Showing 9001 words to 12000 words out of 152254 words

Chapter 4 - ?arfe A Wuta Book 1 Hausa Novel Complete

15 Dec 2024

327

sukuni ba sai ya je hannu, na za ta ma zaku kira ƴan sanda ne"

Ɗaya daga cikin jami'an sintirin, ya ce "Ko zamu kira ƴan sanda, mu yakamata mu fara huɓɓasa mu kama shi, sai mu miƙa musu shi, wannan gudun nasa yaushe muka kira ƴan sanda ma"

"Amma duk da haka, yakamata su san yana zuwa ai"

Shugaban su ya ce"Muddin suka sani, canza taku zai yi, ba zai sake zuwa ba".

Malam lawan da gidan sa ne a jikin gidan da yake zuwa ya ce "In ji wa? Ba zai taɓa iya daina zuwa gidan nan ba, yadda ka san ya binne asiri a ciki, kodayeke sai ta yiwu ma asirin ya binne, wannan hatsabibancin nasa akwai lamarin sihiri a ciki, amma zan cigaba da saka ido, da ya zo zan kuma kiranku"

"To shikenan malam lawan mun gode, yanzu ka koma gida, bari mu koma bakin aiki, ko kuma a raka ka ne?"

"Ahha haba, kamar ba namiji ba, ba wani abu bari na koma, ai ya riga ya gudu" Suka yi sallama ya nufi layinsu.

Sai dai yana daf da ƙarasawa gidansa, kawai ya ji an yi ball da shi, kasancewar sa ɗan ƙaramin mutum, sai jin sa yayi, ya yi sama ya dawo ƙasa kamar wani karmami. Ya tashi a gigice yana zaton ko gamo yayi da aljani, ya hau waige-waige.

Haske shi ya yi da fitila, sannan ya ce "Kwana da yawa malam lawan, tsohon butulu, da na ƙyale ka ban yi maka komai ba, shi ne ka cigaba da yi mini bita da ƙulli?"

Cikin kwakwazo, da tsananin razani ya ce "Na tuba, na bi Allah na kuma bi ka, dan Allah" kan ya ƙarasa, ya karya shi ɓaras, ta hanyar saka ƙafa, ya yi masa wani irin duka a ƙafarsa ɗaya.

Malam lawan ya a kurma ihu, cikin tsananin zafin nama, ya cire hular kan malam lawan,, ya tura masa a baki, sannan ya ciro wuƙar ƙugunsa ya yanke shi a damtsensa, aikuwa jini ya ɓalle.

Ya durƙusa a gaban sa ya ce "Yanzu ai ka ji daɗin bayar da rahoton zuwana, ragon maza kawai" ya tashi tsaye ya ja da baya ya ɓace a cikin duhu, ya bar shi a mawuyacin hali, ga karaya ga yanka, gashi kuma ya toshe masa baki.

Ko da ya koma gidansa da yake zaune, ciro wuƙar da ya yanki malam lawan yayi, yayi jifa da ita. Ya tsaya yana haki, abun da ya yi alƙawarin dainawa, yau ya yi, ya zubarwa da wani jini.

Ya dafe kansa yana huci cikin tsananin damuwa.

**
Yau sumayya ba ta haɗa tafiya da Nabila ba, dan da wuri sosai ta fita, za ta shiga asibitin murtala ta duba wata yayar babansu da aka kwantar a emergency, za ta kai musu abinci.

Su na tafe da mai adaidaita sahu, ta hango mutane na ta shiga su na fita a wani layi, duk da lokacin gari bai gama hasken da za ace, mutane suna wannan tururuwar ba.

Da sauri ta tsayar da mai baburin, ta biya shi kuɗinsa, ta  sauka, ta nufi layin da mutane ke shiga su na fita.

Wurin duk babu mata, sai maza, amma hakan bai hanata kutsawa da son gano abun da yake faruwa ba.

Tsayawa ta yi ta tambayi wani magidanci, abun da yake faruwa. Ya sanar da ita, gawar wani yaro aka tsinta, a bayan maƙabartar unguwar, an yanke masa al'aura da wasu sassa na jikinsa.

Jikinta na tsuma ta cigaba da kutsawa tana faɗin "Ku matsa, ni ƴar jarida ce" tare da nuna musu id card ɗin ta.

