Showing 96001 words to 99000 words out of 135321 words
duvet din ta fuce daga dakin badan taso ba sai don tsoron kar hidaya ta shugo ta taddata a cikin daki wannan yasa dan dole ta futa daga part din ta sauko kasan a hankali.
daidai wajen parts din dake jere a wajen ta soma jin karar kofa, dan rakubewa tayi daga wajen sakon stairs ta boye gudun kar a ganta, daidai nan tareeq ya fito daga part din afiya, ya dauka kusan mintuna biyu kafin yabar wajen yana mai duben duben, saida ya tabbatar babu kowa a wajen ya wuce bangaren shi da fadwa, saida ta tabbatar ya shige ta futo daga wajen tana mai bin inda ya fito da kallo, bata kawo komai aranta ba don bata son shiga abunda ya shafesu don haka ta shige part dinta da gaggawa.
tana shiga ta wuce bathroom ta dauro alwala ta fito ta hau kan carpet ta zura hijab dinta ta tada kabbarar sallah, ta dade sosai kanta a kasa tana rokon allah kafin ta sallame, tana idarwa barci ya kwasheta anan kasan tana azkar.
Yana shiga part dinsu yayi kicibus da fadwa tsaye da kayan barci, kallo daya tayi mashi ta dauke kanta,saurin tattara courage dinshi yayi tare da cire duk wani suspicious expression yayi murmushi ya karaso inda take zaune, ‘’morning habibity’’
kallonshi tayi daga sama har kasa,ganin yanda take kallonshi ya sashi cewa ‘’yaushe kika tashi? do you need anything?’’kauda kanta tayi daga kanshi fuskanta a hade ‘’ina kaje’’
‘’naje daukan ruwa ne’’
‘’babu ruwa ne anan part din saika futa?’’ ta bashi amsa kai tsaye, hade rai yayi yace ‘’kina tunanin zan futa wani abunne daban?’’
maido da dubanta tayi gareshi tace ‘’ka fita yin wani abunne daban?’’ ta karashe tana mai kallon fuskanshi trying to see his reaction, shima kallonta yakeyi chan kuma saiyaga tayi murmushi ‘’why the long face kamar wani mara gaskia, i’m just trying to pull your legs’’
dariyar shima yayi kafin ya miqe ya wuce bathroom ya dauro alwala ya fito, tana nan daga zaune harya idar da sallah ya hauro gadon suka kwanta.
Matar Taj (destined with you
🩵🤍
)
Written by
Queenmarh
✍️
Free page
Chapter 48
‘’’’
karfe tara daidai ya bude idanunshi da sukayi mashi nauyi, ba tareda tunanin komai ba ya tashi zaune yana mutsika idanunshi ya wuce bathroom, wanka ya farayi da ruwa mai dumi kafin ya futo ya wuce closet ya saka kayanshi, daidai nan hidaya ta shigo bedroom din, bin dakin ta soma yi da kallo ganin baya kan gadonshi, daidai nan ya fito daga closet room din, ganin hidaya ya sashi karasowa cikin hanzari ya rungumeta kamar wani dan baby, ‘’good morning first love’’
‘’morning big baby,’’
‘’first love bakizo jiya ba, i was sick’’
kama fuskanshi tayi cikin lallami tace ‘’sorry baby, i was busy, akwai wanda ya shugo dakinka jiya?’’
shuru yayi yana nazari, kafin yayi saurin girgiza mata kai, ‘’okay good, yauma basai ka saukoba, ga abuncin ka na kawo maka da medication dinka idan kanasha you will be strong okay?’’
