Showing 6001 words to 9000 words out of 152254 words
ki je ki kama ki yi zaman kan naki mana, ke dama banda Abba a tsaye yake a kanki, ai ƴar zaman kantan za ayi, kuma ƴar gagara".
Nabila ta buɗe baki za ta yi magana, suka ji gyaran muryar Abba, daga saman bene. Tuni idon Nabila yayi jawur, saboda kuka da ɓacin rai.
Ya ce "Magajiya" cikin sauri ta ce "Na'am ranka ya daɗe"
"A gabanki kina tsaye yaran nan suke faɗa? Ki ka kasa tsawatar musu?"
Ta risuna ta ce "Tuba nake ayi mini afuwa".
Sauda ta ce "Wallahi Ab...." Ya dakatar da ita ya ce "Ban tambaye ki ba, kukan me ki ke yi ke kuma?" Yayi maganar yana kallon Nabila.
"Faten wake aka yi, ba a dafa mini komai ba, kuma yunwa nake ji"
Ya ce "Wannan abun kawai shi ne abun kuka kuma? Ke a rayuwarki ba zaki taɓa girma ba kenan?" Tayi shiru tana sheshsheƙar kuka, kukan da yake jin sa har zuciyarsa.
"Magajiya, ko aikin wa ki ke yi, ki ajiye ki sama mata abun da za ta ci, ba biyanki nake dan a farantawa wani a ɓatawa wani ba, duk ƴaƴana nawa ne, babu banbanci a tsakaninsu"
Ta risuna ta ce "In sha Allah Alhaji, za a kiyaye"
"Ke kuma, ki cigaba da faɗa da yayyenki, zaki ga yadda zan yi da ke. Kuma na gode da furunciki Arfa, zaki yi zaman kanki ko? Tun ina raye ki ke wannan iƙrarin, ranar da na mutu ban san me zaki aikata ba, kin kyauta" bai tsaya jiran me za ta ce ba, ya wuce ya koma ɗakinsa.
Sauda ta yi wa Nabila gwalo, Nabila ta ce "Ai ke yakamata na yi wa gwalo, ni na yi nasara, tun da an ce a ajiye aikin babarki ayi nawa, banza ƙatuwar kwabo" Nabila ta wuce ɗakin su, tana tunanin ko dan wannan tijarar, ya isa tayi fatan tayi aure ta bar gidan nan.
***
Ɗan siririn matashi ne dogo, wankan tarwaɗa, sanye da kakin ƴan sanda, da ɗan hanzari yake bin wata doguwar baranda, wadda ta sa da shi da wata ƙofa.
Ya buɗe ya shiga da sallama, ya sarawa wanda ya tarar a cikin ofishin, wanda da gani babu tambaya, ka san babba ne sosai a cikin rundunar jami'an tsaro, duba da yanayin ranks ɗin da ke maƙale a kafaɗar uniform ɗin sa, da kuma haɗuwa da tsaruwar office ɗin na sa.
Ya ƙame tare da sarawa mai office ɗin, ya yi masa alama da ya zauna.
Ya zauna tare da sake gaida wanda ya tarar a office ɗin, da uniform ɗin sa ke ɗauke da sunan ACP Solomon wada.
ACP wada ya kalli matashin ya yi murmushi ya ce "CSP Nasir Yusuf"
Nasir ya waro ido ya ce "Wane ni Yallaɓai, Dsp ɗin dai"
"Au Csp ɗin ne ba ka so? Ba abun mamaki ba ne ba, ka ji gobe kai ne Cp na garin nan, kai koma IG gaba ɗaya"
Nasir yayi murmushi yana sunkuyar da kai.
"Ƙwazon mutum babu in da ba ya kai shi, kuma kar ka yi mamakin ƙwazonka ya kai ka in da ba ka zata ba. Yanzu ba karatunka da kuma ƙwazon ne ya kawo ka matakin da ka ke yanzu ba?"
Ya jinjina kai ya ce "Haka ne ranka ya daɗe".
Acp Wada ya ce "Good, wani aikin za'a sake baka, wanda mu ke buƙatar sa da gaggawa, direct order ce daga Cp,ya kuma ce a jinjina maka aikin office ɗin ka yana kyau"
Nasir ya tattara hankalinsa ya ce "Ok sir, na gode sosai"
Solomon wada ya ce "Nasir, idan ka mayar da hankali yadda ake so, ka gudanar da aikin nan, za ka samu cigaba a aiki sosai da sosai"
Cikin girmamawa ya sake cewa "I will do my best in sha Allah".
