abubuwa da sauƙi ba, ki ƙyaleta mana kanta ta yi wa, ni na ce me?, abun da nima ake yi mini, ni kusan kullum ake yi mini, ke yau ne kawai, kuma arfa matsayi na duniya ba na kiyama ba"

Nabila ta girgiza kai ta ce "Wannan ke ki ka ga zaki iya, kuma ƙaramar alhaki ce ta wurin aikinku, wannan kuwa dizgin da ta yi mini, in sha Allah rabbi, sai na rama shi, dole na ajiye shirme, na mayar da hankali a kan aikina, ko dan fansar nan, kut wallahi matar nan ta gama cuta ta, kuma ba zan huce ba har sai na rama wallahi. Rakani titi in tafi gida" ta ƙarasa maganar tana ƙoƙarin tashi tsaye.

Sumayya ta danƙota ta ce "Nabila ki din ga sanyawa zuciyarki salama mana, kin fiye zafin rai, ki bi komai a hankali, kalli yadda ki ka kusa kashe kanki a banza. Idan Allah ya yi nufin ɗaukakaki fiye da ita, ita ɗin banza ta hana, dan Allah ki manta da ita, ki cigaba da rayuwarki".

Ta kalli sumayya cikin takaici ta ce "Lallai ma sumayya, dan ba ki ga abun da ta yi mini ba, a gaban mutane har da masu yi mini dariya. Ni gaba ɗaya ma ji na yi ban yarda da ita ba, abun da ake faɗa a kanta daban, abun da na gani yau a kanta daban, akwai wani abu a ƙasa, and i will run a background check on her, for the first place ma, wacece ita? Idan ta kama har bunkuren zan je mahaifarta, meyasa abun da ake faɗa a kanta daban, ita kuma halinta daban".

Sumayya ta ce "Na shiga uku, Nabila" kafin ta yi magana, Nabila ta yi waje, ta tarar da umman sumayya na salla, ta ce Umma na tafi, ta fice daga gidan.

Sosai abun da ya faru ya tsayewa Nabila,da ta tuno abun sai wani irin takaici yakamata.

Yau ba kowa ya san ma ta koma gida ba, dan yau babu surutu da hayaniya.

Abu kamar wasa, har dare Nabila ta kasa walwala, ko fitowa daga ɗaki taƙi yi, gani take kowa yana kallonta zai gane an dizgata yau, duk iyayin na ta da jan ajin.
Nabila irin mutanen nan ce masu saka abu a ran su, dan haka ko ta yi niyyar manta abun da ya faru, sai ta kasa.

Ta ɗaukko wayarta, ta kunna data, ta tarar da messages ɗin sumayya, ta na ta yi mata faɗan ta yi haƙuri ta manta da abun da ya faru.

Nabila ta yi mata reply da "You are not serious, ki saka ido ki yi kallo"

Social media ta hau, ta shiga searching ɗin sunan barrister Naja'atu Bunkure, nan da nan sai ga hotunanta, da wasu daga cikin ayyukanta na jin ƙai, sai dai ba ta samu wani cikakken bayani da take son samu a kanta ba.

Tsaki ta yi, bayan tuna yadda take mutuwar son matar nan a baya, har hotonta take sakawa a dp ɗin ta, saboda yadda take ƙaunarta, amma lokaci ɗaya a yanzu ji take yi, ba ta da wani maƙiyi idan ba ita ba.

Har sha biyu da rabi na dare, ba ta samu cikakken abun da take son sani ba, sai ma zarge-zarge da suka din ga ɗarsuwa a ranta game da matar.

Saukkowa ta yi daga kan gadonta, ta fice daga ɗakin, fita tayi can babban falo, ta nufi kitchen ta samu abun da za ta ci, dan yunwa take ji sosai.

Fridge ta buɗe, ta samu ruwa mai sanyin gaske, da coc ta fito falo tana sha.

Hasken fitila ta hango a baranda, ba a kashe ƙwan wurin ba, ga abba kullum sai yayi magana a kan rashin kashe kayan wuta, kafin a kwanta bacci.

Wurin ta nufa, da niyyar ta kashe ƙwan, ta na zuwa ta leƙa, ta hango nasir a kan kujera, yana ta danna system.