‘okay first love’’ ya amsa ta, miqa mashi maganin tayi ya karba, maganin yana da daci sosai haka nan yake sha dan dole saboda first love ta fada mashi zai zama very strong.
saida ta tabbatar yasha kuma yaci abunci kafin tabar dakin.
wunin yauma haka yayi shi a daki bai fito ba, sabeeha kuwa bata samu damar zuwa ganinshi ba saboda yau su fadwa a saman suma suka wuni, saida daddare wajen karfe sha daya ta samu ta shiga bedroom din ta taddashi yana barci, saida ta tabbatar lafiyarshi kalau kafin ta fito ta sauko kasan zuwa bedroom dinta.
wajen karfe hudu da rabi ta farka da kishiruwa, fitowa tayi daga bedroom din zuwa kitchen, ko’ina duhu babu haske sosai sai na inner lights da ake bari randomly, hanyar kitchen din ta nufa, sama sama ta soma jin muryoyin mutane daga wajen corridor din bangaren maids, tsoron kar a ganta yasa ta wuce kitchen ta dauka ruwan ta fito, tana fitowa ta soma jin sheshekar kuka, sai kuma maganganun da bata jiyowa, gabanta na faduwa haka ta nufi wajen a tsorace ta don babu wani haske sosai, mutane biyu ta hango bata ganinsu da kyau kwata kwata saidai inuwarsu dake reflecting, on a blink of eye kuma ta nemesu ta rasa.
tsoron dataji yasa ta juya tabar wajen cikin sassarfa zuwa bedroom dinta ta rufo kofar gabanta na faduwa.
Afiya na ganin shigewarta daki ta fito daga wajen data labe, tareeq ma fitiwa yayi daga wajen yana mai kallon afiya yace ‘’sai mu jira zuwa gobe ko’’
jinjina kai afiya tayi tare da matsowa kusa dashi ta soma shafa hannunshi zuwa ga wuyanshi, ‘’you’re genius tareeq, thanks for this’’ tana kaiwa nan ta stoma bakinta cikin nashi, sunkai wajen minti biyar suna kissing juna kafin ta sakeshi, ‘’anything for my lady’’ ta karashe yana kanne mata idanu, hanyar dakinta ta nufa
yana mai bin bayanta da kallo, she’s arousing him so much da baya iya resisting dinta musamman idan tana cikin kayan barci.
dakinsu shima ya wuce inda ya tadda fadwa nata sharara barcinta hankali kwance.
kallonta kawai yayi tare da girgiza kai, kwata kwata batada clue akan tsiyar da yakeyi gaba daya, she’s too easy.
Washe gari da safe duk suka hallara for breakfast, gaba dayansu, banda sabeeha da jamid da barad da aka kaishi school very early, jamid yayi tafiya cikin kwana biyun, sabeeha kuma na daki, tunda ta lura jamid baya nan tabar futowa,daga hidaya sai fadwa da afiya sai kuma tareeq daketa faman teasing taj da sunan zolaya, shi tareeq baya aiki kwata kwata, yaci burin yayi aiki a taheel group amma hidaya taqi employing dinshi, babu yanda baiyiba akan fadwa tayi convincing hidayar akan ta bashi aiki taqi, bangaren hidaya daman tun farko bata sonshi kuma bata yarda dashi ba, kuma she believe he’s not good for her sister saboda bashida background mai kyau da asali, shiba dan kowa bane iyayenshi sun rasu orphan ne a street fadwa ta kwasoshi inda ya nuna yana sonta itama tana sonshi ta aureshi don bai nuna mata yana son kudinta ba shi ita yake sa (fuska biyu) sannan akwai side hustle din da yake da babu wanda ya sani a gidan ga neman mata kamar kare, hidaya na sane dashi saidai bata da time dinshi yanxu sabida fadwa, amma koba yanxu ba tayi alkawarin saita raba kanwarta da wannan useless womanizer din.
‘’uncle tareeq yau zamuyi football tare ko’’
‘’yes of course taj, kayi breakfast sai muje garden muyi’’
maid din dake serving dinsu ce ta matso ta soma serving dinshi sanin abunda yakeci kullum, tana gamawa ta koma baya, anatse duk suka soma cin abuncin babu abunda ke tashi sai karar cokula sai surutan taj, hidaya ce ta fara miqewa ta fuce daga wajen taj nayi mata bye ta nufi sama don karasa shiryawa.