Ta ɗaɗɗauki hotunan yaron, sannan ta tsaya tattaunawa da mutanen da suka fara zuwa su ka tarar da abun.

Sai kiranta ake yi a waya, ana jiran ta kai abinci, amma sai da rana ta ɗaga sosai, aka gama komai ƴan sanda suka zo, sannan ta yi shirin tafiya, shi ma sai da ta karɓi lambar wayar wani ɗan sanda, da zimmar zai din ga ba ta update na sakamakon binciken da za su yi, a kan gawar.

Ko da ta je asibiti ta sha faɗa,na rashin kai musu abinci da wuri, ko a jikinta, saboda ta samu rahoto, dan haka tana ajiye musu abincin, ta yi waje.

Sai dai ba ta fito daga emergency ba, ta din ga jin ihun wani babban mutum, kamar mara gaskiya, haka ta koma tana leƙawa ta ga abun da yake faruwa.

Magidanci ne, ake yi masa ɗinkin wani uban yanka a damtsensa, jikinsa yayi kaca-kaca da jini, duk da ana ta yi masa allaurar kashe zafi, amma sai ihu yake yi.

Babu neman izni, ta afka ciki ta ce "Sannu bawan Allah, ka yi haƙuri Allah ya baka lafiya, ka daure"

Duk sauka waiwayo su na kallonta, har da ma'aikatan, mutumin ya ce "Na gode sosai"

Ta ƙara matsawa ta ce "Amma hatsari ka yi ne? Kodayeke wannan ai yankan makami ne ba hatsari ba"

Ya ce "A'a wani ɗan daba ne, ya sare ni jiya cikin dare, dama hukuma ta daɗe ta na neman sa"

Sumayya ta gyara tsayuwarta ta ce "Subhanallah, bawan Allah a wace unguwa ce haka? Ko rigima ku ka yi da shi ne?" Ƙanin malam lawan da yake tsaye a wurin, a fusace ya kalli sumayya ya ce "Dalla malama fita, mutum yana fama da kansa, kin zo ki na yi masa wasu surutan banza"

Ta ce "A'a Allah ya baka haƙuri, ka sani ko akwai wani taimako da zan iya yi masa. Kalli saran da aka yi masa fa, idan ba za ka damu ba, zan naɗi muryarka, mu saka a radio, ko Allah zai saka, hukuma su bi maka haƙƙinka, barin su da ake yi suna cin bulus ya sanya suke cigaba da ɓarna".

Malam lawan ya ce "Ke rufawa kanki asiri, hatsabibanci da ta'addanci yaron, ya wuce tunanin ki"

Sumayya ta zaro wayarta, za ta yi magana, sai ga wasu mutane guda biyu sun shigo da wani kaki a jikinsu, da ba ta san na menene ba, suka mayar da ƙofar ɗakin suka rufe.

Malam lawan ya kalle su, ba su ne ƴan sandan da aka kirawo suka tsaya masa, likitoci suka zo kansa ba ne.

Sumayya ta yi tsilli-tsilli da ido,  ɗaya ya ƙirga mutanen da suke cikin ɗakin, da likita ɗaya, nurse ɗaya, sai ƙanin malam lawan da sumayya. Dan duk maƙwabtan da suka kawo shi, sun tafi wurin sana'oin su. ya ce "Ku biyar ne a ɗakin nan, idan ka sake mu ka ji labarin sunan wanda ya yi maka wannan raunin, to za ka maye gurbinsa da ya bari na gidan yari, dan haka ka ja bakinka ka yi shiru".

Sumayya ta ce"Ban gane ba Yallaɓai, mutum mai laifi kuma ace kar a faɗi waye? Ba ka ga irin illar da aka yi masa ba ne, ga karaya ga rauni, da ya kashe shi fa?"

Ya ba ta amsa da "Da ya kashe shi, bakinki zai iya sakawa, ki ɗauki hukuncin da za ayi masa na kisan" daga nan suka juya suka fice.

Mamaki ya mamaye sumayya, ta ce "Kai kuwa bawan Allah, waye wannan shi kuwa, da har jami'an tsaro masu kaki, za su hana bayyana laifinsa, ana sane aka ƙi kama shi kenan?"

