Showing 78001 words to 81000 words out of 152254 words

Chapter 27 - ?arfe A Wuta Book 1 Hausa Novel Complete

15 Dec 2024

351

sallar la'asar a gida aka yi ta a unguwar, saboda tashin hankali.

Bayan Baba ya yi sallar la'asar, ya kira mama ya ce, ya shirya masa jauhar, ya kaita da kansa, tun kan yaran nan marasa ji su ce za su yi mata illa.

Idanun jauhar duk sun kumbura, sun jawur saboda azabar kukan da ta sha.

Mama tana dariya take cewa "Haba Jauhar, kowa da haka yake kafa nasa iyalin, da haka kowa ya saba"

Jauhar ta kalli mama, iya wannan tashin hankalin bai isa ya sanya su gane sun jefa rayuwarta a garari ba, amma take yi mata wannan surutan? Haka ta yi alwala ta yi sallar la'asar, sai dai ta kasa addu'a ma.

Ko kaya ba ta canza ba, mama ta ɗaukko mayafi, ta ce tare za su kaita ɗakin miji.

Sun fito waje, Saifu ya kawo kai, yayi turus ya ce "Baba, yanzu wannan tashin hankalin da aka yi a unguwar nan, duk a kan auren nan, bai sanya ka saduda ba, ka haƙura? Baba ya yi masa shiru, ya yi gaba hannunsa riƙe da na jauhar, ya buɗe mata mota ta shiga baya, suka ja suka tafi.

A can suka tarar da wasu daga danginsu Al'amin, a gidan suka din ga rangaɗa guɗa, da aka ce an kawo amarya, dan sun baro can gidan su Al'amin, a kan Abbu zai aika da motocin ɗaukko amarya, sai dai suna ganin Baba suka nutsu suka yi shiru.

Har kan gado ya kaita ya zaunar da ita, ya riƙe hannunta, ya din ga yi mata addu'a, sannan ya sunkuya ya yi ƙasa da murya ya din ga yi mata nasiha, yana yi tana kuka, sai da ya gama ya din ga saka mata albarka ya ce mama ta wuce su tafi.

Angon kuwa yana can dabar su, ban da bushe-bushen sigari, babu abun da yake yi, hatta dambarwar da aka yi a gidan su amaryar bai sani ba, shi dai ya san Walid ya ce za su gayyato 'yan gangi da 'yan tauri, ayi nishaɗi.

Bai ma san a ina aka ya ba, balle ya san abun da ya faru.

Sai wajen ƙarfe takwas na dare, Walid ya dawo, ya din ga ba shi labarin, abubuwan da suka faru, da yadda suka yi da 'yan sanda. A ƙalla ya kai mintuna goma sha biyar yana zuba, yana bawa Al'amin labari, amma bai tanka ba.

Ya gaji ya ce "Maza, ka tashi mu shirya, mu raka ka gidan amarya".

Sai a yanzu ya ɗago ya kalleshi, amma ya yi tsaki ya koma ya kashingiɗa.

Walid ya ce "Wallahi ba ka isa ba, wai so ka ke sai Abbu ya yi fushi da kai? Dama na haɗa maka kayanka jiya, yau sai ka bar gidan nan, kai Allah ya ɗaga darajar ka, kana wasa da damar ka" walid ya cigaba da mita, yana ƙara haɗawa Al'amin kayansa a ghana must go, da masu dauɗa, da wankakku, har da takalma da brush, haka ya din ga danna su.

'yan uwan su Al'amin, babu yadda ba su yi ba, su ga fuskarta, amma fafur ta ƙi, ta din ga ƙudundunewa, suna nan tare da ita har tara na dare, suka gaji ga dare, masu zuwa ganin gida, duk suka gama, suka din ga tafiya, har ya rage saura itakaɗai aka bari.

Nan hankalinta ya fara tashi, daga ita sai farar fitila mai batir, tana ta addu'a a cikin zuciyarta cike da fargaba da tsoro. Tana ta tunanin kar 'yan daba su lallaɓo su zo su kasheta.

Ta gaji da zaman wuri ɗaya, ta ga ledar pure water, a ajiye a falo, da 'yan ganin gida suka zo da ita, ta ɗauka ta yi alwala, ta yi sallolin da suke kanta, ta zauna zaman dirshen tana tuna ƙalubalen rayuwa da ta haɗu da su kashi-kashi yanzu kuma ga ta kuma a wani mataki, mai hatsarin gaske.

