Showing 135001 words to 138000 words out of 152254 words
zuwa masallacin idi.
Shi rabonsa da zuwa sallar idi ma, har ya manta lokacin, amma yau albarkacin auren mace ta gari, ta saka shi a gaba har zuwa masallaci.
Aka idar da sallar idi, suka haɗu a wani gate ɗin daban, bisa koyi ga sunna, jauhar ta bawa wata wayarta, ta ce dan Allah tayi mata hoton first eid with habinbi.
Ta ɗauka zai ce baya so, bisa ga mamakinta, sai ta ga ya saka hannu, ya dafo kafaɗarta jikinsa, yana kallonta, ta saka hannu ta zagaya a ƙugunsa kasancewar da kaɗan ta wuce ƙugunsa, ta kalleshi ita ma tana murmushi. Hotunan sun yi kyau sosai, banda wanda ya yi wa Al'amin kyakkyawan sani, ba zai gane shi ba, sai ya zama very decent and calm.
Har suka dawo gida, hannunta na cikin nasa, cike da shauƙi da nishaɗi.
Ya karɓi mukulli ya buɗe musu gida suka shiga, jauhar baba ta fara kira, ta yi masa barka da salla, ya ce mata idan mijinta na da account, ta tura masa ya saka mata barka da salla.
Ta kira yaya saifu ma, haka ta din ga bin family tana yi musu barka da salla.
Ta kalli Al'amin ta miƙa masa wayarta ta ce "Saka mini lambar baba, mu yi masa barka da salla"
"Bani da ita" ya bata amsa.
Ta marairaice ta ce "Dan Allah master"
Ya ce "Sai kuma ki yi"
Haka ta haƙura ta tashi ta ƙyale shi, ta tafi ɗakinta, ya din ga kallon kayan jikinsa, yana sake jinjina ƙoƙari da ƙarfin hali irin na jauhar, wai shi ta yi wa kayan salla.
A status ɗin ta, ta yi posting "Alhamdilillah first eid with my amazing Habibi, Allah ya ƙara wa zamaninka tsayi, ya maimaita mana"
Surayya ce ta fara ganin status ɗin, ta din dariya tana nuna wa 'yan gidan, suka din ga cewa pretending ne, na lallai sai ta nuna wa mutane tana cikin kwanciyar hankali, sai dai suna tsaka da gulmar, ta sake saka hotonsu riƙe da dadduma a filin idi, wanda hakan ba ƙaramin girgiza su yayi ba da ba su mamaki.
Master ya kai mintuna goma sha biyar yana zaune, ta fito sanye da leshinta da ta saka ranar ɗaurin aure, ta shafa powder da jambaki, ta saka kwalli, ta kwantar da gashin gaban kanta, da gel, ta yi ɗauri mai kyan gaske, gashi ta kaiwa Suwaiba tela ta gyara mata ɗinkin, dai-dai jikinta.
Har ya tashi zai shiga ɗakinsa, ya waiwayo ya ganta ta fito, mp ce a hannunta, tana bin waƙar da aka saka, a cikin nishaɗin barka da salla.
Cikin waƙar m sharif *Farin gani kai ne tauraro, ko a cikin samari, mai ji da ni ba ka yin ƙwauro ka sa na wuce gori, na ɗau takarda na riƙe biro, kai na saka a fari, kai zan ba dawakai, kowanne da silkai, matsayinka ya kai ba zan yi ma kishiya ba.......
Da haka ta ƙaraso gabansa tana rawa, tana yi masa fari da ido.
Tsayawa yayi yana kallonta yana murmushi, sai dai bai tsinke da lamarin na ta ba, sai da ta ƙaraso gabansa ta riƙe hannunsa wai sai ya yi rawa.
Karo na farko da ya buɗe haƙoransa talatin da shida yayi dariya.
"Ba dariya zaka yi ba, ka yi mini liƙi ko ka yi mini rawa" ya buɗe baki ya ce "You are not serious"
"Am serious mana, rawa ko liƙi, biyani ɗari shida ta ma da ka korar mini coustomer's" ya saka hannu a aljihunsa ya ciro dubu biyu da ɗari uku ya ce "Suke nan nake da su, uwar son kuɗi"
"Ungo dubu ɗaya, sauran bari na bayar da ayata a markaɗo mini, na haɗa da snacks da tuwon salla na raba. Ba ka ce ma na yi kyau ba, ka taɓa ganin mace da tayi kwalliya tayi kyau kamar yadda na yi yau?"