anan dining kuwa taj ne ya fara gama karyawa, duban agogon hidaya yayi dake kan dining din, cikin sauri ya dauka agogon ‘’laa first love ta manta bari na kai mata’’
ya fada yana miqewa, ya fuce daga wajen, yana futa ya nufi hanyar stairs daidai nan hidaya ta sauko kasan cikin shiri hannunta rike da handbag dinta, sauke mata kaya’taccen murmushinsa yayi yace ’first love kin manta watch dinki’’
kallon agogon tayi kafin ta miqa mashi hannu don ya bata, noqewa yayi yace ‘’no first love ni zan saka maki’’
‘’karka bata min lokaci, hand it over’’
sake noqewa yayi a shagwabe yace ‘’no first love nidai saina saka maki’’
squesszing fuskanta tayi ta miqa mashi hannunta, wanna yarinyatar ba karamin bata mata rai yake ba, don dole take binshi a haka saboda ta samu abunda take nema, sa mata ya farayi yana jin dadi, yana gab da danna maballin hannunshi ya
soma karkarwa take agogon ya fadi kasa ya fashe tass, rai a bace hidaya ta dago da balbalin masifa, kallonshi tayi ta sake kallonshi ganin kunfa na fitowa daga bakinshi, take kuma ya zube a kasa wanwas yana wulla kafafunshi a kasa, kallonshi ta dunga yi yana burgima a kasa, ‘’whats the meaning of this big baby, pick that thing up’’
bawan allah baima san tana yi ba, he is struggling with his breath, wannan kumfar ce ta sake yin ambaliya sai tari ya biyo baya da aman jini daga hanci da fuska, ‘’BIG BABY’’
‘’TAJ’’ ‘’TAAAJ’’
ta doka mashi kira tana mai sauke jakar hannunta ta tsugunna gabanshi ta soma taba fuskanshi, ‘’hey!! whats going on’’ daidai nan su fadwa suka karaso, tsugunnawa tareeq yayi da niyar tabashi hidaya ta mashi wani irin kallo da yasashi dakatawa, ‘’’ukty meya sameshi?’’
rai abace ta doka masu tsawa ‘’how d hell do i get to know?, ya kawomin wristwatch kawai ya fadi,’ ta karashe rai a bace, ganin duk sun tsaya qiqam suna kallonshi yasa ta cewa ‘’tsayuwan me kukeyi, call an ambulance’’
gaba dayansu shock yasa su ka kasa motsawa sai tareeq ne ya miqe ya zaro wayarshi ya soma dialing number ambulance, cikin gaggawa afiya ta tsaidashi, ‘’stop!!! we can’t call an ambulance, zai yi causing commotion, kusan lalurar da yake ciki ni ina ganin a kira doctor shi qila matsalar kwakwalwar tashi ce’’
cikin gaggawa hidaya ta bude jakarta ta zaro waya ta soma dialing health team din taj din, hankalinta gaba daya ya gama tashi, tana gama waya dasu bayan ta sanar dasu emergency ne wayar jamid ta shigo, tana dagawa ya soma mata bayanin parents event din daya kamata suje shi da ita na barad,already shi yana chan, baima karasa yi mata bayani ba tace ‘’i can’t attend, there’s an emergency here’’
batama tsaya yi mashi bayani ba ta kashe wayar, ruwa tasa tareeq ya kawo ta yayyafa ma taj din, haka suka zagayeshi gaba dayansu suna kallonshi kowannensu da abunda ke ranshi, yanata faman burgima a kasan,kirkiri sukaqi kaishi asibiti gudun kar duniya suyima abun wata fassara daban kuma hakan zai iya affecting company, tun yana shure shure harya fara kakarewa ya damqe makogaronshi trying to survive.
hankali hidaya ya tashi sosai haka ta dunga kiran health team dinnan suna shaida mata sun kusa karasowa,.
