Showing 51001 words to 54000 words out of 135321 words
wallahi,”
Ogan su ne ya kalli wanda yayi magana kafin ya shago wuyanshi yace “ba saida na fada maka kan cewa karkace komai ba? “
“Sorry sir”
“Ina footage din, yau babu wanda zaibar wajennen, inason mu sake duba footage din again and again”
“Yes sir”
Karfe uku da rabi daidai sabeeha ta koma part din, dakinsa ta wuce direct bakinta kunshe da sallama, tundaga bakin kofar dakin ta soma jin fitar nunfashinsa kamar yana battling da breath dinshi.
Karasowa inda yake tayi hankali a tashe, yana nan kwance kamar an qame shi, nunfashi sa ne kawai ke fita da kyar tsabar zazzabin dake cinshi.
“Friend friend are you okay”
Duvet din ta yaye mashi, ya jike jargab gaba dayanshi,tabashi ta soma yi don ya tashi don duk a tunanin maybe mafarki yake yi saboda ayanda yake nunfashin da yanda zufa ta wankeshi saida taji zafin ne ta gane cewa zazzabin da yayi dazu ne ya dawo mashi.
“Friend friend” ta soma kiranshi, shuru babu response, at that point hankalinta ya gaba tashi, gaba daya tama rasa ya zatayi, takai wajen kusan 30mins shuru babu response, wani tunani ne yazo ranta, to kodai ya suka ne? Ta tambayi kanta, bata jira bama kanta amsa ba ta wuce bathroom ta debo ruwa a bowl ta dawo bedroom din, wash cloth ta tsoma cikin bowl din kafin ta soma shafa mashi a fuskanshi, nan ma dai shuru, ta dade sosai tana goga mashi tana hawaye har ruwan yayi sanyi, lokacin ana maganar wajen karfe hudu, kamar da wasa ta dago taga idanunshi sun soma budewa, idon yayi jaa sosai,
Hamdala tayi kafin tace “meysa Kaqi tashi? Hankalina duk ya tashi na dauka wani abu ne ya sameka”
Da hausa tayi maganar so bai gane abunda take nufi ba don haka kawai ya zuba mata idanu, wannan ruwan data goga mashi a jiki ya sashi jin sanyi sosai, saida ya farka nema zazzabin yayi doubling, take ya fara karkarwa kaf kaf, hakoranshi na gogayya dana juna, burkice dai sabeeha ta burkice sosai don unexpectedly ya fara jijiga ba kamar dazu da yake barci ba kwata kwata baya motsawa, “innalillahi wa inna ilaihi rajiun” ta furta ganin idanunshi na neman qafewa, “na shiga uku don Allah meke damunka? Ka fada min menene?zazzabin ne?”
Ta sake tambayarshi hankali a tashe, burgimar daya farayi ne yasa ta shiga wani sabon hankali, kankace me bata ankara sai ji tayi dimm ya fado kasa, cikin sauri ta nufi hanyar fita daga dakin harma part din gaba daya, karar dataji na futowa daga sitting room dake saman ne yasa kawai ta nufi wajen hankali a tashe kamar an jeho ta, fadwa dake zaune tana waya afiya kima na daga gefenta tana cin pizza tana kallo suka zuba ma sabeeha ido da mamaki, jikinta na kyarma ta shugo bedroom din.
Kallonta sukeyi afiya ce tayi saurin cewa “ke bakida hankali ne, wannan illiterate dinfa ko harda mahaukata ne suke mana aiki”
Fadwa ce data gane ta tayi saurin katse wayarta ta kalli afiya tace “thats new maid din big baby”
“Oh da alamu itama haukan ya taba kanta kenan” afiya ta fada sounding so annoyed
Fadwa ce kawai ta kalleta tace “me ya shugo dake?
