Showing 105001 words to 108000 words out of 152254 words

Chapter 36 - ?arfe A Wuta Book 1 Hausa Novel Complete

15 Dec 2024

355

komai ba.

"Ka santa ne?" Yayi shiru bai amsa ba, daga haka ta ja bakinta tayi shiru.

Babu yadda ba ta yi ba, a kan ya je a ƙarasa allurar nan, amma ya ƙi. Da ya ji ƙwarin jikinsa ma, fita ya cigaba da yi.

Jauhar na zaune a falonta, tana tunanin ƙirƙirar sabbin styles na abun hannu da jigida, ta fara sayarwa.

Aka bubbuga mata gate, ta tashi ta je ta buɗe, ta ga wani mutum da ba ta san shi ba, fuskarsa sanye da facemask ya ce "Mai zamani yana nan?"

Ta girgiza kai ta ce "Ya fita"

"Ga wannan ki ajiye masa". Ya bata leda mai baƙi da fari.

Ta karɓa ta ce "In ji wa zan ce?".

"Idan ya zo zai gane, ki ajiye masa a ɗakinsa, zan kira shi"

Ta ce "To shikenan"

Ta rufe ƙofa, kamar ta buɗe, sai ta fasa ta kai masa cikin drower sa, ta ajiye masa ta cigaba da sabgoginta.

Kayan da anty lubabatu ta bata ta ɗauka tana duddubawa, ta ɗan ɗanɗana abun, tayi shiru tana tunani, ita sam abun da ake faɗa a auren, ba ta ga alamar sa ba, dan shi ba ta tata ma yake yi ba, ya ƙule a ɗakinsa yayi shaye-shayensa ya ci abinci ya fita yawonsa shi ne kawai a gabansa.

Ta ɗan taɓe baki, ta ɗauki turaren wutar, ta tirara na gidan, ta turara na jikinta, ta ɗora girki.

Da daddare da wuri ya dawo gida, gidan sai ƙamshi yake yi na musamman, giftawar farko da tayi, sai da ya ɗaga kai ya kalleta, ƙamshin har cikin ƙwaƙwalwarsa ya ji shi.

Yau  faten dankalin ta yi, dan shi ne kawai da su, sai dai yayi masa daɗi bai taɓa sanin ana faten dankalin hausa ba, sai yau da ta bashi, har mamakin yadda take sarrafa abinci yake yi.

Ya gama cin abincin ta ce "Master yanzu allurar nan dai ba za a ƙarasa ba ko?"

"Eh" ya faɗa kai tsaye.

"Ai shikenan, thank God tun da ka warke ai. Ka yi mini addu'a mun kusa fara WAEC, Allah ya sa result ɗina yayi kyau".

"Sai ki yi karatu"

"Ina yi ai" ya kalleta ya ce "A hakan, kina shirme dai" ta gane da kayan beat ɗin ta da stone yake, tayi murmushi jin yadda yau yake yi mata doguwar magana.

"Ina karatu sosai da sosai fa".

"Akwai kwaɗo a ƙarƙashin kujerar nan da ki ke" da sauri ta kalli kujerar, sai kuma ta yi dariya ta ce "Ai na daina jin tsoron" wai nan tsokanarta yake yi, amma fuskar nan a haɗe.

Har wajen ƙarfe goma suna tare, yana ta danna wayarsa, mai madannai, ita kuma tana jin radio tana aikinta, ba hira suke yi ba, amma kasancewar su a hakan ma, daɗi take yi mata.

Ya yi miƙa ya tashi zai tafi ɗaki ta ce "Tafiya babu sallama"

Ba tare da ya yi Magana ba, ya ɗaga mata hannu, murmushi ta yi ta ce "Asuba ta gari mijin Angela" ɗan rausayar da kai ya yi kamar zai yi murmushi ya shiga ɗakinsa.

Ya kwanta yana shaƙar ƙamshin da bedsheet ɗin sa yake yi, bai taɓa tunanin zai yi aure ba, dan babu wannan lissafin a gabansa, ba dan albarkacin auren ba, da a cikin tsummokara zai kwana a can gidan da suke tare da su Walid.

Tsakar dare jauhar ta ji motsi, kamar ana watsi da kaya.

