Showing 27001 words to 30000 words out of 152254 words

Chapter 10 - ?arfe A Wuta Book 1 Hausa Novel Complete

15 Dec 2024

325

fito daga prison ba mu sake ganinsa ba"

Ɗaya ne ya miƙe tsaye ya ce "Ke, ba ki da hankali, a dabar madaki ki ke naman wannan ɗan iskan? Kai kan taba, sako su mass su rakata, tun kan oga ya zo ya saka ayi gunduwa-gunduwa da namanta"

Sai yanzu ta fuskanci shigo-shigo babu zurfi wanda ya yi mata kwatancen ya yi mata.

Cikin sauri ɗaya ya ce "Meyasa za'a bari ta tafi? Bayan ka san yau zamu fasa ɗaukar fansa, ta kanta ya kamata mu fara" yayi maganar yana ƙoƙarin zare makami.

Sai dai tuni suka sako wa Nabila wasu irin murguza-murguzan karnuka, masu kama da zakuna.

Cikin ihu ta kwasa da gudun tsiya, tana kururwar neman agaji, saboda yadda take ganin kamar karnukan za su cinyeta ɗanya, sai dai gudun da suke yi ya wuce hankali, ga takalminta mai tsini ne sosai, dan haka suka kusa cimma ta.

Babu tsammani ta faɗi, saboda yadda numfashinta ya fara sama-sama.
Ayshercool.
08081012143
[7/22, 1:49 PM] null:               *ƘARFE A WUTA*

AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

P8

Ta saka hannu, ta kare kanta, tana jiran su hauta da cizo.

Wani irin fito ya yi wa karnukan, suka juya suka koma da gudu in da yake.

Matashin nan ne na ɗazu, da ta biyawa bashi, ya kalleta ya ce "Kin san meyasa na taimake ki?"

Bai jira amsar da za ta bashi ba ya ce "Ba na tunanin Aminu yana da wata ƴar uwa mace, dan haka ƙarya ki ke yi, akwai wata manufa a ranki da yasa ki ke nemansa. Sannan ya taɓa yi mini alfarma a lokacin da ya samu damar da zai kashe ni, kuma kin kyautata mini, alhalin baki sanni ba.
Ɗan daba ba mahaukaci bane ba, shaye-shaye ne yake ruɗa mana tunani.
Wannan shi ne kaɗan daga abun da ka iya samunki, idan ki ka cigaba da neman sa, ko bibiyarsa, wannan dabar babu abun da suke buri da fata, sama da su riga ƴan sanda kama aminu, mace ce ke ki kiyaye kanki, tashi maza ki tafi gasu can tahowa, idan suka cimmiki babu lallai na iya hana su illata ki"

Da ƙyar ta tashi, ta yi gaba da sauri, tana cigaba da haki, adaidaita sahu ta hau, ta yi masa kwatancen in da zai kai ta.

Kasancewar mai rabon shan duka, baya jin bari, suna tafe tana sauke numfashi, tana tunanin son sanin su kuma waɗan nan me yayi musu suke son su riga ƴan sanda kama shi, suna ƴan uwansa ƴan daba.

"Ko wani ya kashe musu?" Ta tambayi kanta.

"Yayi kisan kai, kuma a sake shi?
Aikuwa sai na ga ƙwal uwar daka" ta furta a hankali.

Ta so ta gaya wa Nasir, abun da ya faru yau, amma ta san tsaf zai ce zai zaneta, saboda kasadar da ta yi, dan haka ta bar wa ranta cewa sai ta samu wata gagarumar nasara, sannan za ta sanar da shi.

Ko sumayya ma ba ta gaya wa ba, tayi shiru da bakinta, sai dai faɗuwar da tayi, duk ta goge gwiwa.

Haka kurum tausayi, da tunanin makomar rayuwar matasan da ta gani, a harkar daba da shaye-shayen nan, ya dami zuciyarta ta rasa abun da yake yi mata daɗi, tana matuƙar son sanin me suke ji a cikin kayan shaye-shaye? Tabbas da ita wata ce, sai ta taimakawa rayuwar su, ko a mutum goma, idan biyu suka shiryu ai an rage.

Kamar wadda ta sha kayan maye, haka yau tayi bacci da wuri, gudun da tayi jikinta duk ciwo yake yi mata, ga numfashi sai wahala yake ba ta.

