Showing 36001 words to 39000 words out of 152254 words
office could you imagine. Sai an yi magana ace ba ma taɓuka komai, an janye jami'an tsaron da aka ajiye a unguwar ma"
Nabila ta daki tebur tana huci, zuciyarta har wani tafasa take yi ta ce. "Shikenan, da wanda suka kashe, da kwanciyar hankalin mutanen unguwar, duk ba matsalar su ba ce ba? Personal interest ɗin su ne kawai a gabansu?"
"Gashi kuwa kina gani, yanzu idan na matsa zasu iya raba ni da state ɗin nan ma gaba ɗaya, ni kuma bana son barin garin nan saboda, i don't want to miss you dear"
Kamar za ta yi kuka ta ce "Wallahi Yaya gaba ɗaya aiki ya fita daga kaina, anya ba haƙura zan yi na kama kasuwanci ba, kai babu daɗi, sumayya ma haka, nima dan jan wuya ce, idan aka addaba mini ajiye aikin zan yi, gaba ɗaya ayyukanmu na taimako ne, amma ɓata gari sun yi kane-kane a ciki. Yanzu menene abun yi?"
Nasir ya ce "Abun yi kawai na mayar da hankali, na yi musu abun da suka ce, shi kansa wanda suke son a kama ɗin, ina zargin wani abu ne akansa, ko tsakaninsa da wani ya sanya suke son in kama shi, ban da baka ya za ayi ace ɗan daba ya gagara kamuwa, alhalin yana cikin garin nan"
Ta ce "To ka ce ba zaka yi ba mana, idan sun matsu su manyan su kama shi mana"
Yayi dariya cikin takaici ya ce "Ba zai yiwu ba arfa"
Ta kwantar da murya ta ce "Ka kwantar da hankalinka yaya, komai lokaci ne, sai dai duk ranar da Allah ya sa muka kai wani matsayi, mu yi iya yinmu, wurin ganin ana tsage gaskiya duk ɗacinta, lokaci ne ka yi haƙuri"
Yayi murmushi ya ce "Idan ban yi haƙuri ba, ya zan yi, dolena ai, na san lokaci ne
Ta ce "Yauwwa, in sha Allah, da ni da kai da sumy, zamu yi nasara a rayuwar aiki, and zan yi duk iya yi na, na ga ka kama aminu"
Nasir yayi murmushi ya ce "How? Na yi amfani da techniques ɗina, na kama masu laifi, amma na kasa samunsa, akwai alamun shi ma yana da masu tsaya masa"
"Mu ma Allah ya tsaya mana, zamu yi yaƙi da duk wani mai kawo cikas ga aiki da adalci"
Dariya ta bawa Nasir ya ce "Ka ga ƴan ƙasa nagari" suka yi dariya gaba ɗaya.
***
Sanye yake da gajeren wando, da riga armless baƙa, joint ne mai kyau sosai da sosai, yanayin matasan da suke shiga suna fita, zai tabattar da na masu hannu da shuni ne.
Ya ɗora ƙafarsa a kan kujera, yana ta shan shisha, kusa da shi wasu matasan ne, suma suna ta nasu shaye-shayen.
Sai matashi ɗaya da yake kujerar da take facing ɗin sa, yana shan sigari, ya kalli Abdul ya ce "Kai Abdul, wai wannan lumshe idon da ka ke yi, lafiya kuwa?"
Ya sauke ƙafafuwan sa, ya tashi ya gyara zamansa ya yi wani murmushi ya ce "Ba lafiya ba" yayi maganar yana murmushi.
"Ba lafiya ba kuma ka ke dariya?"
Ya girgiza kai cike da shauƙi ya ce "Na rasa ya zan yi ne, tun ranar da na samu wata cika, under 18, na sarara na kasa mantawa da ita, duk matan da nake harkata da su, na kasa samun abun da nake so, kamar yadda na samu a wurinta. Ashe duk wahalar banza nake yi da nake biyewa manyan yaran nan"
Saif ya ce "To ka koma mata mana"
Abdul ya ce "I rape her" yayi maganar yana sake sakin hayaƙi a iska.
"Rape kuma? How?"
Abdul ya ce "I don't know, i was drunk, bai gama sakina ba kuma, na je gidan aunt maijidda, na tarar da yarinyar ashe ba ta gari ita da mijinta, duk yadda nake da ƙyanƙyami, nake son manyan mata, amma na kwaɗaitu da yarinyar nan, tun a ranar farko da na fara ganinta.