Ta window ta je ta zura hannu, tana taɓa masa kunne. Caraf! Ya riƙe hannun ba tare da ya ɗago ba.

Tayi dariya ta ce "Shi ne ba ka tsorata ba"

"Me ki ke tunanin zai razana ɗan sanda?"

Ta ce "Ai dai ɗan sanda mutum ne, kuma na san ka ji tsoro mazewa ka yi"

Yayi murmushi ya ce "Tsoro sai lauyoyi"

Ta buɗe ƙofa ta fita ta zagaya in da yake ta ja kujera ta zauna sannan ta ce "Duk tsoron lauya bai kai ɗan sanda ba"

Ya ɗago ya kalleta, sanye cikin kayan bacci pink, masu bargo kanta ko ɗan kwali babu, tayi parking ɗin gashinta"

Murmusawa yayi ya ce "Ke kin san babu tsoro ga wanda yake riƙe makami, yayi yaƙi da ɓarna"

"Hmm, yi dai a hankali, dan harshe ya fi makami dafi, kar lauyoyi su baka mamaki watarana"

"Ina aiki kin zo zaki dame ni, ina nawa aikin, ina kallabinki?"

"Yana ɗaki" tayi maganar tana lashe murfin jarkar lemon hannunta.

"Kalli abun da ki ke yi kamar ƴar ƙauye, sai an yi magana ki fara ke barrister ce, ke degree holder " yayi maganar yana mayar da hankali a kan system.

Ta numfasa ta ce "Wai aikin me ka ke yi ne?"

"Wani aiki ne mai wahala, wanda nasara a kansa, na iya sawa na samu cigaba a aikina".

Nabila ta ce "Haba dai, to Allah ya taimaka"

"Amin" ya amsa ba tare da ya kalleta ba.

Shiri ya wanzu na wani ɗan lokaci, sannan ta ce "DSP"

"Na'am barrister"

"Sannu da aiki" ya ɗago ya kalleta ya ce "Kin isheni fa, za ki tashi ki bar wurin nan"

"Yi haƙuri, na daina magana"

Ya cigaba da aikinsa, ta na shan lemonta, tana jin yadda iska ke kaɗata.

Duk abun nan, Abba ta ɗakinsa ya na hango su, sai dai ba ya jin me suke cewa.

Can ta sake cewa "DSP"

A hasale ya ce "Ke! Meye ne? Tashi ki je ki kwanta dare yayi"

"Ni na kasa bacci, raina ne a ɓace".

"Ai dama kullum cikin ɓacin rai ki ke, tun da ke a rayuwarki ta duniya, baki da haƙuri tashi ki bani wuri"

Ta marairaice ta ce "To ka tsaya ka ji me aka yi mini mana, dan Allah kafin na tafi, ka gaya mini me zan yi, wanda zai saka na yi suna, kowa ya sanni" tayi maganar very serious.

Cikin gatse ya ce "Ki nemo in da Aminu Viper yake, ki taimaka mini na kama shi, kin ga sai ki yi suna, ni na samu cigaba a aiki"

Ta fuskance shi sosai ta ce "Waye shi, a ina yake? Kamar na taɓa jin sunansa"

Ya kalleta ya ce "Shi nake ta aiki a kansa, galibin aikin ta'addancin da ƴan daba suke yi, a wasu shiyyoyin da saka hannunsa, yaransa ne. An ce lallai na kamo shi, tun da yankin da ake ɓarnar ƙarƙashin kulawata yake akwai zarge-zarge a kan guduwa yayi daga prison"

"Dan Allah idan na nemo maka shi, zan yi suna, kowa ya sanni?"

Kallon baki da hankali yayi mata, ya cigaba da abun da yake yi.

"Ka ga riba biyu kenan, na yi suna, kuma ka samu cigaba a wurin aiki, yes! Amma na ji ka ce akwai zarge-zarge a kan guduwa yayi daga prison how? Kun tabattar da hakan ko kuwa? Ka bani hints mana, laifin me ya yi a ka kai shi prison ɗin?".

Takalminsa ya ɗauka ya miƙe tsaye ya ce "Tashi ki bar wurin nan, tashi maza"

Da haka ya koreta, ta tafi ɗakinsu. Sai dai  da ga koma ɗakinta, ta dinga sintiri a cikin ɗakin, sosai ta ji maganar Yaya Nasir ta shiga ranta, ina ma hakan ta tabatta.

