Showing 54001 words to 57000 words out of 152254 words
a tsakiyar tsakar gidan.
A tsorace ta ce "Lafiya kuwa? Meyafaru?"
Ya ƙarewa gidan kallo ya ce "Dama a nan ku ke rayuwa, ƙasƙantattun matsiyata, amma har ki ke fatan ganin an kai ni kotu an karɓowa ƴar ki hakkinta? Har wani hakki ne da ita? Talaka yana da wani hakki ne ko ƴanci?"
Cikin rawar baki ta ce "Waye kai malam?"
"Na yi miki kama da malam? Ni na yi wa ƴar ki fyaɗe, da ki ka tafi nema mata hakkinta?".
Sakin tsintsiyar ta yi, tana kallonsa, a ƙalla zai kai shekaru talatin da takwas, kallon idonsa ta yi babu mutunci ko imani a cikin su.
"Yanzu kai ka iya samun ƙwarin gwiwar zuwa gabana, ka gaya mini ka yi wa ƴa ta fyaɗe? Bayan ka turo mini waccan bayahudiyar ta yaudaremu, ba ta yi nasara ba, shi ne ka zo gabana ka gaya mini ka keta wa ƴa ta haddi?"
Ya fara takowa gabanta ya ce "Yes, na zo na ƙara kashe ƙishirwa ta ne, sannan in yaba wa baiwar Allah da Allah ya yi wa ƴar ki, kin iya haihuwa"
Yayi maganar yana wata irin dariya, a fuskar maman rahama, da tuni idonta ya fara zubar da hawaye.
Ya saka hannu ya riƙe ɗan kwalin kanta, haɗe da gashin kanta, ya tsuke fuska ya ce "Kin san ko ni waye, da ki ka saka na tako ƙafata wannan ƙazamin kucakin ƙauyen"
Ihu ta saki, saboda zafi.
Salim ya ce "Kai Abdul wannan yawa ne fa, ba wurinta mu ka zo ba fa"
"Bar ni Salim, duk da hausawa sun ce abun cikin ƙwai, ya fi ƙwai daɗi, what if na wajen ƙwan ya fi?" Yayi maganar yana riƙe rigarta.
Salim ya ce "No, kar ka yi haka, akuyanci kenan ai, dan Allah ka bari"
Abdul zai yi magana, suka yi ido huɗu da rahama, a tsaye a ƙofar ɗakin su, tana kallonsa.
Ayshercool
08081012143
🔞*PAID BOOK NE, ₦500 BOOK1-3 VIA 0009450228, AISHA ADAM JAIZ BANK, SAI SHAIDAR BIYA TA 08081012143*
*Ina masu buƙatar sayen nagartattun kayan magungunan mata, wanda babu cuta ko algus a ciki, ku yi joining link ɗin nan, domin samun nagartattun magungunan mata*
https://chat.whatsapp.com/BLqFsnlyNf0B483RhoWq8v
15
A take ya hankaɗe uwar a gefe, ya yi wa ramma wani irin miskilin murmushi, ya nufe ta yana wata irin tafiya, irin ta riƙaƙƙun ƴan iska ya ce
"Hi baby girl, long time almost 2months kenan fa ko?"
Hawaye ne ya fara bin fuskar ramma, jikinta ya hau rawa.
Ya sanya hannu ya dafa jikin bango, yana ƙare mata kallo ya shafi sumarsa ya ce "To ya ki ke, kin warke?"
Shiru ta yi ta sunkuyar da kai, tana tuna waccan ranar, da irin yadda ya keta mata haddi cike da zalunci.
Ya ce "Ohh, wai waccan ranar ce haryanzu ba ki manta ba ki ke kuka? Ya wuce ai wancan, kin bar ni da tsananin kewarki, duk ruwan da na sha komai sanyin sa, ya daina kashe mini ƙishirwa".
Ya kai hannu ya ɗago fuskarta, ya shafi hawayen da suke ta ambaliya a kan fuskarta.
Yinƙurawa mamanta ta yi da sauri, tana kururuwa ta ce "Kar ka taɓa mini ƴa, mugu azzalumi, wai babu wanda zai kawo mini ɗauki ne?"
Ya kalli su Salim ya ce "Ku saka mini matar nan a silent"
Haka suka rirriƙeta, suka ɗaure mata baki, suka shaƙa mata wani abu, a take jikinta yayi laƙwas.