Yayi murmushi ya ce "Ni da ba kallon mata nake yi ba, ya za ayi na sani, ni dai ba ki yi mini kyau ba, kamar babyn roba haka ki ka zama" yayi maganar yana matsa kumatunta.
"Daga Angela zuwa 'yar madara, yanzu kuma babyn roba?"
"Eh, irin na wasan nan ba"
Jauhar ta ce "Kyau nayi maka ne"
Ta fice tsakat gida, tabbas tayi kyau kam, tayi fresh farar fatarta ta karɓi baƙin leshin sosai da sosai, kwalliyar ta yi mata kyau.
Tana tsakar gida, wasila ta shigo ta kawo mata tuwon salla, suka gaisa tare da yi wa juna barka da salla.
Wasila ta ce "Jauhar iyayen soyayya, mu matan layin nan, tare muka haɗa kai muka tafi idi, a hanya muka hango ku, an maƙalƙale hannun master ana yashe baki, kai jauhar a ji tsoron Allah"
Jauhar ta ce "Anty wasila kina saka mini ido wallahi, ki sa ka in ta jin kunya"
"Ke ba wata kunya, riƙe abunki wallahi, abunku gwanin sha'awa, kafin lokacin ya wuce, ba kowane namiji ne yake jure ayi ta soyayya ba".
Al'amin ne ya fito, Wasila tayi tsit dan ba ta san yana nan ba, ta gaishe shi ya amsa ciki-ciki.
"Master ina zaka? Kunun aya ka san baya daɗewa"
"Nura ne a waje ya kirani, ba nisa zan yi ba"
Ta ce "Ok to"
Daga jikin gate guduma ya ce "Antynmu barka da salla".
Jauhar ta ce "Yauwwa malam nura, ina fatan ka je idi?"
"Eh na je, na biyo mu gaisa sannan ki bani tuwon salla".
Jauhar ta ce "Aikuwa ka samu, amma sai ka kai mini markaɗen aya, ka sayo ƙanƙara sai na haɗa maka da tuwon"
Ya ce "Ba case matar babban yaya"
Al'amin bai sani ba, har gidansu jauhar ta aika da abincin salla, guduma ne ya kai ya kai na gidan su ita ma.
Ta zuba wa Al'amin, ya tafi da shi, tun da ya shiga wurin na su, Liti da sauran yaran suke bin sa da kallo.
Liti ya ce "Maza, wannan shuɗiyar audugar ruwan sararin samaniya fa, waye ya sayeka cikinta?"
"Ban sani ba"
Walid ya ce "Abun a tambaya ne, ni fa tun da na sanka sau ɗaya na ga ka saka manyan kaya, ranar da aka zarga maka uku, ina nufin igiyar sunnar ma'aiki da bint laban ɗin ka, wato madam 'yar madara"
Ya tsuke fuska ya ce "Mai laya"
Walid ya ɗaga masa hannu ya ce "Tuba nake, na kiyaya wannan ma'adanar abincin fa?"
Al'amin ya ajiye musu kwanuka, suka dirarwa abincin nan da ci babu ji babu gani.
Baba kuwa yaya saifu ya aiko, aka kawo mata fulasanta, da kuɗi dubu goma, kasancewar ba ta tura account number da ya ce ba a matsayin barka da sallar ta.
Da daddare da ya dawo, yana shigowa ta ji warin sigari, dan da alama ma a cake yake, bai kulata ba, ya tafi ɗakinsa ya baje a kan katifa, ta bi bayansa har cikin ɗakin, cikin matsananciyar damuwa ta ce "Haba master, shi ne ka je ka sha da yawa, kalli a yadda ka dawo fa, gaba ɗaya ka ɓata mini ɗan farincikin da na tsinci kaina a ciki yau" yayi shiru yana sauke numfashi.
Ta ƙaras ta ce "Tashi a cire kayan to, sai ka saka wasu"
"Get out"
"Ai zan tafi amma......
"I said get out" yayi maganar cikin tsawa.
Ta tashi a razane, ta bar masa ɗakin, cikin azumi dai Allah ya taimaketa ya ɗan nutsu, saboda baki a rufe yake, ba ya shaye-shaye sosai, yau da ga sallacewa ya koma ruwa.
Saboda tsabar takaici, ko baccin kirki ba ta yi ba.