A wani ɗaki ta ganta, mai duhu sai haske kaɗan a ciki, ga karnuka duk a cikin ɗakin, sai haushi suke yi mata, an ɗaure su da sarƙa.
Ihu take yi tana neman agaji, amma babu wanda ya san tana yi.

Can sai ga wani mutum ya shigo, dogo sosai, mai cikar halitta, ba ta ganin fuskarsa saboda duhu, ya shigo ɗakin bai ce mata uffan ba, ya danƙo hannunta ya biyo tsakanin karnukan ya fito da ita daga ɗakin, ya ciro wuƙa zai caka mata a ciki.

Wani uban ihu ta saki, tana kiran sunan Allah, da na Abba da Nasir.

Tana buɗe ido, ta ga Abba a kanta, da Nasir, da su walida har da Anty da baba magajiya, ana ta tofa mata addu'a.

Kallonsu take yi ɗaya bayan ɗaya, ta ce "Abba ya na ganku a nan? Meyafaru?"

Nasir ya ce "Sannu"

Abba ya ce "Arfa ba kya addu'a ko?"

Ta girgiza kai ta ce "Ina yi Abba"

"A'a ba kya yi, da kina addu'a babu yadda za ayi, ki kwanta kina yi mana ihu da safiyar nan, shiyasa nake hanaki wannan shegen fentin da bulbula turare a jikinki, dole sheɗanu su yi ayari, su yi ta binki"

Nasir ya ce "Dan Abba ka yi haƙuri, haryanzu a tsorace take ma, a bari ta dawo hayyacinta gaba ɗaya, sannu Arfat, ki ɗauro alwala ki zo ki ɗauki Alqur'ani ki karanta".

Abba ya miƙe ya ce "Aishikenan, zan yi waya da Barrister, su baki day off, ki samu ki huta"

Nabila ta yi shiru tana rarraba ido, ta san lafiyarta ƙalau, tsabar tsorata ne da tayi.
Tayi shiru ba ta faɗi abun da ya faru ba, suka din ga yi mata sannu.

***
YALOKO ƘARAMAR HUKUMAR UNGOGGO

Matashiyar yarinya ce, wadda dudu shekarunta ba su fi goma sha huɗu ba, take ta iza wuta a cikin murhu, gefe ga garin tuwo a cikin ƙwarya.

Yaro ne ya yi sallama, ta ɗaga kai ta amsa masa.

Ya kalleta ya ce "Ramma ki zo ana sallama"

Ta ɗan waro manyan idanunta ta ce "In ji wa? Ko Habu ne?"

"A'a, wani ne da mota"

Ta miƙe tsaye ta ce "To mota kuma, ina zuwa?"

Daga tsakar gidan ta ɗan ɗaga murya ta ce "Mama, wai ana nemana a waje, bari na duba waye, ruwan ya kusa tafasa"

Daga cikin ɗaki matar ta amsa mata da "To ramma, hanzarta ki dawo, ina son zan fita ne"

Ramma ta amsa da "to" ta ɗauki hijjabinta ta saka ta fice waje.

Mintuna goma sha biyu ta dawo, jiki a sanyaye.

Mamanta ta kalleta ta ce "Menene?"

"Mama daga Kano ne, wai Anty mai jidda ce gidan da nake aiki, ta yi waya wai azo a ɗauke ni a mayar da ni, a satin nan za su dawo"

Matar tayi sak ta ce "Da wuri haka, ba cewa aka yi sai bayan wata guda zaki koma ba?"

Ramma ta ja ta tsaya ta ce "Jikina duk yayi sanyi, wai yanzu-yanzu zamu tafi"

"To shikenan ai babu wani abu, ki yi haƙuri kin ji ramma, ni kaina ba a son raina ki ke barin gabana ba, da Allah ya sa mun tara kuɗin kayan gado, shikenan sai ki dawo ki yi auren ki. Maza mu je na tayaki haɗa kayan"

Cikin abun da bai fi mintuna arba'in ba, suka haɗa kayan, suka yi sallama ramma ta bi direba zuwa gidan aikinta da yake Kano.

Yana zaune ya zuba musu ido, suna haɗa masa tea, Walid ya zuba ƙwayoyi a cikin kofin, sannan ya zuba shayin.

"Ƙara wannan ba zasu ɗauke ni ba"

Walid ya ce "Amma boss, kai fa ka ke hanamu sha a baya, tayi yawa wallahi".

"Ka ƙara mini na ce" yayi maganar a hasale.

