Showing 144001 words to 147000 words out of 152254 words

Chapter 49 - ?arfe A Wuta Book 1 Hausa Novel Complete

15 Dec 2024

361

Abbu yake salla, ya yi sallar asuba a waje, ya jira ya fito, Abbu yana tafe ya ji kamar ana bin sa a baya, ya tsaya ya waiwaya, duk da gari bai gama yin haske ba, da sauran duhu, amma hakan bai hana abbu gane Al'amin ba.

Ya tsaya, jiki a sanyaye ya ƙaraso, Al'amin ya risuna ya ce "Ina kwana"

"Kai daga ina? Ina ka tafi tsawon kwanakin nan? Duk yawonka ba ka wuce kwanaki kaɗan, amma ban sake saka ka a idona ba" kallon Abbu yayi, yana tunanin da ma yana jin wani abu idan bai saka shi a idonsa ba?.

"Ina nan"

Abbu ya ce "Kana can kana shashanci, gaishe ni ma ba zaka iya zuwa ka yi ba ko?"

Ya ce "Korata ka ke idan na zo"

"Ba dole in kore ka ba? Tun da kai a rayuwarka ba ka gaya wa kanka gaskiya, kuma duk in da ka zauna sai an yi faɗa da kai. Ka yi salla ne?" Al'amin ya jinjina kai.

"To wuce mu tafi" yayi maganar yana nuna masa hanya, sai Al'amin yayi ajiyar zuciya, tare da tuna masa baya, da yake ɗora shi a wuyansa idan suka dawo daga masallaci, har tsere suke yi da Abbu, duk yadda Abbu yake ji da shi, yanzu ya zama tarihi.
Yana tuna abun da ya faru ƙarshe, sharrin da Rahila ta yi masa, sai ransa ya ɓaci, ya ƙi shiga layin ya tsaya.

Abbu ya waiwayo ya ce "Ya ka tsaya kuma?"

"Tafiya zan yi"

"Zuwa gidan uban wa?"

Al'amin ya ce "Da wani idon zan kalli sauran mutanen layin, bayan ga sharrin da aka yi mini, idan na ga matar nan, zan iya kasheta, sai anjima kawai na tafi, dama ganinka nake son na yi, tun da kana lafiya Allah ya ƙara lafiya" ya juya ya tafi, Abbu ya tsaya yana kallon Al'amin har ya ɓace wa ganinsa.

Ko da ya koma gidan da suke, walid ya fuskanci Al'amin yana cikin damuwa, yayi masa tayin sigari, ya girgiza masa kai, can ya ce "Walid"

Ya amsa da "Na'am"

"Dan Allah ya aka yi ka fara Shaye-shaye?"

Walid ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Wan babana ne ya cinye mini gado, nake ta wahala ina fama da rayuwa, matsin rayuwa ya isheni, kuma shi ba tallafa mini yake yi ba, kawai na fara dafar kan kayan mutane, kuma da nasa na fara, aka kama ni aka kulle, rodi ma na sata lokacin, aka ɗaure ni watanni shida, da aka kai ni prison ban saba ba, nake ta kuka saboda wahala, a can na haɗu da mai gida, sarki dodo, ya din ga kula da ni, bayan ya fita ya dawo ya biya mini tarar aka yanke mini, sake ni, kawai ya cigaba da kula da ni"

"Ina mamanka?"

Walid ya ce "Taɓ tana can tana fama da rayuwarta, kinko ya kanannaɗe rayuwarta, wannan tsohon auran wan baban namu, ya tattare gadonmu ya cinye, Sakandire kawai nayi, ita ma ba ganewa nake yi ba da kyar na kai. Tana fama da kula da ƙannena, ga bata da cikakkiyar lafiya, ni kuma bana iya tallafa mata, har gara yanzu mai gida ya kan bani kuɗi ya ce na je na gaishe ta"

Al'amin ya jinjina kai ya ce "Ka cigaba da kula da ita, dan duk ranar da ka rasata, za ka yi kuka, kuma kar ka bari ta san irin rayuwar da ka ke yi"

"Na nawa kuma, ai wancan tsohon munafukin tuni ya gaya mata, tana yi mini nasiha sosai da addu'a, ba ta taɓa fushi da ni ba"

Daga haka Al'amin yayi shiru, yana cigaba da tunani.