Ya sake kallon ramma ya ce "An ce akwai unborn ɗi na a cikin ki ko? da gaske za ki haife shi kuma?"
Cikin kuka ta ce "Ban yafe maka ba, ka lalata mini rayuwa, ban sanka ban taɓa ganinka ba, ka biyo ni gida kana wulaƙanta mini uwa, dan bamu da kuɗi, Allah ya saka mini" tayi maganar tana fashewa da kuka iya ƙarfin ta.
Salim ya sunkuyar da kai ya yi shiru, haka nan ya ji abun yayi masa wani iri a zuciyarsa, sauran matan da suke lalata da su, suke kai kan su, wannan kuma yarinya ce ƙarama.
Dariya ya yi ya ce "Dan kin ce baki yafe ba, ba zai hana ni shiga aljanna ba, kun ƙuduri aniyar neman hakkinku, duk da an yi muku tayin kuɗi kun ƙi, zan nuna muku ƙarfi da izzar kuɗi a ƙasar nan".
Ya danƙi hannun ramma, da jikinta ya ɗauki zafi sosai.
Tana ihu tana kiran mama, ya ja ta suka fice daga gidan, suka sakata a mota suka tafi da ita.
*****
Ɗan mama ne ya shiga ɗakin Viper, ya tarar da shi yana ta sintiri a ɗakin.
"Ka daɗe ka yi ƙarko uban gidana"
Viper ya tsaya cak, yana jiran ya ji me zai ce.
"Na yi aikin da ka saka ni, ya tafi yadda yakamata "
Ya kaɗa kai tare da yi masa alamar ya ƙaraso.
"Ina labarin malam lawan?"
"Kamar dai yadda ka ce, an kula da komai, sai dai babu wanda ya sake zuwa, gashi yanzu yana yawo a cikin unguwa".
"Madaki fa?"
"Shi ma kamar dai yadda ka sani, Honorable indabo yake yi wa aiki yanzu".
"Ina buƙatar isassun kayan aiki, a kwanakin nan zan dirar masa, mu ɓalla ƙarfe, sai dai mu yi mutuwar kasko, ayi wadda za ayi".
"Ba yanzu ba" suka ji muryar Walid.
Suka mayar da hankalinsu kan sa.
Walid ya ce "Viper da sauran lokaci, kai ka san madaki ba haka kurum yake daba ba, da zai kasu cikin sauƙi, da tuni mun kawar maka da shi, ka ɗan saurara tukuna"
A hasale ya ce "Ba zan saurara ɗin ba tukuna"
"Viper!"
Ciki ƙaraji ya ce "Walid ka ƙyale ni"
Walid ya girgiza kai ya ce "Da zan iya, da tuni na yi, mutumin nan ya fi ƙarfinmu ko ta ina, idan ka yi amfani da zuciya wallahi ba zamu yi nasara ba, ka bari mu bi komai a hankali mu lissafa, yadda ko mutuwar kasko ce mu yi"
Cikin ƙaraji ya ce "Ba zan jira ba, na gaji, na gaya maka na gaji. Na so bin komai a hankali, meyasa ka kawo mini yarinyar saboda me? ka san ka ƙara tunzara zuciyata yaya ka ke so na yi, so ka ke sai na haukace tukuna? Kalli yadda na koma walid, kalle ni, abun da nake ta ƙoƙarin dannewa ka fama mini, dan me zaka kawo mini wannan yarinyar sannan ka ce na nutsu how? Ta ɗauki wayata ta tafi, ka na da tabbacin hannun wa wayata za ta shiga? Idan aka tashi kama ni, kana da tabbacin su waye za su kama ni, idan na ƙare a haka ban aikata abun da nake ƙuduri ba fa? Ko dai ka nemo duk in da yarinyar nan take na kasheta, ko kuma a yau ba sai gobe ba, sai na yi gaba da gaba da madaki ko na kashe shi ko ya kashe ni, amma kafin nan sai na fara gaba da gaba da wancan dabban" tuni gumi ya tsatsttsafo masa, jijiyoyin kansa suka mimmiƙe, kafofin gashinsa ya bubbuɗe.
Walid ya taka gabansa a hankali, cike da shirin ko ta kwana, dan ya san ƙarshenta sai ya ba shi gwale-gwale, ko ya mangare shi.
Ya shammace shi, ya soka masa sirinji a damtsensa, kasancewar jikinsa babu riga, ya fara yi masa allura, sannan ya fara yi masa magana.
