Showing 87001 words to 90000 words out of 135321 words
mutane zai zama scandal kuma zai kawo downfall din TG group daga baya kuma mai ya faru? abunda kayi ma ya zame masu cigaba a maimakon ya kashe masu kasuwa, tell me amfanin me kayi min?’’ ya daka mashi tsawa, take reporter din ya saki futsari, yana roko da magiya,
‘’sir wallahi nayi duk kokarin da zanyi wajen ganin nayi attacking dinsu da waennan questions din saidai saidai…’’
baima jira yaji wani ba asi ba ya harbeshi pauu shima babu imani, haka ya harbi kanshi da idanunshi harda cikinsa yanayi yana dariya gaba daya jini ya gama fallatsa akan fuskanshi da hannayeshi dukda ya saka gloves.
kallon yaronshi yayi yana mai miqa mashi bundigar hannunsa da gloves din ‘’clean this mess up’’
‘’okay sir’’
‘’i need more information akan wannan yarinyar dake gidan da duk wani movement dinta,sannan check those useless dogs dake bamu rahoton gidan, makesure that basu kawo mana wata matsala ba, any small mistake daya sake afkuwa you will be responsible for it’’
yana kaiwa nan ya futo daga warehouse din zuwa wajen motarshi, zame wannan shades din nashi yayi take fuskanshi ta bayyana ‘’Abdul basit kenan, shugaban kamfani Bulgari kuma babban dan adawar kamfanin TG groups’’
toh!! fa!! wace yarinya ake magana akai? badai sabeeha ba? daman waennan ne suka turo ta? indai haka ne to tabbas rayuwarta na cikin hadari, ku biyo ni don sanin amsar curiosity dinku da tambayoyinku acikin littafin matar taj…
Nagode.
Taheel’s resident..
Bayan tafiyar khaal jamid ya zabarma sabeeha daki daga cikin guest rooms din dake kasa,sannan ya umarci head rubuta mashi list din abubuwan da mace zata buqata a cikin bedroom.
bayan tayi mashi list din yayi order wasu daga cikin abubuwan wasu kuma ya futa da kanshi don yaje ya sayo mata su.
kan kace me gaba daya bangaren ma’akata ya kachame da surutai, kowa na tofa albarkacin bakinsa don zanje yaje kunnensu saidai head ta umarci duk wanda ya
futar da zancen sai an hukuntashi hukunshi mai tsauri sosai,wanda jamid ne ya umarci hakan bisa ga umarnin khaal.
sabeeha kuwa bayan jamid ya umarceta data koma part dinsu na yan aiki don ta tattara duk wani belongings dinta, jiki a mace ta shugo head maid na biye da ita don ta taimaka mata, har wani girma take bata na musamman abun ya gama daurema sabeeha kai sosai, da taimakon head ta tattara abubuwanta dukda basuda wani yawa ta ajiyesu gefe kafin jamid din ya dawo.
shiko jamid bayan fitarshi baiyi branching ko’ina ba sai wajen sayyyan abubuwa, haka ya dunga jido mata sabulai, mayuka, kayan kamshi harda few kayan sawa da dai sauransu wanda zata buqata immediately duk wani abu dayasan zata buqata saida ya sayo, ya dade sosai kafin ya dawo gida ya bama head ta shishirya komai daman already an kawo waennda yayi order har an gyagyara mata.
shugowa part dinsu na yan aiki head tayi donta shaida mata an gama shishirya guest part din.
‘’hello ma’am, the room is ready’’ head ta fada cikin ladabi yanda take ma sauran yan gida,
kasa kallonta sabeeha tayi don saita ji wani irin da yanda head din ke bata respect, miqewa tayi head tayi saurin karbar jakar kayanta ‘’let em help you ma’am’’ ta karashe tana mai karban jakar sabeeha, gaba maid tayi sabeeha na biye da ita a baya har suka karasa part din daidai nan fadwa ta sauko kasa tana mai kallon inda head ta nufi sabeeha, har suka shige cikin part, wani irin murmushi fadwa tayi tana mai tuna maganganun da sukayi da ita,
“I pity you” ta fada beneth her breath, kafin tabar wajen tana mai nufar part dinta, daman na sabeehan yana daga chan sako sosai don wajen na baqi ne kawai idan anyi baqi.
