Showing 99001 words to 102000 words out of 135321 words

Chapter 34 - Matar Taj Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

536

soma bayani. ‘’he was poisened with animal sedation, wanda ake bama dabbobi, it takes an hour yake circulating jikin mutun inda yake kashe duk wani organ dake supporting gangar jiki, yakai 55mins a jikinshi, inda yakai cikon hour guda ba tare da taimakon gaggawa da muka bashi ba zai iya rasa ranshi babu makawa, but thankfully yanxu munyi treating poising din yabar jikinshi, idan ya farfado zai amayar dashi duka’’

tunda doctor ya soma magana khaal ya runtse idanunshi yana sauraron sa har saida ya tsaya kafin ya dago ya dubesu gaba dayansu,  ‘’who did this?’’ ya daka masu tsawa, gaba daya shuru sukayi daman yasan hakan ce zata kasance saidai this time around sun kaishi bango sosai bazai taba yin shuru ba, babu sautin dake tashi saina kukan sabeeha, bude baki afiya tayi tana shirin nuna sabeeha daidai nan hidaya ta dago kanta daman tasan hakan zata kasance, cikin hanzari fadwa ta take kafar afiya wannan yasa tayi shuru, ajiyar zuciya hidaya ta sauke badan fadwa da tuni shikenan, 

‘’jamid..inason kayi informing hukuma yanxu, a rufe ko’ina na gidan nan babu shige babu fice har sai taj ya farka, kowa na gidan nan needs to be questioned, i mean each and everyone’’

sai a lokacin hidaya ta dago, cikin isa da karfin hali tace ‘’khaal bakada ikon yin haka ba tare da iznina ba a matsayi na…’’

wani irin kallo khaal ya mata wanda ya sata guntse bakinta gam, ‘’anyone against this will be considered suspect, har ke dinma da kike claiming kinfi kowa iko akanshi’’

tsit kuwa tayi da bakinta bata sake cewa komai ba, futa jamid yayi ya saka sceurities din gidan suka rufe ko’ina sannan ya umarci kar a sake abar kowa ya futa daga gidan, head maid dake da sanayyar abunda ke faruwa tuni zancen ya karade cikin maids din gidan, kowa anyi grounding dinshi har sai police sunzo, waenda sukayi preparing breakfast kuwa sunfi kowa shiga tashin hankali sosai.

sun shafe a wa guda akan taj din bai motsa ba, likitocin nata monitoring dinshi, su khaal babu abunda suke fata sai farkawar taj din, sabeeha kuwa tayi kuka harta gode ma allah, babu abunda take aranta sai rokon allah ya sassautawa wannan bawa nashi.

afiya dake tsaye daga baya duk tayi zuru zuru hankalinta ya gama tashi, vibration din dataji a wayanta yasa ta duban wayar, tareeq ne yayi mata message akan ta futa zai biyo bayanta, hakan kuwa tayi don allah allah take ta ganshi, futa tayi ta wuce part dinta bayan yan mintuna qalilan sai gashi ya shugo, hankali a tashe ta tunkaroshi, ‘’tareeq ya zamuyi?, kar asirinmu ya tonu, ukty tasan nina saka mashi poised din’’

‘’look, calm down’’ ya fara tausasa ta

‘’ya za ayi kace nayi calming down?, ta yaya zanyi? i cant take the blame for this, i dont want to be sentence for this, akan makiyina i can’t’’

‘’listen to me’’ ya daka mata tsawa ganin tana neman furgice, ‘’kalleni’’ kallonshi tayi jikinta gaba daya kyarma yakeyi, ‘’you have nothing to do with this, komaizai faru bakisan komai ba okay?’’

jinjina mashi kai tayi tare da gamsuwa, ‘’but tareeq maid dinnan fa?, baka tunanin zata kawo mana matsala?’’

‘’just trust me okay’’ tareeq ya bata amsa

yana kaiwa nan ya fuce daga dakin, yana futa ta zauna bakin gado tana jijiga kafafunta, gaba daya ta gama tsorata da al’amarin.

