Showing 27001 words to 30000 words out of 135321 words

Chapter 10 - Matar Taj Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

504

tana kokarin kare kirjinta.

Gaba daya kitchen din zuba mata idanu sukayi, gata dai bata da kiba kuma itadai bazaace mata doguwa ba kuma baza a kirata da gajeruwa ba saidai  allah yayi mata sura mai fuzgar hankali, baga mace bama balle namiji, full option, she’s well curved and pictured kamar an zana surarta saboda yanayin kayan jikinta riga da wando na aiki Kenan.

Tsugunnawa tayi ta kwashe savage din da suka zube a kasa kafin ta miqa ma maid din dake tura trolly din, ….No wonder take ta fama kakkare kirjinta ashe a

cike suke kamar zasu yaga rigar jikin nata kuma daidai jikinta, a hakan ma bata ji hutu ta koshi bama tukunna,masha allah kamar yar Brazilian don sune masu irin perfect shape dinnan da ba kowa keda irinshi ba, one ina million Kenan.

 

Gyaran murya da akayi ne yasa duk suka koma kan ayyukansu, sabeeha dai na daga tsaye a gefe tana kallonsu suna abubuwan su cikin kwarewa.

 

 

**

Cikin isa ta soma sauko daga stair din cikin shigarta mai aji, babu abunda kake ji sai sautin takalminta da kamshinta, hanyar dining ta nufa hannunta rike da Jakarta.

 

Waigowa sukayi gaba dayansu suna kallonta daya bayan daya harta karaso dining din, itama binsu tayi da kallo, suna zaune har sun fara karyawa, afiya, fadwa da barad.

 

Wajen zamanta ta nufa kafin gaba daya suka soma gaisheta, amsa su tayi kafin maid din dake tsaye ta soma serving dinta as usual, daman ita bata cin abunci sosai daga coffee sai dan low calories English breakfast.

 Baka jin komai sai karar cokula a dining area din, fadwa ce ta fara gama breakfast din kafin afiya, basuyi gigin tashi ba saida hidaya ta gama tukunna kafin ta miqe tana mai duban afiya dake zaune ta hade rai.

Barad ne ya fara futa daga dining din yana mai kissing din aunties din nashi a kuma kafin yabar dining din.

 

 

‘’naga kinyi requesting for kudade masu yawa,na tura maki approval letter’, anything else’’  ta karashe tana mai dubansu su biyu

Da mamaki duk suka dago suna kallonta, don kwata kwata basuyi expecting haka daga wajenta ba.

Kallon juna fadwa da afiya sukayi kafin suyi murmurshi, godiya sukayi mata kafin ta fuce daga dining din, head of maids na biye da ita da Jakarta a hannu.

‘’Ma’am yarinyar da aka kawo wadda zata kula da part din sir…’’

Tsayawa chak hidaya tayi tana wani nazari kafin ta dubi head of maids din, ‘’I trsut her with you make sure ba a samu matsalar da aka samu ba da previous one’’,

 

‘’okay ma’am’’

Maid din ta bata amsa kafin ta rufe mata matar dake janta zuwa office, barad na daga gefenta don ita ke kaishi school da kanta.

 

Futar matar nan ce daga kitchen din ya baima yar Ghana daman jan sabeeha, gaisawa sukayi kafin yar Ghana ta soma tambayarta akan aikin da aka bata.

‘’a bangaren ina aka saka ki?, girki ko gyare gyare?’’

‘’bata fada min ba’’ sabeeha ta bata amsa cikin nutsuwa

 

Nunfasa yar Ghana tayi kafin tace ‘’hmm ina maki fatan dai a wannan bangare guda biyu zaki yi aiki don…’’

 Zuba mata idanu sosai sabeeha tayi don jin abunda take shirin fada, ganin haka yasa yar gana rage murya don suna da dan yawa a kitchen din ‘’kinga ayki a gidan nan yana da wasu qalubale daban daban,’’

 

Samun kanta tayi da cewa ‘’menene qalubalen?’’