Ya ƙara masa ƙwayoyin yana kallonsa, saboda ƙwayar da suke yi wa laƙabi da raina kama, a baya sam baya shan irinta, saboda yadda take bugarwa, wasu lokutan rabi suke ɓallawa su sha, amma ya ce a saka masa kusan biyar yanzu.

Ya ɗauki kofin ya kai bakinsa zai fara sha, Walid ya ce "Yau fa madaki za su je ɗaukar fansa cikin unguwa, daga majiya mai ƙarfi na ji zancen, daga jiya zuwa yau ya ce idan ɗan arearmu ya shiga ta su, a aika shi kawai"

Ya cigaba da girgiza kofin ba tare da ya yi magana ba, ya sake yinƙunrin kai kofin bakinsa, walid ya sake cewa "Wata ta je nemanka a arear, aka kaita dabar madaki, Allah ne ya yi da kwananta a gaba, da kasheta za su yi"

Duk da cikinsa yayi wata ƙara, jin an ce mace ta na nemansa. Wace mai tsautsayin ce wannan? Me take nema a wurina?, amma ya maze ya ɗago jajayen idanunsa ya kalli walid ya ce "Ni kuma?"

Walid ya ce "Ba zan yi maka ƙarya ba, da gaske nake"

Wani dogon tsaki ya ja, ya dungurar da kofin shayin, ya tashi ya ce "Ku ɗebo yaran nan na cikin unguwa, da na can wajen gari, ku sake dira a dabar madaki, ina son ɓarnar da za ku yi ta fi waccan, kar ku basu damar cutar da kowa. Ko kun gaya wa jami'an tsaro ƙudurinsu, babu abun da za su yi musu, ku far musu kawai, ka shirya komai, a bawa yaran na shan sigari" bai jira amsar walid ba ya fice.

Walid ya yi ajiyar zuciya, ɗan mama ya kalle shi ya ce "Da gaske ka ke wata ta je nemansa, ko kuma ka faɗa ne, dan ka hana shi shan ƙwayar nan?"

Walid ya ce "Duka, kai da ya sha abun nan, zai iya mutuwa fa"

Ɗan mama ya ce "Ai rigimar da yake yi kwanan nan, ta ƙara yawa, sai an ƙara saka masa ido sosai, kashe kansa yake son yi wallahi, wasu lokutan bana son muke watsewa  mu bar shi shikaɗai a gidan nan".

Walid ya girgiza kai ya ce "Ba zai kashe kansa ba".

"Ya aka yi ka san hakan?"

"Yana da abun da yake son cimma, kawai kayan ne gaba ɗaya ba sa ɗaukarsa gaba ɗaya yanzu, ka san yana cikin matsananciyar damuwa, duk kayan cajin nan kansa ba ya ɗauka kamar aljani, amma ina bincikawa, an yi mini alƙawarin wata zazzafar ƙwaya, daga kudu suke kawota.
Yanzu dai wannan aikin da ya ce , maza-maza ka kira kwangila a waya, ya haɗa mana yara, a basu kayan caji, zamu fasa ƙofa, ai Madaki shi da ɗaukar wata fansa a kanmu, sai dai a lahira idan ana yi. Sai mun ga abun da ya turewa buzu naɗi.
Ɗan mama ya miƙe ya ce "Ok, bari na hanzarta na fara haɗo su ta arear wajen garin nan".

Walid ya ce "Nima fitar zan yi, wurin liti zani, zan shiga karɓar balance". Suka fice gaba ɗaya.

Bayan tafiyar su Aminu ya koma cikin ɗakin, ya fara duba in da walid yake ajiye ƙwayoyi, amma ya dudduba bai gansu ba, ya zazzage ko ina, amma babu.

Wani irin takaici ya tokare masa ƙirji, ya ja dogon tsaki, ya ɗaga gefen katifarsa, allurar sa saura kwalba biyu kawai, kuma ya san ba ɗaukarsa za ta yi ba.

Haka ya zuƙe ta ya yi wa kansa, sai dai kamar kullum, yau ma ƙirjinsa ne ya fara da zafi, kansa yana juya masa.

Wuƙar da take gefensa yake ta kallo, zuciyarsa na raya masa abubuwa daban-daban.

Tun da Ramma ta suka isa cikin kano, gidan da take aikatau, kayanta kawai ta sauke a ɗakinta, ta hau aikace-aikace.

Duk da akwai wata mai aikin, wadda ta girmewa ramma, sosai da sosai, amma matar gidan ita ta yarjewa ta shiga sashenta, har uwar ɗaka da na maigidan ta gyara mata, a cewarta ramma ta fi nutsuwa, kuma ba ta taɓa ƴar aikin da ba ta yi mata sata ba, sai ita.