Bayan awa daya ya soma motsa hannunshi, sabeeha ce ta lura da hakan tayi saurin raising alerm, ‘’hannunshi yana motsawa’’

matsowa doctor yayi ya dubashi, daidai nan ya soma bude idanunshi da sukayi jaa sosai har ciki ciki sukayi, binsu ya somayi da kallo daya bayan daya har idanunshi ay sauka kan hidaya, furuci na farko daya farayi shine kiran sunan ta, ‘’first love’’ 

‘’alhamdullah alhamdullah’’ khal ya furta yana mai godiya ga allah, ‘’taj are you okay?’’

girgiza mashi kai taj yayi, shugowan jamid yasa suka juyo gaba dayansu, karasowa wajen yayi shima yana farin ciki ganin taj din ya farka, hamdala yayi

tare da godiya ga allah, nan khaal yasa jamid ya kira hukuma, kiransu ya farayi ya shaida masu abunda ake ciki kafin ya ajiye wayar, ihun da suka soma jine daga kasa yasa khaal ya umarci jamid kan cewa yaje yaga meke faruwa a kasan, futa yayi hidaya data zama kamar wata yar boyi boyi tabi bayanshi,suna fita khaal ya kalli sabeeha dake rakube a gefe, tausayinta yaji sosai don kamarma tafi kowa shiga damuwa sosai, miqewa yayi yabar dakin don ya bata dama ta gana da taj din, 

a chan kasa kuwa gaba daya maids din gidan ne suka fito suna ihu, karasowa hidaya tayi daidai nan head maid ta matso inda take ta soma mata bayani, ‘’ma’am one of our maids committed suicide’’

zaro idanu hidaya tayi jamid najin haka ya nufi bangaren maid din hidaya na biye dashi hardasu fadwa suna shiga sukayi kitibus da gawar maid din kwance ga farin kumfa daga bakinta na futa, gefenta kuwa takarda ce da rubutu a ciki, hannu jamid yasa ya dauka ya karanta, ‘’karku bata lokacinku wajen yin bunciken wanda yayi poisening sir taj, i did it all by my self’’ abunda ke rubuce kenan.

kallon takardar jamid yayi kafin ya maida dubansa ga hidaya, ya dauka kusan minti biyu yana kallonta tana kallonshi ai kawai yayi murmushin takaici ya fuce daga dakin, ‘’you can never cover this up hidaya’’

da mamaki hidaya ke kallonshi cluelessly, don batama san meke faruwa ba, kanta ya gama kullewa gaba daya, dawowar jamid da doctor ne yasa ta fuce daga dakin.

daidai nan hukumar ta karaso da ambulance, khaal na tsaye a sitting room shima kanshi ya gama kullewa, ya gama tabbatar da komai yanxu bashida wani sauran excuse akan hidaya, fadwa da tareeq harma da afiya duk sunyi tsuru, kowa yana tunani, ya akayi maid din ta mutu.

 investigation hukumar suka farayi har aka futo da gawar maid din, saida suka tabbatar da komai da bunciken da sukayi, wannan dan note din data bari ya basu damar closing case din a wajen don tayi admitting itace tayi poising taj din so babu wani abu da yayi saura don haka suka fuce daga gidan da gawarta.

khaal da jamid suna kallo suka kasa yin komai akai, kwata kwata basu san cewa rashin imanin hidaya hidaya yakai ga haka ba sai yanxu, su sun san cewa rufa rufa akayi akan wannan wanda suke tunanin duk shirin hidaya ne kuma akan idanunsu, saidai basuda kwakwarar hujjar da zasu tuhumeta da hakan, kuma basu da right din accusing dinta saidai khaal yayi alkwarin saiya tona aisirin koma waye yayi hakan, hankalinshi bazai taba kwanciya ba mastermind behind all of this yana cikinsu, sanan rayuwar taj da suka maida ta kamar wasan kwallo bazai yi sanya ba yanda yayi abaya, wannan ne babban mistake din da yayi wanda baya fatan maimaici.

daga yanda khaal da jamid ke kallon hidaya ya tabbatar mata da suna zarginta akan wannan, batayi yunkurin yin komai ba don itama kanta tana cikin zulumi wannan yasa ta wuce dakinta.