Nunfasawa yar Ghana tayi kafin tace ‘’akwai wani part a sama wanda muke kira da demon palace, mudai da muke aiki anan kasa bamu taba zuwa saman ba kuma basusan menene a saman ba, saidai muna kallon duk wadda aka tura aiki chan saman bata wuce kwana daya biyu tabar aiki a gidan nan, a yanda naji ma wadda ta dade da ayki a bangaren bata wuce sati guda ba tabar gidan nan a burkice, shiyasa na tambaye ki don sanin inda zakiyi aiki’’

 

Wani tunani ne ya fado ma sabeeha nan take ta danji gabanta ya fadi, ‘’menene a saman to?’’

Yanda tambayar ma ta futo daga bakinta ita kanta batayi tsamanin haka ba.

‘’hmm babu wanda ya sani, saboda duk waenda sukayi aiki acahn din basa fadin komai game da part din, mudai musan nothing comes good daga part dinnan, wata qila wani mummunan abu ne a wajen’’

 

 

Bata kaiga idawa ba sukaji alamun matar ta dawo kitchen,lokacin wajen karfe tara na safe, kallon inda sabeeha take matar tayi kafin tace ‘’muje’’

Binta abaya sabeeha tayi har suka fuce daga kitchen din, girgiza kai kawai yar Ghana tayi tana mata fatan allah yasa dai ba saman za a kaita ba, don idan da anan kasa zatayi aiki da tuni head(head of maids) ta nuna mata ayyukanta, bangare su sabeeha kuwa zuba idanu ta dunga yi don ganin inda za a kaita don ba karamin tashin hankalinta yar Ghana tayi ba da batun part din saman nan da babu wanda yasan menene a saman, binta kawai take a baya har suka shiga cikin gidan tana sauraron bayanan da take mata.

‘’madam bazata samu ganinki ba, so ni zan maki bayanin ayyukanki’’

Girgiza mata kai sabeeha tayi kanta a kasa har suka soma hawa sama, ita tunda suka shigo ma ta burkice don baza ta iya cewa ga daga inda suke fito.

 

‘’aikinki ba kamar kowanne aiki bane, record dinki ya nuna kin kware ta bangare caregiving, so ina fatan baza a samu wata maatsala ba, sannan akwai rules din ayyukanki, abu na farko da zaki kiyaye dashi shine your job is confidential, you can not tell anyone irin aikin da zakiyi da condition din sir, idan kika kuskura kika fada kuma’’

Dan tsayawa matar tayi kafin ta juyo ta maida dubanta ga sabeeha,’’ba sai na fada maki mai zai buyo ba, just keep that in mind’’

 

Dam dam gaban sabeeha ya bada, idan har batayi kuskure ba wannan aikin da za a bata shine aikin da aka turo ta tayi liken asiri akai ko menene?, maganar mutumin nan ce ta fado mata arai ‘’idan kinje zaki san irin aikin da zakiyi’’

Tabbas wannan ne abunda yake nufi Kenan, hannunta har wata irin zufa ne ke tsatsafo mata, sai a lokacin ma ta lura da stairs suke hawa.

Haka suka dunga hawa stairs din mai tsayi kafin su iso saman, kallon wajen sabeeha tayi kirjinta na tsananta bugu kamar ana buga ganga, bin matar ta dunga yi kamar raqumi da akala har suka karaso petion din dake tsakanin part din guda biyu.

Nuni head tayi mata da bangaren hannunta na dama ‘’babu ruwanki na nan bangaren, sannan chan’’

Tayi mata nuni da dayan part din, ‘’anan ne zaki yi aikinki as a caregiver’’

 

Takowa suka soma yi har zuwa part din kafin head din ta dannan security pins, ‘’wannan ne pin din shiga ciki, daga ni sai wadda zata kula da wajen sai madam ne kawai muka san pin din, kin gane me nake nufi?’’