"Malam kar ka shiga wannan ɗakin ba komai a ciki, mata ta ce a ciki, kuma babu in da shari'a ta baka damar shiga in da matata take"

Jin muryar Al'amin, ya sanya ta saukko daga kan gadon da sauri, wata irin dalleliyar fitila aka saka ana haske gidan.

"Shut up, kar ka sake magana, kar na sake jin bakinka"

Cikin ƙaraji ya ce "Sai na yi magana, wallahi ka shiga ɗakin nan, zan illataka".

Da gudu ta fito dan ta ga meyake faruwa, ma'aikata ta gani, har da jami'an tsaro, sun saka wa Al'amin ankwa sun durƙusar da shi a kan gwiwoyinsa.

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Yallaɓai me yayi muku? Laifin me ya yi?"

"Ki koma ɗaki Ki nemi hijjabi ki saka" yayi maganar cike da takaici.

"Oya ku yi searching ko ina a gidan nan, kar ki motsa daga in da ki ke"

Wani jami'in ne ya fito daga ɗakin Al'amin, da wannan ledar da aka kawo aka ce a ajiye masa, ya ce 'Ga abun da muka samu sir"

Shugaban operation ɗin ya karɓa, ya zazzage sai ga ƙwayoyi, da allurai da wiwi da sauran tarkace sai kuma wata 'yar leda mai ɗauke da wani farin gari.

Ya ce "Good, mu tafi da shi mun samu abar"

"Yallaɓai, wallahi wani ne ya kawo su ɗazu, ba shi ya kawo su ba, dan Allah kar ku tafi da shi. 

Ko kallonta ba su yi ba, suka tasa ƙeyar Al'amin.

Ayshercool
08081012143


🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724

Biyo bayansu tayi, tana wani irin kuka mai ban tausayi, tana yi musu magiyar su sake shi, ba shi da laifi, amma babu wanda ya saurareta a cikinsu.

Maƙwabta na jiyo kukanta, amma babu wanda ya iya ko leƙowa ya ga abun da yake faruwa.

Shi kuwa Al'amin ko a jikinsa, kukan da take yi ne kawai ba ya so.

Suka saka shi a mota, ta ce "To Yallaɓai ina za ku kai shi dan Allah"

"NDLEA, daga nan zamu miƙawa 'yan sanda shi, su kai shi gaban kotu".

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, yanzu dai sai kun kai shi NDLEA ɗin kenan? Wancan karon baku kai shi ba sai yanzu, dan Allah ku duba lamarin nan"

Suka saka Al'amin a mota, suka tafi da shi, a falonta ta zauna, ta fashe da kuka, ta daɗe a wurin tana kuka, ganin hakan ba mafita bane, ya sanya ta tashi ta ɗauro alwala ta koma ɗakinta, tayi ta sallar da ba ta da tabbacin tana karanta ayoyin daidai saboda tashin hankali, ta ɗaga hannu tayi addu'a, amma ta kasa kawai ta mayar da kanta sujuda ta fashe da kuka.

Har asuba ta yi idonta biyu, ta yi sallar asuba ta idar, ta zauna tana karanta duk abun da ya zo bakinta, wani abu mai nauyi ya tokare mata ƙirji, ta ji tamkar numfashinta zai ɗauke gaba ɗaya.

Bayan sallar asuba magidantan layin suka tsaya suna salallamin, jiya da daddare ma'aikatan sun shigo layin, amma babu wanda ya fito.

Malam lawan ya ce "Har kwa tambayi lafiya? Ai tun da ɗan daba ya tare muku a unguwa, sai abun da Allah ya yi, wurinsa suka zo, wataƙila ma wata ta'asar ya je ya tafka, suka zo suka yi masa ɗaukar amarya tsakar dare".

Suka yi ta salallami da fatan Allah ya kyauta.

Har rana ta yi haske, jauhar tana zaune a wuri ɗaya, idanun ta sun yi ja, duk sun kumbura fuskarta tayi ja ta kumbura saboda kuka.

Maman halimatu da wata mata mai kallon gidan na jauhar suka shigo, sai da suka yi ta sallama, da ƙyar ta iya amsawa sam ba ta ji sallamar ta su ba ma, ta fito falo ta ce su shigo.

Maman halimatu ta ce "Jauhar, lafiya kuwa? Wai meyafaru ne jiya mun ji hayaniya, babu damar mu fito.