bangaren sabeeha batasan meke faruwa ba tana kunshe a daki, saida yunwa ta nukurkusota ta fito daga part din, daga nesa ta hangosu a tsaye a sitting room, saurin komawa tayi don bata son su ganta daidai nan ta jiyo wayar da hidaya keyi da health team tana masu bayanin halin da yake ciki a lokacin, chak sabeeha ta tsaya jin abunda take cewa, saurin fitowa tayi tana leken su, daga idanunta da zatayi kuwa ta hangoshi a kwance kamar gawa,ga jini na futa daga bakinshi, ga wuyanshi daya shaqe, hankali a tashe ta karaso wajen, ‘’innalillahi wa inna ialaihi rajiun ta so furtawa tare da tsugunnawa, gaba daya binta sukayi da kallo,
hannunta dake karkarwa ta daga da niyar taba taj din hidaya ta daka mata tsawa ‘’karki sake ki tabashi,,’’
jiki na bari sabeeha ta dago ta kalleta, idanunta ya cika da hawaye sunyi jaa sosai, ‘’aman jini yakeyi amai, na shiga uku’’
gaba daya tama fisu firgicewa hannu ta sake miqawa zata taba taj din afiya ta bangajeta ta bige da rail din stairs tuni gefen kanta ya fashe, ‘’munafuka,’’
wani irin dum kanta yayi idanunta nakan taj din tana hawaye, take memories dinta da suke ghana da mamanta ya fado mata, she can feel how he’s struggling with his life a yanxu don irin haka ta taba kasancewa da ita, sai abun ya zame mata kamar reflection din lokacin,
‘’dan allah ku taimakeshi, zai iya mutuwa, yana shaqe wuyanshi, akaishi asibiti’’
daidai nan health team suka karaso, suna shigowa jamid ya shugo shima ya gansu a tsaitsaye ga taj a kwance shure shuren ma ya daina jikinshi ya saki gaba daya, ‘’innalillahi wa innalihi rajiun’’ jamid ya furta, sai yau ya karaso wajen, sai yau ya tabbatar hidaya da yan uwanta azzalumai ne, suna kallon shi babu wanda yayi yukurin taimaka mashi kuma ya tabbatr tun lokacin da yayi waya da hidaya abun ya faru, tun a wajen taron event din jikin ya bashi taj ne bashi da lafiya,kusan minti ashiri zuwa talatin da suka wuce kenan babu wanda yayi tunanin kaishi aisibiti, wani irin ruwa mai dumi ne ya soma ji akan fuskanshi, ‘’move move, sir ka bamu waje muyi aikin mu’’
muryar doctor taj din ta dawo da jamid daga shock din daya shiga, cikin gaggawa suka soma bashi taimakon gaggawa, sun dade sosai akanshi don gano dalilin dayasa yake aman jini, allah ya taimaka ma sunzo don da sun kara koda minti biyar ne da tuni ya mutu.
allura doctor ya mashi don kashe poison din daya gama mamaye jikinshi kafin yasa team dinshi suka daukeshi zuwa bedroom dinshi, haka suka bi bayansu doctor yuu zuwa sama harda sabeeha da jini ke faman saukowa akan fuskanta saboda bugewar datayi tana biye dasu.
toh fah!!!! waye yayi poisoning taj, this is so heartless, allah ka mana tsari da makiyanmu ameen.
Matar Taj (destined with you
🩵🤍
)
Written by
Queenmarh
✍️
Free page
Chapter 49
Update!!
gaba daya haka suka tsaya suka zagayeshi, gaba dayansu jikinsu yayi sanyi musamman jamid da sabeeha wadda ta kasa hana hawayen dake yankowa a fuskanta saukowa, hannunta har karkarwar yakeyi, gaba daya taj din looks pale fuskanshi tayi wani green green kamar wanda baya nunfashi, likitan sai faman duduba pulse dinshi yakeyi don tabbatar da allurar ta fara effect, ga jinin daya danyi loosing sosai wanda poisen dinne ya sa mashi aman jinin, allah yaso ma yana da jini mai karfi badan haka ba da tuni ya mutu saboda poisen din yana da karfi sosai don yanka duk intestines yakeyi, sannan yanakaiwa wani certain minutes zai buga mashi zuciya, kasa kallonshi jamid yayi saboda zuciyarshi karyewa takeyi da zarar ya kalli taj din,ya rasa gane wannan wani irin zalunci ne? babu ta inda bawan allah nan ya tsare masu, yanxu ma da yake cikin larura babu tunani, kwakwalwa ta koma ta yara bashida wani amfani amma bai tsira, futa jamid yayi daga part din ya wuce nashi ya zaro wayar shi immediately ya soma dialing number khaal, hannunshi har karkarwa yakeyi gaba daya bashi da sukuni ko kadan, khaal na daga wayan ko gaisawa bai tsaya sunyi ba ya mashi bayanin yanda ya shigo ya tadda taj din, hidaya na ganin futar jamid ta miqe itama tana mai kallon fadwa da afiya, ko batace komai ba sun gane me take nufi don haka suka bi bayanta, saida sukazo daidai wajen corridor ta tsaya tana mai kallonsu ranta a mugun bace.