Malam lawan ya ce "Ba zaki ja mini masifa ba, ki fita ki bar wurin nan, na ji da masifa ɗaya, bayan ɗinkin nan a karye nake wallahi"

Cikin tsananin naci, da son samun rahoto, ta kwantar da murya za ta lallaɓa shi, ta samu labari, amma da likitan da ƙaninsa suka koreta daga ɗakin.

Fitowa ta yi, tana ta mamakin abun da ya faru, yaya za ayi hukuma ta bawa mai laifi kariya, wane irin abu ne haka?.

Ba ƙaramar makara ta yi ba, amma tunanin abun da ya faru, ya fi ɗaure mata kai.

***
Sannu a hankali yake yi wa kansa allura, yana yi yana fatan samun abun da yake so, a hankali ya gama ɗurawa jijiyarsa ruwan allurar da yake fari tas a cikin sirinji, bayan ya kammala tsaf ya fara jin kansa yana yi masa nauyi.

Take idanunsa suka yi mitsi-mitsi, ya soma lanƙwasa kansa, yana jin idanunsa kamar za su fito waje, suna yi masa yaji, a haka ya kunna sigari, ya kashingiɗa, ya na bawa sama hayaƙi,yana jin yadda jikinsa ke son bijirewa aikin allurar.

Wayarsa ce ta fara vibrating, ya miƙa hannu, ya ɗaukkota ya duba, yana zaton ko a cikin yaransa ne, sai dai ya ga private number ce.

Har zai ƙi ɗagawa, sai kuma ya ɗaga ya saka a kunnensa, amma bai yi magana ba.

Daga cikin wayar aka ce, "Meyasa ba ka gajiya da neman magana ne? A wannan karon ma sai da ka saka na yi abun da na goge ɓarnar da ka yi, yakamata ka nutsu Aminu"

Ya saki hayaƙi, tare da ɗan kaɗe tokar da sigarin ta tara, sannan ya ce "Waye kai? Sannan waye ya saka?"
Mutumin yayi dariya, ya ce "Mutum mai ba ka kariya, domin cimma nasa muradin, yakamata ka sauƙaƙa mini aiki, ka daina aikata abubuwan da za su din ga barin trace a kan ka".

"Ka yi muguwar kasadar ƙoƙarin cimma burinka da mutum irina, kar ka manta viper ake yi mini laƙabi da shi, macijin da ya fi kowanne hatsari, idan ka bari na sare ka, ka gama yawo" yana gama maganar ya cillar da wayar, ya ɓata fusaka kamar ya fashe da kuka.

Cikin fusata ya ce "Ni again? wani ya kuma amfani da ni? Impossible zan watsa dafina a in da ya dace da in da bai dace ba, sai na tabattar da danganawa ga kunyar ƙarshe, ko da kuwa za ayi mutuwar kasko" ya yinƙura da nufin ya tashi tsaye, amma ya kasa sarrafa gangar jikinsa, hakan ya tilasta masa komawa ya nemi wuri ya kwanta.

Duk da irin faɗan da sumayya ta sha a wurin aiki a kan makara, bai dame ta ba, jikinta sai tsuma yake saboda ta zo da rahotanni masu muhimmanci da ɗaukar da hankali.

Ofishin head of news ta je, ta shiga da sallama.

Matar ta ɗago ta amsa mata da ƙyar, ta ƙarewa sumayya kallo, ta ce "Yanzu ne lokacin shigowa aiki ko? Gaba ɗaya yaran yanzu ba kwa ɗaukar aiki da muhimmanci, kodayeke karatun ma ba wani na kirki ku ka yi ba, duk da satar amsa ku ke gamawa. Ki shiga hankalinki kafin na kai maganar nan wurin MD"

Sumayya ta risuna ta ce "Afuwan anty, in sha Allah ba zan sake ba, na samu wasu rahotanni ne masu muhimmanci, da ya san na tsaya a hanya, shiyasa na makara na kawo miki a tantance ne ko za a saka su a news"

A yamutse matar ta ce "Na menene" cikin farinciki da jin ƙwarin gwiwar ta yi abun arziki ta fara da gaya mata abun da ya faru a asibiti.

Amma matar sai cewa ta yi"Amma ba ki da hankali ko? Ta yaya zamu saka wannan shirmen a news?"

"Anty ai a rahotanni, ko a janyo hankalin hukuma.... "Dalla yi mini shiru, business mu ke yi a nan mu, ke fa iyayinki da rawar kanki yayi miki yawa sumayya. Meye hujjarmu idan aka tsutsiye mu, cewar hukuma na ɓoye mai laifi?"