Take wasu hawayen suka ziraro mata ta goge su ta ce "Jami'an tsaro ne suka  zo suka tafi da shi"

"Subhanallah, laifin me yayi?"

Ta girgiza kai ta ce "Ban sani ba"

"To ki yi haƙuri, ki samu ki ci abinci,  sai ki nutsu a san abun yi, Allah ya kyauta ya kiyaye gaba"

Ta amsa musu da to ta gode.

Kai ka ce takaba take yi, duk ta fita hayyacinta, ba ta san wurin wa za ta nufa da maganar nan ba, kuma ba ta san ina hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyin take ba ma, balle ta je, ba kuma ta san ta tambaya a gano wani abun, gashi ko gidan su Al'amin ɗin ma ba ta sani ba, balle ta je ta gaya musu, ko da wani abu da za ayi a kai.

Ta dudduba ta tattara ɗan kuɗin da take da shi, ta fita, ta samu mai napep ta tambaye shi idan ya san ina ne hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi.

Ya ce mata ya sani, ya ɗauke ta ya tafi da ita.

Ta din ga yawo a cikin hukumar, aka ce mata ba ya wurin, ba a kai shi ba, sai da ƙyar aka ce mata yana nan, amma ba zata ganshi ba, babu irin magiyar da ba ta yi ba, amma suka hanata ganinsa, ƙarshe sai gida ta koma a matuƙar galabaice.

Ta rama salollin da suke kanta, ta din ga addu'a da fatan Ubangiji Allah ya fitar da shi lafiya, da ta san abun da zai faru kenan, da ba ta karɓi abun da ba ta san ko menene ba ta ajiye masa.

Ɗaya maƙwabciyar ta ta wasila, wadda mijinta ya taɓa raka su wurin mai chemist ta shigo gidan.

Ta ce "Jauhar yaya ake ciki, kin same shi kuwa, kin je wurin 'yan sandan?"

Ta ce "Eh na je, ba su bari na ganshi ba"

"Kuma ba su gaya miki abun da yayi suka kama shi ba?" Ta jinjina mata kai alamar eh, wasu hawaye masu ciwo suna zubo mata.

"Ki yi haƙuri ki kwantar da hankalinki jauhar, in sha Allah komai zai wuce kamar ba ayi ba, kuma in sha Allah zai fito"

Ta ce "To Allah ya sa".

Yau ma haka ta kwana salloli, da kai wa Allah kukanta, da fatan Allah ya saka mijinta yana lafiya ya kuɓutar da shi.

Da safe ta sai ƙosai da buredi, ta dafa tea, ta kuma wanke ƙafa ta koma wurin nan, amma suka sake ce mata ba za ta ganshi ba, tayi magiyar har ta gaji, ta basu abincin ta ce su bashi.

Ta koma harabar wurin, ta nemi wuri ta zauna, ta rasa abun da yake yi mata daɗi, rabonta da abinci tun a jiya, gaba ɗaya tunanin halin da Al'amin yake ciki, da wanda zai shiga a nan gaba ya dame ta, ta gaji da zama ta tashi ta nufi gida.

Ɗakinsa da suka shiga duk suka watsar da kaya ta shiga, dan damuwa ba ta bari ta shiga ta gyara ba.

Duk sun watsar da komai na ɗakin, ta tattare masa kayan, tana cikin gyarawa ta gano wayarsa, ta ɗauka tana duddubawa sai ta ga tarin kiran walid da liti, cikin hanzari ta kira lambar walid.

"Ya ne maza? Tun shekaranjiya ban sake jin ɗuriyarka ba, na zo gidanka ba kowa ka kuma ƙi ɗaga waya".

"Assalamu alaikum" tayi masa sallama.

Ya ce "Ahh madam ke ce ashe? Ya ake ciki yana ina?"

Muryarta na rawa ta ce "Shekaranjiya da daddare jami'an tsaro sun zo sun tafi da shi"

"Kamar yaya? Me yayi?".

"Abu aka kawo aka ce na ajiye masa, su kuma suka zo da daddare suka ga kayan a leda, suka tafi da shi na je sun hanani ganinsa" tayi maganar cikin kuka.

Walid ya ce "Ya isa haka yi shiru, bari na zo gidan gani nan"

Sai ta ɗan ji sanyi a ranta, tamkar yana zuwa zai fito mata da Al'amin ɗin.

