Showing 75001 words to 78000 words out of 152254 words
shago, gidanka na chiranci, na gado zan je, za ayi masa wasu ƴan gyare-gyare, ba ni da kuɗi sosai a hannuna, za a yi masa abun da ya sauwwaƙa, kai ka ƙarasa gyarawa daga baya".
Ya yi shiru yana wasa da zobensa, kamar yadda ya zame masa ɗabi'a, idan ba ya son yin magana.
Abbu ya cigaba da cewa "Kuɗin aure na kai maka, next week za a ɗaura maka aure"
Lanƙwashe ƙafarsa ɗaya yayi, ya koma wasa da yastun ƙafarsa, yana kallon wani wurin daban.
Rahila ta ce "Taɓɗijan, lallai gagare".
Abbu ya ce "Al'amin da kai nake fa"
Ya ɗago idonsa ya kalli Abbu ya ce "Wai ni ko wa?"
"A'a da ubanka nake ba kai ba, ni da waye a wurin nan?"
Al'amin ya ce "Ni fa yau ban sha komai ba, garau nake balle ace a buge nake ban ji dai-dai ba, wannan kawai zance ne, ni da ake cewa gagarrare haihuwar asara, wa zai bani wani aure? Ni bana buƙata, idan kuma ba haka ba, duk abun da ya biyo baya ba ruwana idan na kashe yarinya, ko na yi mata illa, kar a zo ana yi mini ƙanan maganganu, ba na so bana buƙata".
Ya yinƙura zai fice, Abbu ya riƙe shi ya ce "Umarni nake baka, ba shawararka ko ra'ayinka nake nema ba, dole ne wannan, aurenka wani satin, na kai kuɗin aure da komai, dole ka nutsu ka shiga hankalinka, idan ka illata musu ƴa ko kasheta kuma, zan sallamawa duniya kai, wannan shi ne hukuncin da na yanke"
A fusace ya ce "Meyasa zaka yanke wa rayuwata hukunci, ba tare da amincewata ba bayan ka daɗe da sallamawa duniya rayuwar tawa? Ka yi hakan ne saboda farincikin matarka ko? Ta daina ganina na gusa na bar mata gidan nan ita da iyalinta. Da zan iya wallahi garin zan bar muku na ɓacewa ganinku ku samu cikakken kwanciyar hankali kamar yadda ku ke buƙata, amma ba zan iya ba.
Ka sani ina ta'amalli da miyagun ƙwayoyi, da gaske zan iya kashe ƴar mutane, ko na illata ta, sai dai ba na fatan na fi haka lalacewa, idan ka yi mini baki, zan ƙara lalacewa ne zan bi umarninka, amma duk abun da na yi mata da ni da kai zamu ɗauki nauyin zunubin. Saboda ni babu mata a tsarin rayuwata, miyagun halittu da babu Allah a ransu, bana fatan raɓar su, saboda yadda tasirin kaidinsu ya kassara rayuwata, kassarawar da ba za ta gyaru ba, mace ɗaya da nake wa kallon rayuwata, uwata kenan na rasata a yanzu babu wata mace mai sauran kima da mutunci a idona, nayi alƙawarin nesanta kaina da mata, nesantawa mai nisa ta har abada, amma ka karya mini alwashi, ta hanyar janyo mace rayuwata, ina sake nanata maka, duk abun da ya biyo baya, tare zamu ɗauki nauyin zunubin".
Ya saka hannu, ya cire hannun Abbu da ya riƙe masa riga, ya saka kai ya fice.
Har ya bar gidan, babu wanda ya sake magana, daga ita har Abbu.
Gaba ɗaya aka hana jauhar fita daga gida, ana ta shirin biki, ita kuma tana rama kamar ana tsotseta, duk ta fiƙe sai farar fata da idanuwa.
Maƙwabciyar su ta din ga cewa "Gaskiya mama ban so a aurar da jauhar yanzu ba, na so a bari maƙerin budurci ya gama ƙere mana ita, wannan kyawun da gidan wani hamshaƙin ya dace"
Anty ta ce "Wannan ma hamshaƙin ne".
A gida mama ta saka su surayya sa walida, suka dinga kwaɓe-kwaɓe suna murzawa jauhar da sunan gyaran jiki.
Malam jamilu ya shiga matsananciyar damuwa, da samun labarin auren jauhar, dan har ga Allah yana matuƙar sonta, tsoron kar ta daina ganin mutuncinsa, ya sanya ya ɓoye mata.