"Good" ya ɗaukko wani file ya ajiye masa, sannan ya ce "Kwanakin baya, akwai wani ɗan daba, da ya addabi garin nan, kai ɗan garin nan ne za ka fi ni sani, wai shi Aminu ana yi masa laƙabi da viper.
Shekarun da suka gabata yana tsare, sakamakon laifin da ya aikata, kafin kwatsam mu samu sanarwar cewa an sake shi. So bayan sakin nasa, akwai kokwanto a cikin sakin da aka yi masa ba bisa ƙa'ida ba ne ba, duk da controllern gidan yari ya ce order aka bashi ya sake shi, bayan fitowarsa ya cigaba da aikata miyagun laifuka a ɓoye, na sayar da miyagun ƙwayoyi tare da ƙyanƙysar sabbin ƴan daba, da suka hana jama'a zaman lafiya a garin nan, wanda yaƙi da wannan a ƙarƙashin kulawar office ɗin ka yake, a zone ɗin. Abun da muke so da kai shi ne, Aminu ya shigo hannu, ko ta halin ƙaƙa."
Nasir ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Ok sir, tabbas cases na dillancin ƙwayoyi da harkar daba, yana ƙara ta'azzara, amma laifin me yayi aka kai shi kurkuku? Kuma ya aka yi, aka sake shi ba bisa ƙa'ida ba?"
"Wannan ba huruminka bane ba, duk ba shi ne a gabanmu ba, kamo yaron shi ne abun da muka saka a gaba, wannan abun da ya shafi shari'a ne, ɓarnar da yake aikatawa ta yi yawa. Kuma a zone ɗin ka yaransa suka fi yawa, dan haka ka je ka yi iya ƙoƙarin ka a kai. Yabawa da nustuwarka, da jajircewar ka ya sanya muka baka aikin nan, ina nan ina saurarenka, ba a buƙatar ɓata lokaci. Ka je ka duba file ɗin a tsanake, akwai sauran informations da za su taimaka maka wurin kama yaron, da duk wani record na criminal acts ɗin sa yana ciki. Nan da gobe in Allah ya kaimu zaka dawo mini da file ɗin. ba na buƙatar kuma ka yi wani abu sama da haka, kar ka ƙetare iyakar da na gindaya maka".
"Ok sir, i will do mai best in sha Allah" ya ɗauki file ɗin, tare da sake sara masa ya fita.
Ɓangaren Nabila kuwa, al'amuranta ba a samu sauyi ba, dan duk shari'ar da ba ta yi mata ba, ba za ta mayar da hankali a kai ba.
Director kuma ya bar ta ne, saboda mutuncin mahaifinta Major Yusuf da yake gani, mutum ne na gari kuma akwai tarin alkhairai da ya yi masa, shiyasa ya ƙyale Nabilatake cin karenta babu babbaka.
Nabila gaba ɗaya wasu lokutan sai ta ji tana danasanin karantar ɓangaren shari'a, yadda wasu abubuwan suke gudanawa sam ba sa yi mata daɗi.
Hausawa suka ce sai hali ya zo ɗaya ake abota, ɓangaren ƙawarta sumayya ma haka, kusan ƙalubale ɗaya suke fuskanta, dan har gara ma Nabila tana da alfarma a wurin na ta aikin, Sumayya kuwa na ta babu sani babu sabo.
Yau ganin motar Abba a gida bayan ta dawo daga aiki, ya sanya ta fuskanci yana gidan, dan haka da ta zuba abincinta, sai ta hau saman benensa.
A falonsa ta tarar da shi da Yaya Nasir, suna magana, da alama magana ce mai muhimmanci suke yi, sai dai yayi shirin fita.
"Abba sannu da gida" "Yauwwa" ya amsa a taƙaice.
Sai dai ta na zama ya tashi ya yi wa Nasir sallama, ya fita ya bar falon.
Nasir ya galla mata harara.