Da safe kamar ba shi ba, ya tashi ya fito abun sa, ya sayo abun karyawa, sai share shi take yi, amma ya nuna ko a jikinsa. Kasancewarta mai matukar raunin zuciya, sai kuma ta sake.
Suna karyawa, Hafsa ta kira ta a waya, jauhar ta ɗaga tayi mata sallama ta ce "Amarya ba kya laifi"
"Mhmm, dama anko ne mama ta ce sai an nuna miki, shi 'yan gida za su yi da bikina, zan turo miki ta what's app lace ne dubu goma sha biyar sai atamfar kamu dubu tara, na san ba lallai ma ki yi"
Jauhar ta yi murmushi ta ce "Anty hafsa kenan, aikam dai kun san mijina talaka ne, zan sako dai abun da Allah ya hore mini na zo, in sha Allah"
"Dama na sani ai, mama ce ta takura a turo miki kar abun ya zama surutu, a ga kin fita daban. Allah ya sauwwaƙe tisya"
"Ba tsiya ba ce anty hafsa, idan ruwanka bai isa alwala bane sai ka yi taimama Allah ya kaimu bikin lafiya" ba shi aka gaya wa ba, amma sai ya ji maganganun hafsan tamkar direct da shi take, wani irin haushi da takaici ya kama shi. Sai dai ya basar ya cigaba da karyawa abun sa.
Ya kammala ci, ta tashi ta yi aikace-aikacenta, yau ma wata kwaliyyar ta yi da abun da Allah ya yassare mata.
Ya ce "Babyn roba"
Ba ta kalle shi ba ta ce "Saura ta rodi"
"Zaki gama kumbure-kumburen naki ki sace"
Ta share shi, tana shafa muzurunta d take cewa boti.
"Ina magana ki ka share ni, kina wasa da wannan abun da nake dana sanin kawo shi?"
"To me zan ce maka? Kawai ka je ka sha abun da ka sha, daga yi maka magana ka hantare ni" tayi maganar idonta na cika da hawaye, saboda takaici.
Maimakon ya damu, sai yayi murmushi ya saka hannu ya matsa kumatunta a hankali ya ce "Abun wasa na, you are like a toy to me, wani abu mai ɗan bani nishaɗi wasu lokutan"
Galala take bin sa da kallo, ita ce ma abun wasan.
"Kin daɗe kina yi mini abubuwa, abun da ki ka yi mini jiya ya tsaya mini a rai, ki ka ɗinka sutura sukutum ki ka bani, Allah ya suturtaki ranar da bayi za su tsaya a gabansa babu sutura. Na gode Allah ya baki miji nagari"
Da sauri ta sake kallonsa, sakamon abun da ya faɗa na Allah ya ba ta miji nagari.
"I still mean it, haryanzu ina kan bakana na rabuwa da ke a duk lokacin da ya dace, kina takura mini da yawa"
A fusace ta saka hannu, ta buge hannunsa da ya riƙe kumatunta, ta waiwaya tana kallon gefenta.
Ya ce "Idan ki ka kuskura ki ka jefe ni, yau ni da ke ne" tashi ta yi tana kuka, ta nufi ɗakinta.
Ayshercool
08081012143
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
Arewabooks ayshercool7724
https://chat.whatsapp.com/E3bH5OKBh9jH2aYygj0ArA
Kina bukatar kaya masu kyau da inganci??
Kina bukatar kayan kitchen wnd suke available ba order ba??
Kina bukatar adashin gata wnd zaki dauki kaya kamar kyauta??
Kiyi joining wnn group din namu insha Allah xakiji dadin kasancewa a ciki.
Muna da kaya available masu kyau da rahusa💃🏾💃🏾
Ko kimin mgn ta👇🏽👇🏽
08093932955
Ba ta ƙara kula shi ba wunin ranar, dama kuma ficewa yayi ya bar gidan, ta rasa sai zuwa yaushe Al'amin zai yadda ya karɓeta su yi rayuwa, kullum ba shi da magana, sai maganar da zata tayar mata da hankali na zai rabu da ita, gaba Al'amin yayi hannun riga da duk tausayi.
Abun da zuciyarsa ta raya masa kawai yake yi, ko ya yi maka daɗi, ko akasin haka ba damuwarsa bane ba.
'yan yaran da suka din ga shigo mata yawon salla, su ne suka din ga ɗebe mata kewa da rage mata damuwa.
