Showing 30001 words to 33000 words out of 152254 words

Chapter 11 - ?arfe A Wuta Book 1 Hausa Novel Complete

15 Dec 2024

330

alfarma, reception ɗin ko ina security.

Sumayya ta risuna ta gaishe shi ya amsa, amma Nabila ko kallonsa ba ta yi ba, ta sunkuyar da kai, kamar alla-alla take yi, ta yi ta bar reception ɗin.

Ɗan rikicewa yayi, ya ƙura mata ido, amma ta basar ba ta gaishe shi ba, sai so yake yi ta ɗago su haɗa ido, dan ya tabattar da abun da yake tunani, amma taƙi ta mayar da kanta gefe.

Mamaki ya shiga yi, yana tunanin ko dai gizo idonsa yake yi masa? Sai dai ya rasa abun yi kafin ya yi wani yinƙuri, sun bar reception ɗin.

Ɗaya daga cikin ma'aikatan ya kalla ya ce "Wannan mai hijjabin ma'aikaciyar ku ce ita ma?"

Ya girgiza kai ya ce "A'a sir, she's just a guest here"

Ya ce "She looks familiar to me, anyway shikenan dai" yayi gaba.

Cike da takaici Sumayya ta ce "Kina kallon babban mutum ki ka basar ba ki gaishe shi ba, sai kallonki yake yi, ki ka sani ko shi ne mijin a dace a daidaita ko ƙyasawa yayi? Da irin wannan halin naki, ki ke korar samarinki na kirki wallahi".

"Kin fi kowa sanin bani da baƙin hali, wasu lokutan ma cewa ki ke yi na fiye zaƙewa"

"Haka ne, amma baki kyauta ba, ko dan kallon da yake yi miki, ai kya kula shi".

Nabila ta yi ajiyar zuciya ta ce "Ban taɓa jin na tsani wata halitta a kallon farko da na yi mata a rayuwata ba, sai wannan mutumin. Gaba ɗaya ya canza mini mood lokaci guda"

Sumayya ta waro ido ta ce "Meyasa kun taɓa haɗuwa ne? Me yayi miki?"

"No, ina ganin shi a poster dai, ba ɗan majalisa bane? Ban taɓa jin komai idan na ganshi a poster ba, sai yau da na ganshi ido da ido, bana fatan Allah ya sa na sake sanya shi a idona. Kin san me? ji nake kamar ya taɓa cutar da ni, cuta mai muni"

"Arfa, kina hayyacinki kuwa? Tayaya mutumin da ki ka fara gani yau kawai, ki ce kin tsane shi, ya cutar da ke how?"

"Ban san tayaya ba, amma haka nake ji a raina, kuma da gaske nake jin hakan"

"Ki daina irin wannan wasan, kar ki saka a din ga yi miki mummunar fassara"

"Forget, ba zaki gane ba" tayi maganar a daidai lokacin da suka ƙaraso titi.

Tun ba ayi sallar magariba ba, walid ya riga ya gama tatara gayyar matasa zauna gari banza, wanda suka yi bankwana da fatan samun ingantacciyar rayuwa, suka kama makamai da ta'amalli da miyagun ƙwayoyi.

Kasancewar ba a cikakken hankalinsu suke ba, haka suka raraka kowa da kowa gida.

Yaran madaki, na ta shirin shiga ɗaya unguwar sare-saren ɗaukar fansa. Labari ya iske su cewar, yaran Aminu sun rigasu yin dirar mikiya.

Ba su yi zaton gayya guda, yaran aminun suka ɗaukko ba, dan haka suka fita domin su far musu.

Kamar ba jikin ɗan Adam ba, haka suka din ga sara da sukar junansu, mutanen unguwa duk suka shiga gida suka rufe.

Aka yi rashin sa'a madaki baya nan, ɗaya daga cikin yaransa, ya kira shi ya sanar da shi halin da ake ciki.

Nasir yana zaune ya idar da sallar magariba yana lazumi, so yake ya tambayi ina arfa, ya ga ya jikinta, amma mama na babban falo, ya san da ya yi hakan, za ta yi masa faɗa, tare da sake gargaɗinsa a kan Nabila.

Wayarsa ce ta fara ringing, ya shafa addu'ar, ya ɗaga tare da yin sallama.

Da sauri ya tashi tsaye, yana faɗin gashi nan zuwa.

Da sauri ya ɗauki mukullin motarsa, ya fito daga sashin mama, zuwa falo.