“Madam, frien…. Sorry sir ne bashida lafiya”
Afiya ce tayi saurin cewa “daman wayace maki shi mai lafiya ne? Ni bansan wake kawo irin waennan africans din nan ba? They are the stupidest people”
Sauke kai sabeeha tayi hawaye na gangaro nata, fadwa ce ta sake cewa “go and do your job properly”
Jiki a Mace sabeeha ta juya ta fito daga part din, gaba daya ta rasa ya zatayi, wajen wa zataje? Tunawa da head yasa ta saurin sauka kasa tana hawaye, daidai hanyar dazai kaita ga dakin head tayi karo da yar ghana, kallonta yar ghana tayi ganin duk ta burkice yasa ta cewa “sabeeha? Are you okay?”
Sabeeha batama lura da ita ba ta wuce dakin head, ciki ta shige ta rufo kofar, duve dube ta soma yi ganin bata nan yasa ta saurin fitowa, a bakin kofa ta sake tadda yar ghana a tsaye, “ina head?”
“I dont know but maybe tana kitchen”
Kitchen din sabeeha ta nufa hankali a tashe, tana shiga ta hangota cikin sauri ta karasa inda take ganin babu kowa a kitchen din.
“Head, please ki taimaka min, sir bashida lafiya”
A burkice head ta soma duban kitchen din kafin ta janyo hannunta suka fuce daga kitcehn din, wani corridor sukabi inda take tabbatar da babu kowa a wajen kuma babu wanda zai jisu
“Ke bakida hankali? Wayace maki zaki iya wannan maganar a ko’ina? Shin kin manta you’re not to disclosed abunda ya shafe shi ba?”
“I’m sorry head, wallahi bashi da lafiya he’s sick”
Buge mata baki head tayi “and wayace maki daman mai lafiya ne shi? Ina mai baki shawara idan har kinason rayuwarki da lafiyarki dole sai kinbi yanda aka kayyade maki, dont ever step down and say a word about abunda ke sama”
Tana kaiwa nan ta fuce, sabeeha dai hawaye bata bar yinshi ba anan tsaye, wannan wani irin masifa ne haka, ayanda take ganin yanda yake wahala zai iya mutuwa wallahi, tunawa da kalamanshi da yayi mata dazu inda yake ce mata karta barshi yasa ta komawa zuwa saman, a daidai nan ta bakin kofar kitchen din ta hango yar ghana a tsaye ta labe,bata ma tsaya bi takanta ba don ba wannan ne agabanta ba yanxu ta wuce sama.
Koda ta karaso sama tana jiyo yanda fadwa da afiya ke hirarsu suna kallo, tsugunnawa kawai tayi ta soma hawayen takaici, dukda batasan alakarshi dasu ba amma yanda taga kammanin su ta tabbatar yan uwansa ne suma, ranta yayi mugun baci da yanda suka amsa ta lokacin data shiga wajen su, wannan wani irin ahali ne? Ta soma tambayar kanta? Ita tasan mara lafiya zama ake dashi shi kuma wannan gudunsa akeyi saboda wani dalilin daban wanda bata san koma menene ba saidai tana jin harga allah ba ayi mashi adalci ba.
Tana nan tsugunne dadyn barad ya karaso saman shida barad, daman shi yaje ya daukosa yau, tun daga bakin stairs ya fara jin sheshekar kukan nata, da mamaki kuma ya ganta a zaune bakin kofar dakin tana kuka.
“What’s going on here?”
Cikin sauri sabeeha ta dago kanta, ganin wanda ke gabanta ya sata miqewa cikin gaggawa, “akwai wata matsala ne?” Ya sake tambayarta
Kamar jira kuwa take ta girgiza mashi kai “sir please friend bashida lafiya”
Shuru yayi yana wani nazari, ganin yanda take kuka yasa shi kallon barad yace “go and freshen up okay?”
Yana kaiwa nan ya nufi part din taj, kofar ya bude sabeeha na biye dashi har cikin bedroom din, tun daga nesa ya hangoshi a kasa kamar matacce ga hannunsa daya ballaqe shi gefe, cikin hanzari kuwa jamid ya karasa inda yake ya juyoshi, jikinshi ya koma jawur, har zuwa lokacin karkarwa yake,
“Innalillahi, whats going on here? Me ya sameshi?”
Jiki na bari sabeeha ta soma bayani, “sir tun safe yake zazzabi bayan na bashi medication dinshi sai yayi barci By 3 na dawo zan bashi second dose shine naga baya motsi.
