Showing 132001 words to 135000 words out of 135321 words
gane shine, wannan confidential information ne nake fada maka, ssd organization bata yarda a fiddashi ba musamman ga waenda ba ma’aikatanta ba, i have to go this far just to get this for you, saidai inason ka sani, irin waennan gangs din ba a taba kamasu, countless of time idan munso kamasu bama iyawa saboda akwai waenda ke protecting dinsu saboda dirty work din da suke masu, gudun kar asirin su yafito yasa suke protecting dinsu, so duk aikin dakaga sunyi an basu kwangilar yi ne, kuma yanzu tunda mun tabbatar shine yayi wannan aiki, definitely akwai
master mind behind, duba ga yanda kidnaping dinsu kawai yayi ya zubar dasu a desert ba tare da ya illata su ba hakan ya kara tabbartar min da hunch dina and I believe yanama wasu aiki ne, most importantly”
Ya jinkirta yana mai sauya papers din zuwa ga na kasan su ya fidda hoton da aka dauka inda aka dauko khaal yana musayar hannu dashi kafin yace “as i concluded, this is framing, its a brainwashing trick, someone most be against khaal, don komai has fallen into places, its possible an bashi aiki ne yayi tailing dinsu saida ya tabbatar kabar asibitin kafin yayi stepping har yayi badda kama da suffarka da motarka sannan yayi kidnapping dinsu after 24 hours saiya kirashi wanda zaiyi tricking wato khaal kenan a waya ya umarci yazo same exact location dinnan da akayi hoton don ya shaida mashi inda suke daga nan ne suka samu opportunity sukayi hoto daya fidda khaal a cikin hoton da motar da akayi kidnap din, duk wanda yaga wannan babu wanda bazai yarda da cewa khaal bashida hannu a ciki ta wannan damar suka samu sukayi framing dinshi wannan ne hunch dina da zargin danakeyi kenan, saidai inason ka sani bude case dinnan zai zame mana babban aiki saboda an rigada anyi declaring wanda yayi kidnapping nasu which is khaal, amma inason nasan ko you have someone in mind da kake tunanin zaiyi hakan? ”
Take gaban jamid ya fadi babu wanda ya fadi mashi arai sai hidaya, saidai deep down yanajin bazata iya kashe khaal ba, jininta ne kamar mahaifi yake a wajenta, saidai tunawa da yanda suke rigima akan taj da maganar poisen yasa yaji kawai zuciyarshi gana wasi wasi da lamarin, what if she went that far? What if shes behind all of this? Take yaji wani irin faduwar gaba mai tsanani, Dole yasan yansa zaiyi, idan haka ta tabbata to fa hidaya is very dangerous, zata iya yin komai kenan,katse mashi tunani qalam yayi ta hanyar bugun table din gabansu yace “you have someone on mind?”
Bakinsa na karkarwa yace “I’m not sure gaskia i have no one on my mind, but waye zai yi haka? This is ruthless,”
“Haha bakasan mutun ba, mutun bashida kama, it can be anyone or someone you’ve never expect, it’s always someone close to you that envy the most hoping for your downfall”
Sun dade tare suna tattaunawa akan case djn kafin sukayi musabaha,jiki a mace jamid ya fito daga office din.
Yana futowa ya shige cikin motarshi, yana zama unknown call ya shugo wayarshi, yana duban wayar ya daga tare sa kaiwa kunnenshi.
“I need to talk to you about kisan khaal,khaal
Bai mutu ba yana nan raye”
Jamid na jin haka ya burkice har zai bude motar ya koma office din abokin wanda ya kirashi ya dakatar dashi “i can only reveal myself idan wannan ya tsaya between us”
“Who are you? How do you expect me to trust you?” Jamid ya jero mashi tambaya
“You have to trust me i have all of your answers to your question, saidai inason ka sani wadda kake zargi akai itace behind duk wannan crises din Mrs hidaya!”
Kit wayar ta kashe da “hello hello!!” Ganin wayar ta sauka yasa jamid ya shiga dialing wayar bata shiga ba saiga message ya shugo cikin wayar da address, yana gani yayi saurin kunna motarshi yayi reverse with high speed.
Tafiyar wajen minti goma ta kawoshi lounge din yana parking motarshi ya daga wayar, saiga wani message din ya shugo, “unlock your car and step out”
Yana unlocking harya bude motar aka shugo kai tsaye, wani mutun ne sanye da normal kaya sai wata facing cap daya saka ya rufe fuskanshi, kallonsa sosai jamid yayi nan ya tabbatar shine wanda ya kirashi, “who are you? How did you know where i am?”