Gidan jauhar da aka je jere, yana da girma, sai dai tsakar gidan tsurar ƙasa ce, cikin ɗakuna babu floor, sai dai an yi plasta a ɗakunan, falo ɗaya da ɗakuna uku a ciki, kowanne da banɗaki, sai kitchen a tsakar gida da tsakar gida mai girma.
An yi wearing ɗin wutar lantarki, a gidan.
Sai buhunhuna, aka shimfiɗa a ƙasa, sannan cikin ɗakunan aka saka leda, falo kuma aka shimfiɗa carfet, saboda duk turɓaya ne.
Tagogin duk babu na kirki, sai kame-kame da faci.
Sai kujerunta, ƴan gida masu kyau, ɗaki ɗaya an saka furnitures, ɗaya kuma sai aka saka ƙatuwar katifa da wardrobe mai biyu, abun saka takalma. Duk da haka gidan ya yi kyau.
Amarya ta din ga fargaba da tunanin, waye mijin nan, da haryanzu za ace, bai taɓa ganinta ba, kuma ba ta taɓa ganinsa ba? Kuma ya amince da zai aureta.
Dogon gashinta baƙi, aka gyara mata shi, aka yi mata lalle ja da baƙi.
Haka kurum take tuna Alhaji mu'azzam, a haɗuwarsu biyu, yadda yake nuna yana sonta, ba ta son ya zai ji ba, idan aka ce masa an yi mata aure.
Kodayeke ita ba ta san dalilin fasawa da shi ba.
Su liti suka lura da shirun Al'amin ya ƙara yawa, duk da ba mai yawan magana ba ne dama, sai ya zauna yayi shiru yana zancen zuci.
Walid ya ce "Baaba, wai dan Allah kwanan nan meyake faruwa ne? Kamar ka na cikin damuwa" tabbas ba dan Walid ya tambaye shi yanzu ba, ba zai gaya masa ba.
Ya karkace ya ɗaukko invitation a aljihunsa, ya miƙa wa walid.
Wani irin ihu walid yayi, haɗi da kururwa, yayi katantanwa a ƙasa ya kuza uwar ashariya.
Sannan ya ce "Allah dai ya biya maza, dama zaka afkawa sabgar nan, ka yi mana shiru haka? Ba ka gaya mana ba, balle mu shirya saura kwana uku fa".
Sauran matasan da ke wurin suka miƙe suna tambayar Walid ko lafiya?.
Ya miƙa musu invitation ɗin, take suka hau shewa suma, suna dara.
Kawai ya dafe kansa, yayi shiru.
Walid ya ce "Wai tsaya, auren dole za ayi maka ne? Na ga baka murna, kuma shi ne ba ka taɓa kai mu ehhh, mun gaisa da antyn namu ba, iya wuya mun samu mai dafa mana abinci"
"Walid, Abbu ne ya shirya komai, ni ko ganinta ban taɓa yi ba, kuma ba na fatan na ganta, kuma ba kowa ne ya shirya wannan abun ba, sai wannan shaiɗaniyar matar ƴar haramun, ya ce umarni yake bani ba shawara ba, ni kuma na yanke guduwa zan yi, ba abun da zai haɗani rayuwa da wata mace, ba za a mayar da ni nusari ba, kalli yadda mace ta yi silar rushewar farincikin rayuwata gaba ɗaya"
Walid ya zauna kusa da shi ya ce "A'a maza, duk lalacewar naka naka ne, kai ka san albarkar dattijan ke riƙe da mu, ka daina kallon abun da yake yi maka na rashin jin daɗi, idan yayi maka baki ƙara watsewa zaka yi.
Duk da lokaci ya ƙure, dole ayi celebration, zamu gayyaci gayu a sha shayi a babbaka hayaƙi, abun farin ciki ya same mu" ya ƙarasa maganar suna shewa, ban da Al'amin da zuciyarsa kamar ta yi bindiga.
Hatta kayan da Al'amin zai saka na aure, sai da Abbu ya saya wa Al'amin, dan ko ganinsa bai sake yi ba, sai dai ya fita yawon neman sa.
Ƙarfe goma na dare, su Walid suka shirya party, aka dafa shayi aka raba lemuka, da kayan shaye-shaye.