Mama ta kalleshi ta ce "Ya dai? Ya na ganka a birkice?"

Dai-dai lokacin Nabila ta fito daga ɓangaren ɗakinsu, hannunta riƙe da kofi, hakan ya sanya ya kasa ba ta amsa.

Zuciyar sa ta tsananta bugawa da sauri, doguwar rigar material ce a jikinta, kanta babu ɗankwali, tayi parking ɗin gashinta.
Wani irin kyau ta ƙara yi masa.

"DSP yaushe ka dawo?" Tayi maganar tana kallonsa.

"Da magaribar nan, yanzu nake shirin nemanki, in ga ya jikin naki? Wayarki ba ta shiga"

Anty ta ce "Jiki yayi kyau, har fita tayi"

"Fita kuma, ki ka je ina? Kuma da iznin wa?"

"Dan ubanka ina yi maka magana ka shareni, maganarta ta fi tawa muhimmanci ne ko yaya?"

A ɗan rikice ya ce "A'a mama, yi haƙuri kiran gaggawa aka yi mini, faɗan daba ya ƙara ɓarkewa, ƴan daba sun rufe unguwar babu shiga babu fita, yaran Aminu Viper ne da wani madaki, wai ƴan sandan da aka tura, sun kasa kwantar da rigimar, kin san am incharge of his case, shi ne zan je na ga abun yi"

"To ka kula da kyau, ni wannan aikin ya isheni, shikenan kai ba hutu, ni hankali a tashe".

Ya jinjina kai ya nufi ƙofar fita.

Jin an ambaci Aminu, ya sanya jikin Nabila ya hau tsuma, ya bishi da gudu ta riƙo rigarsa ta ce "DSP, amma ba kai kaɗai zaka je ba ko?"

"Eh, na yi waya za a ƙaro mini ƴan sanda"

"Ko mu je tare?"

Ya zaro ido ya ce "Ki yi me?"

Sai kuma ta rasa me za ta ce "Kawai dai ko zan iya taimakawa"

Murmushi ya yi ya ce "Ba fa kotu ba ce madam"

"Zaki sake shi ya tafi ko kuwa? Wane irin iskanci ne haka, Meye haka ne Nasir?"

Nabila ta saki rigarsa ta ɗan ɗaga murya ta ce "Take care, ka tsaya daga nesa nesa dan Allah, kar wani abu ya same ka, kar mu yi asarar ɗan ƙasa na gari"

Dariya ya yi, ya fita da sauri.

Mama ta hayyayaƙo mata "Wallahi ki kiyayeni da rashin tarbiyyar ki a kan ɗa na, na gaya miki" mama ta yi maganar tana nuna Nabila da yatsa.

Nabila a ranta ta ce 'Ni yanzu ba ke ce a gabana ba, akwai abubuwan da suka fiki muhimmanci a wurina"

Tayi gaba tana kiran lambar sumayya, ta sanar mata da halin da ake ciki, na rikicin faɗan daba.

Sai dai kamar kullum, faɗa suka yi, sumayya ta gargaɗeta a kan ta fita sabgar harkar faɗan daban nan.

Nabila tayi zuciya ta kashe wayarta, tare da jin da ita ƴar jarida ce, sai ta shiga unguwar nan, ta samo rahoto, tana matuƙar jin haushin yadda sumayya take ɗari-ɗari da gudanar da aikinta, sai dai ko ba dan sumayya ba,  ya zama dole ta taimakawa Nasir, kuma ta taimaki tata career, dan idan ba ta rama abun da Najar bunkure tayi mata ba, ba zata huce ba dan haka za ta cigaba da bibiya.

Ayshercool
08081012143
[7/23, 1:37 PM] null:                    
                *ƘARFE A WUTA*


AISHA ADAM (AYSHERCOOL)


Follow this link, to join autar manya channel, domin samun litattafanta na baya da na yanzu.

https://whatsapp.com/channel/0029VakTcGc5Ejy40GSTWA0h



Masu neman book ɗin ƘARFE A WUTA daga farko, su bi wannan link ɗin, su yi following channel ɗin, za su samu previous pages👇👇👇.

https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g



9

Har ƙarfe goma na dare, Nabila tana kiran wayar Nasir, domin jin ko yana lafiya, amma shiru wayarsa ba ta shiga, abu kamar wasa hankalinta ya fara tashi, zuciyarta ta din ga raya mata wani abun ya same shi.

Da sauri ta tashi ta fita farfajiyar gidan, tana cigaba da kiran wayarsa.