tunda shugo cikin dakin sabeeha ke faman kalle kallen dakin, dakine mai girman gaske ga katon english bed mai kyau yasha beddings masu laushi, gefen gadon kuma harda bedside lamp mai kyau, samun kanta tayi da bin dakin da kallo har head tayi mata sallama ta fuce bayan ta tambayeta idan tana buqatar wani abu.
har zuwa lokacin mamaki baibar sabeeha ba da abubuwan dake faruwa a cikin rayuwarta, komai is moving so fast, gaba daya it’s so hard for her to accept and go with all of this, sai take ganin abun kamar a mafarki.
hanyar bathroom ta nufa, shima babba ne sosai babu abunda babu a ciki, an jera mata abubuwan wanka harda bathrob, fitowa tayi jiki a mace tana mai kallon wall closet dake facing bathroom din na glass, daga nan tsaye tana hango yan few kayayyakin dake cikin wajen ga gefen dresser an saka turaruka suma basu da wani yawa, danshi danshin data soma ji ne kan fuskanta ta yasa ta sanya hannu a wajen, hawaye ne ya soma sauko mata tama rasa dalilin hawayen, na farin ciki ne ko na bakin ciki ko na tsoro da fargaba.
yau itace a cikin daki na alfarma harda gado da katifa ga kayan sawa na mutane, abunda bata taba samu ba kaff rayuwarta kuma tana tsaye a matsayin matar
wani, wanin ma mai arziki da girma da zati dukda yana da matsalar kai, wanda ko a mafarki bata taba tunanin zata iya hada hanya dashi ba,ita da ba kowan kowa ba, kaskantacciya kamarta? mara gata kamarta?, ga kuma sarqaqiya dake cikin rayuwarta sai takejin abun kamar a mafarki ga wata masifa dake tukarota wadda takeji a jikinta koda ba’a fada mata ba she can sense it,
‘’ya Allah kaine gatana, kaine jigona, ya allah ya karfafamin, ka dafamin, ka bani ikon taimaka wa wannan bawa naka, karka bari na karaya ya Allah,’’ ta karashe tana mai kuka mai tsuma zuciya mai ban tausayi, hawayenta masu dumi na saukowa kan tafin hannunta.
Allah sarki sabeeha!!
Akwai aiki jaa agabanki
😭
Matar Taj (destined with you
🩵🤍
)
Written by
Queenmarh
✍️
Free page
Chapter 45-46
Update!!!
washe gari da safe tayi wankanta tun karfe biyar ta tashi don ta saba already, sallah ta farayi tana idarwa ta shiga wanka, tana gama wankan ta fito da hijab dinta ajikinta.
gaban closet ta tsaya tana mai kallon kayan dake wajen, wata doguwar riga ta zaro mai mayafi blue ta ajiye a gefe kafin ta dan shafa mai datagani a wajen tana gamawa ta zura rigar, ciff kuwa kayan yayi mata masha allah ita kanta saida ta kalli kanta ta sake kallon kanta, gashinta dake daure da wani kyalle ta warware, take jelar da tayi kitso daya ya sauko har gadon bayanta, gashin ya dankare yayi due sosai saboda rashin mai da kulawa ta musamman, saurin maida kyallen tayi ta nade gashin kafin ta nado mayafin rigar akanta sannan ta zagayo dashi wajen bakinta ta rufe.
knocking da akayi ne yasa ta maida dubanta ga kofar, head ce ta shugo tare da gaisheta respectfully, ‘’good morning ma’am, sir jamid yace ki fito zakuyi breakfast’’
shuru sabeeha tayi tana nazari ga fargaba, hakanan badan taso ba tabi bayan headmaid suka fito tare tana daga bayanta har suka karso dining din, kasa dagowa tayi ta kalli mutanen dake dining kanta na kasa, su kuwa juyowa sukayi suka zuba mata idanu banda hidaya data sdauke kanta daga ganin sabeehar.