I don't know why, but i still need her, na kasa samun yadda nake so, ita ɗin dai nake son sake kasancewa da ita.
Warin da jikinta yake yi, make me more crazy on her, she was the first under 18 virgin i mate, i don't think...
Saif ya katse shi ta hanyar cewa "Anya kana hayyacinka kuwa? Ko ka sha wani abun ne bai sake ka ba, ka ke yi mana surutun banza, ka yi raping ɗin under 18 old girl, kana vewa warin jikinta make you more crazy are you well?"
Abdul ya gyara zamansa ya ce "Saif da gaske nake, i rape her, dad is even working on it, mamanta wai har sun shiga media sun kai ƙara. I don't care what so ever, i still need her, at any cost".
"Abdul, ka ce dad ɗinka yana ƙoƙarin a rufe case ɗin, amma kana wannan zancen, ka san idan magana ta shiga media sai a hankali, da kai da dad ɗin abokan hamayya za su saka ku gaba".
"Abu nawa na yi babu wanda ya fashe? I don't care, you will help me in nemo yarinyar nan, na ji dad ya ce naja ta shiga case ɗin, kuma ba wata ba ce ba, she's just maid da gani ka san yar talakawa ce"
Cikin tsoro, Saif ya waro ido ya ce "Wannan barrister? Aikuwa ka kaɗe Abdul, an ya zaka sha wannan karon?"
Abdul ya kwashe da dariya, har sai da ya janyo hankalin wasu kansu ya ce "You don't get sense, malam zaka taimake ni na sake nemo yarinyar nan, itakaɗai ce maganin ƙishirwata" yayi maganar yana cigaba da ƙyaƙyata dariya.
***
Abun da Nasir ya gaya wa Nabila, ya ƙara azalzalar ta, akan son samun Viper, ta tabbatar da kama Viper zai iya zama silar cigabansa da ɗaukakar da take nema.
Sai dai ta kawar da tunanin daga zuciyarta, a lokacin da ta nutsa, tana kallon hotunan Barrister Naja'atu a social media. Ayyukanta na jin ƙai, da makamantansu.
Babu wani information da zai gaya mata haƙiƙanin wacece Naja'atu Bunkure, amma ta barwa zuciyarta lallai akwai wani abu a ƙasa a kan ta, kuma zata tono shi.
Ranar talata da safe tana shirin fita aiki, sumayya ta kirata ta ce su haɗu, a in da suke saba haɗuwa, su tafi tare.
Tun da Nabila ta ji haka, ta san akwai wani abu a ƙasa, dan haka ta amsa mata da to.
***
Walid ne yake ta yi wa Al'amin lissafi, da bayanin ayyukan da ya saka ayi masa, amma sam hankalinsa baya kan abun da walid ɗin yake faɗa.
"Viper" walid ya kira shi.
Maimakon ya amsa sai ya ce "Haryanzu babu wani labari a kan masu zuwa gidan malam lawan?"
Walid ya numfasa ya ce "Babu"
Ya ce "Yaran nan gaba ɗaya aka sake su, tare da yaran madaki ko?"
"Eh, ɗazu duk suka fita, an sake su duka".
Yayi ajiyar zuciya ya ce "Zuciyata tana bani, kamar so ake a ɗauke hankalina daga abun da na ƙuduri aniyar yi, ni kuma wallahi muddin ina numfashi a doron duniya, sai dai ayi mutuwar kasko"
"Amma tayaya haka zai yiwu, alhalin ka kasa sakin jikinka ka ɗauki ƙaddara, ba ka cin abinci, baka walwala, daga kwanciya, sai shaye-shaye, sai bayar da umarni, yakamata ka sakawa zuciyarka salama"
"Walid!" Ya ambaci sunansa da ƙarfi.
Ya amsa masa da "Viper"
"Tashi ka fita"
Cikin mamaki ya kalli Viper ya ce "In fita kuma? Ni ɗin walid ne fa?"
"Eh ka tashi ka fita ka bani wuri"
"Saboda ina bibiyarka, ina yi maka biyayya ka ke neman ka wulaƙanta ni? Ban da darajar ni ɗan halak ne da ba na manta alkhairi, kai ka san da tuni na daɗe da barinka"
Aminu ya ce "Idan kai ɗan halak ne, a wannan karon ina son ka bar ni"
Ya sake kallon viper ya ce "Ni ka ke kora?"