Sai bayan sallar magariba sannan ta sake ganinsa, tun da ta yi masa sannu da zuwa, ta ajiye masa abinci, ta koma gefe ta na danna wayarta.
Sai da ya ci ya ƙoshi, ya samu wuri a kusa da ita ya zauna, ya ce "Abun wasan, ya dai?"
Ta ɗaga kai ta kalleshi ta sunkuyar, ta hau wasa da yastun ƙafarta.
Hannunsa ya saka shi ma a yatsun ƙafarta yana tayata wasan da take yi da su.
"Master"
"Mmm"
"Meyasa ka ke son lallai sai ka sake ni ne? Saboda ka ga bani da makoma ko? Ban taɓa burgeka, duk ƙoƙarin da nake yi, ba ka appreciating kullum cikin tsorata ni ka ke, kana gaya mini abun da zai ɗaga mini hankali, me nayi maka ne?"
"Baki dace da ni ba, da salihin mutum nagari ki ka dace. Da zan iya samun mutum mai amana da zai riƙe ki, zan iya rabuwa da ke ya aura, you have an innocent soul, that doesn't deserve someone like me, shiyasa nake yawan gaya miki haka. Ko jiya a fusace nake, na yi miki tsawa sai da ki ka yi kuka, ina ɗaukar hakkinki"
"To ni na ce maka bana son zama da kai ne? Ina yi maka addu'a, wataran zaka daina ai ko?" Tayi maganar tana kallonsa.
Yayi shiru bai yi magana ba, "Dan Allah ka yi magana, zamu iya rayuwa tare, irin damuwar ɗaya, matsalar iyalan da muka tashi a tsakanin su, ba sai mu zama familyn junanmu ba, mu rayu cikin aminci da walwala. Amma master meyasa ka ke shaye-shaye bayan ka san yana da illa ga lafiyarka? Yana saka aikata abubuwan da bai kamata ba, kayi faɗa da mutane a zubar maka da jini, ko ka zubarwa wani, har kisan kai fa yake saka".
"Wa na kashe?"
Ta ce "Ranar da na fara ganinka, a unguwarmu, gawar wani na ganka da ita ka soka masa wuƙa"
Yayi murmushi, ya haɗiyi wani abu mai ɗacin gaske.
"Ban taɓa kisan kai ba, ranar ce haɗuwarmu ta farko ko? Ban kashe kowa ba"
Cikin damuwa ta ce "Amma wuƙa fa na gani a gefen cikinsa, kuma meyasa ka ke shaye-shaye?"
"Bana son silly question, rabu da ni" ta gyaɗa kai kawai ta ƙyale shi.
Ranar hawan salla kuwa, Jauhar ba ta san me ake yi ba, Al'amin ya haɗa yaransa, da miyagun makamai, da sunan tsaro kar wasu daga wani wurin su zo su fake da kallon hawan salla, su kawo musu farmaki su cutar da wani.
Sai dai sun yi ba ta kashi da wasu marasa jin sosai da sosai, ciki kuwa har da yaran madaki.
Sai da 'yan sanda suka yi kame sosai da sosai, daga wurin hawan Al'amin bai koma gida ba, ya wuce cikin gari, saboda kar jauhar ta ganshi da makami, da jini.
A cikin garin ma, sai da suka yi wata fitinar, aka yi sare-sare da faɗace-faɗace.
Sai bayan kwana biyu, jauhar take jin labarin abun da ya faru a wurin hawa, ganin Al'amin lafiya ƙalau ya sanya ta kwantar da hankalinta, tare da bawa kanta yaƙinin cewar babu shi a rigimar.
Kwana na huɗu, tana kitchen tana girki, tana shirin kaɗa miyar cin tuwo, maman halimatu ta shigo gidan a gigice.
Jauhar ta ce "Maman halimatu lafiya kuwa?"
"Ke kina nan baki san abun da yake faruwa ba?"
Cikin rashin fahimta ta ce "A ina?"
"Wani ɗan daba ne wai madaki, daga can unguwar ku ya zo unguwar nan wai neman mijinki, wai ya illata masa yara, sai tarwatsa mutane suke yi, suna sara kan mai uwa da wabi a guje na ƙaraso"
Cikin tashin hankali ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un" take kanta ya sara, jikinta ya hau rawa, ta ɗauki wayarta ta kira lambar sa, sai dai tayi ta ringing baya ɗagawa.