Girgiza kai kawai sabeeha tayi kafin su shige ciki, suna shiga maid ta rufo kofar, nan take haske ya bade ko’ina hanyar walkway zuwa cikin part din, gefen wajen kofar maid din ta dan latsa wani electric dispenser nan take sanitizer ya futo, hannunta tayi sanitizing kafin ta umarci sabeha datayi hakan itama.

Tana gamawa ta soma cire takalmin kafarta daga gefe akwai wani rack da aka jera crocs, daya head ta dauka kafin ta bama sabeeha dayan.

 

 

‘’rule number 2, you should be very clean sosai, sannan duk sanda kika shugo ki tabbatar kin saka mask and kinyi sanitising hannunki, uniform dinki should be clean as well,ko digon datti a kayanki is not allowed’’

 

Girgiza mata kai tayi alamun gamsuwa dukda a tsorace take sosai,ciki suka fara shiga, haske ne ya gauraye ko’ina bau nan take komai ya bayyana, parlor ne mai girma da kyau fari qal komai is organise babu wani karikice sai camera’s ta kowanne lungu da sako acikin parlorn.

Sabeeha dai bata ma tsaya duban parlorn da kayu ba don tunaninta yayi nisa da abunda matar nan ke fada ma da wanda yar Ghana ta fada mata ga kuma wanda aka turo ta akai.

 

Saida suka zo dan nesa da kofar dakunan cikin part din matar ta tsaya, ‘’karfe shida zaki fara aikinki, sannan daga inda karfe hudu tayi ki tabbatar kin gama komai kin sauka kasa, daya daga cikin ayyukan da zakiyi shine gyaran part din nan, akwai kitchen da duk wani abubuwan buqata,’’

‘’the most important part of your job shine,kula da movement din sir,da abuncinsa, sai medication dinsa,sannan akwai timetable din abunda yafi buqata on a daily basis zaki samu wannan a kitchen, and lastly I will advice you duk abunda zakiyi kiyishi cikin natsuwa banda hayaniya saboda baya son hayaniya.’’

 

‘’waye kuma sir?’’ abunda ya fado ma sabeeha arai Kenan, tasan me caregiver ke nufi, saidai abunda bata gane bane shine dalilin da yasa aketa wannan boye boyen da wannan ka’idojin, komai looks so strange.

Kofar dake facing dinsu suka nufa, nan matar ta bude ta soma mata bayani, ‘’nan ne activity room din sir, duk ranar Friday zaki dunga kawoshi nan’’

Kallon wajen sabeeha tayi, wajen cike yake da kayan wasa na yara, babu abunda babu mota ne jirgi da keke dadai sauransu da mamaki take kallon wajen har suka fito daga dakin.

 

 

Nuni da kofar tsakiya matar tayi kafin tace ‘’nan ne kuma bedroom din sir,first thing first by 8 dot yake tashi so duk abunda kikeyi na gyara ki tabbatar kin gama kafin lokacin, idan zaki shiga bedroom din ba’yin knocking saboda baya son any sound ko karar komai, zaki bashi first medication dinshi by 8:30 dot, sannan kafin yaci abunci zaki taimaka mashi yayi wanka ya shirya by 9 zaki bashi breakfast, sai second dose of medication dinshi’’

 

Jin haka yasa sabeeha shiga tunanin waye wannan sir din, kalaman matar dataji ne da yanda komai suke yin shi cikin tsari da ka’idoji yasa ta soma tunanin to kodai raino aka sake kawota, to amma rainon da zatayi ne leken asiri?, ita gaba daya ma kanta ya burkice da ala’amarin,

 

‘’that’s all for now, zuwa gobe zaki fara’’ matar ta karashe tana mai nufar hanyar futa daga part din sabeeha na biye da ita a baya.