gaba daya a tsorace take tama rasa me zatayi, sai kawai ta nemi dukawa don gaishesu jamid ya tsaidata,
‘’good morning sister inlaw’’
jamid ya gaisheta, wata iriyar kunya ce ta lulubeta sai taji wani irin, cikin sauri ta karasa dukawa kasan ‘’no please ….get up, come and have a sit, bismillah’’ ya mata nuni da kujerar dake gefe wajen da taj ke yawan zama.
jikinta kamar babu laka haka ta zagayo wajen kamar munafuka ta nemi zama a kujerar, sai a lokacin hidaya tayi magana, ‘’stop…’’ ta dakatar da sabeeha,
tsayawa chak sabeeha tayi ba tare data kalleta ba kanta a kasa, ‘’joining us here doesnt mean nayi accepting dinki, and you have no right to sit and have breakfast before your husband, go and call him’’
saurin kallon hidaya afiya da fadwa sukayi jin abunda ta fada har afiya zatayi magana fadwa ta zungureta da kafa tayi shuru.
jiki a mace ta juya ta futa daga dining area din, saitaji wani irin aranta, maima take tunani ne da har zata zauna kusa dasu, sunfi karfinta ita ba kowan kowa ba, tana wannan tunanin ta karaso saman ta bude kofar shiga, tana shiga ta nufi bedroom dinshi ta sanya hannu domin bude, bamm taji kofar a rufe a, da mamaki ta sake danna kofar shuru a rufe, kocking ta soma yi har wajen sau biyar shuru ba a bude ba, muryanta yayi sanyi ta soma magana ‘’friend, are you okay? open the door bibi ce’’
bangaren taj yana zaune tsakiyar gado yayi wanka ya shirya hidaya ta kawo mashi breakfast yaci ya koshi abunshi, yana jin sabeeha na knocking amma ko gizau baiyi ba, karshe ma dai puzzle dinshi ya cigaba da wasa dashi.
30mins later shuru, babu irin knocking din da sabeeha batayi ba yaqi budewa harta soma tunanin kodai wani abun ne ya sameshi, tunanin sauka ta soma yi saidai tsoron abunda hidaya zatace yasa ta kasa samun kuzarin sauka din, haka ta hakura ta zauna bakin kofar abun tausayi.
shuru shuru babu sabeeha babu taj wannan yasa jamid haurowa saman, yana shugowa part din kuwa ya ganta a zaune a bakin kofa, da mamaki ya soma tambayr lafiya take zaune, ‘’sir na knocking ba a budeba, ban sani ba ko wani abu ne ya sameshi’’
‘’meysa baki sauko kin fada min ba’’ jamid ya tambayeta yana kama handle din kofar
‘’taj, are you there? are you okay’’
ya sake tambayarshi shuru babu response, tuni hankali jamid ya tashi ya sake knocking, ‘’Big…’’
bude kofar da akayi ne yasa jamid ya shigewa cikin bedroom din da gaggawa, karasawa inda taj din yake yayi bakin gado ya zauna gefensa inda sabeeha itama ta shugo bedroom din,
‘’hey dear are you okay maysa ka rufe kofa kaki budewa’’
nuni yayi da sabeeha tare da miqewa yana ‘’futa min a daki na, leave my room i hate you’’
da mamaki suke kallonshi ganin yanda ya rufe ido yana nuni da sabeeha ta futar mashi daga daki, ‘’calm down, tell me meysa kake so ta fitar maka daga daki’’
jamid ya tambayeshi, ‘’i hate her uncle, i hate her,itace tasa first love take fushi dani, she’s wicked….fita min a dakina na fita i hate you’’
‘’taj, stop this okay, she’s not wicked, ka manta friend dinka ce fa’’
jamid ya tambayeshi cikin lallami, ‘’no uncle, she’s not my friend anymore, muguwace, fitaaaa’’, ya daka mata tsawa yana mai turata,
‘’TAJ!!’’ jamid ya daka mashi tsawa, tuni ya saki kuka kamar karamin yaro, turo kofar da akayi ne yasa suka juyo don ganin wanda ya shugo, hidaya ce afiya da fdwa na gefenta, yana ganinta kuwa ya tafi wajenta a guje ya rungumeta, itama rungumeshi tayi tsam a jikinta tana mai kallon jamid da sabeeha rai a bace ta soma magana
‘’what’s going on here, me kukayi mashi yake kuka?’’