Walid ya ce "Na san na yi laifi, amma ka bari na gyara laifina da kaina, na san abun da ka ke ji ɗan uwa, ba kai kaɗai ka ke ji ba Al'amin"
Viper ya zubawa walid ido, ya rasa me zai yi, yana tsaye ya kashe masa jiki, ba zai iya komai ba, kasa tsayuwar yayi, ya tafi zai faɗi walid ya riƙe shi ya kwantar, ɗan mama kuwa dama tuni ya arce, dan yana tsoron a shaƙe shi.
Barrister Naja'atu ce zaune a katafaren ofishin ta, tamkar na matar gwamna, yana ɗauke da duk wani kayan alatu da ake buƙata.
Sannu a hankali take shafa screen ɗin wayarta, daga bisani ta saka wayar a kunnenta.
"Honorable, ka isa Abujan ne?".
Ya amsa da "Eh ma sauka"
"Ok, yaya maganar yarinyar nan da Abdul ya yi raping?"
"Yes, he handle the case himself, yayi maganin abun".
Ta ce "Ok, ina fatan ka ja masa kunne, kar ya je ya aikata wani shirmen da ba zamu iya gyarawa ba".
Ya ce "No, kar ki damu, zai yi abun da ya dace".
Tayi ajiyar zuciya ta ce "Shikenan, dama ina tsoron ya yi wani shirmen ne, amma tun da ka ce haka, shikenan"
Ta katse wayar, ta mayar da hankalinta kan sakatariyarta da ta shigo.
Cikin gyatsine ta ce "Ke kuma ya aka yi?"
"Kin yi baƙi ne ma"
"Suwaye?"
"Eh to, da alama dai ƙorafi suka kawo, ke suke.....
"Ke bani da lokaci, ayyuka sun yi mini yawa, su ganki ko wani daban, hutawa nake buƙata, wannan jaraba a uzzurawa rayuwarka, london zan wuce ma ni this week na je na huta. Ki fita ki je ki sallame su" ta juya jiki a sanyaye ta bar office ɗin.
Salim ya kalli Abdul da ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, yana shan giya a cikin wine cup ya ce "To wai yanzu ya zaka yi da yarinyar nan da ka kawo ka ajiye, Ga abun da aka tsara, kai kuma ga abun da ka yi?"
Ya ɗan girgiza giyar a cikin kofin sannan ya ce "Gani na yi za ta ci bulus idan ta tafi a haka, sai na gama moreta zan aikata kawai"
"Amma ba ka ganin, hakan zai iya kawo matsala, yanzu ko a nan gaba?"
Ya girgiza kai ya ce "Ba wata matsala, na ɗan lokaci ne, zan gama abun da zan yi da ita, zaka iya tafiya ma kawai"
Ya jinjina kai ya ce "To shikenan"
Sannu a hankali ta buɗe idonta, ta din ga gani dishi-dishi, ta kasa tantance a ina take, dan ba ta taɓa ganin wurin ba.
Ji ta yi an rufe ƙofa, ta ɗaga kai ta kalli mai shigowar, take gabanta yayi mummunar faɗuwa, duk da idonta bai gama washewa ba, amma sarai ta gane shi.
"Kin tashi kenan? abun da aka shaƙa miki bai taka kara ya karya ba, amma ki ka yi wannan dogon zangon" yayi maganar lokacin da ya tsuguna a gabanta yana kallon idonta.
Ƙirjinta ya din ga bugawa da sauri da sauri.
Ganin ba ta ce komai ba, ya sanya ya tashi ya fita, babu jimawa ya dawo da plate a hannunsa, ɗauke da indomie da kifi a ciki, sai ruwan roba, hannunsa ɗaya kuma ledar magunguna ce.
Ya tura mata plate ɗin gabanta, sannan ya fara haɗa alluran.
Tayi shiru ta zuba masa ido, har sai da ya ce "Ki ci mana, allura zan yi miki"
Cikin kuka ta ce "Dan Allah kar ka kashe ni"
Abdul ya yi wani murmushi ya ce "Saboda me?"
"Ni dai kar ka kashe ni, dan Allah ka mayar da ni wurin babata"
Ya kalleta ya ce "Kashe ki fa sai na yi, ba dai ke taurin kai ba ke da babar taki, zan nuna muku cewa talaka ba komai bane illa bawa kuma takalmi ga masu kuɗi da dukiya, ba yanzu zan kashe ki ba, sai kin gama yi mini amfani tukuna.