"Eh bana buƙatar sake ganinka"
Walid ya jinjina kai ya ce "Ok, na fahimta" ya tashi tsam, bai sake cewa komai ba ya fita.
Aminu ya nemi wuri ya kifa kansa, ya dafe saitin ƙirjinsa.
"Ni zaku mayar tamkar ƙwallon ƙafa, ku din ga bugani a tsakanin ƙafafuwan ku? Kun yi kuskure" ya furta cikin sanyin jiki.
***
Tun da suka haɗu, sumayya na tsuma ta fara bawa Nabila labari.
"Arfa kin san menene?"
"Faɗi kar ta kashe ki"
"Wannan satin, Honorable Ma'aruf indabo, zai yi program a gidan rediyon mu, kuma ni manager ya ce zan yi hirar da shi"
Nabila ta yi murmushi ta ce "Wow congrats baby"
Sumayya ta ce "Nabila, ba abun congratulations bane, indabo fa, wanda kwanaki aka ci mini mutunci a kansa, da na je mazaɓarsa ban tarar da ayyukan da aka ce yayi ba, shi ki ka gani a reception fa, da baki gaishe shi ɗin nan ba".
Nabila ta ɗan waro ido ta ce "Aikuwa sai ki rama, ki zaƙulo masa tambayoyi na tsitsiyewa, tambayar yaya uwarka ta haifeka, ke har waccan maganar ma ki ɗaukko, ki tutsuye ɗan bantan uba, ƴan siyasar nan wasu babu Allah a ran su"
Ta ce "I wish ina da wannan damar, sai dai program ɗin ba live bane ba, kuma wai rubuto mini tambayoyin da zan yi masa za ayi mini, kamar dai karantawa zan din ga yi yana bani amsa"
"Ban gane ba, interview zaku yi, ko kuma tattaunawa a kan cigaban da ya kaiwa mazaɓarsa?".
Sumayya ta ce "Bari kawai nabila, dama murtala ne yake program ɗin, kuma baya nan aka ce na yi, ina ta murna amma gwiwata tayi sanyi, kuɗi ya biya sosai za ayi program ɗin, amma a ɓoye campaign kawai zai yi, kin san zaɓe ya fara ƙaratowa"
Nabila ta ce "Taɓ abun tsiya, toshi da ƙosan rogo, wannan kawai tambaya da amsa zaku yi, haka yaya Nasir yazo yana gaya mini wai ƴan daban da ya kama, an kira shi daga sama wai ya sake su, abun babu daɗin ji, naga alamar sai mun zama jan wuya mun zage a kan ayyukanmu, yanzu dai ki ƙarasa, zamu yi waya zan shiga wata unguwa, muna da client zan duba wata shaida ne"
Sumayya ta ce "To shikenan, mu yi waya ko kuma ni sai in zo gida"
"Ok bye" ta tsayar da mai adaidaita sahun ya tsaya ta sauka.
Wata adaidaita sahun ta tsayar ta hau, ta tafi unguwar ƙofar na'isa.
Shagon nan da ta taɓa tsayawa ta sai lemo, nan ta tafi.
Cikin mutuntawa, mai shagon ya karɓeta suka gaisa, da yake ya gane ta ya ce "Hajjaju kin dawo unguwar ta mu kenan?"
Ta ce "Eh malam, da wata alfarma na zo nema ne"
Ya tattara hankalinsa a kanta ya ce "Ok, ina jin ki"
Ta ce "Last da na zo, wannan mutumin da na tarar a nan, na ce masa ya taimaka mini ina son na haɗu da aminu Viper, amma ya kwatanta mini wani wuri, wai lungun iraƙi, suka kusa kasheni"
Mai shagon ya zare ido ya ce "Viper kuma? Ke menene haɗinki da shi?"
"Ɗan uwana ne, tun da ya fito daga prison, ban sake ganinsa ba"
Ya ƙare mata kallo sannan ya ce "Allah ya rufa miki asiri da ba su kashe ki ba, kin san yadda suke nemansa ruwa a jallo kuwa? Idan suka riga jami'an tsaro kama shi, kashe shi za su yi.