Da sannu Al'amin ya zama gawurtaccen mashayi, duk in da dodo za shi, da Al'amin. Ta kai ta kawo har kudancin Najeriya yake tafiya da Al'amin, ba fatauci ba, har wuraren sarrafa miyagun ƙwayoyi Al'amin ya sani, har manyan mutane a ƙasar nan da suke ta'amalli da su da kasuwancin su ya sani.

Ya haɗa Al'amin da wani inyamuri, ya ƙara gogar da shi a kan harkar na'ura mai ƙwaƙwalwa, yadda ake amfani da ita a aikata laifuka daban-daban, suka sake danganawa da wani bature, ya ƙara koyar da Al'amin sarrafa computer wurin yin laifuka.

Ya zamana kasuwancin miyagun ƙwayoyi, na ƙasashen da suke maƙwabtaka da Nigeria, Al'amin ke tafiyar da kasuwancin su ta online.

Bai tsaya a nan ba, har cikin manyan 'yan fashi, dodo yake shiga da Al'amin.

Dodo ba ya fashi da makami, amma zama a gidajen gyaran hali daban-daban ya sanya ya san masu laifuka kala-kala da yadda ake aikata su, bai fiye harkar daba ba, yafi gane wa safarar ƙwayoyi da makamai.

Idan aka cewa Al'amin magajin dodo, sai dodo ya ce "Wannan dodon, da sauran imani a ransa, ɗan ƙaramin dodo ne, ba zai iya zama kamar ni ba, sonake ya horu, yadda zai iya tunkarar kowane ƙalubale, ciki har da babban burinsa na son ganin bayan madaki, dan kuwa madakin ma ya ƙwafe shi a rai, na cewar sai ya ga bayansa, tun da na saka ya sanya gwiwar sa a ƙasa wurin bashi haƙuri".

Duk wani sirri na dodo, babu wanda Al'amin bai sani ba, kallon abu dodo yayi Al'amin ya san me yake nufi.

Kai tsaye ya kan tura Al'amin wurin indabo, a lokacin yana fafutukar neman kujerar ɗan majalisa, sai dai wasu lokutan baya son dodo ya aika masa Al'amin, dan idan yayi masa abun da bai yi masa ba, tafiyar sa yake ya ƙyale shi, ba ya jure cin zarafi ko wulaƙanci, komai ƙanƙantarsa, ya yaɓawa indabo baƙar magana ya ƙara gaba, duk ba abu ne mai wahala a wurin Al'amin ba, Indabo ya kai wa dodo ƙarar Al'amin.

Amma ya ce "Ina nema masa afuwa, ka riƙe Al'amin yaro ne mai amana, kuma duk cikin yarana babu wanda zai iya yi maka aikin da ka ke so bayan shi, yaro ne mai amana sosai da sosai, kuma ba shi da surutu, hakazalika yayi hannun riga da tsoro.

Dodo ne ya nuna masa makamai kala-kala samfurin wuƙaƙe, da in da in ka sakawa mutum zaka kashe shi, da wanda za ka yi masa illa.

Dodo yana yawan faɗar, Son da yake yi wa Al'amin daga Allah ne, bai taɓa son abu sosai da yake jin sa a ransa kamar shi ba. Ya san son da yake yi masa, ba zai kai na ɗa da uba ba, dan haka ya din ga mamakin yadda aka yi, mahaifin Al'amin ya wofantar da shi, duk da soyayya irin ta ɗa da uba.
Ba yadda bai yi da Al'amin ya ɗora karatu ba ya ƙi.

Ya ce "Aminullahi, harakar daba da shaye-shaye ba abune da nake yi maka fatan ka ɗore a kai ba, yakamata ka koma makaranta.

Al'amin ya ce "Ni ma ba na fatan na ɗore, ina ɗaukar fansar abun da madaki yayi mini zan bar daba".

Ya dafa kafaɗarsa ya ce "Ina maka fatan hakan, sai dai haryanzu ba ka kai ƙarfin da zaka tunkari yaron nan ba, dan kuwa shi har da tsafi yake yi, kai kuma na san komai za a yi maka, ba zaka yi tsafi ba, amma ba a shiga dawa dan ƙarya, ko na kare kai, zan nema maka".

Duk da an ɗauki lokaci, yaran madaki ba su shiga unguwar su Al'amin ba, sai rana tsaka, suka shigo unguwar neman faɗa, a karon farko Al'amin ya ɗauki makami, jikinsa na wata irin tsuma, zuciyarsa na tafasa, wanda hakan ya faru ne a sakamakon abubuwan da yake ta'amalli da su.

