Showing 114001 words to 117000 words out of 135321 words
zakuce game da mutuwar qanin mahaifinku? Shin shine yayi wannan aika aikar, ko kunada sanayya akan kudaden daya sace na kamfanin ku? Me zakuce game da wannan?”
“Madam kuce wani abu akai, rashin magana shi zai sa mutane suyi zargin ko kuna rufe duk wani laifin nashi saboda…”
“How can you say that? What right do you have as a reporter to say that” fadwa ta fada rai a bace, saurin janta tareeq yayi gefe ya fuskance su yace “kuyi mana uzuri, we just lost him, zaku samu amsar tambayoyin ku daga baya”
Yana kaiwa nan suka shige daga ciki gaba dayansu, daidai nan jamid ya futo da matar khaal, gaba dayansu idanunsu yayi jaa sosai,dagowar da jamid zaiyi idanunshi ya shiga na hidaya dake fuskantarshi, likitocin wajen da sukasan ko ita wacece sukayi saurin karasowa inda take suka gaisheta tare da jagorantarta cikin wajen sukabar su jamid a tsaye.
***
An tabbatar da gawar khaal kuma an sallaceshi yanda addini ya halarta sannan aka kaishi ma’kwancinsa, it was very tough days for jamid da iyalan khaal harda sabeeha, musamman ma iyalenshi da zaman kasar ya gagaresu, saboda yanda ake sukarsu da laifin da ake tuhumi khaal din da maganganun da akeyi akanshi kan cewa ya kashe kanshi saboda laifukan da yayi, dan dole matarshi da yayanshi suka bar kasar ta koma kasar haihuwarta.
Suma su hidaya ba a barsu a baya ba don suma danginsa ne,gudun kar abun ya shafi kamfaninsu yasa hidaya tayi press conference (hira da manema labarai) inda ta shaida basuda hannu da laifukan da qanin baban nasu yayi, duk abunda yayi yayishi ne don kanshi.
Wannan abu da tayi ba karamin fusata jamid yayi ba sosai, how could she even gather the courage da zqtayi hakan, ko sati guda ba ayi ba da mutuwar khaal din ko ba komai khaal mahaifine a wajensu, koda kuwa ace yayi abunda ake zarginsa bai kamata ta watsar da adalcin da yayi masu ba, da kulawan da yayi dasu shekaru da suka wuce bayan mutuwar iyayensu bayan wannan ma yanxu yakeji komai doesn’t seat well, a day before ayi kidnapping su sabeeha khaal ya kirashi a waya da daddare inda ya umarci ganinsa da zarar ya kai su sabeeha asibiti washe gari, the next day kuma akayi kidnapping din su sabeeha, cikin abunda bai wuce 24hours ba aka fidda labarin karyayyaki da sharri akan khaal din sannan kuma later on aka kayyadar da mutuwar khaal din,gaba daya komai abun zargi ne wajen jamid, dole akwai sa hannu a ciki, wannan observation din da yayi ya tabbatar mashi akwai wata a kasa, kuma yanajin kamar mutuwarsa is related to abunda yake son fada mashi wannan yasa ya fara bin didigin, cause he never believe khaal zaiyi haka duk yanda akayi sharri akayi mashi.
Washe gari hukuma sukazo gidan don questioning taj da sabeeha, akan binciken kafin suyi closing case din, hidaya da jamid na daga zaune harda jamid din
hukuma suka dunga tambayarta yanda akayi suka shiga motar da abunda ya faru, sabeeha bata boye masu komai ba ta fada masu abunda ya faru da yanda aka kirata a waya har suka shiga motar a tunaninsu uncle ne, daga nan basu sake sanin ina kansu yake ba sai tsintar kansu sukayi cikin desert land.
A karshe dai haka akayi closing case kan cewa khaal dinne keda hannu akan kidnap din saboda kwakwarar hujjar da suke da ita dake pointing dinshi da tuhumar da ake mashi na wannan pictures din da wayar sabeeha da aka tsinta a cikin motarsa, kuma same wayar ne aka gani yana exchange da wannan unknown mutumin mai bakin kaya daya dauke su.