Kuma a iya sanina, babu wata mace da Viper yake da alaƙa da ita, dan haka ki rufawa kanki asiri, ko sunansa kar ki fiye ambata a cikin unguwar nan"
Nabila ta waiwaya bayanta, babu kowa a wurin, ta ɗebo kuɗi ta ajiye masa ta ce "Waye shi, ko a taƙaice ne ka gaya mini wanene shi, a ina zan same shi"
"Ki ka ce ɗan uwanki ne?"
"Ka manta kawai, ni dai ka taimaka mini"
Yayi ajiyar zuciya sannan ya ce "Hajiya, na tabatta kina da alaƙa da hukuma, gaskiya ina jin tsoro, ina da iyaye da ƙanne, da nake taimakawa, ko basu saka an kashe ni ba, sai an yi mini illa, muddin na gaya miki wani abu, daga baya su gano ni na faɗa"
Nabila ta ce "Manta da batun hukuma, ba ni da alaƙa da ita, kuma babu yadda za ayi na bar wata ƙofa da zata nuna ka gaya mini wani abu, taimakona zaka yi, idan kuɗin sun yi kaɗan zan ƙara maka wallahi".
Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Aminu sun taɓa zama a unguwar nan, bayan ya zama ɗan daba na iraƙi ake ce masa ko kuma mai dogon zamani, ƴan sanda ne suka saka masa Viper, saboda rashin tsoronsa, da azabar kwarjinin da yake da shi, gagararre ne sosai, kuma dealer ne na miyagun ƙwayoyi. Kuma matasan yaran nan marasa ji, suna jin maganarsa fiye da ta iyayensu, ba zan iya gaya miki sama da haka ba, amma zan kwatanta miki, in da zaki samu wani yaronsa, amma dan girman Allah, kar ki bari sunana ya fito, ki taimaka"
Nabila ta ce "Na yi maka alƙawarin babu wanda zai ji".
Ya ce "Idan magariba ta yi, ki je tal'udu, hannunki na hagu, akwai wanda yake zuwa a kan babur ya zauna yana sayar da katin waya, ya saka facemask.
Ba katin yake sayarwa ba, balance yake karɓa na yaran da suke rarrabawa tabar wiwi, ƙananan dealolin su, da suke yi sayar musu da katan maye, yaron Viper ne makusantansa ne sosai, amma dan Allah ki riƙe alƙawari".
Nabila tayi ajiyar zuciya ta ce "Zan riƙe in sha Allah, na gode sosai". Ta sake ƙara masa kuɗi.
Fita daga shagon, tana jin kamar ta riski fiye da rabin matsalarta, idan Allah ya sa ta yi wa DSP hanyar kama aminu, atleast ta taimaka masa.
Babu tsoro ko tunanin komai, ta ƙallafawa ranta ko ta halin ƙaƙa za ta yi nasara.
Honorable Ma'aruf indabo, yana kashingiɗe a katafaren falon sa, hannunsa riƙe da waya ya kara ta a kunnensa, yana jiran a ɗaga.
Muryar madaki ce ya amsa da "Sai mai gida"
Indabo ya numfasa ya ce "An sakar maka yaran?"
"An sake su mai gida"
"Yayi kyau, ka fara ƙoƙarin yi mini aikina, zan shiga Abuja wannan satin, ka tabattar aikin nan ya kammala kan na dawo"
"Baka da matsala oga"
"Yauwwa, ya batun Aminu?"
Madaki ya ce "Wallahi duk wata kafa da za a bi wurin samunsu, ya tsosheta, jiya wani ɗan sanda yake tambayata wai idan na san in da yake"
Da sauri indabo ya tashi zaune ya ce "Waye shi? Meyasa yake tambayarka?"
"Wallahi ban sani ba, amma dai shi ne ya kama mini yara, Nasir mai tama na gani a jikin kakinsa"
Indabo ya jinjina kai ya ce "Shikenan zan bincika"
Wata mata ce ta buɗe ƙofar ɗakin, ta shigo, hannunta riƙe da ƙaramin plate ɗauke da tuffa, ta ƙaraso kusa da shi ta zauna.
"Ya dai na ganka kamar a tsorace?"
Indabo ya ce "Madaki ne ya ce mini wai wani ɗan sanda yana tambayarsa Aminu jiya, dole na saka a bincika waye".
Cikin takaici ta kalleshi ta ce "Au da kanka ka ke waya da ɗan daba, abun da ya faru tsakaninka da Aminu bai zame maka izina da darasi ba, kana ganin yadda ya zame mana barazana, ɗan tahaliki ɗaya ya hanaka sukuni".