Kasa suka sauka, maids din dake gyara gyare suna kallonsu ta wutsiyar idanu kamar hankalisu baya kansu, saida sukaga head ta wuce kafin daya daga cikin su ta soma Magana kasa kasa ‘’nandini, ayna fada maki, wannan a sama zatayi aiki kai amma I pity her,’’

Dayar da aka kira da nandini ce tace ‘’to me she looks like she’s happy, bata san inda ta jefa kanta ba, ki duba kiga yanda last maid dinnan ta gudu, ta bani tausayi ko kwana biyu bata yi, ni im curious wallahi, menene a saman nan’’

 Matsowa dayar tayi ta rada ma nandini wani abu a kunne………  

 

Bayan sun sauko daki sabeeha ta koma na bangaren su, tana shiga babu kowa a dakin don koda suka sauko daga sama ta gansu suna aikace aikace anan kasa, daman yan dakin nasu bangaren aikace aikace suke handling.

Zama bakin gadonta ta doka uban tagumi, tunani kala kala na yawo a kwanyar kanta.

 

 

California……

Envision academy high school…….

School Bus ce ta fito daga cikin school din, dauke da student, babu abunda ke tashi a cikin bus din sai hayaniyar yara, maya da gang dinta na zaune daga gefe su uku ashe wata yarinya suka saka a gaba suna bullying,yarinyar na gabansu a

tsugunne maya ta daura kafar ta akan labs din yarinya, su kuma student me zasuyi banda dariyar mugunta, saida aka zo first stop kafin wasu few daga cikin student din suka fita daga cikin motar ciki kuwa harda maya da kawarta inda suka shige cikin yaran da suka futa don kar a gansu.

Suna fitowa maya da kawarta kloe suka yanki wata hanya cikin sauri gudun kar driver yayi noticing din futar su, saida sukayi ma bus din nisa kafin su dan tsagaita, dariya kloe ta fara kafin ta maida dubanta ga maya ‘’kai babes this is the toughfest part of running away from school, I can’t wait to be 18 and free muyi mu gama exams’’

‘’hmm, nima kaina na gaji da guje gujen nan just to have fun, meysa sai lallai mutun ya zama 18? Other countries baa yin haka’’

Daidai nan suka karaso kan titi inda wata mota ke parke daga gefe, cikin hanzari suka karasa wajen motar, maya na gaba while kloe kuma na daga baya.

Suna shiga wanda ke zaune mazaunin driver ya miko hannu zai rungumeta, ‘’come here babe’’wani irin kallo ta watsa mashi wanda ya sashi komawa mazauni yana mai kunna mota, saurayi ne white American yasha wasu kananun kaya, daga baya kuma kloe ce ita ma da nata saurayin black American,

Wanda ke bayan ne yace ‘’girls where are heading to?’’

Maya ce tayi saurin cewa as usual, tana kaiwa nan wanda ke tukawan ya zugi motar suka bar wajen.

Basu tsaya a ko’ina ba sai a wani wajen shakatawa, wajen kamar restaurant, ciki suka shiga, inda daga nan basu tsaya ko’ina ba sai wani sirrintaccen bangare dake cikin restaurant din, kamar koda yaushe zaida wannan black American din yayi Magana da mai wajen don abokin yayansa ne kafin abarsu su shiga ciki don ba a yarda underage su shiga.

 

Wurin so very dim sai blue light kamar dare, maza da mata na zazzaune kowanne yana harkarshi da drinks a gabansu wasu kuma na cin abunci wasu kuma hayaki suke busawa.

 

Zama sukayi wajen da suke zama koda yaushe inda sukayi nasu order drinks din, wannan white ameriacn dinnan dai yana kusa da maya, da alamu saurayinta ne don daga yanda yake ta faman bata hakuri kamar yayi mata laifi ne.

‘’shut up u cheater,’’ ta daka mashi tsawa wanda yasa hankalin kowa ya koma garesu

 

‘’maya please’’ kloe ta fada tana kallonta don suna zaune opposite dinsu.