Hijjabinta ta ɗauka, maman halimatu ta ce "Ina zaki? Saran mutane fa suke yi, duk wanda suka samu duka ko sara".
Ai ba ta ko tsaya bata amsa ba, ta fita cikin matsanancin sauri da tashin hankali.
Ba ta san in da za ta nufa ba, addu'a kawai take yi da roƙon Allah, Allah ya tsare mata mijinta.
Mutane na guje-guje ita kuwa kutsawa take tana duba ina zata ganshi tana kuka.
A wani layi ta hango shi, ya riƙe wani matashi, idon Al'amin kawai ta kalla ta san a buge yake, babu alamar mutunci a idonsa, idanun sun yi jawur sai gumi yake yi, yanayin sa ya tabattar mata da ha tafka ɓarna, kafin ta ƙarasa, ya fito da harshen sa waje, kamar yadda yake yi, idan ya ƙudirci aniyar yin wani abu, ya ɗaga sweazland ɗin sa, babu tsammani ya ganta a gabansa, ta riƙe rigarsa tana girgiza masa kai cikin tsananin tashin hankali.
"Idan ka kashe shi, rufe mini kai za ayi, ba lallai na sake ganinka, ka yi haƙuri kar ka yi kisan kai dan Allah"
Jikinsa tsuma kawai yake yi, ya aiwatar da abun da zuciyar sa take raya masa, saboda yadda haɗin da yayi amfani da shi, yake fizgar kansa yake jin sa tamkar jinjirin doki, zuciyarsa kuma kamar an kunna wuta.
Ta rirriƙe hannun da ya riƙe wuƙar da shi, da hannu ɗaya ya yi jifa da matashin gefe, shi kuma ya saki wuƙar, sai tangaɗi yake yi, ya kasa tsayuwa, sai gumi da yake tsatsafo masa ya furta "Madaki" kawai ya yanke jiki ya faɗi, sai a lokacin ta ga uban saran da yake gadon bayansa, ashe duk abun nan an sare shi a baya, rigarsa ta rine da jini.
Wani irin gigitaccen kuka ta saki, ta ce "Na shiga uku, dan Allah ku taimaka mini a kai shi asibiti" tayi maganar tana girgiza shi. Ya kalleta da idanunsa, suka yi jawur, jikinsa ya fara rawa ga gumi ya jiƙa masa fuska.
Ragowar mutanen da suke wurin, suka dare suka bar ta da shi, a wurin.
"Master dan Allah kar ka rufe idonka, yanzu zamu tafi asibiti, Allah ka kawo mini ɗauki, Allah ka duba lamarin nan".
Guduma ne ya shigo cikin layin da gudu, ya jefar da makamin hannunsa ya ƙaraso, wata irin ajiyar zuciya ta saki, yana zuwa ya jijjiga Al'amin ya ce "Master" sai dai idanunsa sun lumshe, saboda jinin da ya zubar.
Yayi ƙoƙarin ɗaga Al'amin, ya saɓa shi a kafaɗarsa, amma abu ya gagara, ba ƙiba ce da shi ba, sai dai akwai nauyi.
Ya kalli Jauhar da ta rikice, take ta kuka ya ce "Anty ki kwantar da hankalinki, in sha Allah yanzu zamu kai shi asibiti".
Ya din ga wani irin fito, kan ka ce kwabo, wasu matasa suka din ga ɓullowa da ɗaya ɗaya, su ma suna fiton wasu suna fitowa.
Suna zuwa suka yi tara-tara suka sunkuci Al'amin, guduma ya saɓa shi da ƙyar, da ƙarfin tsiya suka ƙwaci 'yar ƙurƙura a titi, suka ce mai ita ya bi si Asibiti su karɓa.
Sai dai da suka je, ma'aikatan lafiya, suka ce ba za su karɓe shi su duba shi ba, sai da jami'an tsaro.
Cikin kuka ta ce "Dan girman Allah kar ku yi mini haka, ku ceto ransa kar ya rasa ransa, dan Allah ku fara duba shi, kan a kawo 'yan sandan" ma'aikatan suka ƙeƙashe ƙasa suka ce, sai fa jami'an tsaro sun zo".
Ta din ga rusa kuka a cikin emergency, guduma sai bata haƙuri yake yi.
Ta kasa jurewa, ta tashi ta bi wani likita, ta riƙe rigarsa tana kuka ya ce