Dan shaye-shaye nasa, kala-kala ne, kowanne akwai lokacin amfaninsa. Idan wani aiki yake son yi, ba ya son gajiya da wuri, sai ya banki wiwi sai ya daɗe yana abun da yake so, ba tare da ya gaji ba. Idan kuwa rashin mutunci yake son yi, haka zai yi mata haɗe-haɗe na mussaman, haka ma idan so yake ya bugu. Bai fiye ta'amalli da ƙwaya sosai ba, ya fi ƙarfi ga wiwin.

Ya je ya samu yaran, kan mai uwa da wabi, yayi musu ɓarna, sannan ya taka har dabar madakin, ya yi masa warning, "Ka gargaɗai karnukanka, a kan shigar mini area su nemi faɗa, idan ba haka ba, kan babban karen zan zo, na yi masa takunkumi, yadda haushi ma sai ya gagare shi"

Madaki tun da dodo ya sanya ya bawa Al'amin haƙuri, ba su sake arangama ba, kusan shekara biyu, sai a wannan lokacin, sai da gabansa ya faɗi, saboda yadda kamannin Al'amin suka juye, ƙarara alamun shaye-shaye suka bayyana a tare da shi, yadda ya sake zuwar masa kai tsaye ba tsoro ko fargaba, ya sanya shi gane kuskuren da ya yi na barin Al'amin a raye.

Tun da Al'amin yake tare da dodo, bai taɓa rashin kuɗi ba, kuɗi yake kamawa manya da ƙanana, kuma bai taɓa ci wa dodo amana ba.

Har a cikin ma'aikata, ana samun ɓata gari waɗanda suke sayar wa dodo kayan maye, idan sun kama, duk wani salo na yadda ake sayar da kayan, ba tare da an gane ba, Al'amin ya goge, haka idan kana ta'amalli da su, kallo ɗaya zai yi maka ya gane.

Yan kwamutin unguwa, suka kai ƙarar Al'amin wurin hukuma, a kan yana tayar musu da tarzoma, ba tare da la'akari da yaran da suke rashin jin tun kafin ya fara ba.

Dodo ya je ya samu shugaban 'yan vigilant, ya ce masa "Wallahi duk wanda ya sake ɗaukar ƙafa, ya kai ƙarar Aminullahi sai ya ci ubansa, lokacin da aka kashe ɗan uwansa ku nawa ku ka tashi ku ka je wurin jami'an tsaro domin ganin an ƙwatarwa yaron hakkinsa, saboda ba yaranku aka kashe ba. Lokacin da yake ragaita ba shi da sana'a, mutum nawa ne suka mayar da shi makaranta? Ko suka bashi sana'a, dan mahaifinsa ya wofantar da shi, kuna 'yan unguwa ba ku ga dacewar ku nusar da shi kuskuren sa ba? Ai duk society da suka yi watsi da yaran su irin su Aminullahi muna nan muna jiran su, mu zamu karɓe su, mu mayar da su abun da ya dace. Gargaɗi nake yi, ni dai an san ba zan kamu ba, to haka Al'amin ma, ko bayan raina, ina da masu fito mini da shi idan ya shiga cakwakiya. Ku shirya Al'amin bai fara yi muku rashin ji ba tukuna"

Ƴan unguwa suka rasa abun yi, yaransu da suke ƙanan rashin ji, suka fara bin Al'amin, yana ba su kayan wiwi suna sayarwa, yana ba su kuɗi, dama gashi da kyauta kuma ba shi da baƙin ciki.

Duk yaran dodo, suna shakkar Al'amin, ko dan saboda masifar dodo idan aka taɓa shi, dama Al'amin ya fi yin faɗa da Walid, dodo ya kan ce masa Mai laya, ka kiyayi mai zamanin nan, idan ka ƙure shi, ba zan saka baki ba, idan ya tashi yi maka ɓarna ba. Su yi faɗa su yi daɗi.

Tafiyar gaggawa ta kama dodo, zuwa kudancin Najeriya, sai dai ya ce wa Al'amin ya zauna, ya kula masa da harƙallarsa ta kano, ba zai tafi da shi ba.

Abun da Al'amin bai taɓa yi ba, sai a wannan karon ya ce "Meyasa ba zaka tafi da ni ba?"