Har bayan sha ɗayan dare, sai itakaɗai a gidan.

Fargaba da tsoron da take ciki, ya ninku a zuciyarta. Kasancewar bacci ɓarawo ne, haka ya yi awon gaba da ita daga nan in da take a zaune kusa da gado.

Sai dai ba ta san adadin lokacin da ta shafe tana baccin ba, ta farka a razane, taga hasken wutar lantarki an kawo wuta. Ji ta yi kamar motsi a falon, ta lallaɓa ta leƙa cikin tsoro da tashin hankali bakinta ɗauke da addu'a.

Wani dogon mutum ta gani a kwance a kan doguwar kujera, ya juya bayansa, ya duƙunƙune da babbar riga, da alama sauro ne ya dame shi, ya lulluɓa.

Gabanta ya faɗi, ta koma ta zauna tana tunanin, wannan shi ne angon ko kuwa? Iya ƙoƙarinta ta dage kar ta kuma komawa bacci, saboda tsoron da take ciki.

Al'amin kuwa, Walid ne ya taso shi a gaba, ya kai shi har gidan, daga shi sai shi, da ƙullin kayansa a ghana must go wajen sha ɗaya da rabi na dare.

Suna tafe yana lallaɓa shi, sai da ya tabbatar ya shiga, sannan ya tafi.

Ya shiga yana ƙarewa gidan kallo, shi dai ya san gidan kango ne, amma yadda aka jera masa kaya, yayi kyau.

Yana shiga falon, bai bi ta kan ina amaryar take ba, ya tuntsurar da ƙullin kayansa ya haye kujera ya mimmiƙe kamar gawar sababi.

An fara kiraye-kirayen sallar asuba, ta shiga banɗakin cikin ɗakin, tayi alwala ta din ga nafilfili, har aka yi sallar asuba.

Bayan ta idar tana cikin azkar, wani irin nannauyan bacci, ya kwashe ta a wurin.

Sai da gari ya yi haske, sannan ta farka, ta tashi tana salati, ta tashi tana ƙarewa ɗakin kallo. Yayi kyau sosai da sosai, duk ko fenti babu amma furnitures ɗin sun yi kyau.

Ta fita falon gabanta na faɗuwa, domin gaida mai gidan da no nemanta bai yi ba, sai dai ba ta gan shi ba, ta leƙa ɗaya ɗakin, amma baya nan, sai ghana must go a falo.

Ta fito tana ta lelleƙa gidan, abun ya burgeta, duk da ba ƙerarren gida bane, amma ta ji daɗin cewar gidanta ne ita ke da iko da shi, amma da ta tuna haryanzu ba ta yi ido huɗu da angon ba, sai gabanta ya faɗi, ta fara tunanin ko shi ma auren dolen aka yi masa da ita.

Tunawa ta yi, da 'yan dabar Unguwar su, sun ce idan suka kuma ganinta a unguwar su, sai sun sassarata. Gaba ɗaya ranta ya ƙara dugunzuma.

Ta zauna shiru a falo, tana ta jira, ko wani zai zo mata daga gida, amma shiru babu wanda ta gani, ga yunwa tana ji, dan wunin jiya ba abun da ta ci, gashi ta kwana ta wayi gari ba ta saka komai a cikinta ba.

Can kuwa, Rahila kuwa kamar ta taka rawa, ta rabu da ƙaya, Aminu ya bar mata gida, ta ƙara sakewa da ita da yaranta yadda take so, fargabar ta zata ragu sosai da sosai, ta san yanzu dole zai tattara ya bar unguwar ya ƙara gaba.

Dangin mahaifiyar Aminu da suka zo, daga can ƙauyen tofa, ta din ga wulaƙanta su, dan sai da ta yi wa Abbu masifar dan me za a gayyato su, sai dai a hakan gudunmuwar dubu ɗari biyu suka bawa Abbu na auren.
Ban da uban kayan abinci da suka taho da shi, suka ce a ƙara a kan na biki. Sai dai har suka yi kwana biyun, ko sau ɗaya ba su ga Al'amin ba, sai kwasar takaicin rahila, yadda take wulaƙanta su, tare da aibata shi, tana an mutu an bar mata riƙon masifa da tsiya.