"In taimaka masa ya kama ɗan ta'adda, in nemo haƙiƙanin dalilin barinsa daga gidan yari, idan guduwa yayi me ma'aikatan suke yi, idan sakinsa aka yi laifin me yayi, aka sake shi duk da hatsarinsa, na bankaɗo ainihin identity ɗin Naja'atu Bunkure, na gyara career ta, wai ma menene dalilin da ya sa ban zama ƴar sanda ba?, na zama wata lauya yau ka kare mai gaskiya gobe mara gaskiya.
Ta yi wani irin shu'umin murmushi ta ce "Accepted DSP Nasir, zan nemo maka Aminu Viper, na bibiyi laifin da ya aikata, da yadda aka yi ya bar prison.

Ayshercool.
08081012143
[7/19, 1:11 PM] null:                   

                 *ƘARFE A WUTA*


AISHA ADAM (AYSHERCOOL)


MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION

BRIGHT PENS SECOND BATCH.

https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

5




Wurin shiru, ba ka jin motsin komai, hantsi yayi, yana zaune a kan wani dutse, yana jin yadda ɗumin ranar ke ratsa shi, dan ba ta riga ta yi zafi ba, hannunsa ɗaya ɗauke da taba sigari, yana ta zuƙa yana busawa, idonsa yayi jawur.

"Viper" matashin  ya kira sunansa, yana ta sauke haki.

"Ina jinka" yayi maganar ba tare da waiwayawa, ya kalli matashin ba.

"An kama ɗan mama da kayanmu fa jiya da daddare, a chamber yamma da gari, yana tsaka da raba kayan ga mutane, kuma wadda aka kama da yawa"

Ya saka yatsansa ya ɗan daki jikin sigarin, tokar jiki ta zube, ya ja numfashi ya ce "Wace hukumar ce?"

"Masu ƙwaya ne"

Ya miƙe tsaye ya ce "Shikenan, kar ka damu, ku bar shi a hannunsu"

Ya waro ido ya ce "A bar shi, Ka manta a halin da ake ciki? Idan wani abu ya faru fa?"

Cikin takunsa na ƙaƙƙarfan namiji, ya ƙarasa gaban matashin, ya riƙe kwalarsa a hankali sannan ya ce "Ba na butulci walid, ɗan mama ni yake yi wa aiki, dole na fito da shi. Ni ba zan kamu ba, da zan kamu da basu bari na fito ba. Kuma ko a yanzu suna sane suka bar guzuma, suke harbin karsana. Ni na shirya a kama shi, sannan ina son ku je dabar Madaki, ko wurin da yaransa suke, ku tayar da hayaniya, ku zubar da jini, kar ku raga musu ko kaɗan, ko da kuwa hakan yana nufin jami'an tsaro su kama ku"

Yayi shiru yana kallon viper.

Ya shafi sumar walid, da tayi cibiri-cibiri ya ce "Ya ka ke kallona kamar kana tantama a kaina?"

Ya risuna ya ce "Tuba nake mai gida, duk abun da ka ce dole ayi shi, umarninka muke yi wa biyayya"

"Good. Idan aka kama ku, ko da mutum ɗaya ne daga cikinku, ku ambaci sunana, ku ce ni ku ke yi wa aiki, ni ne na saka ku. Ina sake jaddada maka, kar ku ragawa kowa a cikin su. Amma ku kiyaye ƙa'idar aikina. Babu kisan kai, babu taɓa wanda babu ruwansa mata ko kuma ƙanan yara"

Walid ya ce "An gama maigida"

" Ɓace " ya furta a hankali.

Yau Nabila ko karyawa ba ta tsaya yi ba, haka zalika ko sumayya ba ta jira ba, ta tafi aiki.

Daga office ɗin ta, tana hangen harabar chamber, ta ga isowar motar Barrister Bashir. Bayan mintuna talatin ta bishi office ɗin sa, suka gaisa ya dube ta ya ce "Ƴar ƙwalisa ya jiki?"

Ta ce "Jiki kuma, ba ni da lafiya ne?"

Ya ce "Ranar da muka dawo daga court, kina ta tari har ki ka tafi gida, ko kin manta?"