Sumayya ta ce "Wallahi a gabana aka yi, mutumin yana nan a emergency"

"Kin ga idan ba ki da abun faɗa, fita ina da abun yi"

Sumayya ta yi iya ƙoƙarin ta, ta danne abun da yake taso mata na fushi ta ce "To shikenan, sai kuma akwai abun da na gani, ina kan hanyar tahowa nan, a nan wajen gari, an tsinci gawar yaro an cire masa wasu sassan jikinsa".

"Almara kenan, wa zai yadda da wannan zancen?"

"Ba zance ba ne ba, na yi recoding ɗin maganar wasu daga mutanen da suka fara cin karo da abun".

"Sumayya, ba irin wannan labaran mu ke buƙata ba dan Allah, je ki su murtala sun fita neman rahotanni, ki din ga kawo sensitive abubuwa"

Summaya ji tayi wata irin ashar na kai komo a wuyanta, da take ƙoƙarin narkawa matar nan, ta rasa abun da ta yi mata, haka kurum ta tsane ta. Ta yi ta kyararta ba ta son ta ga tayi wani abu na cigaba.

Sumayya ta fice daga office ɗin kamar ta yi kuka, ta koma reception ta nemi wuri ta zauna.

Ba uwar da ta tsinana a aikin yau, tun da head of news department ta yi mata wulaƙanci.

Kasancewar a makare ta je, ya sanya lokaci yayi gudu, Lawisa, wato head of news ɗin, ta din ga shiga tana fita, ta na kaiwa tana komowa, idan ta kalli in da Sumayya take sai ta haɗe rai.

Wannan karon bayan ta fita, a tare suka shigo da managern director, sai karairaya take yi masa, tun da ya shigo ma'aikatan suke ta gaishe shi.

Ban da sumayya da ɓacin rai ya saka ta cika ta batse.

Sai da yayi gyaran murya ya ce "Wannan ba sabuwar staff ɗin mu ba ce? Ya na ganki a nan? Wane department aka kai ta ne?"

Lawisa ta yi caraf ta ce "Sir ba ta da ƙwarewar aiki ne haryanzu, ana ɗan nunnuna mata aiki ne, kafin ta gama gogewa".

Ya ce "Ok, babu laifi" sumayya kamar ta kwaɗawa lawisa mari, a fusakarta da ta sha uban bleaching, duk tayi taruwar jini.

Ta daure ga gaida MD, sannan suka wuce gaba.

Tsaki Sumayya ta ja, tana duba wayarta.

Sai dai jin sallamar Nabila a reception ya sanya ta ɗago da sauri tare da amsa mata.

"Ya na ganki a nan?"

Nabila ta ce "Ke baki iya karrama baƙo ba ko?" Ta tsaya suka gaisa da admin ɗin da ke reception, sannan ta ƙarasa kusa da Sumayya ta zauna.

"Arfa, ya na ganki yanzu ne? Lokacin tashi daga aiki bai yi ba?"

"Kema ya na ganki a nan kamar mara galihu, ke baki da office ɗin da zaki zauna ne? Ki zo chambermu ki ga ofishin da aka bani hajiya, kamar wata sarauniya"

Sumayya ta ce "Eh ofishin da baki damu da aiki ba ko, sai sun dawo da ke gadin chamber tukuna".

Nabila ta yi dariya ta ce "Kin san wani abu, wai nan aikena aka yi, zan je na lallaɓa na zo da wata mata, ko in tattauna da ita, sannan in je shagari firm, zan haɗu da wani lawyer, kuma ni wallahi kaina ciwo yake yi"

Sumayya ta kalleta ta ce "Ba zaki ba kenan?"

"Ai faɗa ma ɓata baki ne, sumayya wurin nan naku mai kyau, tashi ki rakani na zaga" duk da ran sumayya babu daɗi, amma ganin Nabila ya sanya ta jin sanyi a zuciyarta.

Suka shiga zazzagawa, ta kaita news room, sai dai su na buɗewa suka tarar da MD da lawisa a ciki, suna aiki.

Sumayya ta risuna ta ce "Am sorry sir, ban san ku na ciki ba, Arfa mu je ki ga....