"Ke Arfa, me ki ke yi a wurin nan da daddare haka?" Ta ji muryar Abba babu tsammani.

Cikin damuwa ta ce "Abba Yaya bai dawo ba, kiransa aka yi kwantar da tarzomar faɗan daba, kuma haryanzu bai dawo ba".

Abba ya ce "Yana nan lafiya in sha Allah, da ki ka dawo nan kina sintiri,ai ba bin sa zaki yi ki nemo shi ba, harkar aiki ne yana nan lafiya in sha Allah"

Abba yana rufe bakinsa, sai ga ƙarar motar Nasir, yana ta horn ba ƙaƙƙaitawa, gaba ɗaya suka nufi gate a tare.

Suka tsaye har ya shigo yayi parking ɗin motar.

Ya fito yana kallon su da mamaki ya ce "Abba lafiya na ganku a nan tsaye?"

Major ya ce "Arfa ce ta fito tana jiran dawowarka, ya ya aka yi wayarka ba ta shiga gaba ɗaya?"

"Tana cikin mota ne abba, ina ga network ne amma a kunne take"

Cikin zaƙuwa ta ce "Yaya, komai lafiya dai ko?"

Ya ce "Alhamdilillah, an sha artabu dai, yaran sun ninka yawan da muke tunani, mun kama wasu, wasu sun gudu, amma mun kama su da yawa".

Mama ce ta fito ita ma, tare da su sauda, suna yi masa sannu da zuwa yana amsawa.

Arfa ta ce "Amma dai ba su yi maka rauni ba ko?" Yayi murmushi ya ce "Da sun yi mini rauni, ai da baki ganni a haka ba"

Nabila ta ce "To Alhamdilillah, bari na je na kwanta na yi bacci a nutse, tun da kana lafiya"

Ya ce "Ki bar wayarki a kunne, za mu yi magana"

Ta jinjina masa kai ta bar su a wurin ta tafi, mama kuwa kamar ta bi Nabila ta naɗa mata duka, ta kalli yadda Nasir yake wani sassanyan murmushi kamar shashasha, shi ma ji ta yi kamar ta kwaɗe shi da mari, duk ƙoƙarin da take yi a kansa na nesanta shi da Nabila, abu ya ci tura.

Ta daure ta ce "Shiga ciki ka ci abinci, ka je ka nemi wuri ka kwanta".

"No na tsaya na ci abinci a hanya ma, sai da safe, gajiye nake kwanciya zan yi"

Major ya ce "To Allah ya tashemu lafiya" suka watse.

A galabaice suka koma mafakarsu, domin kuwa sun sha artabu da jami'an tsaro, duk da an kama wasu, wasu kuma sun tsira da ƙyar. Sai dai sun yi wa su madaki mummunar ɓarna, dan ma Aminu ya yi musu kashedin babu ruwansu da cewa za su kashe madaki, saboda ya san hatsabibancinsa.

Yana zaune suka faɗo ɗakin, suna ta mayar da numfashi, jikin rigar ɗan mama face-face da jini.

Walid ya ce "Boss, an yi aika-aika amma kwaɓarmu ta so yin ruwa, dan an kama da yawa daga cikin yaran nan da muka gayyato, amma fa yaran madaki sun yi ɓarna, dan sun taɓa wanda ba su ji ba, ba su gani ba, duk da mun yi yinƙurin daƙile hakan".

Maimakon Al'amin ya yi magana, kawai ya tashi tsaye ya shaƙo wuyan walid, ya haɗa shi da bango, ya ware masa idanunsa ya ce "Ina ƙwayoyin da ka kwashe a nan wurin?"

Cikin takaici walid ya ce "In fita yi maka aiki, in dawo da ƙyar amma ka shaƙe ni?" Yayi maganar muryarsa na fita da ƙyar saboda shaƙar da ya yi masa.

"Suna ina na ce?"

"Na kwashe su na fita da su, dan ba zan bari ka kashe kanka ba, allurar da ka ke yi wa kanka ma, ba abun da take yi maka sai ƙara maka zafin zuciya"

Fusata yayi da maganar Walid, ya ƙara shaƙe shi, Ɗan mama ya tashi da sauri yana yi wa Al'amin magiyar ya rabu da Walid.

Walid ya ce "Idan ka kashe ni ma, ba zaka huce ba, ai na yi maka alƙawarin kawo maka sabuwar ƙwaya, amma wannan kashe kanka zaka yi, idan ka cigaba da sha, dan ba ta karɓe ka ba." A fusace ya hankaɗe Walid ƙasa, ya koma ya zauna ya dafe goshinsa.