Ta ce "A'a na tuna, na ji sauƙi ai"

"Wai meyafaru ne a kotun, bayan na je na ga abokina, da na dawo na tarar da ke gaba ɗaya ranki a ɓace, na tambayeki kin ce ba komai"

Nabila ta ce "Da ma fa dan bana jin daɗi ne, ai ni ba zan manta da ranar ba, na ga masoyiyata kuma mudubina"

Barrister ya ce "Wa kenan?"

"Barrister Naja'atu, ina son matar nan sosai "

Yayi murmushi ya ce "Bunkure ki ke nufi?, mace mai hatsari kenan"

Ta waro ido ta ce "Hatsari kamar yaya?"

"No, kin san ba ta da wasa da aiki, duk shari'ar da ta saka gaba, sai ta ga bayanta, ke kuma gashi ba haka ki ke ba, ba kya mayar da hankali a kan aikin".

"Ai in gaya maka ganinta kawai da na yi, na ji wata irin ƙwarin gwiwa, na ji sonake na nutsu na mayar da hankali sosai a kan aikina. Sonake na bi footsteps ɗin ta, nima na yi nasara kamar ita. Amma me ka sani a kanta da zaka iya gaya mini?"

Yayi murmushi ya ce "Nothing much, ki tambayi barrister Habib, ya santa sosai " sai da ta ji wani dummm! Yadda suke faɗa da barrister Habib, amma hausawa su ka ce ranar biyan buƙata, rai ba a bakin komai yake ba, dan haka ta ce "To shikenan, na gode sosai ayi aiki lafiya". Ta juya ta fita tana nanata "Dangerous woman, zamu gani ai".

Ba ta zame ko ina ba, sai ofishin barrister Habib, ta tarar da shi da wasu client suna tattaunawa, ya ɗago ya kalleta ya ce "Meye?" A ɗan hasale dan a ƙule yake da ita.

Ba tare da ta yi fushi ba, ta yi masa murmushi sannan ta ce "Wurinka na zo, amma bari na jira ka gama".

"Idan na gama ina da abun yi" ya faɗa a taƙaice.

"Dan Allah yaya habib ko mintuna goma ne"

"Na gaya miki ina da abun yi, fita ki bani wuri" tsayawa ta yi tana kallonsa, tare da tura baki, babu alamar ma za ta fita ɗin.

"Ba magana nake yi ba?"

A shagwaɓe ta ce "Dan Allah"

Ɗaya daga client ɗin ya ce "Barrister a taimaka mana, kar ta yi kuka"

Ya ce "Ta daɗe ba ta yi ba, ba zaki fita ba?"

Nabila ta ce "Ya ka ke korata kamar wata kare ne? Na san ina yin laifi, ka yi haƙuri na shiryu ai"

Tsaki yayi, ya cigaba da rubuce-rubuce.

Ta tura baki ta fice, a zuciyarta ta ce "Ai ko da me ka ke yawo, sai na samu abun da nake son ji a wurinka"

Ta je ta samu MD, suka gaisa, sannan ta ce "MD, ka ga Barrister Habib ko, na je na bashi haƙuri, amma ya kore ni a gaban mutane".

Ya yi murmushi ya gyara gilashin fuskarsa ya ce "Anya ba wani laifin ki ka yi masa ba?"

"Ba laifi na yi masa ba, haƙuri na je ba shi fa, amma ya kore ni a gaban mutane"

MD yayi murmushi ya ce "Ai ke ɗin ce ba kya ji, ya so ya koya miki aiki yadda yakamata, mussman yadda ki ke da faran-faran da mutane, amma ki ka ƙi ba kya so, idan ya saka ki aiki ki ƙi yi, dole ku din ga faɗa ai"

Nabila ta ce "Na daina fa, so nake na zama ƙwararriya a kan aikina, ko dan farincikin Abbana, ku yi haƙuri"

Ya jinjina kai ya ce "Shikenan, Allah ya sa, ki je ki bashi haƙuri"

Ya ce "Bayan ya kore ni, yauwwa sir dan Allah ka san barrister Naja'atu Bunkure?"