Duk rikicewar sabeeha bata kai jamid ba, jijiga taj din ya soma yi “Tajudeen hey hey!!! Open your eyes”
Ay Inaaaa taj baya ji kwta kwata, idanun nan sun rufe ruff, rasa abunyi jamid yayi, tunani kala kala Na yawo a ranshi, karshe dai kawai yayi deciding daukarshi gaba daya,
“Zoki taimaka min”
Matsowa tayi ta kama hannunshi don taimaka mashi, dakyar take jan hannun tana zufa harda nishi, haka nan jamid ya daukeshi duk da shi namiji ne dakyar ya daga shi ya sashi a bayanshi don yana da girma sosai masha Allah.
“Bude kofar” ya umarci sabeeha,
Kofar ta bude ya fito dashi a bayansa, sabeeha na biye dasu tana kuka har suka fito daga part din, suna nufin sauka kasa saiga hidaya ta hauro last stair,da mamaki take kallon abunda idanunta ke ganar mata, tabbas big baby ta hango a bayan jamid.
Ganin yana neman wuceta yasa ta saurin damqo hannunshi ta daka mashi tsawa kamar ba mijinta ba
“Jamiddddddd…whats going on here whats this? Are you out of your mind ina zaka kaishi?”
Yasan halinta don haka ya amsa ta “bashida lafiya he’s in a critical condition?”
“Wait what? Ina zaka kaishe then?”
Wata iriyar tsawa ya daka mata “Shin bakiji me nace bane? He’s in critical condition and you’re still questioning me?”
“Toh daman wa yace yana da lafiya? Look jamid babu inda zaka kaishi, zan kira medical team dinshi suzo yanxu”
“Hidayaaaa!!! Meysa bakida tunani ne? Whys your heart sore? Shin kina jin abunda kike fada kuwa”
“Majid!!!!!” Itama ta daka mashi tsawa, su fadwa tuni suka fito suka tsaya suna kallon ikon allah
“ how dare you? How dare you? Kai waye nashi? Who are you to him? His guardian angel or what? Ni ce guardian dinshi? He’s under my care saboda shi kadai ne kanina, kana son ka nuna min ka fini sonshi ne ko ka fini damuwa dashi? You’re making me look at you as a hypocrite,”
Yanda kasan ta buga mashi arrow a kirji haka yaji, yau hidaya da bakinta ke fadin mashi cewa tana kallonshi a matsayin hypocrite?
Kasa motsawa kawai yayi, badan taj yana da special waje a tarihin rayuwar shi ba daya barshi da ita kawai saidai bazai iya ba dole ya zama strong and komai zata ce bazai taba saka shi giving up akan taj ba saboda karfin alqawari.
Wayarta ta daga ta soma dialing heath team din dake kula dashi.
Bawan allah taj yana nan ya gama galabaita sabeeha kuwa kukan da take ya wuce musali dukda kunshe kukan takeyi don karya futo fili, fadwa da afiya kuwa kamar suna kallon tv, yau wata takwas kenan rabon da su ganshi sai yau, ya chanza sosai kamar bashi ba, Taj mai kwalisa mai class da girman kai da aji shine ake fada akanshi, idan ance masu he will look helpless kamar yanxu zasu rantse karya ne,tabe baki afiya tafi ita ranta ya gama baci ganin yanda ake ta fada akanshi, sai taji tsanarshi na ninkuwa a ranta, whys the world revolve around him? Kowa is trying to protect him, abunda yafi damunta shine yanda hidaya ta tsaya akanshi, ita wannan abun yana damunta sosai.
****
Cikin yan mintuna kadan saiga health team sunzo, lokacin jamid ya maidashi daki ya kwantar dashi.
Cikin gaggawa suka soma dubashi suka sa mashi ruwa da allurori irin nasu na masu matsalar amnesia, wani irin special care aka bashi na gaggawa har aka samu ya soma dawowa daidai.
Saida doctor ya tabbatar masu cewa zaiji sauqi kuam he’s stable kafin ya fita da team dinshi.