Kusan awa ɗaya da rabi, ta ji ana knocking gate.

Da sauri ta tashi ta je ta buɗe, liti ta gani da Walid, har ƙasa ta durƙusa ta gaishe su.

Walid ya amsa ya ce "Ya aka yi, meyafaru?"

"Yadda dai na gaya maka, wani ne ya kawo wata leda ya ce a ajiye masa, na manta ban nuna masa ba, kawai suka zo cikin dare suka tafi da shi, naje na je hukumar sun hana ni ganinsa"

Liti ya ce "Ki yi haƙuri, ki daina kukan haka, kuma kin tabattar bai yi wani laifin ba?"

"Ni dai a iya sanina bana tunanin yayi wani abun, duk da ba tare muke yawo da shi ba, amma dai sun ce a kan kayan da suka gani a gidan nan ne"

Walid ya ce "Ki kwantar da hankalinki, in dai Viper ne, mutum ne mai sa'a koma menene zai fito, amma ki kwantar da hankalinki, yanzu idan muka je babu lallai su sauraremu, amma in sha Allah gobe in Allah ya kaimu da wuri zamu je mu ga yadda za ayi".

Ta ce "To shikenan na gode sosai, bari na kawo muku ruwa"

"Kar ki damu a ƙoshe muke, ki kwantar da hankalinki idan da wani abu ki kira lambata"

Ta ce "To na gode"

Ta rufe ƙofa suka tafi, liti ya ce "Ikon Allah"

"Menene?"

"Kawai rayuwar Mai zamani nake kalla, yadda yake gararambarsa da kamar babu mai so, idan muka faɗa cakwakiyarmu, iya mu muke warware kayarmu, babu wanda ya damu da mu, shi kalli Allah ya kawo masa mai kula da shi".

"Haka ne, amma tausayi ta bani wallahi, yarinya ce sosai. Yana ta buyagi da rashin mutunci an yi masa aure, amma sai da ya mari madaki saboda ya tankata".

Liti ya kwashe da dariya ya ce "Kai mace fa aka ce maka, na raba ka"

Walid ya kwashe da dariya ya ce "A ƙi faɗinsa, da madaki ya ce ya kashe ta, mazewa yayi ba zai motsa ba, wai ba shi ya aiketa ba, amma ka ga wasu jijiyoyi da suka tashi a goshinsa, ga wani gumi da yake a iya karan hancinsa, bai san yana wasu abubuwan ba" suka sake kwashewa da dariya.

Liti ya saka su guduma ɗan gidan mai unguwa, su din ga kaiwa sun komowa, suna ɗan zagaywa a layin gidan viper, idan suka ga wani abu da ba su yadda da shi ba, su sanar masa.

Suka cigaba da kaiwa suna komowa a hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi, amma su ma ba su samu ganin Viper ba, suka ce sai dai idan sun kai shi wurin jami'an tsaro su je can su ganshi.

Hankalin Jauhar ya ƙara mummunan tashi, ta rasa in da za ta saka ranta ta ji daɗi.

Ta sake amfani da wayarta, ta kira walid a waya, da yake sun ce kar ta sake zuwa hukumar, ta bari za su din ga zuwa su.

Ta duba wayar kaf, babu sunan wani mutumin kirki a ciki, balle tayi tunanin akwai lambar wani ɗan gidansu,  ta kira duk sai sunayen su Liti da ire-iren su.

Sai kuma ta fara tunanin ko ba shi da kowa ne? Amma da ba shi da kowa ai ba zata ga kakarsa ba, kuma an nuna mata Rahila ranar da aka yi bikinsu Anty Zakiyya ta ce mata wai babarsa ce, amma tana tantama tun da aka yi auren, bai taɓa kai ta gidansu ba, kuma babu wani wanda ya zo daga gidan.

Walid suka Kuma dawowa suna rarrashin ta, a kan suna ta ƙoƙarin ganin ya fito, ta gaza haƙuri ta ce "Dan Allah to ina ne gidansu, yakamata ace sun sani"

Walid ya ce "Taɓ ke 'yan gidan na su da suna ta tashi, da baki gansu ba, ki manta da maganar su kawai ki cigaba da addu'a".

Ta ce "Amma kamar yakamata a gaya musu halin da yake ciki, ko ba za su yi komai a kai ba".