Ya jinjina kai ya ce "Yes, she's famous a tsakanin lauyoyi, har ma da jama'ar gari ma, ai sananniya ce sosai"

Nabila ta yi murmushi ta ce "Wow ina yin matar nan sosai da sosai, yadda take gudanar da aikinta, ya ƙara jan hankalina a kan aiki, ai mun ganta kotu a lokacin da mu ka je kotu last, ni da barrister Bashir, ƴar gayu da ita"

"Nabila, ke dai ki na son harkar gayu, amma ba gayun ba, ki mayar da hankali sosai a kan aiki, ki yi ƙoƙari ki kamo ta, ko ma ki fi ta".

"In sha Allah, na yi maka wannan alƙawarin but i need your support"

Ya murmusa ya ce "Kin samu, ɗari bisa ɗari, ƴar gidan major"

"Yauwwa to ka bawa barrister Habib haƙuri, zan koma team ɗin sa dan Allah kar ya sake korata, mussaman a gaban mutane"

"To za a bashi in sha Allah"

Ta miƙe tsaye tare da faɗin "Godiya nake" ta fice ta bar office ɗin cikin nishaɗi.

"Bunkure na ki zai zo mini da sauƙi, saura kuma Aminu Viper"

***
Major ya ɗan tsurawa Uwargidan sa mama da ta tattare kwanukan da ya kammala cin abinci.

Ta ɗago su ka haɗa ido, ta ce "Ya dai?"

"Nasir"

"Me yayi?"

"Ki ja masa kunne, hawainiyarsa ta kiyayi ramata, na daɗe da gane in da ya dosa, amma tun da kin daƙile abun, to ya ƙara nesanta kansa da ƴa ta, kar ya kuskura in ji ko in ga wani abu da zai sosa zuciyata, kuma kar ya kuskura ya saka ta fara son shi, tun da ba ki amince ba, balle a jefa ta cikin yanayi mara daɗi".

Cikin rashin fahimta ta ce "Amma major, wani abun ya yi ne?"

"Bai yi komai ba,gugar zana dai nake yi, idan ma yana shirin yin, to ya shiga hankalinsa" cikin mamaki take bin sa da kallo, tabbas idan aka ji major  yana magana da kurman baƙi, akwai abun da ya gani, kuma ko me za ayi, ba zai fito yayi bayanin abun da yake nufi ɗin ba.

****
Kamar ɓarawo haka yake zagaye tilon matsakaicin gidan, wanda can nesa da gidan, kamfanunnunka ne, sai gonaki.

Cikin ƙasaita yake tafiyar, yana yi yana duba ƙaramar wayarsa mai madannai.

Kamar korarre, haka wani matashi ya ƙaraso in da yake tsaye.

Ya ɗaga kai ya kalle shi ya ce "Menene labari, yaya aka yi ka fito?" Cak matashin ya tsaya, ya ce "Wai dama ba kai ne ka fito da ni ba?"

"Me zan tambaya idan na san komai?" Yayi maganar a ɗan hasale.

"Wallahi master....

Cikin wata irin razananiyar tsawa ya ce "Kar ka sake kirana da wannan sunan"

Cikin tsuma ya ce "Tuba nake oga, suɓutar baki ce, ban san waye ya fito da ni ba, kawai cewa aka yi na tafi"

Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Kuma ka tabattar da ka gaya musu sunana, cewar ni ne me kayan?"

"Wallahi na faɗa musu"

Ya jinjina kai ya ce "Shikenan"

Ya ɗaga rigarsa ya zaro wata sharɓeɓiyar wuƙa, ya danƙa masa ya ce "Maza ka fasa cikin gari, unguwarmu, su walid sun tafi yaran Madaki zaku farwa babu sani babu sabo, idan an yi ram da wani daga cikin ku, ku ambaci sunana, ku ce ni ne jagoran aika-aikar, amma ku kiyaye ƙa'idar aikina"

Ɗan mama ya risuna ya ce "Umarninka ne abun biyayya a gare ni, an gama za ayi yadda ka ce" ya soke wuƙar ya juya, ya tafi da sauri yana haɗa hanya..

Cikin ƙaramin gidan ya shiga, ya nufi ɗakin kwanansa, ya kunna fitilar wayarsa, ya kunna ƙwan solar, haske ya gauraye ɗakin.

Ya saka mukulli ya rufe ɗakin, sannan ya zauna yayi shiru tsawon mintuna, daga bisani kuma ya ɗaukko wiwi ya naɗa ta, ya kunna ya fara zuƙa.

Madadin ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login