“Na dade ina bibiyarka for past few months, if i may introduce my self, sunana mutallib, agent mutalib, ni na sanka saidai kai baka sani ba, i’m one of the most trusted fellows din khaal, ina bibiyarka ne harna gano bunciken da kakeyi wanda hakan ya tabbatar min kana tare da khaal, and you believe framing dinshi akayi bayan wannan ma inason na tabbatarda zan iya trusting dinka da zan information din da nake dashi wanda khaal ya daura yardata akanshi.”
Nunfasawa jamid yayi confusedly yace “kace khaal bai mutu ba? How do you expect me na yarda dakai”
“I’m sorry for mentioning that, dole yasa na fadi hakan don na samu attention dinka, don wannan ne kadai zaisa ka yarda ka amince mu hadu”
“And the last name you mentioned? What doea she have yo do with this?”Jamid ya sake tambayarshi.
Nunfasawa mutumin yayi kafin ya zare hular dake kanshi “its started wata takwas da suka wuce, bayan taj ya samu babban hadarin daya kusa kawo Karshen ranshi, bayan accident din khaal yayi suspecting ba normal accident bane, cause komai looks suspicious, it’s planned which is, khaal ya fara buncike na tsawon watanni takwas da farko bamu gano komai ba saboda duk evidence anyi fabricating dinsu, and its shows normal accident ne wanda we believe ba hakan bane, abubuwa sun fara zama suspicious lokacin da khaal yaga yanda hidaya ke treating taj din, ta hana kowa ya kusanceshi sannan ta tabbatar komai nashi ya dawo hannunta da responsibility dinshi saboda yafi yarda da ita akan kowa, a lokacin ne ta qayyadarda zamanta na ceo of the company dukda duniya batasan cewa taj ya samu matsalar kwakwalwa ba.
Bayan wannan tayi hiring doctor da zai dunga kula da taj din inda ta bashi contract kan cewa yayi monitoring taj din karya bari ya samu aani progress din lafiyarshi ta hanyar bashi maganungunan da zaisa karya samu improvement, nan doctor ya shaida mata dole saidai idan za a rufeshi ga duniya ta hanyar nisantarshi ga kowa da abunda zaisa ya tuna rayuwarshi a baya, hakan kuwa akayi, lokacin da khaal ya buqaci a fiddashi kasar waje ta nuna bazata amince da hakan ba don already tayi providing mashi likitoci kwararu, khaal ya damu sosai wannan yasa mukayi buncike akan likitocin don tabbatarda taj da safe with them, i had to do the dirty work ba tare da sanin khaal ba, inda na gano cewa biyansu tayi maqudan kudi akan kudirinta, lokacin dana kaima khaal report dinnan hankalinshi ya tashi sosai nan ya fara tunanin maisa zatayi haka? Rashin sanin amsar tanbayoyin yasa mukayi doubling kudin data basu don suyi mana aiki
sannan su dinga bamu report din taj din, maganar magunguna kuwa saida khaal ya tabbatar ba a chanza mashi su ba saidai kulleshi da akayi aka hanashi mingling da duniya wanda hakan zaisa ya samu massive improvement saidai khaal bashida yanda zaiyi da wannan don haka muka cigaba da zuba idanu, duk wani improvement din taj da cases din rashin lafiyarshi dake zuwa hannun hidaya yana zuwa hannunmu, duk wani olans dinta da abunda ta buqaci ayi mashi doctor yana kawo mana information din.
Daga karshe khaal was not feeling at ease for over 5 months babu wani progress gashi shi kansa baya samun ganin taj din kwata kwata, wannan yasa ya fara tunanin yanda zaiyi ya aamu connection to taj din all the time.
Wannan yasa muka kawo nigerian caregiver dinnan dake kulashi dashi, ba tare sa saninta ba khaal ya turota gidan a matsayin yar leken asiri, nine nayi suggesting hakan saboda muyi komai cikin sırrı, a ranar da khaal ya fara ganinta kuwa a gidanshi ne inda aka kawota aiki, she was very hard working and patient da kananun yara, bata sa ha’inci ko mugunta, wannan yasa nayi mashi buncike akanta gaba daya da rayuwar datayi achan kasarsu harda parents dinta, he tested her countless of times ta hanyar ajiye kudi inda yasan zata iya dauka kuma ta boye ba tare da sanin masu gidan ba saidai bata taba dauka ba, ita bata san yana monitoring dinta ba don bangaren mai gida ma aikata basa dira kafarsu a wajen, dalilin barinta gidan was her facial appearance, baima san madam ta sallameta ba saidaga baya yaji zancen wannan ya bamu damar yanke hukuncin daukarta sannan muka turata gidan as yar leken asiri, abun yazo mana da sauqi saboda caregiver dake kula dashi an sallameta daga gidan, wannan yasa muka turata gidan ita kanta bata san cewa khaal ya kawota gidan ba”
Nunfasawa yayi kafin ya cigaba, “zuwanta was the best decision da khaal yayi making, don dictor ya shaida mashi tana kula da taj din sosai in a protective sannan itace maid ta farko daya shaku kuma ya amince da ita lokaci guda, lokacin da taj ya samu seizure da daddare she couldn’t leave his side dukda tasan zai illatar da ita, she protected him and stay with him.