"A'a tsaya mana na ga nan ɗin, Nabila ta shiga cikin fara'a ta ce "Yallaɓai ina wuni?"

Shima cikin fara'ar ya ce "Lafiya ƙalau, ya ki ke?"

"Lafiya lau sir, ina fatan ba zan takura muku ba, ina son sanin abubuwan da ban sani ba a rayuwata, mussaman wanda ba field ɗina ba, sister ina wuni?" Tayi maganar tana kallon lawisa da ta yi bala'in haɗe rai.

Lawisa ta takurawa Sumayya ne, saboda tana ganin ƴar gayu ce, ga ta baƙa amma baƙinta mai kyau ga ƙwazo, tana gudun ta ƙwace mata matsayin ta, kuma ita bazawara ce, a da a wurin babu wanda ya kaita gayu a wurin, amma yanzu sumayya ta fita.
Yanzu kuma ga Nabila, ita da take da hasken fata ma sosai.

Nabila ba ta san lawisa ta amsa ko ba ta amsa ba, ta ja kujera ta zauna, tana yi wa MD tambayoyi, a kan abubuwan da suke cikin news room ɗin.

Lawisa ta ƙulu,ta din ga harar Nabila, amma ko a jikinta, ita kanta sumayya sai da haushi ya kamata abun da Nabilan take yi.

Nabila ta ce "Yallaɓai, ko zaka saka mini lambarka, idan wani abu ya kama na aiki, zan iya taimakawa i am barrister Nabila Yusuf"

Ya ce "Wow, what a very young and beautiful barrister, kin zama lawyer da ƙananan shekaru, ya karɓi wayar Nabila, ya saka mata lambarsa, ta tashi ta yi musu sallama.

Sumayya kamar ta yi bindiga, su na fita ta din ga ɗurawa Nabila ashar, a kan abun da ta yi, tare da gaya mata alaƙar Lawisa da kuma MD.

Nabila ta ce "Sumayya, dan Allah kar ki ɓoye mini, idan yana da kuɗi na ci rabona, na ga zai yi son mata"

Ganin Nabila na neman mayar da ita mahaukaciya, sai ta canza maganar.

"Ke kin san menene? wai ni zan kai rahoto har kashi biyu, sakaryar matar nan ta ce ba za a saka ba, wai ba sa buƙatar irin wannan labarin, MD ya tambayi me nake yi a reception ba na aiki, wai ta ce masa ban iya aiki ba, na rasa uban da na tsare mata ta tsane ni, dama ni na samu damar da ake baki, a wurin aiki, in yi wata shida ina aiki a wurin, wai ban iya aiki ba, da yake kwanan nan ya dawo daga ƙaro karatu, tun da aka ɗaukemu ya tafi".

Maimakon Nabila ta tausaya mata, sai ta hau dariya, "Ai kawai ki fara soyyaya da MD ko ta bala'i, shi ne zaki rama".

Sai da ta ga Sumayya ta yi fushi sannan ta ce "Sorry my sumy, maganar gaskiya babu daɗi, kuma kishi take da ke kuma tana ƙoƙarin kare abun da take so, shikenan"

Idon sumayya ya tara hawaye ta ce "Sai kuma ta din ga daƙile ni a harkar aikina? Ta yi mini adalci kenan?"

Nan ta ba wa Nabila labarin abun da ya faru, daga fitowarta daga gida, zuwa yanzu.

Nabila ta ce "Na shiga uku, sumayya me ƙasarmu ke son zama ne? A zahiri an nunawa mutane ana neman mai laifi, a baɗini kuma hukuma na ɓoye shi? Duk yadda ake fama da ƴan daba da masu ƙwace a garin nan, tirƙashi ana maganin ƙaba kai yana daɗa kumbura, ke ba ki san sunan wanda ya yi laifin ba?".

Sumayya ta girgiza kai ta ce "Ban sani ba, bai faɗa ba, korata ma suka yi".

"Mu ƙarasa titi mu tari napep mu je asibitin, mu tattauna da shi mutumin, ni kin san ba na tsoron a mutu ko a yi rai. Sannan zan je na samu Yaya Nasir na yi masa maganar wannan ai abun kunya ne"

Sumayya ta girgiza kai ta ce "A'a, na tsorata da kashedin da aka yi mana, a bar zancen kawai, ban san suwaye mutanen ba".

Nabila ta ce "Wallahi sai mun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login