afiya da fadwa ma kowacce part dinta ta wuce, ya rage daga jamid sai khal su kuma suka wuce saman, suna karasawa suka tadda sabeeha a gefen taj, tana goge mashi fuskanshi saboda aman daya dunga yi sosai.

khaal ya dade sosai wajen taj din kafin ya umarci sabeeha data dawo nan part din gaba daya ta kula da mijinta, abuncinsa cin sa da shansa gaba daya ya dora yardarsa a wajenta, sannan daga karshe ya roketa data kula da taj din sosai, nan ta mashi alkawarin zata kula shi kafin ya masu sallama jamid ya rakoshi waje.

tattaunawa khaal ya soma yi da jamid, inda jamid yayi suggesting ko su dauke taj din daga gidan don yana tsoron kar su sake yunkurin cutar da taj din nan khaal ya shaida mashi cewa ya bar komai a hannunshi, sannan ya tabbatar ayanxu bazasuyi yunkurin yin komai ba saboda hukuma ta shiga wannan zai basu damar aiwatar da plans dinsu don cin galaba akan hidayar, don khaal ya gano duk ta kwashe duk properties din dake cikin sunan taj da inheritance dinshi, ba tare da sanin kowa ba,hatta gidan da suke ciki ma yana karakshin sunan ta ayanxu wanda ada sunan taj ne, bayan wannan ma shares din taj din na  company yana wajenta, yanxu idan suka dauke taj din taci galaba akansu wanda khaal yayi alkawarin bazai bar hakan ta kasance ba saboda amanar da mahaifinsu yabar mashi,koda kuwa taj din baya cikin hayyacinsa bazai taba bari a ha’ince shi ba.

Yau gidan gaba daya a burkice da tarin kidima akayishi, afiya tayi magana da tareeq ya shaida mashi bashida hannu a cikin mutuwar maid din da suka sa ta bama taj poisen,inda suke suspecting kodai hidaya ce ta rufe masu zancen.

bangaren hidaya koda ta tambayi afiya akan batun mutuwar maid din bata boye mata komai ba ta shaidda mata maid din tasa ta zuba ma taj poisen a brekfast din da yayi, da haka dai suka rufe zancen.

bangaren sabeeha a dakin ta kwana tana jinyar taj, haka ya kwana yana amai kamar zai amayar da hanjin sa, kwata kwata bata runtsa ba ko kadan, daya motsa zata kusantoshi don jin ko yana bukatar wani abun ko wani abun na damunshi, haka ta kwana tana kallonshi tare da alkawarin komai zai faru bazata bari a sake cutar dashi ba indai tana nunfashi.

Washe gari da safe saiga khaal ya shugo gidan tare da family lawyers, wannan rana ta kasance rana mafi tashin hankali wajen hidaya, gaba daya properties din da take tunanin sun koma hannunta saitaga akasin haka, don gaba daya asalin takardun authentic papers din suna wajen khaal, na wajen fabricating akayi bana asali bane, wannan abu ya bata mamaki sosai bata taba tsammanin khaal is so powerful ba sai yanxu, abunda ta kasa ganewa shine dama chan mutanenta suna yima khaal aiki ne ko kuwa siyesu yayi?, ko dama chan yasan intentions dinta abunda bata gane ba kenan, khaal kuwa bai nuna mata yasan tana da fabricated papers din property din dake da sunan taj ba, saima shiada masu da yayi ya maida inheritance din taj zuwa ga sabeeha matarshi, wannan rana ta kasan rana mafi furgici a wajen hidaya, ba ita kadai bama harda su afiya gaba daya, suna ji suna gani sabeeha tayi sighning gaba daya property din taj ya koma

hannunta,which means gaba daya responsibilty din taj ya koma kan sabeehar lawfully, itace keda ikon deciding komai akanshi, batun lafiyarshi da arzikinsa da kudadensa duk suna hannunta.

wannan abu ba karamin dadi yayi ma jamid ba, yana kallon downfall din hidaya akan idanunshi, khaal yayi movement dinshi adaidai lokacin daya kamata, lokacin da hidaya ta kasa yunkurin yin komai akan idanunta.

bacin raima yasa tabar parlorn, suma su fadwa suka bi bayanta kowa da abunda ke ranshi, suna barin parlor khaal yayi hamdala yana mai kallon sabeeha, ‘’fatima, ‘’ ya kira sunanta,