Bayan wannan ma tunda ya mutu babu buqatar cigaba dayin wani buncike, babu yanda jamid baiyi ba akan case amma suka rufeshi don bai yarda da tuhumar da akayi ma khaal dinba da mutuwar tashi ma gaba daya saidai bashida hujjar dazai basu da zaisa subar case din
On the third day of mutuwar khaal Ammu (halima qanwar su khaal)ta shigo kasar, ammu itace qaramar kanwar su khaal, tana aure a kasar ukraine,mutuwar khaal dinma a wajen jamid taji, ba karamin tashin hankali ta shiga ba haka tabar mijinta dakeda special needs don ya manyanta ta taho saudi.
Koda ta iso, gidan yana nan yanda tabarshi shekaru da dama da suka wuce, babu abunda ya sauya, tunawa da yanxu babu wanda ya rage mata sai yayan yan uwan nata yasa kawai saita fashe da kuka sosai, rashin yan uwanta duka biyu ba abu ne mai sauqi a wajenta ba musamman dataji abubuwan da a kace khaal yayi wanda taqi yarda da hakan itama,sannan kwata kwata ammu batasan situation din gidan ba da abubuwan da ke faruwa tsakanin yayan dan uwan nata da khaal din, harma da kiyayyar da sukema taj, abu daya ne ta sani shine auren da khaal yayi ma taj wanda ya shaida mata few months ago.
Koda ta buqaci son ganin sabeeha tayi mamakin ganin matar da aka aura ma taj din don ta dauka balarabiya ce, su daman suna da akidanci wajen aure cikin alada, sai kuma taga akasin haka, bata nuna komai ba dai haka tayi zaman kwana biyar kafin ta koma ukraine.
Cikin kwanaki biyar din datayi tayi observing kowa na gidan, sabeeha da taj dake zaman part dinsu kamar basa existing a gidan, sai kuma su hidaya da fadwa, afiya daman bata taddata a gidan ba koda ta tambayi inda take nan hidaya ta shaida mata ta tafi vacation, wannan abu ya batama ammu rai sosai, batace komai ba dai ta zuba masu idanu, bayan wannan ma taga hirar da hidaya tayi da manema labarai, wanda ya bata mamaki sosai nan ta tabbatar something is going on wanda bata sani ba, haka dai tabar gidan ta koma wajen mijinta da abun a ranta.
Bangaren hidaya she was so pleased da ammu ta tafi already saboda yanda ta dunga questioning dinta musamman akan iyalan khaal data bari har aka kwace gidansa da dukiyarsa wanda hakan yasa dole suka bar kasar a maimakon su zauna anan gidan, wanda batajin zata taba barin hakan ta faru, anything daya shafeshi bata buqatarsa a yanxu musamman data tabbatar zai shafi image din kanfanin ta.
Abunda yafi damun hidaya ayanxu shine yanda jamid yaqi nuna komai game da mutuwar khaal din, tasanshi da rashin yarda kuma tasan ita zai fara zarga akan abubuwan da suka faru musamman akan kidnap din saidai bai cemata komai ba kuma bai tuhumeta ba wanda hakan ya bata mamaki sosai.
Ta wajen jamid bai tunkareta ba saboda yasan koya tuhumeta zata karyata hakan ne, bayan wannan kwakwarar hujja yake nema don ya tabbatar tana da hannu cikin kidnap din.
After 2months….
Abubuwa da dama sun faru cikin watannin nan,komai ya sauya musamman ta wajensu sabeeha, kullum suna kunshe a daki kamar wasu prisoners ita da taj, jamid yana kokari sosai wajen yayi protecting dinsu, kwanciyar hankalisa daya da hidaya ta maida hankalinta wajen aikin company ko ta kansu bata bi kwata kwata.
Abunda yafi damun sabeeha ayanxu shine yanda tareeq ke kokarin ganin ya zubar da mutuncinta, yanxu abun yakaiga har threathening dinta yakeyi, he’s so obsessed with her,tana daga zaune ma haka zai shigo part dinsu kai tsaye yayi ta mata abubuwa, countless of times idan tanason ta fada ma jamid saita kasa saboda threat din da tareeq din yayi mata.