A shagwaɓe ta ce "Dsp me na yi ne? Kwana biyu duk Abba ya canza mini, kai ma kuma kana hararata"
"Ba dole ya canza miki ba, duk kin gallabi kowa a gida, bayan na dawo daga kaduna ake gaya mini wai kin je biki kin yi dare, ƙarshe a haraba ki ka kwana yayi punishing ɗin ki, ba ki zo kin bashi haƙuri ba. Law firm ɗin ku director ya kawo masa ƙara, daga danna waya sai kwalliya ki ka iya, ba kya son aiki, yayi ta bashi haƙuri ya ce a kula da ke a koya miki aiki, ko ba a biya ki ba, shi zai din ga biyanki salaryn. Kwatsam jin kunnensa ya ji ki na cewa ba dan shi ba, zaman kanki zaki yi, kin san kwana nawa ya ɗauka ba ya bacci saboda wannan maganar da ki ka yi? Duk cikinmu babu wanda Abba yake lelensa kamar ke, amma sai ba shi kunya ki ke ko ta ina?"
Cikin sanyin jiki, da tashin hankali ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ban zaci ran Abba zai ɓaci har haka ba, to kuma ba ka bashi haƙuri a madadina ba? Yaya sauda ce fa take ce mini agola, ni kuma ba na son na gaya masa. Ba na son fushin Abba, dan Allah ka tayani ba shi haƙuri. Maganganun Sauda ne suka ɓata mini rai, na yi dana sanin abun da na faɗa, amma dan Allah Yaya Nasir ka bashi haƙuri"
Ya girgiza kai ya ce "No ni ba ruwana"
Kuka ta saka masa tana cewa "Wallahi ba zan ci abinci ba, sai yanzu na ji maganar da na yi, ta yi nauyi ban san abba zai ji ba"
"Kin ga ya isa, kar ki saka ciwonki ya tashi na shiga uku, ya mayar da fushin da yake yi da ke kaina" ai kamar ya sake tinzirata, ta cigaba da sheshsheƙar kuka.
Cikin tsawa ya ce "Ke wai dan ubanki meye haka? Am i your mate, ba magana nake yi miki ba?" Sai da ta razana, amma hakan bai saka ta daina kukan ba.
Ya zuba mata ido, Nabila tun asalinta tun tana yarinya take fama da taurin kai na tsiya, yanzu ko dukanta zai yi, ba za ta daina kukan da take yi ba, balle ma yanzu ba wannan dan ta girmi duka. Har mamakinta yake yi, ƙatuwar budurwa ta kammala degree, kusan shekara ashirin da huɗu amma tana abu kamar yarinya ƙarama. Tsaki yayi, ya tashi shi ma ya fice, ya ƙyale ta, ta ci uban kukanta, ta kwanta a kusa da flask ɗin Abincinta ta hau baccin gajiya.
A tsanake Nasir yake duba file ɗin da aka bashi, a kan Aminu viper, da aka ce lallai ya kamo.
A record ɗin da ya duba, ya gano zuwan Aminun gidan yari, ba sau ɗaya bane ba, a kan mabanbanta laifuffuka da suke da alaƙa da harkar daba, da ta'amalli da miyagun ƙwayoyi.
Sai dai abun da ya ɗaure masa kai, ba a shigar da dalilin da ya sanya, aka kai shi prison na ƙarshe ba, an dai nuna ya aikata wani babban laifi ne, da ga cikin manyan laifuka da bai kamata daga lokacin faruwar abun zuwa yanzu ace an sake shi ba, haka zalika an cire wasu abubuwa masu muhimmanci da yakamata ace ya gani a cikin file ɗin, sannan ga shi solomon Wada ya yi masa umarni da ya yi amfani da iya abun da aka bashi.
"To menene dalilin haka?" Ya tambayi kansa, a lokacin da kan na sa ya ƙara ɗaurewa.
Sake duba file ɗin yayi yana tunani, kamar ya taɓa duba wani case, makamancin record ɗin da yake cikin file ɗin, sai dai kamar sunan ba haka yake ba.
"Aminu Viper" ya sake maimaitawa.
Ayshercool.
08081012143
[7/17, 1:25 PM] null: ⚔️*ƘARFE A WUTA ⚔️
AISHA ADAM AYSHERCOOL
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
3
Sama-sama Nabila ta ke jin hayaniya a kanta. Amma ta ƙi motsawa.
"Ke Arfa" yayi maganar yana riƙe hannunta.
Tashi ta yi zaune tana buɗe idonta a kan Abba, a sanyaye ta ce "Abba ka dawo?"
"Na dawo, tun da na tafi ki ke kwance a nan, ko abincin ba ki ci ba?"