Matar gidan da ƴaƴanta gaba ɗaya sun tafi dubai hutu, shiyasa ta sallame ta, ta ce ta je gida ta huta, za su yi wata biyu kafin su dawo, kuma kwatsam yanzu sati biyu wai dawowa za su yi.

Tana falon matar gidan, tana ta uban aiki, ɗan kwanakin da aka yi ba a taɓa wurin ba, duk ya yi ƙura.

Ƙofar falon aka shigo, ta tashi da sauri, tana kallon mai shigowar, dan ba ta yi tsammanin ganin kowa a sashen ba, dai-dai wannan lokacin.

***

Nabila kuwa kusan kwanaki uku curr, ta kasa nutsuwa da kwanciyar hankali, da ta kwanta bacci, sai mafarkin karnuka, tayi ta ihu.
Haka Anty da baba magajiya za su danneta, su yi ta shafa mata man gelo da miski, ta ja bakinta, ta yi shiru, ba ta gaya musu abun da ta aikata ba.

Yau kuwa gajiya ta yi da zaman gidan, dan baka cikin hijjabi ta shirya, ta ɗauki ƴar ƙaramar wayarta, ta fito falo.

Umma ta kalleta ta ce "Ke da baki da lafiya, ina zaki je kuma?"

Nabila ta ce "Wurin aiki, akwai buƙatar in je zan kai wani bayani ne mai muhimmanci"

"Amma kin gaya masa, kar ya dawo ya tarar kin fita, ya yi ta faɗa"

"Umma ba daɗewa zan yi ba"

Saudat ta ce "Mhmm, a ma faɗi gaskiya, ko yawon banza za aje".

Nabila har za ta yi shiru, ta ga idan tayi shiru, za ta cutu, dan haka ta ce "Idan fitsari banza ne, kaza ma tayi, idan yawon ma zan tafi, mai lasisi ne akwai riba, ke ki yi mana"

Umma ta kalli Sauda ta ce "Sauda dan Allah ki din ga jan girmanki, Nabila fa ba sa'arki ba ce ba".

"Na saka da ke ne?"

Umma ta girgiza kai ta ce "A'a baki saka da ni ba, Allah ya taimaka".

Sumayya tana ta aiki a news room, Nabila ta yi sallama ta shiga.

Sumayya ta kalleta ta ce "Ina aikin?"

"Ban je ba, ya aikin?"

"Lafiya ƙalau, meyasa ba ki je ba?"

Nabila ta ce "Ke ba wannan ba, yanzu na ga managern ku a waje muka gaisa"

Sumayya ta ce "Good, ya aka yi?"

"Rahotonki na last week, a kan case ɗin yarinyar nan da aka yi wa fyaɗe, na ji shiru baku sake cewa komai ba"

Sumayya ta ce "Eh ya aka yi?"

Nabila ta ce "ina da intrest a kai ne, ina son shiga lamarin, na ji shiru haryanzu babu wani update, na an ɗauki mataki"

Sumayya ta ce "Dalla ware, kamar wata lawyer kirki, you are not even serious about the job"

Nabila ta ce "Ke ban son wulaƙanci fa, am serious, na ji an ce wanda yayi laifin mai lasisi ne a garin nan, ina son sanin waye shi?"

Sumayya ta ce "Nima ban sani ba"

"Kamar yaya ba ki sani ba, am serious fa, da gaske nake sumayya ina son shiga case ɗin, free of charge na taimaka wa yarinyar, na ji tausayin su sosai da sosai, yadda uwar take kuka. Kuma daga ji ƴan karkara ne, masu ƙaramin ƙarfi".

Sumayya ta galla mata harara ta ce "Sannu ambulance uwar taimako, manyan lawyoyi sun riga sun shiga case ɗin tuni, sai ki ja gefe"

"Suwaye manyan lawyoyin? Kuma wai waye dan Allah, waye yayi fyaɗen?"

"Ke! Nifa a rubuce aka bani, karantawa kawai na yi, hatta recording ɗin da aka saka, na muryar uwar da ƴar, tararwa na yi an yi, ban ma gansu ba, ban ga suwaye ba, balle na samu wani bayani. Case ma fa lamarin ya kusa zama a gidan nan, saboda saka muryar matar da aka yi, murtala ne dama ya yi recording ɗin ya saka, sai da aka kusa korarsu"

Nabila ta ce "To fa, ina murtalan yake?"