Wayarsa ce ta yi haske, ya ja wayar yana dubawa.

"Aminu ka daina wannan gangancin da ka ke yi, idan ka sake shiga hannun mutanen nan, kar ka yi zaton za su hukuntaka da adalci, dai-dai da abun da doka ta tanada, ka nutsu ka daina wannan mugun wasan, ka mayar da hankalinka a kan burinka" iya ƙarfin sa ya saka wurin yin jifa da wayar, ta dagargaje a tsakiyar ɗakin, ya tashi zai fita.

Duk da mugun ciwon da jikin walid yake yi masa, saboda artabun da suka yi, amma haka ya tashi ya sha gaban Al'amin ya ce "Ina zaka je ne?"

Hankaɗe Walid yake ƙoƙarin yi, amma walid ya sanya ƙarfin sa, ya tura shi baya.

"Ka rabu da ni walid, ya zan yi ne? So suke sai na haukace, waye wannan? Me yake nema da rayuwata? Wace manufarsa ce da su a kaina? Me kuma suke buƙata yanzu?"

"Easy master"

Cikin ƙaraji ya ce "Na ce kar ka sake kirana da wannan sunan"

"Sorry boss, na san komai ai, ka kwantar da hankalinka"

"How? Duk abun da suka yi mini bai ishe su ba, wai yaya zan yi ne? Kalli idona walid, ba na bacci fa, zuciyata kullum zafi take yi, ba na iya saka komai a bakina na ji ɗanɗanonsa,  ya zan yi ne?"

Walid ya ce na sani, ya amsa yana yi wa ɗan mama inkiya da idonsa.

Viper ya a sake cewa "Ka san kwana nawa na shafe ba na bacci? Ba kwanaki ban ba fa kawai, shekaru ne, ba na baccin da ya kai awanni biyar, ka san me nake ji kuwa?"

Walid ya ce "Ban sani ba, amma na san da yawa daga abubuwan da ka lissafa"

Jikinsa na tsuma ya ce "Wallahi zuciyata ci take yi da wuta, ka sani, wallahi idan na riƙe makami sai na yi kisan kai" yayi maganar yana rintse idanunsa, a lokacin da ruwan allurar da walid yake yi masa, ya fara ratsa jijiyoyin jikinsa.

A nan take jikinsa ya saki, ya zubawa walid ido.

Walid ya ce "Ko ba zaka yi baccin ba, ka rufe idanunka master, za ka samu releif" shiru yayi, domin ba zai iya motsa kowacce gaɓa daga jikinsa ba.

Ɗan mama ya ce "Walid, anya ba zamu yi wani abu a kan lamarin nan ba kuwa? Ba za a kai shi ya ga likita ba? Kar ya haukace tuburan fa"

Walid ya ɗora yatsansa a kan laɓɓansa alamar ɗan mama ya yi shiru.

A hankali al'amin yake buɗe idonsa yana lumshewa, sai dai ya kasa ƙwaƙwƙwaran motsi.

***
YALOKO ƘARAMAR HUKUMAR TOFA.

Cikin tsananin ƙyanƙyami take ƙarewa ɗan ƙaramin ginin ƙasar kallo, rabin katangar gidan  ta zube, sai ciko aka yi da kara da buhu, aka rurrufeta.

Abunka da mutumin ƙauye, cikin mutunci da girmamawa, matar gidan ta karɓeta, tana yi mata sannu da zuwa.

Ta yi mata iso, har cikin ɗakinta, ta ba ta abun zama.
Kamar ta zauna a kan kashi, haka ta ɗan ɗosana ta zauna, tana kame jikinta ta kalli matar ta ce "Baki gane ni ba ko?"

Matar ta ce "Eh ban waye ki ba"

"Ni ce barrister da na karɓi case ɗin ƴar ki, na zo mu tattauna ne, in yi magana da ita"

Nan da nan hawaye ya cika idon matar ta ce "Tana banɗaki, bari ta fito"

rufe bakinta ke da wuya, yarinyar tayi sallama a ɗakinta, muryarta ƙasa-ƙasa.

Mahaifiyarta ta amsa, barrister kuwa zuba mata ido ta yi, yadda yarinyar take ɗingishi, take tafiya da ƙyar, har ta zo ta zauna.

Ta kalli uwar ta ce "Kun kaita Asibiti ne?"