‘’naam’’ ta dago tana mai kallonshi cikin ladabi, ‘’this is going to be a big battle, ina mai fatan zaki jajairce, nida jamid zamuyi supporting dinki in every way, na baki duk wani abunda ya shafi taj saboda na yarda dake sosai kuma na baki amanar sa, yanxu ke zaki fadi duk abunda kike so ayi’’

wata nauyayyaiyar ajiyar zuciya sabeeha tayi don kamar ya daura mata dutse a kanta that is so heavy, saidai tayi alkawarin taimaka ma taj din’’

‘’khaal duk abunda kukace shi zanyi, duk abunda kayi deciding shi za ayi’’

ta karashe tana mai dafe kirjinta dake mata nauyi sosai saboda tsoro da fargaba, anya zata iya kuwa?, saurin hana zuciyarta karaya tayi ta nunfasa.

nan khaal ya mata bayanin komai game da taj din da medication team din daya sauya mashi.

AFTER few months…..

Abubuwa da dama sun sauya,ta bangaren khaal komai ya zo mashi da sauki saboda decision din da yayi making wajen maida alamuran taj ga sabeeha, kula dashi da komai yanxu ya koma wajenta, duk abunda ya shafi arzikinsa yana wajenta, sannan yanxu khaal ya sauya mashi masu kula da lalurarshi, experts ya samu ta fannin masu matsalar kwakwalwa amnesia, duk ranar tuesday ake zuwa ayi mashi CTB psychotherapy treatment, ya dan samu improvemnt don therapy din treatment ne sosai inda suke koya mashi abubuwa irin na adult da sauransu, saidai tunaninshi har yanxu na yaran ne, ya dan rage yin wasu abubuwan dai kamar na yara saidai idan ya samu complications,  saidai major problem din which is memories dinshi da bai dawo ba ne har yanxu, tun suna hoping har suka sama sarautar allah idanu don likitan dake ganinshi yanxu ya tabbatar masu saidai a saka idanu kawai har lokacin da tunaninshi da memories dinshi zasu dawo.

Tun bayan abunda ya faru hidaya ta danyi sanyi,saima maida hankali datayi wajen harkar company, afiya kuwa tun bayan abunda ya faru ta shiga furgici sosai wanda hakan yasa tabar kasar ta tafi vacation, fadwa dai na gidan tareeq ma yana nan gidan.

***

‘’bibi….bibi..’’ ya kwalo mata kira, sabeeha dake tsaye a kitchen din part dinsu tana dafa masu abunci tayi saurin kashe gas din ta juyo, zuba ma fuskanta idanu nayi, wato talauci da wahala babu abunda baya saka ma mutun, har kamanni yake sauya wa mutun gaba daya, saida na kalli hazel idanunnata na tabbatar da sabeeha ce, kamanninta sun sauya sosai, fara ce tass, fuskanta ko pimple daya babu kamar na jariri, har wani glowing takeyi, tana da cikar gashin gira da idanu, ga hanci kamar irin na celebrities da suke bada kudi ayi masu surgery,

ta nufi hanyar futa daga kitchen din, tayi qiba tayi kyau sosai abunta, skin dinta yayi kyau sosai sai glowing takeyi, duk wannan dafewar datayi ya tafi natural color dinta ya fito, farace tass ashe,alamun hutawa ya gama bayyana a jikinta, sanye take da doguwar riga abaya mai kyan gaske, ta nada mayafin akanta bai zauna sosai akanta ba kwatattun gashinta dake wajen goshinta sun bayyana, gashi sai wani irin kamshi takeyi mai dadi,