Yanzu ki ci abincin nan, zan yi miki allurai na zazzaɓin da yake jikinki".
"Ni ba zan ci ba" ta yi maganar za ta tashi tsaye, amma ya daka mata tsawa ya ce "Wallahi idan ba ki ci ba, a yanzu zan kashe ki, ko gawarki babarki ba zata gani ba".
Babu shiri ta fara cin abincin, sai dai a loma ta uku, ta hau amai, ta amayar da duk abun da ta ci.
Cikin tsananin takaici ya ce "Ke mahaukaciyar ina ce zaki yi mini amai a nan? Nan yayi miki kama da wurin juye ƙazanta?.
Tayi shiru ta sunkuyar da kai.
"Tashi mu je in nuna miki in da duster da mopper suke ki gyara"
Cikin tsoro ta tashi, tana jiri tana bin bango, haka ya saka ta gyara wurin da ta yi aman.
Bayan ta gyara, ta shiga banɗakin tayi alwala, ta fito ta tayar da salla, ba tare da ta san ina ne gabas ba, da kuma adadin sallolin da ake bin ta ba, dan ba ta san adadin lokacin da ta shafe, ba a hayyacinta ba.
Ya dawo ya tarar da ita a zaune, a takure wuri guda, bai kulata ba, ya ƙarasa ya sanya hannun sa a goshinta, ya ji shi da zafi rai. ɗaga ta ya ja ta ya dungurar da ita a kan gadon.
Ya kama hannunta, ya saka sirinji, ya fara ɗaukar jininta.
Bayan ya gama ɗaukar jininta, ya yi mata wasu allaurai duk a jijiyar hannunta.
Ta zubawa saurautar Allah ido, dan kasa magana ta yi, tun yana allurar ta fara jiran jin alamar ciwonta ya ƙaru, dan ta sallama kashetan zai yi kamar yadda ya faɗa, amma bayan ya gama yi mata ya tashi ya fice, ya kulleta a ɗakin, ba tare da ta ji yanayinta ya sauya ba.
***
Abun duniya fa ya ishi Nabila, wayar Viper ta zame mata wahala, dan kuwa kashe ta tayi gabaki ɗaya, sai dai duk in da ta zauna, musamman da daddare, idan ta shiga cikin duhu, Viper ne yake yi mata gizo, har abun ya fara tasiri a yanayin mu'amalarta.
Tana toilet tana wanka, wayarta ta din ga ringing babu ƙaƙƙautawa, ta kammala wankan ta fito, ta ɗauki wayar tana dubawa.
Lambar Nasir ta fara kira, ta nemi wuri ta zauna a gefen gado, tana jiran ya ɗaga.
"Ina ki ka shiga ne? Ko kina wurin aiki ne?"
Ta ce "A'a, yanzun nan na dawo gida"
"Baki da lafiya ne?"
"No, gajiyar aiki ce kawai"
"To, aikin ki yayi kyau arfa, na yi waya da mu'azzam, gayen nan da ki ka faɗa mun kama shi, tare da tabar wiwi da ƙwayoyi"
Sassanyar ajiyar zuciya ta yi ta ce "Alhamdilillah ala kulli halin, Allah shi ne abun godiya, what next?"
Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Na saka lallai su fara tuhumarsa, ya faɗi in da Viper yake".
Zuciyarta ta din ga raya mata ko ta sanar masa kai tsaye, abubuwan da suke gudana, ta bashi wayar hankalinta ya kwanta, amma zuciyarta ta gargaɗe ta a kan aikata hakan.
***
In da ya bar ta a kan gadon, nan ya je ya sake tarar da ita, ta tashi ta zauna ta dunƙule jikinta a wuri ɗaya tana bacci, sai ajiyar zuciya take yi.
Wani irin murmushi ya yi, yayi miƙa lokaci guda, ya fara rage kayan jikinsa.
Motsinsa ya sanya ta farka, fes ta buɗe idanunta, sai dai hankalinta ya yi mummunan tashi, ta ja da baya, ba ta ƙaunar ganinsa ko kaɗan.
Ya hawo kan gadon ya nufota, ta din ga ihu tana kiran sunan Allah, ta na yi masa magiyar ya ƙyaleta, ya mayar da ita gida.
Amma kamar ya kamo ƴar kaza, haka ya danƙota zai yi mata rashin mutunci, sai dai yana haɗa ta da jikinsa, ya ji kamar ana hura wuta a Jikinta, saboda zafin zazzaɓi, gashi sai wani irin ƙarni take yi, da warin man kaɗanya da take shafawa ya haɗe da ƙarnin koren sabulun da take wanka da wanki da shi.