Gogan yana gefe, yana zancen zuci, har ga Allah so yake ya gudu, amma ya san ya gudu alaƙarsa da Abbu za ta ƙara tsami. Kuma ya san ko ya gudu sai ya dawo, ba zai iya barin Abbun ba.
Tunani yake kowace mai tsautsayin da ba a so, ce haka, aka zaɓi a aura masa oho.
Ana tsaka da walimar hayaƙin, faɗan daba ya kaure, Al'amin kuma ya koma gefe ya ƙi magana, ƴan sanda suka yi wa wurin dirar mikiya, saboda rahoton da ƴan unguwar suka kai wa jami'an tsaro, ai kuwa suka kame su har da shi suka tafi da su ana gobe ɗaurin auren da bai san wacece matar ba.
Ayshercool
08081012143
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
Arewabooks ayshercool7724
Abbu kuwa hatta ɗinkin da Al'amin zai saka, ya yi masa, sai dai tun ranar da ya gaya masa, bai sake saka shi a idonsa ba.
Yana zaune yana ta mitar rashin ganinsa rahila ta ce "Ba fa zama zaka yi ba, tashi zaka yi ka je ka nemo shi duk in da yake, kar ya kunyataka a idon duniya.
Kana kallo yanzu na sauke mayafina daga gidansu amaryar, sun yi walima, duk sun gama shiri, na kai musu mukullin gida, har jere sun yi, fita zaka yi ka nemo shi ai"
Haka Abbu ya shuri takalama ya bazama, aka sanar da shi, su na can wata unguwar, suna walimar aurensa.
Ya bazama ya tafi, yana zuwa ya tarar da labarin ƴan sanda sun kama su duk sun tafi da su.
Hankalin Abbu ya tashi, ya tafi division ɗin nan unguwar aka masa a station ɗin ma artabu aka yi da su, an kwashe su an kai su anti daba, ya ce wallahi ba za shi anti daba a daren nan ba saboda shi.
Da ya koma gida kuwa, rahila kamar ta ari baki saboda mitar, meyasa bai je ba a sake shi, kar ya basu kunya, ya ce idan za ta iya, ta tafi.
Jauhar kuwa su mama suka sakata a ɗaki, suna yi mata nasiha, fuskokinsu ɗauke da fara'a da jin daɗi, da nanata mata ba zasu zaɓa mata abun da zai cutar da ita ba.
Ita dai ta damu sosai ta ga waye wannan mijin, da har suka ga ya dace da ita? Har a ranar idonta da kwanciyar jinin jifan da mama ta yi mata da takalmi.
Washegari ranar juma'a, za a ɗaura aure a babban masallacin juma'a, amma Al'amin yana tsare.
Sha ɗayan rana, sai ga P.A ɗin Honorable indabo a anti daba da kansa, ya je belin Al'amin, wanda ya yi hakan ne, saboda aikinsa da yake son ya ƙarasa masa.
Suka din ga sara masa, suka gaisa ya gaya musu wurin wanda ya zo, yake son ya yi beli, da wanda ya aiko shi"
"Gaskiya malam yaron nan ba zai ci bulus ba, state CID zamu kai shi"
P.Aya ce "Ayi haƙuri, in anjima za a ɗaura masa aure, ko dan albarkacin wannan a sake shi mana"
"Wai ka san me ya yi kuwa?"
"Eh, an ce sun yi shaye-shaye sun tayar da tarzoma ko?".
"Ai da wannan ne da sauƙi, ya saba zuwa wurin nan a kan haka, jiya ƴan sandanmu sun kamo su, saboda sun sha tana gaya musu gaibu, a tsakiyar harabar station ya ɗaga ɗan sanda ya buga da ƙasa, saboda yana ganin ya isa, ya na ji da ƙarfi. Kuma ya din ga yi wa mutane wani shegen kallo kamar kumurci, zai gane kurensa, CID zamu kai shi"
Ana haka shugaban kula da sashen ya shigo da shi da wani matashin ɗan sanda, suka ƙame suna sara masa, ya kalli P.A ya ce "Lafiya kuwa?".