"Aminullahi, tafiya ce mai hatsari, ka kula mana da harƙallarmu, sannan kar ka manta rules ɗin, a tafiyarmu babu BODMAS, idan ka ji wuta, ka wargaza komai ka ɓace"

Al'amin ya jinjina kai ya ce "Allah ya taimaki sarki babban dodo"

"Na gode, Allah ya ja zamaninka, zuwa in da ba ka zata ba, a cigaba da riƙe amana Aminullahi" haka nan Al'amin ya ji baya son dodo ya tafi.

Kwana uku da tafiyar Dodo, suna zazzaune, suna shan sigari, aka jefo wata jaka ta katanga.

Walid ya ɗaukko jakar, wasu daga cikin yaran wurin, suka fita da gudun tsiya, suna neman wanda ya jefo jakar, ba su ga wanda ya jefo ba.

Al'amin ya ja jakar ya buɗe, kawai yayi tozali da kayan dodo a ciki, face-face da jini, har da takalminsa.

Cikin ƙaraji Al'amin ya ce "Nooooo" ya tashi jikinsa yana tsuma ya girgiza kai ya ce "Impossible, ba zai yiwu ba, sarki yana raye, raina mana hankali kawai ake yi"

Walid ya riƙe Al'amin ya ce "Al'amin ka nutsu mana, musulmai ne mu, idan ba a kashe sarki ba, babu yadda za ayi a ciro kayans jina-jina a kawo mana".

Al'amin ya fara neman ya fita hayyacinsa, Walid suka danne shi, suka shaƙa masa wani abu, jikinsa ya saki ya hau bacci.

Al'amin ya razana, ya shiga tashin hankali, ya ɗimauce sosai da sosai, da mutuwar dodo, ba zai manta gudunmuwar da ya bashi ba, duk da ba ta arziki ba ce ba, Al'amin kamar zai zare.

Duk wata hanya da zai bi ya gano wanda ya kashe dodo, ya rasa, damuwa ta ƙara yi masa yawa.

Ya ɗaukko makaman da ya saka aka ƙera masa, sweazland, Russia da kuma iraƙi, ya zuba musu ido, bai taɓa zaton ya shaƙu da shi haka ba.

Mussman madaki ya zo ya sami Al'amin, yana ƙyaƙyata masa dariya, wai garkuwar da fake a bayanta, an samu wani gwanin saitin ya rusata, yanzu zai koma Al'amin ɗin sa matsoraci na ainihi.

Sai dai cikin sa'a, Al'amin yana tare da sweazland, dan haka madaki ya fara yi wa rauni da ita ya ce "Dan an fasa garkuwata, ba ya nufin zaka cim mini,  *Ƙarfen cikin wuta nake* na fi ƙarfin ɗauka da hannu, ko da mariƙin roba, daga yau ka rubuta ka ajiye, ɗaya ya riski ajalinsa ne kawai zai kawo ƙarshen gabata da kai".

Madaki ya kalli cinyarsa da ke jini ya ce "Meyasa ba ka kawo ƙarshen gabar yanzu ba, ka kashe ni?"

"Saboda na fika sanin waye kai, akwai lokacin da ya dace da hakan".

Yaran dodo, sun so Al'amin ya gaji harƙallar dodo, ba ita ba har manyan hada-hadarsa da manyan mutane. Amma Al'amin yaƙi, ya ce baya buƙatar duk wani abu da zai din ga tuna masa da dodo, kuma zai yi abun da zai Allah zai gafarta masa, ba ɗorar da laifukansa a bayan ƙasa ba.

Da yawa sun so su ya basu sirrikan dodo, su cigaba da sana'arsa, amma Al'amin ya ƙi, ƙarshe ma suka bar wannan gidan gaba ɗaya, ya je ya kafa masa sansanin.

Walid suna zuwa da Al'amin duba mahaifiyarsa, da ciwon Cancer ya kama, aka kwantar da ita a asibiti, kullum cikin neman jini ake, duk wani kuɗi na Al'amin, sai da ya ƙare a wurin kula da mahaifiyar Walid.
Liti dama shi isaknci ne da abokai, suka saka ya lalace, dan har waje babansa ya kai shi yin karatu, bai koyo komai ba sai shashanci ya dawo.