"Abba Yaya ne ya ce kana fushi da ni, dan Allah ka yi haƙuri ba zan sake ba"
Major ya ce "Eh ya kira ni ya gaya mini, na haƙura tashi ki wanke fusarki ki zo ki ci abincinki" ta tashi ta shiga banɗakin falon, ta wanke fuskarta, ta zo ta zauna ta saka spoon ta fara cin abincin.
Ya numfasa ya ce "Rashin ji ne, ya yi miki yawa arfa, duk yadda na so na yi haƙuri sai kin ƙure ni, ban bi daɗin abun da kunnuwana suka jiye mini ba, kina iƙrarin zaki yi zaman kanki"
"Abba ka ce fa ka haƙura, ba zan sake ba"
"To shikenan na ji, ci abincin"
Umma tayi sallama da flask ɗin shayi, matarsa ta biyu, kasancewar yau girkinta ne.
Ta zauna a kusa da shi, ta haɗa masa tea, ya karɓa yana sha ya na yi wa Nabila hira, kamar bai yi fushi da ita ba, har ta ɗan ware.
Kiran sallar magariba ne, ya sanya ta tashi ta bar ɗakin, dan umma ta ji haushin zaman da Nabila ta yi, ita kanta Nabila ta so ba su wuri, amma Abba ya cigaba da jan ta da hira.
Da ya dawo daga sallar magariba, kai tsaye ɓangaren mama ya wuce, tana zaune a falonta, da Sauda su na kallon tv.
Gyaran murya yayi, sannan yayi sallama, suka amsa suna yi masa sannu da zuwa.
Ba tare da ya amsa ba ya kalli Sauda ya ce "Sauda nan gidan waye?" Ta ɗan yi turus tana kallonsa.
"Ki amsa mini"
"Gidanka ne Abba"
Ya ce "Masha Allah, idan ba zaki iya zama da ni, da tsarina ba, ko ki koma gidan tsohon mijinki, ko kuma ki fitar da miji ki yi wani auren"
Cikin damuwa Mama ta ce "Major me yayi zafi haka?"
"Baƙar aƙidar ki, da ta ara ta yafa, ba zan lamunta ba. Kun sani ba na ɗaukar duk wani abu da ya shafi Nabila da sauƙi, yadda na yi mata shamaki, da wanda ya zama katangar rayuwarta, dole na tsaya tsayin daka, na kula da ita kamar yadda na yi alƙawari. Ba zan lamunci a cigaba da wulaƙanta mini ƴa ba, har ta fara iƙirarin za ta yi zaman kanta. Babu wani ɗa da ya fi Nabila a cikin gidan nan, idan ki ka sake ce mata agola, to zaki fita ki bar mini gida ki nemi wani uban".
Cikin takaici mama ta a ce "Amma da kunnenka ka ji ta faɗa mata haka? Ka san dai makirci irin na yarinyar nan ko?".
"Kunnena ne ya jiye mini, ko zan yi mata ƙarya ne?"
Suka yi tsur-tsur baki daya.
Ya ja guntun tsaki ya bar falon.
Yana fita sauda ta ce "Mama dan Allah sai yaushe Abba zai daina fifita yarinyar nan a kanmu, tun da aurena ya mutu bai taɓa yi mini gori ba sai yau, saboda ita?"
"Ba ke kaɗai ba, ni kaina yadda ki ka san na yi mata kucciya, duk ita ce matsalar gidan nan, amma zan kawo ƙarshen komai da kaina, ki bar ni da su".
Nabila kuwa na ɗakinta, itakaɗai, tana duba document ɗin shari'ar da director ya saka aka ba ta, sai dai gaba ɗaya ba ta da intrest a kan shari'ar, da ta gaji ma, ajiyewa ta yi ta hau waya da saurayi.
Wata matashiyar budurwa ce ta shigo ɗakin ta ce "Wallahi Nabila abun da ki ke yi ba kya kyautawa"
Nabila ta ɗan kalli Asiya, ta katse wayar ta ce "Da na yi me?".
"Kin saka Abba ya yi wa mama da Anty sauda kaca-kaca saboda ke, sai da Anty sauda ta yi kuka".
"To ai cewa zaki yi, Abba bai kyauta ba ni meye nawa a ciki?"