Suka gaisa sannan ya ce "Honorable ne dai ya kuma aikoni ayi ban baki, a saki Mai dogon zamani "
"Ba su gaya maka laifin da yayi ba? Jami'inmu fa ya daka, ba ya ji yaron nan ko kaɗan"
"Sun gaya mini, amma kamar yadda aka saba, honorable ya bayar da saƙo"
Ya numfasa ya ce "A fito da shi da sauran yaran da ku ka kama" aka buɗe Al'amin, da yaransa, ya fito yana ɗan jirga ƙafarsa a hankali, saboda taron dangin da suka yi masa jiya, suka yi masa dukan tsiya, daga jami'in ya tankaɗa ƙeyarsa, ya waiwayo a fusace ya saka ƙafa ya kwashe shi a wurin.
Daga shugaban, har PA ɗin babu wanda ya kalla, ya kama hanyar ficewa daga cikin station ɗin.
Ya girgiza kai ya ce "VIPER kenan, Allah ya shirya".
PA ya ce "Viper kuma?"
"Eh sunansa kenan a gidan nan, sunan da suka saka masa kenan, ban san sau adadin da muka kama shi ba, ban taɓa ganin mutum mai bala'in taurin kansa ba, mu daka mu daka wallahi ko gezau ba ya yi, ga wani sheɗanin kallo da yake yi wa mutane, kai ka ce kumurci ne zai kai sara, shiyasa nake yi masa sha'awar hakar tsaro, yana da girma da kwarjini na gaske, amma shi ba a saka shi ba a hana shi".
P.A yayi murmushi ya ce "Ai tun da ka ga honorable ya riƙe masa wuta, ba ya wasa da lamarin sa, kai ka san ba ƙaramin mara ji ba ne".
"Eh ai ku ne ke goya musu baya"
"Ai sabgar tamu ce dole sai da su".
Kafin PA ya gama sallamar su ya fito, tuni su Viper sun ɓace.
Har gida walid ya je ya sanar da Abbu, an sako su, amma yayi yayi da shi, ya taho gida yayi shirin ɗaurin auren yaƙi.
Abbu ya bi walid, har in da Al'amin yake, ya mimmiƙe yana bacci, jikinsa duk shaidar dukan da ya sha a station.
Maganar duniya Abbu yayi, amma yayi burus ya ƙi tashi, sai da ya cire takalmi ya hau ƙwala masa, sannan ya tashi da ƙyar yana muzurai, Abbu ya tasa shi a gaba zuwa gida.
Ba ƙaramin kyau manyan kayan suka yi masa ba, yayi wani irin kyau na mussaman, kwarjinin da Allah ya yi masa ya fito sosai da sosai.
Bayan sallar juma'a aka ɗaura masa aure, bayan an saukko daga masallaci, babu wanda ya sake ganinsa.
Jauhar kuwa gabanta sai tsananta faɗuwa yake yi, ƴan ƙawayenta na makaranta, suna ta tsokanarta, suna yi mata raha, amma ta kasa sakewa.
Mama ta hau ta da zagi a gaban mutane, wai sai ta saka an ce aure dole za ayi mata, taƙi walwala ko wanka ba ta yi ta shirya ba.
Jiki babu ƙwari, jauhar ta yi wanka, aka yi mata kwalliya.
Tayi kyau sosai da sosai, dama dai-dai gwargwado tana da hasken fata da kyanta na fulani.
Baba ne ya fara dawowa gida, gaba ɗaya jikinsa a sanyaye, ana ta yi masa Allah ya sanya alkhairi.
Ya saka aka kira masa jauhar, zuwa ɗakinsa.
Cikin tsananin tashin hankali da damuwa, Saifu ya shigo gidan, yana ƙwalawa baba kira.
Mama ta ce "Saifu lafiyarka ka ke yi wa mahaifinka irin wannan kiran haka?"
Bai saurareta ba, ya shiga ɗakin baban, mama da anty suka bi bayansa, 'yan biki kuma suka yi cirko-cirko.
"Baba wane irin miji ka aurawa jauhar? Tun a masallaci nake nemanka ban ganka ba"
Baba yayi shiru, ya ƙi bashi amsa.
"Baba magana nake yi fa kayi mini shiru yanzu zaka yi alfahari da wannan zaɓin da ka yi mata?marainiyar Allah, ka rasa wa zaka aura mata sai tantirin ɗan daba? Laifin me tayi maka har haka, mutumin arziki ya fito yana sonta, amma ka hana shi ka bawa mutumin banza, yanzu wane mutumin kirkin ne zai so haɗa zuriya da mai dogon zamani"
A gigice jauhar ta ɗago idonta, gabanta ya shiga faɗuwa, tana jin yadda sunansa ya karaɗe arear unguwannin, duk da ba ta taɓa ganinsa ba, amma ya shahara da rigima da 'yan unguwar su, da shi da madaki tana jin sunayensu, ta san dai madaki, tun da cikin unguwar su yake.