‘’first love please kice ta fita min a daki na bana son ganinta, i hate her’’
kallon inda sabeeha take hidaya tayi, ‘’bakiji me yace bane?, get out!!’’
jiki na bari sabeeha tabar dakin tana hawaye, gaba daya ta kasa gane meke faruwa, yau taj ke korarta daga dakinshi?, meysa toh? me tayi mashi haka? ko kallonta baya sonyi ma kwata kwata.
rai a bace jamid ya fice shima daga bedroom din yana fita hidaya ta jawo taj din bakin gadonsa ta zaunar dashi, ‘’sorry big baby na, sun bata maka rai ko?, don’t worry bazata kara shugowa bedroom dinka ba, ka tuna abunda na fada maka ko?, karka bari ta sake zuwa inda kake, zata cutar dakai okay? kaga abunda ya faru jiya saboda ita, tana son ta raba mu, and i will not allow that okay?’’
girgiza mata kai yayi ‘’i love you first love’’
‘’and i love you more my big baby, yanxu ka zama big boy and i’m proud of you okay? murmushi afiya da fadwa sukayi tare kai kafin su fice daga dakin,
suna fita afiya tace ‘’wato nayi underestimating ukty da yawa, ya akayi cikin overnight ta sa ya tsani yarinyarnan? how’’
‘’yanxu kin soma gane game din kenan? wannan ake kira da manipulation, kinata mita akan taqi yin komai akan common maid dinnan, yanxu tunda khaal ya shiga lamarin dole saida plan komai zai tafi, nasan ukty gaba da baya, kuma i believe in her shiyasa ban damu da lamarin nan ba, kinsan flies? wannan yarinyar kamar flies haka take a wajen ukty, kawar da ita ba komai bane a wajenta its just like dumping trash in a can’’
fadwa ta karashe tana murmusawa, ‘’hmm ay na shaida hakan’’ afiya ta amsa ta suna dariyar keta.
bangaren sabeeha daga nan saman kasa ta wuce zuwa dakinta, tana shiga ta zauna sai hawaye,watan ta biyu zuwa uku a gidan nan taj bai taba korarta ba ko ya nuna baya son ganinta sai yau, ko ranar data fara haduwa dashi baiyi mata haka ba sai aynxu, maisa? haka ta dunga tambayar kanta abunci da bataci ba kenan sai yamma.
da rana haka ta sake komawa dakin nashi, lokacin kofar na bude don haka tasa kai ta shiga, baya cikin dakin don haka ta dan jinkirta tunaninta ko yana cikin bathroom, shuru shuru bai fito ba haka ta karasa toilet din ta kwankwasa jin shuru yasa ta bude wayam babu kowa haka ta hakura tabar dakin ta fito jiki a mace.
washe gari haka jamid ya sake aikawa a kirata don yin breakfast, saman ta fara hawa dan duba taj din, dakin na bude don haka ta shiga yauma ba kowa cikin dakin don haka ta fito ciki a mace ta sauko kasan ta nufi dining area, yana nan zaune cikin yan uwanshi, yana daga gefen hidaya, dadi ya gama lulubeshi saboda yanda take bashi abunci a baki yana murna,jamid dai mamaki bai sashi ya maida dubanshi garesu ba,,sallamar sabeeha yasa suka dago harda taj din, tuni ya hade rai, gaishesu tayi jameed ne kawai ya amsa ta kafin ya mata nuni da wajen zama, tana nufo wajen taj ya miqe tsaye da cup din hot chocolate hannunshi, tana zuwa daidai wajenshi don inda zata zauna na kusa dashi ya saki cup din akan kafarta, take zafin hot chocolate din ya ratsa ta tuni tayi baya, ‘’oupss sorry’’ taj ya fada yana mai komawa ya zauna, afiya mai zatayi banda dariya don abunma abun dariya don yanda ya dauka cup din da gangan ya zuba mata is so obvious, ‘jameed da bai lura da abunda ya faru ba saida yaji dariyar afiya da yar karar da sabeeha tayi ya dago.,’’subhanalla garin yaya!!’’ ya miqe yana janyo paper towel ya karaso inda sabeeha ke tsugunne tana faman sharce kafarta da hannu har kafar ta danyi jaa don har turiri hot chcolate din yake,tissue din ya miqa mata yana mai yi mata sannu, ‘’sir banji ciwo’’
saida yaga taj yana dariya ya fuskanshi abunda ya faru,
‘’Taj, kaga abunda kayi kuwa….?’’