Akwai ranarda tana zaune a sutting room tana karatu a cikin laptop din da khaal ya bata, tabar taj a daki yana barci saiga tareeq ya shugo, da farko tama dauka jamid ne saida ta dago ta ganshi, ba karamin furgitata yayi ba don batayi tsammanin ganinshi ba gashi tana sanye da normal riga, binta ya somayo da kallo kamar zai cinyeta wanda hakan yasa ta miqewa cikin hanzari zatabar wajen yayi saurin shan gabanta, yana mai lashe lebenshi kamar wani maye, saurin yin baya tayi tana mai kallonshi qiyayyarsa na ninkuwa a zuciyarta, baima tsaya wani dogon surutu ba ya nemi lalata da ita, a daidai wannan lokacin ne kuzari da bakin da bata taba sanin tana dashi ba ya fito, gaba daya ta koma jaa tsabar bacin rai, ta daka mashi tsawa gaba daya ta sauya kamar ba sabeeha ba mai sanyi sanyi “wallahil azeem idan ka sake ka taba ni saina lahantaka, kana tunani tsakanina dakai akwai wani banbanci ne? Kaiba kowan kowa bane a gidannan, auroka akayi, wannan abubuwan da kakeyi ya tabbatarmin bada alkairi kake zaune a gidan nan ba,kuma idan ka sake neman shiga harkata saina tona maka asiri fasiqi kawai, la’ananne”
Haka ta zageshi tass idanunta a rufe hannunta har karkarwa yake tsabar masifa, shiko saqe yayi yana kallonta bai taba sanin zatayi baki haka ba, da yanda take magana ma kana gani kasan abunda tace zatayi zata aikata shi, he can’t lie yadan tsorata da kalamanta saidai bazai taba bari ta raina mashi hankali ba ko ya nuna ya tsorata,
Dariya ya soma yi irin ta yan iska yana mai nunata da yatsa, da mamaki take kallon yanda yake kyalkyacewa da dariya dukda gabanta na faduwa haka taqi yarda tsoronta ya fito fili,
“wa zaki fada ma? Wa zai yarda dake? Me zakice? Ina nemanki or what? Babu wanda zai taba yarda da hakan, idan kuma kina tunanin zaki iya go ahead, ki fadama kowa na gidannan and i will make sure that na bataki, just wait and see” yana kaiwa nan ya fuce ranshi a mugun bace.
Yana futa ta sauke wata doguwar ijiyar zuciya, ayau ta tsallake tarkonshi zuwa gobe kuma batasan me zaiyi ba, saidai tana rokon allah ya kubutar da ita daga sharrinsa, abunda ta lura dashi shine sanyin da takeyi shiyasa yake mata abunda yaga dama amma a yanxu data lura ya dan tsorata da kalamanta hakan ya bata damar daura damara duk sanda yayi mata irin haka zata tona shi.
Daki ta koma jiki a mace tana shiga ta tadda taj zaune ya dafe kanshi, karasowa tayi har inda yake ta zauna gefenshi “didi!! Ka tashi?”
Ta kira sunanshi, dagowa yayi ya kalleta fuskanshi gwanin ban tausayi yace “yes bibi kaina yana ciwo sosai”
“Sorry didi bari na kawo maka magani kasha” harta moqe ya kamo hannunta, dan dole ta dawo ta zauna, tana zama ya rungumeta, batayi expecting side hug dinba kuam batayi kokarin nisantar dashi daga jikinta ba, tun bayan batansu ya zama wani iri gaba daya, ya rage magana sosai kamar yasan abunda ke faruwa a cikin rayuwarsa ayanxu tun bayan mutuwar khaal ta fuskanshi hakan a tattare dashi.