Kasancewar jinin Al'amin da na babar Walid iri ɗaya ne, ya bayar da jininsa sosai an saka mata, kullum cikin Kwantar wa da Walid hankali yake, tare da bashi tabbacin zata warke.

Har zariya suke kaita Asibiti gashi, amma cikin ikon Allah ta koma ga Allah, abun nan da Al'amin ya yi wa walid, ya sanya ya sanya duk abun da zai yi masa baya fushi da shi, ko yayi sai ya huce.

Suka koma ƙaramar harƙallar sayar da wiwi, idan kuma aikin ƙarfi ya samu su yi.

Al'amin ya numfasa sannan ya ce "Ban kuma taɓa kashe kowa ba, duk rashin ji na, wanda ki ka ganni da shi, liti ne, yaran madaki suka soka masa wuƙa, kar ki sake cewa na yi kisan kai".

Jauhar wani irin kuka take man ban tausayi, rayuwar Al'amin akwai tarin ƙalubale, sai ta ga ita tata rayuwar nafila ce.

"Ki yi haƙuri, da yawan furta miki zan sake ki da nake yi, baki cancanci mutum mai tarin laifuka irina ba, wallahi ba zan iya yafewa madaki ba, da shi da wanda suka kashe dodo. Ban yi miki alƙawarin daina abun da nake nan kusa ba, binciken da na ƙara yi akan ki, na fuskanci kusan ƙalubale ɗaya muka fuskanta, dan na san duk wani abun alkhairi wannan shegiyar matar ba zata bari ya raɓe ni ba, dan haka na yi zaton ta shirya mini wata maƙarƙashiyar ne, dan haka ta aura mini ke, ashe wai wani mai kuɗi zaki aura, suka hana ita da wannan banzar matar ta gidanku, ban manta lokacin da take zuwa gidanmu ba ita ma. Haryanzu a shirye nake, mu rabu ki auri mutumin kirki, baki dace da ni da rayuwata ba, rayuwata ta riga ta gurɓace, kullum kina cikin tashin hankali bai kamata ba, duk a sanadina. Dama kin ga ke kalar matan masu kuɗi ce, in da zaki huta a kula da ke sosai. Ni kuma na gurgura na ƙarasa rayuwata"

Jikinta na rawa, ta toshe masa baki, ta kalleshi, hawaye wani na bin wani a fuskarta, amma ta kasa magana ta cigaba da sheshsheƙar kuka iya ƙarfin ta.

Ya sauke hannunta daga bakinsa ya ce "Lafiya kuwa? Wannan kukan fa?"

"Zan zauna da kai a haka, na san wataran zaka daina, a lokacin da raɗaɗin kaɗaici da damuwar da ka ke ciki suka barka, a lokacin da ka fahimci wani zaluncin idan an yi maka wata shari'ar sai a lahira, ba zaka iya ɗaukar wa kanka mtaki ba. Zan zauna da kai har zuwa lokacin da komai zai zama tarihi. Ni ba zama da mai kuɗi ne damuwata ba, kwanciyar hankali nake so, in da za a ga mutuncina a kula da ni, dama miji nagari nake fata ba mai kuɗi ba".

Ya lumshe idonsa ya buɗe ya ce "To ni na garin ne?" Ta jinjina masa kai alamar eh.

Murmushi ya yi ya ce "Tashi ki je ki kwanta, ɗaya da rabi yanzu. Ba zan manta ƙoƙarin ki a kaina ba, kina cikin mutane ma su muhimmanci da ba zan manta da su ba" da ta kalleshi, sai ta cigaba da zubar da hawaye, wani irin tausayin sa na ratsa zuciyar ta.

Ya gyara pillow zai kwanta, ya kalli yadda take ta kuka, ya ce "Har mamki ki ke bani, yadda ki ke taƙarƙarewa ki yi ta kuka, ni fa da wayona, zan iya ƙirga sau nawa na yi kuka". Yayi maganar yana kwanciya amma ta cigaba da zama a wurin.

"Idan ki ka bari na rufe ki a ɗakin nan, akwai ƙura" ta kalle shi ya ce "Ban taɓa ɗaga sweazland na fito da harshe, ba ta sha jini ba, sai a wannan karon da ki ka hana ni, ko ki tafi ko in sha naki jinin in huce".

Wato shi gaba ɗaya labarin da ya bata ma, ko a jikinsa.

Sai da ta gama koke-kokenta, sannan ta tashi ta fita daga ɗakin.

Ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login