hanyar bedroom dinshi ta nufa hankali a tashe ta shugo cikin tana mai dube dubenshi, taj dake tsaye sanye da fararen kaya jumpers sai wani cute bedroom slippers a kafarshi yana tsaye bakin kofar tana shugowa ya rufe kofar da karfi, cikin furgici ta juyo tana juyowa ya rungumeta tsam a jikinshi, saqe tayi ta kasa motsawa yanda kasan gunki, tabarshi yana barci ne fa mintuna kadan da suka wuce ashe harya tashi, kokarin fidda jikinta ta soma yi daga jikinshi yaqi bata dama, saida tayi gyaran murya ta kirashi ‘’didi let go of me’’ tukunna ta samu da ya saketa, cikin kwanakin nan ta kasa gane dalilin da yasa yake yawan rungumeta musamman idan ya tashi daga barci idan bai ganta ba haka zai dunga kwala mata kira, ita kuma bata son abunda zai hada jikinta da nashi kwata kwata,yanxu sunyi sabo sosai, sabon da sukayi harya ninka na da, she has special place a cikin zuciyarshi, saidai bai kai na hidaya ba, babu abunda ya sauya game da yanda yakema hidaya saima abunda ya ninka dukda sai yayi kwana kusan biyar bai sanyata a idanunshi ba, yanxu ya san me ake nufi da kulawa da mutun don shi sabeeha ke mashi koda yaushe, duk wani bukatarshi ta dauke masa, she is very careful da duk abunda ya shafesa.

sakinta yayi yana mai tabe bakinshi so cute, itama kallonshi takeyi tace ‘’yaushe ka tashi?’’ murmushi yayi mata yace ‘’yanxu,! ina kikaje ban ganki ba bibi na’’ ya karashe a shagwabe harda pouting bakinshi waje, dariya tayi take hakoranta da aka saka mata braces suka bayyana, hakoran sun danyi baya kadan saidai da zarar ta bude bakin gaston ke dan fitowa, braces dinne ma suka rufa ma bakin asiri, sai ya zama kamar wani stylish abu a cikin bakinta.

‘’zakaci abunci?’’

‘’yes bibi na’’ ya amsata excitedly

‘’okay tohm muje’’ wucewa tayi yayi saurin kama hannunta suka fuce daga bedroom din zuwa kitchen, nashi ta saka mashi a bowl sannan ta saka nata itama kafin su fito a tare, anan sitting room suka zauna ta kunna masu tv station din dayafi so.

a maimakon yaci nashi saiya ture ya tsoma hannunshi cikin nata, bata hanashi ba saima tsame hannunta datayi daga karshe ganin kamar bazai ishesu ba abinci tana mai kallonshi yanacin abunci,duk sanda ta sanya idanunta akanshi samun kanta takeyi da kasa dauke idanunta akanshi, akullum fatanta allah yasa ya samu sauqi ya dunga abubuwa kamar kowa.

da yamma barad ke shugowa cikin part din nasu, daman yana dawowa daga school yake zuwa nan part din nasu, wani sa’in idan yazo wasa sukeyi ko suyi creative abubuwan da therapist din ya umarci adunga nuna ma taj din  ko kuma sabeeha ta koya masu addu’oi da karatun addini, cikin abunda ta dan iya itama.

ba karamin sabo tayi da barad ba shima harda jamid, suna sonta sosai, khaal ma kusan koda yaushe yana zuwa gidan don ganinsu.

zama da ita yasa taj ya koyi abubuwa da yawa sosai, ya koyi yanda akeyin sallah da ibada, yawanci ma tare sukeyi dashi da ita, wannan abu ba karamin dadi yayi ma jamid ba.

abu daya dake damunta ayanxu shine yanda tareeq keyi mata wasu abubuwa data kasa gane ko menene, duk sanda suka hada hanya a kasa daya ganta sai ya dunga mata wani irin kallo wanda ta kasa tantance ma’anarsa, akwai ranarda ta sauka kasa daidai nan tayi kicibus dashi ya nufo hanyar dining, kamar da gaske ya karaso inda take suka gaisa tayi wucewarta don daukan abunda tazo dauka, ashe yana biye da ita a corridor, juyawan da zatayi kuwa suka kusa yin karo tayi baya hartana tuntube don ta tsorata sosai ya tarota, yanda ya riko qugunta abun ya tsaya mata arai sosai, tama rasa yanda zata fassara abun,don kamar da gangan ya riko kugun nata, cikin hanzari ta hankadashi tare da barin wajen.

bayan wannan ma akwai lokacin data sauko da laundry din taj tuunda washing machine dinshi ya samu matsala ita ke wanke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login