Fiddashi tayi daga jikinta tana mai kallonshi, tausayinsa take ji sosai musamman yanxu da babu khaal a cikin rayuwar su, har yau ta kasa daina mamakin rashin khaal din, tayi kuka sosai ganin yanda aka tuhumeshi da batansu, tayi yaqinin bazai taba yin haka ba, kuma sharri ne aka kulla masa, dukda tana shuru shuru kamar batasan abunda yake wakana ba idanunta nakan lamarin gidan, duk sanda ta tuna cewa dagashi sai jamid ne kawai tsayyayu cikin rayuwar taj din kuma suke kokarin protecting dinshi hakan na breaking zuciyarta, tsoronta daya yanxu da babu khaal kar hidaya ta kore ta daga gidan, dukda jamid ya tabbatar mata da hakan bazai yuwu ba tunda already khaal
Ya shigar da ita cikin record din gidan a matsayin matar taj, saboda haka futar da ita daga familyn daidai yake da futar da taj.
Bangaren tareeq yana futa ya kira abokinshi wanda suke harqalla a tare ya umarcesa daya hada masa clip da hotanta a jiki, ya tura masa hotonta daya taba dauka batama san lokaci da yayi ba, abunka da professional ta fannin hacking da fabricating abubuwa, a ranar ya tura masa abunda ya buqata.
Koda clip din ya shugo wayarsa haka ya soma kyakyacewa da dariya yana playing video din, ni kaina nayi mamakin yanda akayi har aka iya hada abu kamar wannan, sabeeha ce a cikin video tana rokonshi akan ya bata hadin kai, abundai yana nuna cewa itace ke nemansa, saida ya gama kallo tass kafin ya ajiye wayar “fada da gagararru ba abun wasa bane, zanyi amfani da wannnan don na samu abunda nakeso akanki”
Ya karashe yana jujuya kanshi, fadwa data shugo part din nasu kallonshi ta dunga yi tana suaradon abubuwan da yake fada, dukda bata dago inda ya rufa ba don bataji farkon zancen nashi ba batayi mamaki ba, juyowar da zaiyi kuwa yana ganinta ya soma washe baki innocently yanda ya saba, “welcome back
wifey”wani irin kallo ta mashi wanda ya kasa karantar irin kallon kafin ta wuce cikin bedroom’ dinsu.
Binta yayi da idanu harta bace ma ganinsa, yana mamakin yanda ta sauya mashi gaba daya, yanda yake gaslighting dinta da son da take mashi ma ada yanxu bata falling victim, daya fara zata katseshi direct ko kuka ta soma dariya kawai.
Miqewa yayi yabi bayanta zuwa bedroom din ya yafdata zaune tana kokarin kwance takalminta, kai tsaye ya soka mata magana “wife nayi maki wani laifi ne? Whats going on,”
Banza tayi dashi kamar batasan yanayi ba tabar wajen, harta bude kofar shiga closet ya rufe kofar yana mai fuskantar ta ranshi a bace dagowa tayi ta kalleshi kamar ba fadwan daya sani ba haka fuskanta a hade ta soma magana, “move out of my way”
“No way, saikin fada min me nayi maki da kike bani silent treatment, this is not how you are, meysa kike min haka kodan kinga inasonki? Kin daina sona ne yanda kike sona a baya? Are you tired of me and my needs? Ko saboda na buqaci akan ki yi pursuing yayarki ta bani share a cikin company ku?ko kina tunanin inada wani motive dinne akanki?”
Haka ya dunga jero mata tambayoyi, koda ace bata zarginsa ayanxu zata fara saboda gaba dayansa bashida gaskia balle kuma ta gama sanin duk abunda yakeyi ba tun yanxu ba,da affairs din da yakeyi a waje da cikin gida da flirting da yakeyi da afiya duk ta sani,card dinta dayake dauka yana tafiya dashi a sunan zaije vacation da friends din shi, da kashema mata kudi da yakeyi duk wani dirty abubuwan da yakeyi ta sani, duk wani movement dinshi akan tafin hannunta yake, tafiyar da yayi ma cikin kwanaki da suka wuce da sunan zaije kallon kwallon manchester tasan ba chan yaje ba, wajen afiya yaje achan london,diamonds dinta daya saidar ba tare da saninta ba duk ta san komai saidai tak bata taba ce mashi ba haka zalika bata taba nuna mashi tasan komai ba.