Hannunshi ya sake sanyawa ya riko nata ‘’bebz please im sorry, there nothing between us, its just accidental kiss please’’

 

Ajiye juice din maya tayi ta maida dubanta gareshi, ‘’you’re a cheater and a liar, you think I’m stupid? Kiss by accident? For goodness sake rick Zara is my friend, how could you kiss her and call it by accident, I see both of you with my 2 eyes’’

 

Shima saurayi harzuka yayi yana mai kallonta ‘’look, I don’t fucking care about the kind of thought you have on this, how many times do I have to apologies, I’m done please’’

Kallonsu kloe tayi da saurayinta don ganin yanda zasu kare, kamar yanda sukayi hasashe kuwa sai gani sukayi maya ta sauko lokaci guda, don bata taba taba yarda yayi fushi shima don tana masifar son nick kamar ranta, shiyasa duk abunda yakeyi take daga mashi kafa, gashi bai wani girmeta sosai ba, he’s just 22.

‘’okay but promise this should be the last time’’

Amsata yayi yana mai hugging dinta so tightly, ganin haka yasa kloe gyaran murya tana mai duban saurayinta tace ‘’I told you, bazata iya hakura dashi ba’’

‘’what are you gossiping?’’ maya ta karashe tana duban kloe da saurayinta, kafin ta tabe baki ta maida dubanta ga black American dinnan tace ‘’ I cant stay long guys, daddy nay a dawo and its been a week now bai koma ba, my phone has been seized, so lets just do what we have to do, how far with the?’’

Bata gama fada bama ya zura hannunshi cikin aljihunsa ya zaro wata yar takarda ya ajiye a gabansu kowa ya tura mashi gabansa harda maya.

 

Wani irin murmushi maya tayi mai wuyar fassara kafin ta dauki nata nannadaddiyar paper ta soma warwarewa jikinta har tsuma yake…..

 

 

 

 

 

**

Abuja Nigeria.

Gidan Marigayi alhaji santuraki..

Safiyar juma’a Kenan, yau gidan a cike yake tam saboda dama duk Friday ake taruwa a cikin main house bangaren Anne duk da estate daya suke kuma kowa da part dinshi.

Matan uncle Sameer babban dan gidan anne kennan da aunty fadila da iyalanta duk sun hallara ga jikoki harda da yaya ma.

Rana irin ta yau ta zame masu kamar double celebration saboda ayau uncle Sameer zai dawo daga Europe after shekara daya Kenan da tafiyarshi zuwa wani course.

Yaran duk suna zaune a sitting room na kasa don gidan nada girma sosai while iyayen su kuma suna sama wasu kuma suna kitchen ana hidimar girki dasu.

 

Anty Laila (uwar gidan uncle sameer)ce ta shigo dakin da sallama don zuwanta Kenan gidan, don bata samu tazo da wuri ba saboda ta dan tsaya don shirye shiryen tarbar mai gida don anan gidan ta zai sauka,

 

Da sallama ta shugo cikin dakin, anne dake zaune akan gado da wasu tarkacen takardu a gefenta ne ta dago ta kalleta tare da amsa sallamarta fuskanta babu yabo ba fallasa, nanna ce ma dake zaune kan kujera tana cin dambun sadakar

Friday da aka kawo ne ta kallata cikin fara’a tace ‘’ah ah matar babban yaya sai yanxu’’

 

Sunkuyar dakai anty Laila tayi harta karaso tsakiyar dakin ta zauna kan carpet tace ‘’barka da hutawa nanna, barka da huta wa anne’’

 

‘’barka dai’’ suka amsata a tare

‘’ya iyali, yau mai gidan naku zai dawo ko’’ nanna ta fada tana mai kallonta

‘’eh yau zai dawo insha allah’’

‘’toh masha allah ga dambu bismillah’’ nanna ta fada tana mai kallonta

‘’alhamdulillah nanna, sai zuwa anjima zan diba’’

Shuru ne ya biyo baya adaidai lokacin fadila ta shugo dakin hannunta rike da mubin, yaron(aunty mubina) amaryar uncle sameer kenan.

‘’mubin dai akwai barci yaron nan shiyasa yake burgeni’’

Jin muryarta yasa suka dago suka kalleta banda anty Laila da kanta ke kasa, kallon inda take fadila tayi kafin tace ‘’ashe kin iso’’

Kamar anty Laila bazatyi Magana ba tace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login