Washegari da safe, waɗanda ba su je ganin gidan ba, suka ce za su je su ga gidansa, daga nan za su wuce su koma tofa. Da Abbu suka yi sallama, Rahila kuwa ko kallo ba su isheta ba.


Har wajen sha ɗaya da rabi na safe, jauhar na zaune na rarraba ido,  ta ji sallma a tsakar gidan.

Amsawa tayi, tana jiran ƙarasowar masu sallamar.

Mata ne wasu 'yan dattijai, da matasan 'yan mata.

Jauhar ta karɓe su hannu bibbiyu, suka shigo falon suka zazzauna, hannunsu da kaya.

Suka gaisa da jauhar, ɗaya daga cikinsu ta ce "Tubarkallah, Aminullahi ya mori 'yar kyakykyawar yarinya Tubarkallah, ya sunanki?"

Jin abun da suka ce, ya sanya ta gane 'yan uwansa ne, ta ce "Jauhar"

Suka din ga maimaita sunan nata, suna cewa sunanta na 'yan birni.

"Ina Aminullahin ne? Tun da mu ka zo, bamu ganshi ba, gashi daga nan can gida zamu koma" cewat wata dattijuwar.

Jauhar ta ce "Ya fita"

"Ohh, ji soko, daga kawo masa amaryar jiya, har ya saka ƙafa ya fice, to Allah ya kyauta. Kin ganni ni kakarsa ce, ga yayar gyatuma tasa, nan duk 'yan uwan mahaifiyarsa ne, amma ba ya zuwa in da muke. Dan Allah kya ɗan din ga saita shi a hanya, ki yi ta haƙuri kin ji, Allah ya baku zaman lafiya"

Kunya ta saka jauhar kasa amsa musu.

Suka yi ta yi mata hira, amma ta kasa amsa musu, saboda nauyinsu da ta din ga ji, sai dai kakartasa mace ce mai barkwanci, suka ba ta kayan da suka zo da su, su tsintsiyar laushi da ta kwakwa, kaskon turaren wuta, kayan miya har da kuɗi.

Jauhar ta yi tayi musu godiya, sai dai ranta duk babu daɗi, ga baƙi amma babu abun da za ta basu.

Zuwa azahar, suka yi mata sallama suka tafi.

Har la'asar babu wanda ya sake zuwa, ta ji babu daɗi sosai, rashin ganin wani daga gidansu ko mutum ɗaya.

Yaran maƙwabta suka ɗan shisshigo mata, shigowar ta su tayi mata daɗi, ta basu kuɗi, ta ce su sayo musu buredi.

Suka sayo, suka zauna, suka ci tare da su, ta ajiye wani da niyyar idan mai gidan ya zo ta bashi.

Mama kuwa bayan sun koma gida daga kai jauhar, duk 'yan biki sun watse, kowa tayi ta kanta.

Suka ƙule a ɗaki ita da zakiyya ta ce "Zakiyya duk da gidan yarinyar nan babu gyara, amma yayi kyau sosai da sosai"

"Eh ai hakan yayi, ma rage wani surutun, har ku ka taho kuwa kun ganshi ya je gidan shi angon?"

Mama ta ce "Ina fa, itakaɗai muka baro, sai wasu 'yan uwan babarsa, su ma na san ba zasu jima ba zasu tafi ba. Nifa sunansa kawai nake ji, ban taɓa ganin sa ba".

"Zaki ganshi ne, ba dai ya zama sirikinku ba? Ni na san shi, amma lokacin yana yaro, ai kin san daga baya suka dawo ƙofar na'isa da ba a nan suke ba, ni tsoro nake ji ma kar yaran nan su cigaba da kawo mana farmaki"

Mama ta ce "Babu abun da za su dawo su yi mana, mun yada ƙwallon mangwaro mun huta da ƙuda, yanzu menene abun yi?"

"Abun yi, shi ne mu jira dawowar wannan Alhajin, mu ga yadda za a ɓullowa lamarin ya haƙura gaba ɗaya da batun ta"
"Haka ne, to Allah ya dawo da shi lafiya, sai ayi ta ta ƙare, jauhar dai an aurar da ita, sai mu jira mu ga yaya zai kasance da namu 'ya'yan.

Gidan jauhar magariba na yi, yara suka watse suka bar ta itakaɗai kamar tsohuwar mayya. Sai fitila ta kunna, ta saka mayafinta ta din ga korra sauro daga ɗakunan, saboda yadda suke ambaliya kamar a barikin su.