"Amma ke ki ka gaya masa ta ce miki Agola, bayan yayi musu mu ma ya iskemu a babban falo, ya yi ta yi mana faɗa".
Nabila ta ce "Ashsha, ai kin san ni bana kai ƙara, ko dai na ɗauki mataki, ko kuma Allah ya saka mini da gaggawa"
Asiya ta ce "Ai shikenan, kowa yayi na gari kansa".
Nabila ta ce "Allah ya yaye miki Aisya, ke ma fa matar nan idan ta tashi karta miki wulaƙanci, ba saurara miki take yi ba, daga ke har umman, amma ku yi ta bin ta kamar wata shugaba, ni dai ba mai takani ban ɗaga ƙafar na karya ba"
"A'a ai ke ki ka ce, ke ki na da ma dogara"
Nabila ta yi tsaki, tare da furta "Allah ka aurar da ni na huta da wannan kacaniyar gidan, Ya Allah dogo mai gemu" ta fita daga ɗakin tana addu'a.
Bayan kwanaki takwas.
A tsaye yake ƙyam, kamar ƙofa, kasancewar in da yake a tsayen ba a iya ganinsa sosai saboda duhu, sai dai inuwarsa ta nuna dogon mutum, kakkaura.
Ya ɗauki ɗankwali, ya ɗaure kansa da shi, tare da naɗo ɗankwalin ya rufe fuskarsa sai idanunsa kawai ya bari a waje.
Ya laluba hannunsa, ya ɗaukko wata irin doguwar wuƙa, ɓangare ɗaya zarto, ɗaya kuma kaifi, ga ta da uban tsini, a ƙalla za ta yi kamu uku, ya ɗaga rigarsa ya soketa.
Ya sake ɗaukar wata ya soke a jikin wandonsa.
Yanayin takun da yake kawai, ya isa ya tabbatar daƙaƙarfa ne, saboda yadda ƙasa ke amsa takun nasa.
Bayan wasu awanni, duhun dare ya ƙara yi, sahu ya ɗauke, sai haushin karnuka ko ina.
A ƙofar wani gida ya tsaya, ya din ga waige-waige, ya tabattar da babu kowa. Tamkar ɗan biri, haka ya cafke katangar gidan ya dira ciki.
Ya saka mukulli, ya buɗe wata ƙofa a cikin gidan da duk ta yi ƙura, ya buɗe ta ya kutsa kai ya shiga ciki.
Tsayawa yayi ya kunna fitilar wayarsa, yana haske ɗakin, take ya ji wani abu mai tsananin ɗaci ya fara kaiwa da komowa a ƙirjinsa, ya ji numfashin sa na barazanar barin ƙirjinsa.
Jikinsa ne ya fara rawa, ya ji tamkar hankalinsa zai gushe, ya durƙusa a wurin yana wani irin haki, cike da wani yanayi na mai shirin fita hayyaci.
Hayaniya ya fara jiyowa a waje, hakan ya saka shi miƙewa tsaye babu shiri.
Cikin sauri ya fito daga ɗakin, ya kama katanga, ya leƙa, sai dai yana leƙawa ya ga ƴan ƙato da gora da miyagun makamai, sun fara taruwa a kewayen gidan, kasancewar akwai hasken farin wata, kuma akwai hasken ƙwayayen solar hakan ya bashi damar ganin makaman da suke hannun su.
Babu tsoron komai, ya haye katangar, ya hau saman roofing gidan, ya dira ta wani ɓangaren, jin sautin dirarsa, ya sanya suka rufa masa baya, ta in da suke jiyo sautin gudunsa har da karnuka su na kururuwar a tare.
Sai dai duk da wannan ƙira da Allah ya yi masa, ta siffar ƙarfi ba ya jin nauyin jikinsa, ya din ga dukan ƙasar da dukkanin nauyin jikinsa, ba su ankara ba, ya ɓace musu ɓat kamar walƙiya.
A bakin titi suka tsaitsaya suna haki, su na mayar da yadda aka yi.
Ɗaya daga cikin su ya ce "Anya yaron nan, ba da layar zana yake amfani ba?"
"Ba wata layar zana, tsohon hatsabibi ne kawai, ni na yi mamaki ma da ya gudu ai, da da ne fa, wallahi sai ya illata ku kan ya gudun. Ai kamar yadda na gaya muku ne, da na ji alamun ya zo, zan kira ku a waya na sanar muku, ai ba zan sake