Sabeeha na rabe daga gefe ta kasa tafiya, baiwar allah ta tsorata sosai.
Hidaya ce ta futa ba tare da ta kalli inda sabeehar ke tsaye ba, tana fita jamid ya miqe shima, “please take care of him dan Allah karki bar kusa dashi i trust you okay?”
Girgiza mashi kai tayi alamun gamsuwa kafin ta karasa bakin gadon ta zuba mashi idanu abun tausayi.
Majid na fita dakin su ya wuce, yana shiga ganin bata dakin yasa ya wuce closet room, kofar ya banko ya shiga, yana shiga ya ganta tana kokarin rage kayan jikinta,
“Hidaya!!!”
Wani irin kallo tayi mashi, “ please bani da time din wannan surutan naka? Na fada maka whatever comes around matiqar yayi involving big baby ne babu ruwanka, don babu ruwana da kai mijina ne duk abunda nayi…”
Dakatar da ita yayi ta hanyar cewa “Wow,hidaya, you always don’t fail to amaze me so impressive, bazan tsaya muna jayayya dake ba but inason ki sani, babu wanda ya sanki sama dani? Ciki da waje, i know all your movements da intentions dinki, kina ganin wannan abubuwan da kikeyi shi zai rufe abunda ke zuciyarki dana karanceshi tun shekaru da suka wuce? Idan har zaki yaudari duniya ni bazaki taba yaudarata ba, i’m warning you, don’t try my patience, mu tafi a haka har allah ya bashi lafiya, saidai ina so kisan cewa ko me zakice bazai taba hanani shiga al’amarin taj ba, you can never stop me, duk abunda zakiyi kiyi,”
Yana kaiwa nan ya fuce rai a bace.
Saurin runtse idanunta tayi da sukayi jaa sosai, ya zatayi da jamid, ya zatayi da jamid, kamar mahaukaciya haka ta soma watsar da kayan dresser dinta, me yake nufi kenan? Dole yasan da wani abu kenan,? Whats in his mind?
Tabbas tasan jamid shi yafi kowa saninta da halinta tunda shike zaune da ita saidai bata taba tsammanin zaiyi threatening dinta ba,
Zarya ta soma yi tsakanin dakin tana tunani, “i need to do something, kafin lokaci ya kure”
Ta fada ma kanta……..
Matar Taj (destined with you
🩵🤍
)
Written by
Queenmarh
✍️
Free page
Chapter 25-26
Washe gari da safe likitan dake kula da Taj ya sake dawowa don duba lafiyarshi, lokacin da suka shigo sabeeha na daga zaune tana goge mashi jikinsa da ruwa mai dumi, gaba daya ya zama pale har zuwa lokacin barci yakeyi ga drip din hannunshi daya kare da ba a cire ba.
Jamid ya shugo dakin yafi a irga, duk after an hour sai ya shigo ya duba sa.
Ba karamin dadin ganin yanda sabeeha ke kula dashi yaji ba, a yanda yaga alamu ma kamar batayi barci ba kwata kwata, daga yanayin idanunta he can tell how worried she is, sai yanxu yake ganin asalin yanda ake damuwa da mutun tsakani da allah dukda basu da wata alaqa su kuwa yan uwanshi kuma jininshi babu wanda ya damu kamar haka.
Hidaya ce ta fara shugowa sai doctor dake biye da ita a baya yana mata bayani.
Jamid na daga tsaye a gefe while sabeeha ta shiga bathroom don zubarda sauran ruwan.
Gaisawa jamid yayi da doctor, hidaya kuwa ko kallon inda yake batayi ba daman ba a dakinsu ya kwana ba, dayan dakin ya tafi.
Yan dube dube doctor yayi kafin ya cire mashi drip din hannunshi, wasu magunguna ya futo dasu da wasu allurai ya soma yi mashi, yana gama wa ya soma masu bayani akan magungunan da za a dunga bashi kullum saboda kar zazzabin ya dawo.