Ta rurrufe ko ina, tana jiran ta ga ta ina ango zai shigo, amma shiru.

Har bacci ya kuma cin ƙarfinta ya kwashe ta.

Wunin ranar kuwa, Al'amin zarya ya din ga yi, sai da aka sakar masa yaransa da aka kama a unguwar su madaki, har suka sanar masa iƙrarin da 'yan unguwar da suka yi, na idan suka kuma ganinta a unguwar sai sun sassarata.

A ransa ya ce Allah ya ƙara, maganinsu kenan, da suka ga babu wanda ya dace su bawa 'yar su sai shi.

Tare da su ya wuni yana shaye-shaye, Walid ya na son ya yi masa magana, amma ya san yana yi za su yi faɗa, dan haka sai dare ya sake lallaɓa shi, daga can unguwar ya goya shi a babur ya kai shi gidansa na ɗorayi chiranci.

Sai dai kamar jiya, kafin gari ya yi haske, ya sake barin gidan, gashi ko brush ba ta da shi, ba ta da kayan girki, haka ta kuskure baki ta cinye biredin jiya, gashi ba ta son cigaba da taɓa kuɗin da aka bata, yakamata ta nuna masa kayan da aka bata, saboda 'yan uwan sa ne suka bata.

Ta fito tsakar gida ta samu wani ɗan tudu ta zauna, tana tunanin yanzu haka za ta rayu, wanda ya ajiye ta baya ko ƙaunar ganinta, kwana na biyu kenan haryanzu ba ta ga kalarsa ba ma.
Tana son yin wanka da sauran buƙatu, amma ba hali, babu ruwa, ga rijiya a gidan amma babu guga, babu sauran kayan masarufi.

Ƙwanƙwasa ƙofar da ake yi ya dawo da ita hayyacinta, ta tashi ta ɗaukko mayafi ta saka, ta buɗe a hankali.

Saifu ta gani a tsaye, hannunsa riƙe da kaya.

Ta washe baki ta ce "Yaya saifu" yayi murmushi ya ce "Na'am Waliyiyya"

Ta bashi hanya ta ce ya shigo, ta karɓi kayan hannunsa, suka shiga har falo.

Ya kalleta ya ce "Yaya babu wata matsala dai ko?"

Ta girgiza kai ta ce "Babu"

"Ina mijin naki yake?"

"Baya nan, ya su baba? Ya su mama?"

"Suna nan ƙalau, gida yaƙi kyau ba kya nan, duk 'yan matan nan an rasa wadda za ta yi aikin da ki ke yi" tayi shiru tana murmushi.

"Ga sauran kayanki na kawo miki, na harhaɗo da na ɗakinki duk na kawo miki, muddin ki ga ya yi miki wani abu da baki gamsu ba, ki gudo gida kin ji ko?" Ta jinjina masa kai alamar to.

Ya ce "Kina buƙatar wani abun ne?"

Ta ce "A'a"

Ya miƙe ya ce "Na san ba zaki faɗa ba ai" ya shiga kitchen ɗin ta yana dubawa, babu alamar an dafa wani abu.

Ya ɗauki gas ɗin ta, ya fita da shi, ya yo mata refilling, ya yi mata sayayyar kayan shayi da 'yan kayan abinci, ya dawo ya kawo mata.

Ya ce "Ki yi haƙuri jauhar, bani da kuɗi, amma zan sake dawowa in sha Allah, kar ki yadda da wani haƙuri, na san zaman aure haƙuri ne, amma kar ki zauna ana zaluntarki, ko ya ce zai dake ki, zan sake dawowa in sha Allah kin ji ko" ta ɗaga masa kai alamar eh, ya sayo mata guga, ya janyo mata ruwa ya tara mata, ta din ga yi masa godiya suka yi sallama.

Bayan tafiyar sa, tayi wanka ta canza kaya, yaran maƙwabtanta da suka shgo, ta dafa musu taliya, suka ci ba ta gaza ba, ta ɗebarwa maigidan nasa ta ajiye.

Sai dai yaran da wuri suka tafi yau, ta samu wuri tana wanke-wanke, ta ji kamar an wuce ta bayanta.

Tashi ta yi a firgice, tana addu'a da tunanin ko gane-gane ta fara yi.