‘’jamid please,’’ hidaya ta katse shi ‘’bai lura da mutun a wajen bane, and besides bakaji abunda tace ba? bataji ciwo ba so please dont be over reactive’’
hidaya ta karashe tana mai wullama sabeeha wani irin kallo mai wuyar fassara.
afusace jamid ya futa daga wajen ya dauko first aid box ya ajiye a gaban sabeeha, saurin miqewa tayi tana murmushi ruwan idanunta na saukowa kasa tayi saurin gogewa muryanta na cracking ta soma magana ‘’sir tsautsayi ne, ni ce tsaya a gabanshi bai lura ba, banji ciwo bama, zan wanke ne kawai’’
ta karashe tana kokarin barin wajen saboda kukan daya ciyota da idanu duk suka bita harda taj dayaji wani iri ganin tana kuka, sai yaji jikinshi yayi sanyi, hidaya na ganin fuskanshi ya sauya ta kamo hannunshi tana mai yi mashi murmushi ta soma magan’a yanda dagashi sai ita ne zasuji ’good job big baby she will learnt her lesson bazata kara zuwa inda take ba okay?’’
girgiza mata kai yayi alamun gamsuwa, kasa cin abuncin yayi saida ta cigaba da bashi a baki, suna gama ci ta wuce office shi bayan ta raka taj dakinsa sannan ta sake shaida mashi karya sake yabar sabeeha ta zo inda yake.
After 1 week
abubuwa da dama sun faru cikin kwanakin nan, yanxu taj baya taba yarda sabeeha tazo inda yake part dinsa ma ta daina zuwa kwata kwata, yana mata kallon wata abar kyama ko fuskanta baya son gani, wannan abu yana damun sabeeha sosai, she missed him so much, tayi missing yanda suke ada da yanda take kula dashi, da wasan da sukeyi, yanxu kuwa ko inuwa daya baya so su hada ko ganinta baya son yi daya ganta sai fara pushing dinta away, gashi ta kasa gane dalilin haka, wannan yasa kullum tana cikin daki bata futowa kwata kwata ganin she’s more confortable a dakin yasa jamid ya saka headmaid tana aika mata da abuncin.
bangaren taj kuwa hidaya ta gama wanke tunanin shi gaba daya, tayi manipulating dinshi akan cewa sabeeha muguwa ce kuma itace take shiga tsakanin ta dashi, kuma cutar dashi take sonyi shiyasa take son kasancewa dashi har take shige mashi, bangaren hidaya tayi hakan ne don the only way da zata raba sabeeha da gidannan shine idan ta chusa ma taj kiyayya yarinyar, don shi kadai ne zai iya korarta, da wannan kadai zata iya amfani don ta rabasu in badan haka ba komai zai iya faruwa,musamman dataga taj din is into yarinyar kuma shakuwa ya shiga tsakaninsu don ranar daya hana a tafi da sabeeha abun ya tsayama hidaya arai harta soma tunanin komai zai iya sauyawa, abunda ta gina shhekara da shekaru bazata taba bari ya ruguje ba dalilin kaskantacciyar maid.
Ta bangaren jamid duk abunda ke faruwa saida ya shiada ma khaal da sauyin da taj yayi a cikin kwana biyun,harda yanda yake treating sabeeha wanda suka gane duk sharrin hidaya