Ba wannan ya fi damunsa ba, rashin saukar zazzaɓin jikinta ne bai so ba, dan ko a yanzu a galabaice take.
A ɓangaren ramma ma, warin giyar da yake yi, da ƙamshin turaren sa ya sanya ta fara yinƙurin amai, ba shiri ya cikata, ta sauka da gudu, ta tafi banɗakin da yake cikin ɗakin, ta din ga kwara aman, sai dai ruwa kawai take amayarwa, bayan shi babu komai a cikinta.
Ta gama aman tana ta sauke numfashi, ta lallaɓa ta fito, tana bin bango, sai dai ta tsaya cak tana kallon sa yadda ya zuba mata ido.
Cikin kuka ta haɗa hannayenta ta ce "Dan girman Allah ka yi haƙuri, ka mayar da ni in da ka ɗauko ni, hankalin mamana na san yana can a tashe, dan Allah ka yi mini rai ka yi haƙuri" ta ƙarasa maganar tana zubewa a kan gwiwoyinta tana bashi haƙuri".
Strip ɗin gwajin ciki ya ɗago da yake hannunsa, wanda ya gwada da jininta da ya ɗiba ɗazu ya ce "Ke ce mace ta farko da ta fara ɗaukar cikina, kin kafa tarihi, tun da ki ka ce ba za a zubar ba, nima na ji ya shiga raina, ina son abuna, zaki haife shi kafin na kashe ki, kuma ba zan kashe ki ba sai bayan kin haihu" ta yi shiru tana cigaba da zubar da hawaye, wai ita ce ɗauke da ɗan shege a cikinta, a wani keɓantaccen wuri tare da ɗan iska, saboda kawai ba su da kuɗi, sai yau ta ƙara tabattar da illar talauci.
Ya miƙe tsam daga kan gadon ya fice ya bar ta a ɗakin, ba tare da sanin makama ko abun yi ba.
Sumayya ce a office ɗin manager, fuskarta ɗauke da matsananciyar damuwa.
Ya kalleta ya ce "Sumayya yaya aka yi ne? Ko yayi miki wani abun ranar da ku ka yi program ɗin?"
Ta girgiza kai alamar a'a.
"To menene? Na ga kin yi editing ma kin tura mini, komai yayi normal, na ce a saka idan lokaci yayi kin yi ƙoƙari sosai, ina ga program ɗin hannunki zai dawo gaba ɗaya"
Ta sauke numfashi ta ce "Sir"
Ya amsa da "Yes ma"
Sai kuma ta yi shiru.
"Ki gaya mini mana idan da wani abu" ta girgiza kai ta tashi ta fita.
Addu'a ya din ga yi a zuciyarsa, tare da fatan Allah ya sa ba wani abun indabo yayi mata ba, dan ya san halinsa sarai.
Nabila tana office ɗin ta, tana aiki, barrister Habib ya buɗe ya shiga da sallama.
Miƙewa tayi tsaye ta ce "Sannu da zuwa, da ka kirawo ni ai"
Ya ƙarasa gaban teburinta ya ce "Babu damuwa, aikin da ki ka ba ni ne na yi"
Tayi murmushi ta ce "Taimakon da na nema dai aka yi mini"
Shi ma murmushin ya yi ya ce "Zan tura miki court ɗin da aka fara yi masa shari'a, da sunan wurin wanda za ki je ya binciko miki file ɗin, akwai dai wani abu a ɓoye".
Cikin sauri ta ce "Ok, ai daga nan ma kana tura mini sai na tafi"
Ya ce "Wait, ki tafi yanzu ba ki da aiki ne?"
"Ai na kusa kammalawa saura kaɗan ne"
Ya ce "shikenan, zan tura miki ta what's app, amma ki bi a hankali, fa kar ki je ki yi abun da ba shikenan ba"
"In sha Allah, na gode sosai"
Yana fita ta fara lissafi a ranta, tun kan viper ya je hannu, za ta bibiyi cases ɗin sa na baya, domin a shirye take da ta ƙalubalanci hukumar shari'a ciki har da alƙall da kuma hukumar gidan yari, kan sakin Viper ba tare da ƙa'ida ba, ta san ko ba ta yi nasara ba, za ta yi suna sosai.
Tattara