Wanan yasa khaal ya soma tunanin yanda zaiyi don ganin ta zauna a gidan permanently ba tare da hidaya ta koreta ba, at the same time yana lura da abubuwan da hidaya keyi har zuwa lokacin sata buqaci ayi auren taj da care giver dinnan, wanda muka gano dalilin hakan donta zama itace the most highest shareholer, zata samu hakan ne only idan taj yayi aure tunda itace next of kin dinshi, wannan yasa tayi proposing without second thought khaal ya amince da auren,daga gefe kuma yayi handling maganar shares din, yanda yayi bribing law firm din taheel company haka khaal shima yayi bribing dinsu handsomely suka bashi original copy ita kuma aka bata fake property paper ba tare da saninta ba, shares dinne kawai bai karba ba ya barta dashi tunda ta nuna shi take hari.
The nxt day labarin rashin lafiyar taj ta bayyana, da farko munyi suspecting itacw sai daga baya muka gane competitors ne, babban maqiyin ahalin taheel ne is behind, Mr abdulbasit, washe gari hidaya tayi siezing wannan opportunity din ta fito press conference, saida ta fito khaal ya tabbatar da that was her plan as well sai abun yazo mata adaidai.
Dole kamfani ya koma wajenta saboda babu yanda za ayi wanda bashida lafiyar kaakwalwa yayi ruling kamfanin apart from that yanxu she’s powerful sabod itace highest shareholder.
Bayan ta samu abunda take so ta buqaci fidda caregiver daga rayuwar taj saboda tana son responsibility dinshi ya sake dawowa hannunta,inda tayi planing fidda yarinyar daga gidan ta hanyar shigarda kara ga domestic workers org akan cewa yarinyar is not qualified kuma an koreta sau biyu wanda hak zai zama abun zargine a wajensu, we have 2 informat a gidan sune sukayi informing khaal akan situation wanda ya bama khaal damar sanin abunda ke faruwa har yayi stepping in,aranar yayi declaring yarinyar as matar taj sannan ya maida responsibility dinta legally.
After all this crises maganar poisoning taj ta shugo, hankalin khaal ya tashi sosai a ranar inda ya tabbatr da son ganin karshen taj din akeyi, da farko bai yarda hidaya bace ba saboda yayi imanin idan zata kashe shi she will have done it tunda dadewa tunda tana da chance, wannan yasa ya fara buncike akan poisoning din don bai yarda da maid ce haka kawai tayi hakan ba.
Adaidai wannan gabar bunciken muka gano babban sirrin ta, we found a single footage da ba a goge ba wajen wata bishiya daidai wajen accident din, anan muka tabbatr da planed accident ne, allah yaso muka samu fuskar mutun daya wannan yasa mukayi deep buncike, we found him and we bribe din, saidai bamu samu komai daga wajenshi ba don an shaida masu kawai su bi takan motar su tabbatr sun illatashi, ogansu ne yasan komai, i had to go very far on this na gano itace, shes the master mind behind, wannan ya faru a day before kidnap din da akayi,”
Kallon idanunshi da sukayi jaa jamid yayi shima nashu sun sauya kala yace, “so that means wannan ne dalilin dayasa yake nemana?”
“Yes” mutallib ya amsa shi kafin ya cigaba, “i solely believe all if this is her doing, yanda kayi buncike akan serial killer dinnan nima nayi, he has been working for her for almost 5years, shine wanda ya hadu da khaal, nabi didigi akan wannan, kuma duk plan ne da trick sukayi amfani dashi wajen sunga sunyi framing dinshi at the end kuma sun kawo karshen shi saboda ya gano komai, nasan nine on the line, i had to tell you all of this saboda kai zan iya yarda kawai, this is a murder case,”
Yana kaiwa nan ya fiddo da wani hard drive ya miqa mashi kafin ya fuce daga motar bayan ya maida hular,
6pm taheel company…
Zaune take a office dinta kunneta maqale da airpod kamarai sauraron abu, gaba daya idanunta ya sauya sosai yayi jaa, kaf abunda ke faruwa cikin motar jamid da location din daya tsaya da recording din abubuwan da suke fada da komai ta jishi tass saboda tracting rwcorder din data maqala a motar jamid din, tun bayan data tabbatar yana aiki da abokin nan nashi ta fara tailing dinshi ba tare da saninshi ba, saida ta gama ji tasaa sai kawai ta kyakyale da dariya, ta dade tanayi kafin ta hade rai babu imani, “woww wonderful khaal, wannan ne sirrin nawa daka sani
kadai kenan? Saigashi nasara tana tare dani koda yaushe, i will do anything anything to any extent don na samu abunda nakeso, duk kokarin daka dunga yi don ganin kayi protecting dinshi ya ruguje, rayuwar taj na hannuna, alkawarin dana dauka bazan fasa yin shi”
Tana kaiwa nan ta dauka burner phone dinta ta soma waya.