Cikin zafin rai saifu ya sake cewa "Baba ka yi mini bayani, menene dalilinka na yin haka?"
"Saifu, kai ma ka fara shaye-shayen ne? Uban naka ka ke gaya wa haka? Shi ka ke tuhuma? Ba 'yar sa ba ce? Zai zaɓa mata abun da zai cutar da ita ne?"
Ya ce "Zai yi mana mama, ke da wannan matar menene ba zaku iya aikatawa ba, kuma na san ku kuka ƙulla komai, akwai Allah"
Jauhar kuwa kuka ta fara, amma ta kasa magana, jikinta ya din ga tsuma, Hafsa kuwa fita tayi, ta kira yaya tijjani, wai ga saifu can yana yi wa baba rashin kunya.
Aikuwa ya shigo cikin gidan da sauri, zuwa ɗakin baba, sai faɗi in faɗa yake da mama, baba kuma ya ƙi magana.
Yana zuwa ya ɗauke saifu da mari, sai dai yana sauke hannunsa shi ma ya rama, take dambe ya kaure, sai dai jin hayaniya a waje ne, ya sanya suka yi saroro.
Bushe-bushen 'yan tauri ne yake tashi daga ƙofar gidan, nan da nan warin wiwi ya din ga shigowa gidan, yaran Aminu sun cika layin, suka din ga busar 'yan tauri, suna yi wa Aminu kirari, sai dai babu shi a wurin.
Su maman ma waje suka yi, domin zuwa su ga abun da yake faruwa.
Nan 'yan biki suka dare, wasu kuma suka tafi kallo.
Baba ya riƙo hannun jauhar, da take ta uban kuka, kamar shi ma zai fashe da kuka ya ce "Fatima, na yi miki laifi, ban san yaya aka yi wasu abubuwan suka faru ba, dan Allah ki yafe mini, in sha Allah ba zaki wulaƙanta ba, zaki yi alfahari da hakan, na san na daɗe ina zaluntar rayuwarki, ina cutar da ke, dan Allah ki yafewa baba jauhar, kar ki yi fushi da ni, in sha Allah sai auren nan ya zame miki alkhairi"
Ta share hawayenta ta jinjina masa kai ta ce "In sha Allah Baba"
"Yauwwa yarinyar kirki, Allah ya yi miki albarka ya kare ki daga dukkanin sharri da abun ƙi, Allah ya kula mini da ke a duk in da ki ke.Na san dama ke mai haƙuri ce, zaki ci riba in sha Allah" ta jinjina masa kai tana ƙoƙarin haɗiye kukan da yake ƙoƙarin ciwota.
Ba a rabu da bukar ba an haifi habu, ta san wannan auren wani sabon ƙalubalen ne a rayuwarta.
Ƙawayenta tuni suka gudu gida, 'yan biki ma duk sun watse, ta samu wuri ta ƙule a ɗakinta, ta din ga kuka, tana neman agajin Ubangiji.
Kwatsam! Yaran madaki suma suka taho layin, da niyyar tarwatsa yaran Aminu, dan kuwa ba sa jituwar da za su bari su shigo musu layi, su yi musu wannan budurin.
Ba a jiyo komai, sai karafkiyar makamai, da zage-zage tamkar ana yaƙi.
Suna daga cikin gidan, suka jiyo ana cewa tun da aka aurar da ƴar gidan ga maƙiyinsu, idan ta bar unguwar ta bar ta kenan, idan suka kuma ganin ta, sai sun sassarata.
Mama ta ce "Zakiyya, kin ga wata tijara, ni fa hankalina ya tashi, ji kamar ana yaƙi".
"To ke ina ruwanki, da an kaita ba shikenan ba, can su je su ƙarata ba"
Suna cikin maganar, sai ga gwangwanin tiya gas, a tsakiyar cikin gidan ƴan sanda sun sake dira, su tarwatsa su.
Jauhar ta ƙara takurewa tana kuka, saboda tsananin tsoro da tashin hankali, dan a kunnenta ta ji ana cewa, idan aka ƙara ganinta a unguwar ma, sai an sassarata.
Unguwar ba ta yi dai-dai ba, sai bayan sallar la'asar, hatta