Ya ce "Na san abun da nake yi bilikisu, komai a lissafe nake yin sa, ai na yi kuskure na farko, ba zan yi na biyu ba. Aminu kuma ina da tabbacin akwai wani abu a ƙasa, kuma zan kawar da shi, kafin ya buɗe bakinsa".
Ta ajiye trayn hannunta ta ce "Yanzu ya ake ciki da maganar Abdul, haryanzu Naja'atu ba ta ce komai ba?"
"Nima ita nake saurare, na fiki damuwa ma da wannan lamarin, amma dole ki ja masa kunne, na fara gajiya da rashin mutuncin sa, ba zai ɓata mini siyasata a banza ba, ina ta fafatuka a kai, ya je ya yi abun da ƴan adawa zasu samu abun faɗa a kai ba".
Ɓata fuska ta yi ta ce "Kai ma ɗanka ne ai, ka ɗauki matakin da ya dace da shi" ta ƙarasa maganar ta tashi ta bar masa ɗakin.
Yayi guntun tsaki, ya ɗauki wayarsa yana kiran wata lamba.
"Honorable, Allah ya taimake ka"
"P.A ya turo muku list ɗin tambayoyin da zaku yi mini ko?"
"Eh ya turo, mun kuma bawa mai gabatarwar da ka buƙata ta dudduba"
Ya jinjina kai ya ce "Ina fatan yarinyar da na ce maka ce?"
"Eh ita ce Yallaɓai"
Ya ce "Yayi khau, ku turota gidana, ta zo ta yi recording ɗin a nan, ba zan samu zuwa nan ayi program ɗin ba"
Cikin damuwa manager ya ce "Ina fatan ba wani laifin ta sake yi ba ranka ya daɗe?"
Indabo ya ce "Da zan hukuntata, tun laifin da ta yi mini na farko, da tuni na hukunta ta, wani abu mai muhimmancin gaske na gani a tare da ita, da nake son tabattarwa"
"Subhanallah, dan Allah yallaɓai ka yi haƙuri, idan laifi ta yi, ina nema mata afuwa ".
"Jamilu, ka turo yarinyar nan gidana, tayi recoding ɗin program, kar ka sake yi mini musu". Ya kashe wayar ya ajiye.
Yanayin yadda zuciyarta ke tsananta bugawa ne, ya sanya ta din ga karanto duk addu'ar da ta zo bakinta.
Sai dai ba ta ji za ta iya janye aikata abun da tayi niyya ba.
Nesa kaɗan da in ya kwatanta mata ta je ta tsaya, sai dai tun kafin duhun magariba ya gama rufawa, mutumin da aka kwatanta mata ya zo ya kafa teburinsa na sayar da katin waya, ya nemi wuri ya zauna.
Ta ɗan jima a tsaye, tana kallon sa, sannu a hankali ta fara tunkarar in da yake zaunen, tana addu'a a zuciyarta har ta ƙarasa in da yake.
Kafin ta yi magana, wani matashi ya rigata ƙarasawa, suka gaisa ya miƙa kuɗi, aka bashi wata baƙar leda.
Ta tattaro jarumtarta ta yi sallama ta ce "Sannu malam" ya ɗaga kai ya kalleta, sai dai kamar ya razana da ganinta.
Ta sake cewa "Sannu malam"
"Yauwwa" ya amsa da kakkausar muryar sa, yana cigaba da ƙare mata kallo.
"Dan Allah kaya nake so" ya ƙare mata kallo daga sama har ƙasa, ya ce "Wane irin kaya?"
"Irin wanda ka ke sayarwa, amma ni direct nake son na din ga karɓa"
"Jami'ar tsaro ce ke?" Yayi maganar yana cigaba da kallonta
Nabila ta ce "Jami'an tsaron ai sun san da zamanka a nan, ina so ka haɗa ni da Aminu viper ne"
Waro ido yayi ya kalleta ya ce "Ke! Yayi maganar yana zazzaro mata ido"
Tayi ƙasa da murya ta ce "Kar ka ɗaga murya, ka taimaka mini, ɗan uwana ne, tun da ya fito daga prison ban sake ganinsa ba"
"Ƙarya ki ke yi wallahi! Ban da ke mace ce, da namiji ce ke, wallahi sai na ciro hanjinki waje na zubar a titi, bar wurin nan, kafin na karya ki"
Nabila ta marairaice ta ce "Ba