***
Bangaren jamid dai kasa motsawa yayi tun bayan futar mutallib, he’s over mamaki, he’s speechless, hankalinshi ba karamin tashi yayi ba, zuciyarshi tayi tauri soaai, sai ayau yafi jin mutuwar khaal sosai, duban agogon hannun shi yayi ganin its almost night hakan ya sashi dialing number qalam, bayajin zai taba iya yafe ma hidaya , ayanxu daya samu duk wani evidence akanta bazai barta ba.
Qalam na daga wayan ya soma magana “jamid can i call you later, ina asibiti yanxu, my wife is about to deliver”
“Allah ya suaketa lafiya, inason zamuyi magana kan something important i have found…”
“Sorry dude i have to go in the labour room”
Yana kaiwa nan kit ya kashe wayar, kallon wayar jamid yayi jikinshi duk ya mutu yayi la asar, haka ya juya akalar motar zuwa cafe dinshi son ya samu yayi clearing kanshi.
Har zuwa lokacin he cannot belive abund akunnwnshi suka jiye mashi, coffee din da akayi serving dinshi ma bai wani sha da yawa ba ya ajiye ya fuce daga cafe din ya jufi gida.
Tun akan hanya yaketa nazari kala kala, harga allah ko ganinta baya son yi, he can’t stand ya ganta freely while tayi wannan aika aikar ciki harda kawo karahe khaal da tayi, da kyar dai ya samu ya kawo gida yayi parking, ya dade sosai a cikin motar yanajin jikinshi wani irin duk yayi sanyi.
Saida ya dauki hour a cikin motar kafin ya daidaita natsuwarshi, ya kashe motar ya fito, daga gaban dashboard din wani jan abu ne yake blinking saidai kwata kwata bai lura dashi ba, haka daga chan dayan barin wajen mazaunin gaba ma, rufe motar yayi jiki a mace lokacin wajen karfe takwas ya shige cikin gidan,
lokacin daya shugo babu kowa a kasan don haka ya wuce wajen stairs, dan tsagaitawa yayi jin kanshi ya juyawa lokaci guda yaji kamar ana zare mashi jijiyoyin jikinshi,daga chan saman stairs din kuwa Fadwa na tsaye ta hangoshi, yana daga kafafunshi ya fara hawa saman itama ta soma saukowa tana murmushi, shi baima lura da idata ba saboda hajijiyar daya soma ji, yana dafe rail din benen har yakai step din da take, sai a lokacin ya dago don ya mata magana sai kawai ya kasa, jikinshi ya fara kyarma kamar an saka mashi electric shock, wannan rail din daya rike ne kawai ya bashi damar tsayawa badan haka ba daya fadi, “you need help?” Ta tambayeshi?
daga kafarshi da zaiyi sai kawai ya yanke jiki ya fadi, yanda take gabanshin nan zata iya taimaka mashi amma ko a jikinta haka ta tsaya harya gangara tana kallo jini na bin benen saboda fasa kanshi da yayi gashi ta baya ya fado, yana kaiwa
karshe kawai sai tayi murmushi tace “, I’m sorry you have to end up like this…this is just the beginning”
maid din dake shirya dinner najin kara tayi saurin karasowa wajen tana ganinshi kwance jini nabin fuskanshi ta kwala kara wanda yasa kowa ya futo a gigice, daidai nan hidaya ta sawo kanta cikin gidan, su afiya ma a gigice suka futo, suka zagayeshi, sai a lokacin fadwa ta sauko hankali a tashe ta soma magana “meya sameshi?”
Girgiza mata kai afiya tayi, hidaya data karaso ganinshi kwance ga jini yasa ta karaso wajen cikin hanzari, idanunshi ya soma budewa ya kasa saboda rufewa da yakeyi, jikinshi gaba daya kamar an zare mashi duk wani joint din dake karfafa mashi, kamar an tsinke kaf jijiyoyin jikinsa, tun yana iya bude idanu harya rufe idon gaba daya,sama sama ya soma jin hidaya na cewa “call an ambulance”Dipp bai sake jin komai ba.
After 2weeks…
Ahankali ya soma bude idanunshi yana mai kallon dakin da yake kwance, kanshi ya mashi nauyi sosai, sake lumshe idanun yayi ya bude su tare da kokarin daga hannunshi abu kamar a mafarki duk yanda yaso ya daga hannunshi ya kasa, shugiwar hidaya yayi daidai da budewar