‘’waye yayi wannan a cikin ku’’
tunda ta fara magana take kallon afiya don tasan itace mai karamar kwakwalwar da zatayi wannan abun ba tare da tunani ba, kamar yanda tayi hasashe kuwa afiyar ce ta soma magana ‘’abunda kika kasa yi ne nayi ukty, im sick and tired of all this games, i thought this is what we all want, meysa zaki ceceshi?, yana mutuwa komai zai koma into places’’
wani irin miyau hidaya ta hadiye, tare da runtse jajayen idanunta ta bude shi tar akan afiya, ‘’ban taba tunanin bakida hankali da lissafi ba sai yanxu, idan kasheshi abu ne mai sauqi kamar haka aida tuni nayi na gama, shin kinsan shirmen da kikayi kuwa?, you poisend him? kina tunani khaal da jamid zasuyi shuru akan wannan?, ko kin manta munada hukuma?, it doesnt matter how related you are to him, babu abunda zaisa ba’za a kasheki ba yanda kikaso kasheshi, kudin da kike taqama dashi bazai iya fiddaki ba wallahi ban taba tunanin bakida hankali ba sai yanxu, tracking wanda yayi poisening dinshi shine abu mafi sauqi’’
lokaci guda hankalin afiya ya tashi, duba ga abunda hidaya ta fada kuma haka ne, yanxu idan aka gano… katse mata tunani hidaya tayi ‘’keda waye kukayi hakan?,’’ zaro idanu afiya tayi, daidai nan tareeq ya fito daga bedroom din taj din suka hada idanu, saurin girgiza mata kai yayi, hidaya na ganinshi ta basar don batason kowa yaji zancen, ‘’doctor ya buqaci ganinku’’
yana kaiwa nan ya koma bedroom din, yana komawa hidaya ta kalli afiya, ‘’we are not done yet, don’t you dare do anything stupid from now on har sai na baki umarni,’’
ciki suka koma, jamid shima ya shugo cikin bedroom din, yana karasowa doctor ya soma masu bayani, dakatar dashi jamid yayi akan cewa ya bari khaal ya karaso sai ya masu bayanin gaba daya, ganin haka yasa hidaya ta zauna gefen gadon taj din ta kama hannunshi harda hawayenta, ‘’wallahi who ever did this to you bazan taba yafe mashi ba, i’m so sorry for not protecting you my boy’’
idanun jamid yayi jaa sosai, baya jin yanxu zai iya sassautawa hidaya ko kadan koda khaal ya tsaidashi wannan karan baya jin zai iya saurarawa yana kallon abubuwan da suke faruwa, sai yaushe ne zasu dakatar da ita da kudirinta?, sai sun kashe taj din kokuwa? abunda bazai taba bari ya faru ba kenan. ‘’someone did this? ya akayi kikasan hakan?, ‘’
zuru hidaya tayi jin abunda jamid din ya fada wanda ya sata shiga tashin hankali lokaci guda,daidai nan khaal ya shugo cikin dakin hankali a tashe, gaba daya juyowa sukayi suna kallonshi, fadin irin bacin rai da tashin hankalin dake kan fuskanshi ma bata lokaci ne, don zasu iya cewa basu taba ganinshi haka ba, karasowa yayi hidaya ta miqe tsaye ya bita da kallo wanda zance na tsana ne kafin ya kauda kanshi ya maidashi kan taj din dake kwance kamar gawa, ‘’innalillahi wa inna ialaihi rajiun’’ ya soma furtawa a hankali, yana mai shafa fuskar taj din, wani irin nauyi zuciyarshi ta mashi ya kasa cewa komai sai kallon taj din yake, ‘’what happen to him’’ shine furucin da khaal ya fara yi,kallon juna afiya da tareeq sukayi, kai kana ganinsu kasan sun shiga sabon tashin hankali, fadwa na kallonsu saidai batace komai ba,matsowa doctor yayi gaban khaal din ya