Sumayya ta ce "Ba zan nuna ba, kin ganki Nabila"

"Ba wani abu zan yi ba, sonake kawai ya haɗani da matar da yarinyar".

"Babu fa abun da zaki iya yi a kai, shi ma bai san waye wanda yayi fyaɗen ba, yarinyar aiki take a gidan, baƙo ne daga zuwa yayi mata. Dan Allah ki haƙura da case ɗin nan"

A ɗan fusace ta ce "Saboda me?"

Sumayya ta yi murmushi ta ce "Na ji an ce mutuniyar ki da jama'arta sun shiga cikin case ɗin, shiyasa na ce ki haƙura"

Nabila ta ce "Wa kenan?"

"Naja bunkure mana, antynki mudubinki, a bar ƙaunarki" Sumayya ta yi maganar tana dariya.

A take annurin fuskar Nabila ya ɗauke, haka kurum jikinta ya bata babu gaskiya a lamarin nan.

"Uban mudubin nawa, in dai wannan mudubin ne, Allah ya fasa shi na huta, wallahi sumayya tun daga abun da matar nan ta yi mini, kawai nake ji a jikina fuska biyu ce da ita, wadda take kallon jama'a da ita, da kuma wadda take ɓoyewa"

"To ko ma dai yaya ne, sun shiga case ɗin, kin san kuma ba zasu tsaya su saurareki ba, mussaman da ta iya yi miki kallon ke ba komai ba ce ba"

Nabila ta ce "Haka ne, amma rai dai an cire wa fara kai, lokaci ne, yana nan zuwa da zan bawa duniya mamaki, sai na saka ƙafa na bi ta kanta ko da halin ƙaƙa"

"To ki bi a hankali, kar ke duniyar ta baki mamaki"

Nabila ta yi shiru tana tunani.

Sumayya ta ce "Ya dai?"

Tayi guntun tsaki ta ce "Sumy zaman gidanmu babu daɗi, kamar in gudu wallahi".

"Wai Nabila ba zaki daina wannan iƙirarin ba?"

Ta girgiza kai ta ce "Ba zaki gane ba, faɗa muka yi da Siyama, har da Abba ayi mini faɗa, sauƙinta ɗaya ta ci duka da tukunya na din ga dukanta"

"Haba Nabila, wannan ai yawa ne, degree holder da dambe?"

"To yaya ki ke so in yi? In zuba mata ido ta yi mini duka? Ga uwarsu ta addabi rayuwata, ba ta san yadda ta tsane ni, nima haka na tsaneta ba, kawaici kawai nake yi mata ba.
Duk uban ƴan matan gidan nan har da zaurawa, babu wanda duka sanyawa ido sai ni, da na motsa ayi ta janyo mini jafa'in karuwanci" ta ƙarasa maganar hawaye na cika mata ido.

Sumayya ta ce "No dear, dan Allah ki ƙara jurewa, lokaci ne da kin yi aure zai wuce"

"Yaushe zan yi auren? Dan Allah ni mummuna ce Sumy? Duk saurayin da ya zo, sai za a fara maganar aure, sai ya gudu kamar wata jaɓa"

"Nabila kina da matsala, Babu wata halittar Ubangiji mummuna. Ga ki fara, ga gayu da ilimin addini da na zamani, kina da kwarjinin da ki ke bawa maza tsoro ne, ai ke kalar manya ce tawan, ba duk kai ba"

Cikin takaici Nabila ta ce "Ba wasu manya, manyan da suka din ga yaudarata Allah ya isa da ba su aure ni ba suka ɓata mini lokaci, ni yanzu kowaye ma zan aura na bar musu gidan, ko ba na son shi. Idan ba haka ba wallahi wataran sai na gudu"

Sumayya ga tausayin Nabila ga dariya, tabbas Nabila akwai farijinin samari, masu kashe mata kuɗi ma kuwa, sai dai Nabila ta fiye zaɓe-zaɓe, kuma ba ta fiye ba wa masu sonta da gaskiya muhimmanci ba.

"Ki gudu ki je gidan uban wa? Gaki ga Abba nan maza ki gudu kar ki fasa"

Sai kuma ta koma rarrashinta, har bayan azahar suna tare, sai da sumayya ta tashi suka fito tare.

A reception suka tarar da wani mutum, ana ta yi masa fadanci, yana hura hanci cikin manyan kaya na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login