“Meysa bai tashi ba har yanxu?” Jamid ya jefo masa tanbaya
“Saboda alluran da akayi mashi na zazzabin yana da karfi sosai, kuma tasu allurar ba normal injection bane kamar na normal mutane
“Inason bayanai akan magungunan shi da progress dinshi, hope hakan babu matsala?”
Murmushi kawai doctor yayi kafin ya dubi hidaya data kauda kanta gefe, “no problem sir”
Girgiza kai jamid yayi ya nade hannayenshi a kirji, hidaya dai ranta ya gama baci, ashe dai da gaske yake, hada ido sukayi da doctor kafin ya girgiza mata kai, tsaki kawai ta doka wanda yasa suka kalleta gaba daya.
“Babu wani matsala yanxu, kawai yana buqatar proper care ne, nayi mamakin zazzabin shi daya sauka da wuri haka na dauka ma zan dawo na tadda he’s still having it, looks like kunyi natural remedy don shi kadai ke sa zazzabi ya warke lokaci guda ba kamar medication ba, medication process yana daukan lokaci”
Girgiza kai jamid yayi alamun gamsuwa daidai nan sabeeha ta sake futowa da wani warm ruwan data sauyi harda wash cloth a hannunta.
Kallonta sukayi gaba dayansu, ita bata ma lura dasu ba don jamid ta bari anan tsaye, kallonta doctor yayi kafin yace “madam, i have a suggestion, i think keeping her around him so that she can keep an eye on him is safe, don naga last time danazo na ganta anan”
“Okay doctor” hidaya ta amsashi, godiya sukayi mashi kafin ya fuce.
Yana futa majid ya kalli sabeeha yace “please keep an eye on him”
“Okay sir” ta amsa shi
shima fucewa yayi don ranshi a bace yake da hidaya ko kallonta baya son yi, sai a lokacin hidaya ta kalli sabeeha dake tsaye da bowl a hannu.
Hanyar futa daga bedroom din ta nufa said atazo daidai bakin kofar tace “futo”
Bin bayanta sabeeha tayi lokacin harta zauna akan kujera ta daura kafa daya kan daya, sabeeha na karasowa ta dan tsaya nesa da ita kafin ta duqa, kallon ta da kyau hidaya tayi tana wani tunani mai zurfi, at this point babu abunda ke ranta sai abunda tasa kanta, ko hango risk din batayi, bayan wannan ma bata da wani option daya wuce wannan din.
nuni tayi da fuskar sabeeha tace “Remove that thing”
Sai a daidai lokacin sabeeha ta dago da idanunta don ganin abunda take so ta cire, nan take ta soma rarraba idanu, tsoro da fargaba babu wanda bai dirar mata ba, “i said remove that thing”
A tsorace sabeeha ta soma daga hannunta zuwa ga fuskanta, wani irij fargaba takeji da abunda zai biyo ba, idanunta harya soma kawo ruwa, hannunta kuwa har karkarwa yake.
Hidaya dai kafa mata idanu tayi tana kallonta harta soma zame mask din dake fuskanta,Kasa dauke idanunta tayi daga kanta na yan seconds, gaba daya na kasa gane reaction din hidaya don kafa mata idanu tayi kawai kamar mai nazarin wani
abu,kafin tayi mata wani disgusting look “kamar yanda doctor yayi suggesting zaki iya zama tare dashi, karki sake ki barshi shi kadai, keep an eye on him”
“Okay madam” sabeeha ta amsata.
Hidaya na fucewa sabeeha ta miqe jiki a mace ta koma bedroom din bayan ta maida mask din fuskanta, lokacin data shiga ya soma bude idanunshi da sukayi mashi nauyi, sabeeha bata lura dashi ba saida taji ya kira ta, cikin hanzari kuwa ta karasa inda yake, “friend friend ka tashi? Ya jikinka? Are you okay now? Meke damunka yanxu? I was so worried about you”
Murmushin nan dai da baya dainawa yayi mata, kokarin tashi ya sake yi ta taimaka mashi ya zauna da kyau, bakinshi ya bushe yayi jaa sosai har wata yar rama yayi, “friend” ya furta ahakali
“Yes me kake so friend?” Ta amsa shi
“Ina first love