Ta ce "A'a, tun dai a  can an kaita, maigadin gidan ne ya kaita, har aka yi mata ɗinki a goshinta, gashi nan in da aka ya ji mata rauni. Dan Allah baiwar Allah ki taimake mu, kamar yadda Allah ya taimake ki, a karɓar wa yarinyar nan hakkinta. Saura ƴan kwanaki aurenta, ya lalata mata rayuwa, idan zancen nan ya fasu a garin nan yaya zan yi?"

Ta kalli yarinyar sannan ta kalli uwar ta ce "Baiwar Allah kuma hadda halinku, na son abun duniya duk yadda hukumomi ke jan kunne a kan kai yara aikatau meyasa ba kwa ji? Meyasa zaki kaita aikatau, maimakon makaranta?, a ƙa'ida fa kema sai an hukunta ki"

Cikin rauni da damuwa ta ce "Baiwar Allah da ina da yadda zan yi yaushe zan kaita aikatau? An yi garkuwa da mahaifinta an ce mu kai kuɗin fansa, mun tattara dabbobi da gonaki mun sayar, mun bayar a kai a sako shi, sun rike ƙanin mahaifinta da ya kai kuɗin, sun haɗa su su duka sun kashe, gona ɗaya ta rage mana, ita ma wani mutum duk ya tarkata ya ƙwace, wai zai gina kamfani, an ce za a bamu diyya, gonar miliyan uku an bani dubu bakwai, abun da zan girka na basu su ci, ita da ƴan uwanta, bani da shi, nima ba cikakkiyar lafiya ce da ni ba, kuma ita ce babba, makaranta tana zuwa ajinta uku a sakandare, kuɗin da ake biya na makarantar ba ni da su, ya zan yi?" Tayi maganar kuka yana ƙwace mata.

"Shikenan ya isa haka?, Amma kuma irin haka kin yi gaggawa zuwa gidan radiyo ki faɗa, ai wurin jami'an tsaro yakamata ki je".

Maman ramma ta ce "Na je, dan da aka kira ni na je can birnin asibiti, da ƙyar aka karɓe ta wai ba ɗan sanda, daga can na je wurin ƴan sanda naga suna nema su cuce ni, wai ƙarya muke yi, babu yadda za ayi a ɗauki ƴa ta aiki a wannan gidan har ayi mata fyaɗe. Ba ki ga sintirin da na yi ba, na rasa abun yi shiyasa na kai wurin masu radiyo ko Allah zai saka a taimake mu"

Ta jinjina kai ta kalli yarinyar ta ce "Ramma  ko?" Ta jinjina kai alamar eh.

"Gaya mini yaya aka yi abun ya faru?" Ta ɗaga kai ta kalli mahaifiyarta, sai ta fashe da kuka ta kasa magana.

"Hajiya ɗan bamu wuri mu yi magana" babu musu, ta tashi ta fita ta bar ɗakin.

"Kin ga ki yi shiru ki kwantar da hankalinki, ki yi mini bayanin yadda abun ya faru, in ga ta ina zamu ɓullowa lamarin"

Shiru ta yi tana tuna yadda lamarin ya kasance.

"Ke!" Ya kirata cikin tsawa, bayan sun haɗa ido da ya shigo, ƙara razana ta yi, dan ba ta yi zaton wani zai shigo yanzu ba, a dai-dai wannan lokacin, da ta duƙufa tana ta aiki a falon gidan.

cikin tsuma ta kalleshi ta ce "Na'am".

"Ina masu gidan?" Yayi maganar yana ƙare mata kallo, matashiyar yarinya ce, da ba ta wuce shekara goma sha huɗu ba, irin farkon tashen balagar nan, ƙirjinta ya fara tasawa, wannan ne karo na biyu da yake ganinta a gidan. Tun a ranar farko yake jin wani abu na fuzgar shi a kanta.

Cikin rawar murya  ta ce "Ai ba su dawo ba tukuna, gyaran gidan dai muke yi".

"Ke kaɗaice a gidan kenan?"

Cikin rashin wayo ta ce "Eh, amma zulai ta je sayo katin waya, zata dawo, tare muke aiki da ita, wai a satin nan za su dawo".

Yayi wata irin ajiyar zuciya ya ce "Ɗaukko mini ruwa a kitchen zan sha" ta jinjina kai, ta ajiye duster hannunta, ta tafi da sauri har da gudu.

Sai dai tana shiga kitchen ɗin, ya bi bayanta, ya mayar da ƙofa ya rufe.

Turus ta tsaya tana kallonsa, jikinta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login