Walid zai yi magana, liti ya ce "Bari na kwatanta miki gidan na su" yayi mata kwatance sannan suka yi mata sallama suka tafi.

Liti ya ce "A irin wannan yanayin da take ciki, idan ba ka kwatanta ba sai ta tsaneka ai, idan ta je ta ganewa idonta shikenan"

"Haka ne, amma ka san wannan matsiyaciyar matar gidan na su ba mutunci gareta ba, kar ta ƙara mata zafi". Suka cigaba da tattaunawa.

Kusan kwanaki bakwai da kama Al'amin, idan ka ga jauhar sai ka ce tayi jinyar shekaru, duk ta ƙare ta fita hayyacinta.

'yan sana'oin ma ba ta iyawa, saboda tunani da damuwa.

Liti ya zo da safe, tana falo tana karatun Alkur'ani, ta ga kiran waya a wayar Viper, ta tashi ta fita ya ce "Sako hijjabinki mu je, sun bawa 'yan sanda shi, idan Allah ya taimake mu, wataƙila mu ganshi" cikin tsananin zumuɗi, ta yafo mayafinta, ta rufe gidan suka tafi.

Sai dai da suka je ɗin ma, tsugono ba ta ƙare ba, dan sun fi ƙarfin awa biyu, walid da liti suna safa da marwa, da faɗi tashin su ga Al'amin, Jauhar addu'a kawai take yi, tun da ta ga haka ta san lamarin ba ƙarami ba ne.

Da ƙyar aka ce za su ganshi, aka tafi da wasu wani wuri, suka jira a reception ɗin sashen.

Babu tsammani ta ɗaga kai ta ga yana tahowa, yana ɗingisa ƙafa, cikin hanzari ta miƙe tsaye ta zuba masa ido, kansa a ƙasa jami'an tsaro sun taso shi a gaba, su liti ma miƙewa suka yi tsaye, da ya kusantota sai ta ga jikinsa duk alamar duka, gefen fuskarsa a kumbure, haka wuyansa, shirt ɗin jikinsa tayi datti, duk busasshshen jini, take jikinta ya hau tsuma cikin tashin hankali.

Ya zo ya nemi wuri ya zauna kamar basarake, gabansa ta ƙarasa cikin tashin hankali muryarta na rawa ta ce "Master, dukanka suke yi haka?"

"Maza wai meyafaru ne? Me ka yi haka aka kawo ka nan?" Walid ya tambaye shi cikin damuwa.

Jauhar ta ce 'Yallaɓai, dan Allah ku sake shi, dan Allah ku yi haƙuri ba zai ƙara ba, wallahi kayan da ku ka gani a gidan lafina ne, bai san da su ba, dan Allah ku yi haƙuri ku sake shi"

Ɗaya daga cikin 'yan sandan ya kalleta ya ce "Yarinya yayanki ba ya ji, ba zamu sake shi ba, wanda aka kama da cocaine ki ke cewa a saki ba shi da laifi? For more than 7days ya amsa laifinsa yaƙi, ga kaya an kama shi da shi, yayi magana yaƙi kamar dutse"

Gaba ɗaya sak suka yi suna kallon ɗan sandan.

"Wace irin cocaine kuma? Ka ga malam ba ma son rainin wayo, haba kai tare fa muke sabgar nan da shi, a gidan uwar wa zamu ga cocaine ɗin?" Walid ya yi maganar a matuƙar fusace.

Cikin tsawa wani ya ce "Kai ka san a ina ka ke?"

"Na sani mana, ai ba lahira ba ce, balle ace mutum ta sa ta ƙare, ƙarshen abun dai ku kashe mutum, kai da muna harka da cocaine zaku ganmu a haka ne?"

Jauhar ta yadda sai hali ya zo ɗaya ake abota, daga Al'amin har abokansa ba su da tsoro.

Fashewa ta yi da kuka ta ce "Wallahi Yallaɓai zan iya rantsewa ba ya ta'amalli da cocaine, bai san ma in da zai same ta ba".

"Yayi bayani da bakinsa mana"

Cikin hanzari ta koma wurinsa, ta ce "Dan Allah Master ka yi musu magana ko zasu ƙyale ka mu tafi, ka gaya musu ba taka ba ce ba, laifina ne"

Yadda ginin wurin ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login