Sai dai ta ga takalmi a ƙofar falon, kasancewar gidan akwai gate, kuma akwai ƙaramar ƙofa, ƙofar a buɗe take.

Ta lallaɓa ta leƙa, ba ta ga kowa ba, ta shiga falon tana tambayar waye?.

Fitowa ya yi daga ɗaya ɗakin, hannunsa riƙe da baƙar leda, kallo ɗaya ta yi masa ta gane shi, ƙwala ihu ta yi, ta ruga da gudu ɗakin da gadonta yake, ta rufe ƙofar ɗakin.


Ayshercool
08081012143
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724



Hanyar da ta bi ya bi da kallo, yana tunanin a ina ya taɓa ganin fuskarta.

A ransa ya ce "Mahaukaciya ce kenan, Shiyasa aka aura mini ita, haukana ya fi naki" ya fito daga falon ya saka takalmansa ya fice.

Jauhar kuwa durƙushewa tayi, ta ɗora hannunta a ka ta ce "Na shiga uku" a take ta fashe da kuka ta ce "Allah ka sanya mafarki ne ba gaske ba, Allah ka sa ba wannan ne mijin nawa ba? A gabana ya kashe wani, Allah Ubangiji ka rufa mini asiri ka dube ni, ya Allah ka dubi maraicina da ƙangin da na baro, ka sassauta mini a nan, ya Allah ka sa ba shi ne mijina ba". Ta cigaba da addu'ar tana kuka, ta kasa fitowa sai ma ƙara sakata da ta yi a ɗakin tana kuka.

A take komai ya dawo mata fes, yadda ta ganshi, ya yi kisan kai, hannunsa riƙe da mutum da wuƙa a gefen cikinsa.

"Na shiga uku, ko biyoni yayi ya kasheni, me na yi masa wallahi ban gayawa kowa yayi kisa ba" tayi maganar ƙasa-ƙasa tana kuka.

Ko da wasa ba ta yi yinƙurin, sake buɗe ƙofar nan, a banɗakik nan tayi alwalar magariba da ta isha'i, ta kasa addu'a komai, sai fatan Allah ya sa ba wannan ne mijinta ba.

Ba ta sake fitowa ba, har garin Allah ya waye.

Zaman ɗakin ya isheta, fitowa kuma ta gagareta, sai da ta leƙa ta ga babu kowa a falon, bakinta ɗauke da addu'a ta fito.

Ba kowa, ta leƙa tsakar gida, ya rufe mata ƙofar, babu taklmansa kuma a wurin.

Ta dawo falon, ya cinye taliya da man da da ta zuba masa tas, ya ajiye komai a wurin, hatta wadda ta ɗan zube a ƙasa bai kwashe ba, jug ɗin ma daban kofin jug ɗin daban.

Ta kwashe komai ta fitar tsakar gida, ga sauran kwanukan da ta fara wankewa ta bar su a wurin, komai yana nan.

Sai zuciyarta ta fara raya mata, ai ba shi ne mijin nata ba, ya shigo ne kawai ya tsorata ta, sai ta cigaba da addu'a Allah ya ƙara nesanta ta da shi.

Ta yi 'yan gyare-gyaren ta na gida, yaran da suke shigo mata, yau ba kowa duk sun tafi makaranta, ga tsakar gidan wasu irin manyan ƙadangaru suna bin bango, dan haka fitowa tsakar gidanma wahala yake bata, saboda tsoro.

Ta datse gidan, yadda babu wanda zai shigo sai ya bubbuga.

A jere ta sake jera kwana biyu ba ta sake saka shi a idonta ba, akwai ranar da bai kwana a gidan ba. Bai sake dawowa da rana ba, sai cikin daren nan, idan ya tarar da abinci ya zauna ya cinye abun sa, kafin ta tashi ya fice.

Abun ya fara damunta, ga tsoron gidan take ji, sosai da sosai.

Wajen la'asar ta ji ana buga ƙofa, ta din ga tambayar waye, amma ta ji shiru.

Har zata haƙura da buɗe ƙofar, ta zata ba kowa, aka kuma buga gate ɗin maimakon ƙofar da ƙarfin gaske.

A tsorace ta buɗe, aikuwa ya hankaɗo ƙofar, ta kuma kurma ihu, ta kwasa da gudu, ta shiga kitchen ta rufe ƙofa.

Sororo ya tsaya yana tunanin, ihun me take yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login