Baya tayi tana kallonshi yana magana, hannunta nade a kirjinta saida ya gama tass kafin ta tunkaro inda yake ta sanya hannunta na kan fuskanshi idanunta na cikin nashi ta daga mashi gira daya, tana mai yin murmushi tace “duk karen dakaga yana bin mai kiwonsa cikin lallami yana neman makafa ne, learn to watch your mouth while talking to your master who provide for you, this is a word for the wise, be careful with your words okay?” Ta karashe tana mai patting fuskanshi, kasa motsawa tareeq yayi saida ta mashi nuni daya bata hanya, kamar galaho kuwa haka ya matsa mata ta shige, kanshi ya gama daurewa da mamakin kalamanta,haka ya soma questioning kanshi kodai ta kamashi? Kota gano abunda yakeyi ne?
Haka ya dunga tambayar kanshi har yayi concluding indai ta ganeshi bazata barshi yakai har yanxu a gidanba bayan wannan ma yanada confidence kan cewa kota ganoshi bazata iya ravuwa babu shi ba saboda son da take masa.
Hidaya na zaune cikin study room dinta tana duban wani file saiga fadwa ta shugo, cikin hanzari ta maida file din ta rufeshi tana mai fuskantar fadwar data karaso inda take.
Jan kujera fadwa tayi ta zauna “hello ukty”
Jinjina mata kai kawai hidaya tayi tana mai tura file din cikin locker dake gaban table din da taie zaune, binta da kallo fadwa tayi ganin tana neman dagowa yasa ta kauda idanunta daga kan abunda takeyi, “finally ukty, matsalar ki ta kau how do you feel about it”
Gyara zama hidaya tayi tana mai tabe bakinta tace “he made the right decision of ending his life, so pathetic”
Murmushi fadwa tayi tana mai dubanta tace “what’s your next move?” Fadwa ta tambayeta tana mai jefa candies din data dauka kan bowl din dake wajen tace “zaki sani when the time comes” ta amsa ta kai tsaye, shuru fadwa tayi kafin ta miqe tsaye tace “its going to be interesting kenan, ina anticipating for good news ukty,”
Tana kaiwa nan ta juya ta fuce daga study din, murmushi dake fuskanta ne ya dauke tan nazarin abunda hidayar ke boyewa “selfish soul”
Ta fada a bayyane,”let’s see abunda zakiyi next” tana kaiwa nan ta sauka kasan.
Daidai nan tayi kicibus da sabeeha dake haurowa, matsa mata gefe sabeeha tayi bayan ta gaisheta, fuskanta dauke da murmushid a amsata da mamaki kuwa sabeeha ke kallonta jin tana tambayra ya take, tareeq daya futo daga part dinsu ya hangosu daga nesa, hankalinshi ba karamin tashi yayi ba ya nufi inda suke cikin hanzari don duk a tunanin ko sabeeha ta fada ma fadwa ne abunda yayi mata, juyowa sukayi suna kallonshi, “wife let’s go inason magana dake”
Dagowa sabeeha tayi ta kalleshi kawai saitayi murmushi da gefen bakinta, tsaf ta karanci a tsorace yake kuma yana tunanin ko wani abun ta fada mata hakan ya tabbatar mata threat din datayi mashi yayi aiki kenan, wannan kadaice hanyar da zatabi don ta tseratar da kanta daga sharrinshi.
Akan idanunta yaja fadwa suka sauka kasan sai faman haki yake gaba dayanshi bashida gaskia kwata kwata.
Suna shiga part dinsu ta fuzge hannunta tana mai dubanshi da tuhuma, “whats the meaning of this kake jana haka? Maganar me kakeso muyi? Ta tambayeshi, kakarewa yayi yama rasa mai zaice mata sai kawai wata dabara tazo mashi “ina buqatar kudi please,i want to help a friend mamanshi na asibiti za ayi mata operation”
“Okay so? Ka bashi mana cikin naka?”
Da mamaki ya dago yana kallonta bata taba fada mashi haka ba sai yanxu, ganin yana kallonta yasa ta